SANADIN KAWA Page 2

51 3 0
                                    

° SANADIN KAWA 💔💔°

°NA°

°BEENTU ZULKARNAINI°

Umar, Alhaji, Mukhtar da Naja ne zaune a falo. Su Mommy suka nemi guri suka zauna. Suka yi wa Annabi salati... Umar ya cigaba da cewa... Toh Ni zan koma kan aikina Alhamdulillah hutu na ya ƙare sai kuyi ta tayamu da addu'a. Ya dubi Naja da Ummi kana yace 'Naja ku kara dagewa sosai ku maida hankali akan karatun ku sannan kun san banida wasa bana son maganar ƙawaye  barkatai. Na sha yi muku jan kunne akan I don't favor too much of friends, saboda wasu friends ɗin masifa ce a gare ku ba abun alfahari bane yawan ƙawaye. Don Allah ku kiyaye kamar yanda nake faɗa muku a ko da yaushe'.

Cikin sanyin murya Ummi tace eh yaya... In sha Allah zamu kiyaye. Allah ya kai ka Lafiya kuma ya baka Sa'a. Ameen ya faɗa tare da miƙewa. Ya dubi Mommy da Alhaji tare da faɗin Ni zan wuce na bar ku lafiya. Cikin murmushi su ka amsa mishi in sha Allah Umar Allah ya ba ka Sa'a. Ameen ya faɗa gami da fita suna biye da shi a baya har bakin gate suka raka shi ya shiga mota driver ya ja shi zuwa airport domin a daren jirgin su zai tashi...

ZARIA
Tsaf ya gama shirinshi cikin Jeans fari da long sleeve baƙi. Ya fito yana kamshin turaren sa SANTIAGO PARIS.
Ɗakin daddy Nasir ya nufa direct ya shiga da sallama. Mami da Daddy suka amsa masa tare da bashi izinin shiga. Ya shiga ya zauna gefen Mamin tashi.

Cikin ladabi ya gaida su bayan sun amsa Naseer ya cigaba da cewa Daddy dama zan shiga Kaduna ne can Badarawa gidan su Daddyn Kaduna shi ne nace barin muku sallama. Cikin sakin fuska Daddy yace hakan ya na da kyau Naseer adawo lafia kuma ka gaida mutanen gidan. Mami tace a dawo lafia ka gaishe su musamman Ummi na.

Gyaɗa kai Naseer yayi gami da miƙewa har yakai bakin kofa, Daddy yace yawwah Naseer idan ka dawo inason ganinka. Naseer ya amsa da toh Daddy in sha Allahu. Mami tace kada Fah ka manta da gaisuwa ta ga Ummi na. Cikin murmushi Naseer ya ce toh Mami. Yayi waje yana tunanin irin yanda Mami take son Ummi haka. Motar shi ya shiga tare da tada motan yayi gaba....


Bai jima sosai ba ya iso Badarawa. Ya shiga ya gyara parking. Direct falo ya nufo. Mommy ya tarar tana kallon Peace TV. Ya shiga tare da sallama, ta amsa. Aaah Naseer kai ne? Ya zauna yana daria eh Mommy ni ne ya gida? Lafia wlh Naseer ya hanya ya gidan ya Su Mami da Baban naka? Duk suna lafia kuma su na gaida ku. Ma sha Allah muna amsawa bari na kawo maka ruwa. Ta miƙe ta kawo mishi ruwa, ya ɗan sha kaɗan. Mommy tace gashi duk basu nan Kasan jiya Umar ya koma aiki, Mukhtar kuma ya je wajen aiki, su Naja kuma basu dawo daga school bah. Tana idar da magana suka shigo...

Ummi ce ta fara shigowa aiko sukayi ido huɗu da Naseer. Ji tayi gabanta ya faɗi, ta karaso tana fadin sannu da zuwa. Ya amsa yawwa batare da ya dube ta bah. Mommy sannu da gida. Cikin murmushi tace yawwa ummi kun dawo. Eh ta faɗa tare da shigewa ɗaka. Naja ta shigo tayi tubali da masoyin nata. Naseer murmushi yayi sannan ya sauke numfashi. Naja ta dube shi Hmm Ashe zaka zon? Ya lumshe idanun shi masu cike da kwarjini da kaunar ta. Cikin jan aji irin nashi yace gani kina gani na.
Taɓe baki tayi tace Alright I'm coming I will soon be back. Tayi gaba batare da ma ta lura Mommy tana zaune ba balle ma ta gaida ta. Mommy tayi ajiyar zuciya tare da faɗin ikon Allah a ranta, miƙewa tayi ta nufi nata ɗakin...

°Ku kasance tare da Ni a shafi na gaba domin jin yanda za ta kaya....°

SANADIN KAWAWhere stories live. Discover now