BABI NA HUDU

438 55 13
                                    

https://chat.whatsapp.com/EYIYhgb3RyPKaig0QHrOxR

*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA HUDU.

Mai_Dambu.

*Wannan shafin sadaukarwan ce ga duk Matan Arewa! Musamman masu faffutikar ganin sun dogara da kan su! Allah ya tsaya muku Fatan Alkhairi domin da bazarku nake rubutun nan Nagode sosai da yadda kuka amshi Labarin gidan Aure Na*

Janye jiki na, ina kallon shi kawai na tsinci kaina da mik'ewa na bar dakin shi. Nayi alƙawarin ba zan kuma mishi magana ba Insha ALLAH duk abinda yake faruwa Allah baya barci baya gyangyandi. Yana ji yana gani babu amfanin kuka dashi.

   Ranar dakyar nayi barci shima sai da na dauro alola tare da gabatar da sallah nafilla, sannan na samu barci. Ina barin d'akin kamar dama akan shi nake ya kira budurwan shi suka shiga hira tare da mata alƙawarin karya.

   Washi gari.
Da wuri na tashi sabida Nuratu da Nimrah suna zuwa hadda, na gama musu abin karyawa suka karya sannan suka tafi makarantar, Amir kuma na gurin Yahanasu, ban yi abin karyawan dayawa ba, iya bakin mu nayi muka ci muka koshi sauran na juye na saka a frig, da ya tashi yaga babu kome ya fito ya wani sum-sum da fuska na cigaban abin da nake. Mik'ewa yayi ya nufi dakin Mahaifiyarshi. Yana zuwa ta tsare shi da kananun magana.
"Bata kawo min abin karyawa ba, ban san meke damun Sameerah ba, wannan ai rashin mutunci ne ka sayo sannan aki bani ina mahaifiyar ka" bai ce mata kome ba, dake bai da gaskiya dan dole haka ya fito ya dawo falon da nake yaga bana falon d'akina ya biyo ni, ina waya da Mommy.

     "Eh na turo kudin ki duba. Idan za a kuma turowa a had'a da jan wake nan yana shiga sai ganda idan da hali da citta. Akwai masu bukatar shi."   Na fada mata ina kallon list din bakin gadon.
"Toh shi kenan" muka yi sallama, ban d'ago kai na kalle shi ba, na cigaba da lissafi na.

"Sameerah! Ina son muyi magana fahimtar juna!" Ya fada tare da niman guri ya zauna.
"Hm!" Nace mishi ina kallon shi.
"Dama akan abinci ne naga baki bamu ba."
"Wanda ka kawo tun wata uku da ya wuce ya kare shi yasa ban yi tunanin maka magana ba"

"Ina jin yunwa yake nan?" Kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Akwai shago a waje ka tura a karbu maka zan girka maka."  Mik'ewa yayi ya fita can sai gashi, haka na dauki abincin na fito waje na fara kiciniyar had'a itacce.
"Zai dauki awa nawa girkin domin naga ai ke ba itacce kika daura ba?" Ya tambaye ni yana kallon agogon hannun shi.
"Maybe nan da sha biyun rana" na bashi amsa a takaice. "Babu gas ne?"
"Babu" ba fada kai tsaye, komawa ciki yayi ya zauna tare da jiran gawon shanu.

   Ban daura mishi a gas ba, a itacce na daura sabida gas na Yarana ne dan haka ban yi tunanin daura ba. Da ciwo ace yaron nan karami Amir yayi jinya Amma Uban shi bai tako ya duba shi ba, ko waya bai yi ba dan yaji ya jikin shi? Dan haka ban yi mamakin haka ba, dan yace min aure zai yi.

         Dakyar na gama abincin na kashe wutar, na shiga kitchen ɗin falona na girkawa Yarana abincin Rana aka kai musu, nida Yahanasu muka ci namu da Amir.
        Na dauke kome amma ba zan yarda na ciyar dashi ba, haka yayi kwanakin shi nan har ya gama da zai tafi ne naga ya fita yayi cefene yazo ya zuba min har da gas da buhun gawayi. Yana zubawa ya shigo dakin yana kallon yadda nake zubawa Amir madaran da na dama mishi da ruwan sanyi domin tunda ya kone nake yawan bashi madara me sanyi idan na samu danye na bashi idan na samu dafaffe na bashi duk wanda na samu ina bashi.
"Sameerah dan nace zan yi aure ne kika sauya?" D'aga Amir nayi tare da mika mishi kofin.
"Jeka wurin Aunty Yahah ta baka ka sha kaji." Kallon shi nayi badan ina son shi ba, babu abin da zai hana ni. Mishi rashin mutunci amma ba zan iya mishi kome ba, haka yayi ta zuba tare da gaya min ya kawo min abincin, dariya ya bani dan haka na mike tare da nufar hanyar waje.

     Har ranar da zai koma sannu bata kuma had'a ni dashi ba, sai dai zamu hadu. Zan yi girki amma bani da lokacin da zan tsaya kamar da, wasa wasa bayan ya koma na zata zai gyara ne tunda ya fahimci naji zafin abinda yayi min sai gashi mun koma gidan jiya, damuwa ta min yawa, ina dai raye ne amma nasan tuni ruhina ya jima da mutuwa tun ba yau ba, iya yanzun ina zaune ne kodan albarkacin Yarana. A hankali na Fahimci mutanen da muke gidan har da anko suka yi na auren, ranar juma'a da safe suka tafi Kaduna kai kayan auren shi da hajjo. Haka na zuba musu ido. Sai dare suka dawo, inda aka yi ta hira da fadar irin kayan da ya zuba mata, murmushi nayi domin babu amfanin na d'aga hankalina.
Habaici da kananun magana ana yin shi a gidan, gulma kuwa duk inda aka zauna sai an kafa shi. Ban tab'a d'ago kai na kalle su ba, shima wanda ya ajiye ni zuba mishi ido nayi. Wani lokacin sai sun ganin zasu fara niman hanyar da zasu gaya min magana, nan ma na zuba musu ido. Sana'ar da nake da aikina, Allah ya saka min albarka a cikin shi kuma ina samu daidai gwargwado.

     Idan naji ana magana akan mace bana saka baki sabida yadda mata suke fuskarta matsala, toh ina kuma na gayawa duniya tawa matsalar. Sai naga kamar tonawa kai asiri ne, ba mamaki akwai matan da suka fini damuwa amma suka iya lullube nasu bakin cikin, kuma suka rayu.  Matsalar mazan ba sabon abu bane domin kuwa har  kullum matsalar daya ce, kuma babu wanda zai gaya maka meye yake faruwa ba. Kiri kiri Uwar mijina ta tsane ni, dangin shi kuma sun tsane ni ne sabida naki na zama daya daga cikin su. Ban san meye zan musu ba, domin ko nayi ba fita zan yi ba. Dan haka na zuba musu ido.

    Kudin Makarantar yara aka basu takarda su kawo gida aje a biya, mika min takardan Nuratu tayi. Kamar zan yi magana sai kuma na fasa, amsa nayi na ajiye.  Da dare bayan na gama abinda nake nazo kwanciya, sai na kira shi. Aka nuna min yana waya, haka na jira ya gama na kuma kiran shi kamar ba zai dauka ba. Can da ya kusan tsinkewa ya dauka.
"Lokacin barci yayi fa me yasa ba zaki yi hakuri ba sai gobe?"
"Ba dan kaina na kira ka ba, kawai saboda Yaran ka ne. A turo kudin makaranta ne nace bari na tuna maka nauyin da yake kanka."

   "Kinga Yanzun bani da kudi don Allah ki bani aro zan biya ki. Na cire kudin nayi." Kasa magana nayi, ina sauraron shi. A hankali na sauke wayar a kunne na, sannan na kashe wayar. Ribar da na samu na kayan sayarwa na shi na kwashe har dubu sha biyar, na had'a da na banki na. A hankali nake wasa da wayar ina had'a lissafi da rage wasu abubuwan.

      Koda gari ya waye na kai su makaranta, sannan na dawo gida, da hantsi na tafi na ciro kudin na kai musu kudin su. Sannan na koma gurin aikina.

   Ban san bikin shi ba, a gidan naji labarin satin bikin dake naji sun ce zasu kawo Amaryan ayi wuni, amma shi bai gaya min ba, kuma ban damu na tambaya ba, haka ya samar min da kwanciyar hankali.
    
Yarana da ni ne muka yi sabon dinki,  har da Yahanasu.. ranar Laraba suka tafi wai kamu, sun dawo da kaya niki niki. Washi gari Alhamis sai gashi nan ta tawo. Da yamma likis na gama abin bude baki.. ya diro gidan, kallo daya nayi mishi ban kuma bin takan shi ba, tunda yazo na lura da take taken shi abu yake nima. Da karfe goma na dare dai gashi har d'akina.

       Ina kwance ya shigo ya zauna tare da kallona. Ya gama kame kamen shi..kafin ya bude bakin shi yana faɗin.
"Don Allah kiyi hakuri nasan na miki laifi, amma kiyi hakuri don Allah nazo ki bani aron dubu hamsin ne....
*Mu tattauna! Shin mata nawa suke fuskar irin wannan yanayin idan Allah ya kawo ki cikin jahilai! Gidan Aure Na ba kamar sauran Novels bane labari ne me nisan zango zaku iya bada gudummawar ku ta hanyar shawarwari da irin wannan lamarin yake faruwa dasu! Sannan zaku iya turo sakon ku ta wandanann Number domin labarin ba iya nan ya tsaya ba*

+234 708 416 1619

Billy Galadanci
+234 703 809 7759

Aunty Safiya Jos
+234 906 528 2817

Maman Nana Insha Allah sakon ku zai iso...
Allah ya hadu wani makon cigaban labarin Sameerah

#Mai_Dambu....

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now