SANADIN KAWA Page 4

21 1 0
                                    

°SANADIN KAWA 💔💔°

°NA°

°BEENTU ZULKARNAINI°

Naja ke zaune gefen gado tana danna wayar ta. Ummi ta zauna gefen ta tana faɗin anty Naja amma dai kin san babu wani lesson da akayi yau ko? Kuma karya nayi Wa Mommy don na rufa miki asiri, kuma tun da aka tashi daga school na dinga neman ki har... Naja Ta katse ta da faɗin dallah ya ishe ni Ko saka ki nayi ki rufa min asirin? Ko Ni na saka ki kiyi wa Mommyn karya? Ummi ki fita ido na ki fita sha'ani na ta ja tsaki gami da ficewa waje... Ummi ta yi ajiyar zuciya tab ya Allah ka shirya Anty Naja wannan wacce kalar rayuwa take neman jefa kanta a ciki, ta cigaba da zullumi....


★ ★ ★

Naseer ke zaune a falon Mami yana danna laptop dinshi, Mami tayi sallama ta shigo ya amsa kana yace Mami har kin dawo? Ta zauna tana faɗin eh Kasan wajen ba wani nisa ne da shi ba, ta cigaba da cewa tun dazu dai kana kan danne dannen naka, baban naka bai dawo bane? Naseer ya dubi Mami yana faɗin eh Wallahi, ke dai bari aikin ne yawa gare shi.

Kafin Mami tace wani abu daddy yayi sallama tare da shigowa cikin falon. Su ka amsa, Daddy yace ashe duk kuna falo? Naseer yayi yaƙe kana yace uhmm eh Daddy sannu da zuwa. Yawwah Naseer dama kwanaki na faɗa maka ina son magana da kai amma shiru baka zo ka same Ni akan batun bah. Naseer ya shafa kansa tare da faɗin Am sorry Daddy wlh duk na sha'afa ne. Mami tayi saurin cewa ai kwanakin nan naga you're always busy kaman wanda ya fara tara iyalai. Duka suka yi dariya kana Daddy ya cigaba da cewa toh dama ba komai ya sa na neme ka ba sai akan tsakanin ka da Naja'atu kanwar ka, ina so idan har da gaske kake yi kuma kun fahimci juna mu yi magana ayi a gama komai domin kuwa ban ga amfanin wani jinkiri ba ya kamata ayi a ida komai da izinin Allah hakan shi yafi alkhairi.

Naseer yayi ƙasa da kan sa yana murmushi, Mami tayi dariya a fili sannan tace ai Alhaji wannan haka yake, to kai ban da abinka Naseer ai magana za kayi ka bada amsa. Naseer yayi shiru ran shi cike da farin ciki sannan ya ce mun fahimci juna Daddy kuma duk abunda ku ka yanke shi ne daidai, Cikin kunya ya ke maganar. Alhaji ya yi dariya a fili  sannan ya ce toh Alhamdulillah haka mu ke son ji ba damuwa In Sha Allah zan tuntuɓi baban naka na Kaduna mu sa rana mu je ayi magana.

Cikin hanzari Naseer ya miƙe domin ku wa murnar da yake yi yana yunƙurin fin karfin shi har ya ku sa bayyana. Ya fice ya nufi ɗakin sa kai tsaye. Mami tayi hamdala gami da duban Alhaji tace ma sha Allahu, Allah ya sa haka shi ne mafi alkhairi. Amin Daddy ya fada tare da miƙewa yana faɗin Mami bani ruwan wanka nayi freshing up jikina. Mami ta miƙe ta nufi ciki domin shirya masa wajen wankan.

Naseer ya janyo wayar sa ya shiga contacts, ya Danna numbern aminin nasa wato Yusuf. Ya kira bugu na ɗaya a na biyu Yusuf ya amsa wayar tare da sallama, Naseer ya amsa masa cikin farin ciki. Yusuf ya ce ya dai aboki na yau dai akwai labari... Naseer yayi dariya kana yace Hmm kai dai bari at long last dai Finally abu ya kusa zuwa ending. Cikin rashin fahimtar abinda ya faɗi. Yusuf ya tambaye shi kamar yaya? Me ka ke nu fi? Nan dai Naseer ya zayyano mi shi duk yanda su ka yi tare da Daddyn nasa. Yusuf ya taya shi farin ciki gami da yi mi shi fatan alkhairi. Naseer ya ji daɗin hakan nan dai suka ci gaba da hirar ta su da hirar aikin su.....

° Shin wai yaya zata kasan ce?°

°Ku biyo NI a shafi na gaba....°

SANADIN KAWAWhere stories live. Discover now