SANADIN KAWA PAGE 5

40 1 0
                                        


°SANADIN KAWA 💔💔°

°NA°

°BEENTU ZULKARNAINI°

Bayan kwana biyu Daddy ya Kira Alhajin KADUNA ya sanar da shi suna so su zo akwai maganar da za su tattauna. Alhaji ya ce babu damuwa kuma su na sa ran ganinsu...
Can bangaren Naja'atu da ƙawayen ta kuma sai abunda ya cigaba.

Ranar juma'a, bayan sallar juma'a Naseer da Mami da Alhaji suka nufo hanyar Kaduna. Misalin 3:30pm suka iso Badarawa direct gidan suka shiga. Mami ta fara yin sallama ta shiga daidai lokacin Ummi ta fito daga ɗaki. Cikin sauri Ummi ta taho da gudu ta faɗa jikin mami tana faɗin oyoyo Mami, Mami ta rungume ta har suka zauna suna dariya. Ƙarar da Ummi tayi yasa Mommy fitowa daidai lokacin Naseer da Alhaji suka shigo Falon. Mommy tana dariya tana faɗin aaa a ah sannun ku da zuwa maraba. Alhaji ya zauna yayin da Naseer shi ma ya nemi guri ya zauna yana duban Yanda Ummi ta rungume Mami kamar wata karamar yarinya. Nan da nan Mommy suka gaisa da Mami da Alhajin cikin fara'a da murnar ganin juna nan fa suka hau hira. Mommy ta dubi ummi tana faɗin toh Ummi ai rungumar ta isa haka ki tashi ki kawo musu drinks da snacks. Ummi ta miƙe da sauri sannan kuma ta koma ta zauna tana faɗin Mami wlh naji daɗin ganinki kuma na yi kewar ki sosai Mamina... Mami tayi dariya a fili sannan tace nima haka ummi na, ai kullum sai na bada sakon gaisuwa na a gareu ki a wajen Naseer... Kafin Ummi tace wani abu Naseer yayi caraf ya ce wai ke ba cewa akayi ki kawo wa mutane ruwa ba? Ummi ta kalle shi su ka haɗa ido kaman zata ce wani abu sai dai tayi shiru sannan ta tashi domin kawo musu drinks.
Ba jimawa Ummi ta dawo da Drinks da plates ɗin snacks Ta ajiye shi tsakanin Mami da Alhaji kana ta zuba musu a cups suka karba cikin sakin fuska tare da saka mata Albarka.
Naseer da yaga alamun Ummi ba ta da niyyar zuba mishi, cikin haɗe fuska ya dube ta yana faɗin Ni baza a zubamin  bane? Kafin Ummi ta ce wani abu... sai ga sallamar su ya Mukhtar da Daddy. Suka amsa, nan Alhaji ya miƙe cikin dariya suka gaisa tare da yi musu Barka da zuwa. Duka su ka zauna a falo su ka dinga hira.

Bayan wani lokaci Alhaji (Daddyn Zaria) ya sanar da Daddy ya kamata su zauna a keɓance domin sanar da shi dalilin zuwan su. Mukhtar da Naseer su ka nufi ɗakin Mukhtar, yayin da Mommy ta ja Mami sukayi uwar ɗakin ta domin ci gaba da hirar su ita kuma Ummi ta shiga kitchen domin ɗaura girkin dare.

Alhaji Zubair da Alhaji Musa ne suka rage a falon. Alhaji Musa ya fara da cewa dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, ba tare da wani dogon jawabi ba dama nazo ne akan magana ta neman aure. Ina nufin ɗanka Naseer da Naja'atu. Ya gyara zama kana ya cigaba da cewa dama saboda haka ne naga ya kamata mu manya mu shiga lamarin domin ayi a gama ba tare da wani bata lokaci ba, tunda yanzu dai yara sun fahimci juna kaga kuwa yin auren shine mafi alkhairi.
Alhaji Zubair ya yi shiru na ɗan wani lokaci sannan ya dubi kanin nasa Alhaji Musa gami da gyaran murya kana ya ce Toh Alhamdulillah Lallai naji daɗin wannan labari kuma na amince zan bada auren Naja'atu tunda har sun fahimci juna, amma Wani hanzari ba gudu ba, gaskiya ina son sai ta kammala karatun ta na Secondary tunda yanzu haka shekara ɗaya ta rage mata daga nan sai ayi cikin kwanciyar hankali bayan ta kammala idan Allah ya yarda.
Alhaji Musa ya sauke numfashi sannan ya ce ai duk abin da kace babu damuwa zan sanar da shi Naseer ɗin. Kuma ina fatan Allah ya ƙara haɗa kawunan su da mu baki daya. Kuma Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi. Ameen Alhaji Zubair ya faɗa tare da ɗaukan ruwa ya sha. Nan su ka cigaba da hira.

Mami ta dubi Mommy tana faɗin wai ina Naja'atu ne? Tun da muka zo ban saka ta a idanu na bah! Mommy ta fuskan ci Mamin tana faɗin.....

°Shin wai ina Naja ta makale neh?°

°Ku biyo ni a shafi na gaba....°

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 26, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANADIN KAWAWhere stories live. Discover now