SANADIN KAWA Page 1

73 2 3
                                    

°SANADIN KAWA 💔💔°

°NA°

           ° BEENTU ZULKARNAINI°

Bismillahir rahmanir rahim

Da Sunan Allah mai kowa mai komai, zan fara da yabon sa na kasancewa na tare daku a cikin wannan littafi Mai suna SANADIN KAWA.

Ina rokon Allah yanda na fara lafiya ya sa na gama lafiya🤲🏻
Ameen.



Families din su Alhaji Zubair babban family ne wanda Ya haɗa dangi sosai tun daga kakanni zuwa ubanni.

Alhaji Zubair su huɗu ne a wajen iyayensu. Shi ne babba sai Alhaji Musa mai bi mishi sai Alhaji Muhammad sai Alhaji Mansur wanda ya zama ɗan autan su

Alhaji Zubair yana zaune ne a Kaduna tare da iyalansa. Matar sa daya Hajiya Zainab wacce su ke kira da Mommy sai yaran sa guda huɗu babban ɗan sa Umar wanda ya kasance soja ne, sai Mukhtar shi kuma likita ne, sai Naja'atu da Rukayyah suna high school.

Alhaji Zubair asalin Fulanin Adamawa ne su. Alhaji Musa mai bima Alhaji Zubair shi ma yana zaune ne a Kaduna a Zaria tare da matarsa ɗaya Hajiya Hafsah wacce suke kira da mami. Sai ɗansu ɗaya Naseer.
Naseer ya kammala karatun sa ya karanci migration studies inda yanzu yake aikin Immigration.

Sai Alhaji Muhammad da yake zaune a Kano shi da matan sa biyu Hajara da Maryam. Yana da yara biyu Faisal da Nafisa.
Sai Alhaji Mansur yana zaune ne a Adamawa wato asalin tushen su tare da matarsa ɗaya da yara biyu Usman da Jamila...

KADUNA
Misalin qarfe goma da rabi Naja ta fito daga bathroom. Wayar ta kirar Samsung Galaxy S7 ke ta tsala ringing, cikin sauri ta karaso ta ɗaga, murmushi tayi tare da ciza leɓe a lokaci daya ta amsa call din tare da fadin "Dan Allah kiyi hakuri bazan samu zuwa yau bah...." Bata karasa maganar ta ba sai kawar tace "ya isa dama nasan haka zata kasance haka kika saba ai You usually disappoint us" Naja ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Kawata wlh yayanmu ne bai koma Lagos ba har yanzu shiyasa kika ga 2days bana iya zuwa ko ina amma wlh babu zancen disappointment" Na ji ki sai anjima... Kafin tace wani abu tuni kawar Tata ta katse wayar. Naja ta ja tsaki tare da jefa wayar kan gado.
Ummi ce ta shigo dakin wato kamar Najan kenan. "Ki zo inji Mommy Wai tafiyar ya Umar yau ne", shiru Naja bata amsa mata ba. Ummi ta sake magana 'Anty Naja kina ji na kuwa?'
Yoh ba kunne ke ji ba ko dole sai na amsa da baki ? Cikin haɗa rai Naja ta fice. Ummi ta taɓe baki tare da girgiza kai gami da faɗin nidai na rasa irin anty Naja ko da yaushe jaraba duk ta zama masifaffa..

Rukayyah wato ummi kyakkyawar yarinya ce fara mai matsakaicin tsayi, ga hanci, gashi irinta asalin Fulanin Yola. Tana da ilimi sosai, ladabi, tarbiyya ga kuma kunya.

Allah ya sanya mata kaunar Naseer a ranta, babu wanda take so a rayuwar ta kamar Naseer. Hmmm Sai dai In da gizo ke saƙa hankalin Naseer sam baya a kanta yayin da shi kuma nasa zuciyar tayi nisa a son yayarta wato Naja'atu.
Ya Salam abinda Ummi ta furta kenan yayin da ta tuna wannan badaƙalar da rayuwar ta take ciki. Ji tayi wani abu ya faɗo mata wato tunanin yanda mu'amalar ta da Naseer yake, duk cikin dangin su ita da shi ne kawai jinin su bai zo ɗaya ba, sam ba su jituwa. Ko yaya suka zauna waje daya tabbas sai anji su sbd yanda basa jituwa da juna. Hakan yana matukar ƙona wa Ummi rai musamman idan ta tuna yanda take matukar son shi. Sai dai ta san Ya Naseer ba nata bane ya riga ya mata nisa.
Babu wanda ta taɓa faɗa wa wannan sirrin yana cikin ran ta daga zuciyar ta sai mahaliccin ta. A yayin da son shi ke cigaba da cutar da nata zuciyar ba tare da saninta bah. Cigaba tayi da tunanin yadda rayuwar ta zata kasance... Ta daɗe cikin tunanin. Mommy ce ta katse mata tunanin tare da faɗin 'Ummi ke mu ke jira a falo...' Ta ɗan firgita kana tace 'au Ni Fah na ma manta' Su ka fita tare da Mommyn zuwa falo....

°Ku biyo ni a shafi na gaba don jin yadda za ta kaya°

SANADIN KAWAWhere stories live. Discover now