SANADIN KAWA Page 3

28 1 0
                                    

° SANADIN KAWA 💔💔 °

°NA°

°BEENTU ZULKARNAINI°

Cikin kankanin lokaci Naja ta tsara shiri ta tsantsara kwalliya ta sa doguwar riga ta nufi falo jikinta sai tashin kamshi yake. Ta zauna kusa da Naseer tare da watsa masa wani irin kallo mai ɗaukan hankali.
Ya gyara murya tare da faɗin My queen duk wannan kwalliyan haka for me? Tana taunan chewing gum tace eh duka naka ne Sweetheart. Ya dube ta gami da faɗin You look gorgeous my queen. Har cikin ranta taji maganar ya ratsa ta tasan halin shi ya iya tsara magana ga jan aji da kwarjini gaskia nayi sa'ar samun ka a matsayin miji ta faɗa a ranta. Su ka cigaba da hira...

Ummi ce ta fito cikin uniform ɗin islamiyya, ji tayi dama ace ita ce Naja take zaune tare da farin cikin ranta gata Ga shi... Ta fice waje tana tunanin wanne irin farin ciki zata kasance a ranar da Allah ya nuna mata ga ta a ɗakin Naseer a matsayin matar sa. Ta ja tsaki tare da takaicin Ya Naseer ba nata bane ya riga ya mata nisa...

Bayan isowar Umar Lagos, ya tarar da matar ta sa tayi masa tarba ta Musamman. Nafisa ce matar shi wato ɗiyar kanin baban shi Alhaji Muhammad.
Da saurin ta ta rungumo shi tana faɗin sannu da zuwa. Yawwah dear na same ki lafia? Kalau Alhamdulillah Amma Ina cike da kewar ka. Uhmm gani ai na dawo.. Nafisa ta shirya mai wajen wanka bayan fitowar sa ya ci abinci sannan take tambayar shi ya labarin mutan Kaduna....

★ ★ ★

06:30am suka kammala breakfast ba ɓata lokaci suka yi shirin zuwa school cikin ƙanƙanin lokaci suka wuce school. Da isar su Naja ta zarce wurin aminan nata... Barkan ku, kamar dai ba zasu amsa ba chan dai sai Abida ɗaya daga cikin ƙawayen nata tace kin iso lafia? Uhm abun ma 'yar kyaliya ce... Su ka kwashe da dariya sannan Rahma tace gaskia Naja kina yawan disappointing ɗin mu jiya Fah tsaf mu ka shirya ana ta faman jiran ki shiru har sannan Fa'iza ta kira Number ki wai You can't make it... Naja ta dakatar da ita I'm really sorry.
Wlh na faɗa mata yayan mu ne bai wuce ba ku ma kin sani tabbas yana da tsanani.
Anyways yanzu I'm totally free yaushe zamu kara sa rana i wouldn't disappoint you guys this time around. Su ka ci gaba da hirar tasu a karshe su ka kara tsaida ranar outing ɗin...

Bayan azahar suka tashi daga school, Ummi sai faman neman Naja take yi amma Shiru babu Najan. Ganin hakan ya sa tayi tunanin ko ta wuce gida don haka tayi tafiyar ta.
Naja ke zaune gefen Abida yayin da Rahma ta ke ta zabgawa saurayin ta karya ta waya. Kun ga Ni wuce wa zanyi time ya tafi sosai na san yanzu Ummi ta isa gida don haka sai next time. Ta miƙe tare da tarar mota sukayi mata rakiya har ta wuce...

Rahma ta dubi fa'iza da Abida tana faɗin Hmm ni dai rayuwar Naja tana bani sha'awa. Abida tace saboda me ? Meyasa kika ce haka? Rahma ta cigaba da cewa bakiga yanda ta iya basaja ba, tana shagalin ta a waje sannan ta koma gida kuma ba tare da wani ma ya san halin da take ciki ba. Abida tayi dariya gami da cewa Hmmm lokaci ne kar ki damu a hankali za ta rasa nata gidan zuwan itama. Su ka kwashe da dariya suka ci gaba da hirar tasu.

Naja'atu sai yanzu? Mommy ke tambayar Naja bayan shigowar ta gida. Naja ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce Mommy lesson mu kayi ita kuma Ummi ta ƙi jira na. Ummi wai haka ne? Ummi tayi shiru... Kana ta ce Mommy haka ne ina da karatun da zanyi na islamiyya shiyasa na dawo gida ban jira ta ba. Mommy ta ce toh shikenan amma dawowan ku gida a tare shi ne ya fi alkhairi kuma hakan ne zai hana Ni shiga damuwa. Naja tayi cikin ɗaki, Ummi ta bi bayan ta.....

°Shin wai wasu kalan ƙawaye ne a tare da Naja?°

°Menene zai biyo baya bayan shigar Ummi da Naja cikin ɗaki?°

°Ku biyo ni a shafi na gaba domin sanin yanda zata kasance°

SANADIN KAWAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz