Season 2

430 42 12
                                    

*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

*Muna muka sakon ta'aziyar ga daya daga cikin masu amsar sakonnin ku Aunty Safiya Jos, wato Ummu Faisak a bisa rashin Kawunta da tayi! Allah ya gafarta mishi yasa ya huta, Ubangiji yasa tamu tafi tasu kyau Allahummah Amin*

Season 2
Labarin Asiya Bamaina.
BABI NA DAYA.

   Wani irin faduwar gaba naji lokacin da naji dirin motar baban Khalifa. Had'iye yawun  tsoro nayi sannan na na kalle tsakar gidan a shafe tass, ko ina babu alamar kura gashi na share tsakar gidan tass, na kuma tattara ko ina butar da Khalifa ya ajiye ne kawai Matsalata.  A hankali na tashi ina dingishi a hankali, tare da taimakon sandar da nake amfani dashi, na dauki butar tare da nufar hanyar barandar mu.

Shigowa yayi duk da ba wani abu bane zai min amma baki daya na razana da shi, asalima jikina ne ya kama rawa.
"Sann...san...da zuwa" kallon banza yayi min sannan ya wuce tare da kwallo da bokitin da yake gaban shi.
"Wannan ai kutumar Uba ce, akan me za a ajiye min butatta babu ruwa?" Yadda yayi maganar yana hayayyako min ya sani komawa gefe ina bashi hakuri.

   "Ban da Iskancin da rashin daraja aure butatta zaa bar min babu ruwan alola a cikin shi " ya fada alamar yaji haushi, sunkuyar da kai nayi ina faɗin.
"Kayi hakuri"
Kamar zai dake ni domin yadda ya zabura kamar zai make ni yaki ji, amma haka ya wuce.

    Dake gidan daga ni sai kanen shi biyu da suke karatu a nan school of nursing, dan haka ya gama masifar shi ina jin shi na had'a mishi kayan abincin shi na kai dakin shi. A fusace ya d'ago kai ya kalle ni, lokacin da na shiga dakin yana cire kayan shi.

  "Koma ba zan ci ba" ya fada min tare da shiga ban daki, jiki a salube na koma, ina ajiye kwanon na koma dakina daidai shigowar Madinah Kanwar shi. Kallon kayan abincin tayi tare da tab'e baki tana faɗin.
"Uwar marasa zuciya an yi kenan?"
Ban kula ta ba, na cigaba da zaman d'akina,
"Assalamu alaikum!" Hawaye ne ya zubo min tare da d'aga labule ina kallon shi, tare da kallon dan karamin bakin shi da ya iya rangad'a sallama haka.

   Mika mishi hannu nayi, da sauri ya cire takalmin shi zai shigo, Safiyah ta kai mishi mari a bayan shi, wacce shigowar ta kenan.
"Shegen Yaro munafuki, ni na ce maka ka jira ni amma kayi tafiyar ka, wannan dan banzan yaron anya Uwarka bata koya maka mugun abu a dakin ku" cikin shashekar kuka ya ce mata.
"Aunty wallahi ban ji bane"
"Dan Uwar ka gobe ma na maka magana ka share ni sai naci uwarka" ta faɗa tana kallona.

       Kaina a sunkuye, Yaron ya shigo yana faɗin.
"Wallahi ban ji bane." " Toh ka daina mana, kaga abu kyau kyale Babba kaji" gyada min kai yayi sannan ya ce min.
"Mama yaushe zamu bar gidan nan, na gaji ba zan iya zama ba, mu koma wurin kaka"
Wato yana nufin garin mu, gyada kai nayi ina danne kuka na, nace mishi.
"Mun kusan tafiya"
"Munafuka kina kitsa mishi mugun abu ko? Idan nace kina haka kice ba haka ba, kai kuma sai naci Uwarka shege munafikin Yaro kawai."

     Ya fadi haka yana gyara tsayuwar shi.
Yana son lallai na kalle shi domin na gane yayi shirin fita wurin budurwan shi..baki d'ago kai na domin bana son na ga abin da zai dame ni.

   Yana gamawa ya juya ya fita, bai ce min kome ba.
Shekaru biyar da suka wuce.
Ni yar garin Bamaina ce, iyayena suna can, amma sabida budin da Yayuna suka samu sun dawo da su garin Dutse.

         Mun hadu da Sagir ne lokacin candy din mu, muka hadu dashi, A lokacin iyayena suka ce ba zasu bashi ni ba, sai na fara N.C.E, haka yayi ta hakilon bibiyar rayuwata, har na fara karatuna. A garin Dutse kasancewar yan uwana suna nan da zama. Yayuna maza biyu ne sai Mace Aunty Kubrah.

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now