Najma
Baƙaramin wahala tasha wajan Faisal ba domin ba tayi tsammanin hakan ba,ta ɗauka abin zai ƙayatar za taji daɗi fiye da yadda ake fasallata mata daɗinsa,ta ɗauka zai mantar da ita duniyar da take cikin ta hanyar dulmiyar da ita a cikin salon nasan ƙwarewar,ta ɗauka zai jiyar da ita daɗi da kuma farin cikin da'a taɓa yiwa wata ƴar mace  ba,amma saiya shayar da ita gubarsa da kuma ɗacinsa haɗi da azabartar da ita ya dasa mata tsoran abun.
Da rarrafe ta shiga toilet ruwan zafi da haɗa tare da zare rigar jikinta cikin ruwan ta shiga azabar data jine yasa ta fawa ihu tare da ƙanƙame jikinta waje guda,sosai take kuka cike da muradin rama abinda yay mata danta ɗauki alƙwarin nemo maganin dake saka feelings in five minutes,wanka tayi tare dayin wankan tsarki  tare da ɗaura towel a jikinta tana tafe tana kwala ƙafa,ta kusa zama kan bed ta hangi wani dairy  ɗauka tayi tare buɗe shafin farko da manyan baƙi taga an rubuta MY BEBY BOO kafin a rubuta wasu zafafen kalaman soyayya a haka ta shiga duba sauran shafukan har tazu last page inda aka rubuta "WHEN ALL IS GONE" tashin hankali wanda ba'a saka masa rana jikin Najma ne ya shiga ɓari tare da karkarwa yayinda wata zufa ta shiga ƙeto mata dai² lokacin da tabbas baya nan da Faisal ya rubuta ya gama tabbatar mata Dad da Mamy haɗi da Fahad sun jima da rasuwa kuka ne ya ƙwace mata ta rerawa saida tayi mai isarta kafin ta duba bayanin ƙarshe.

_ko kowa zai yarda kin mutu babu ni domin zuciyata a kullum da tunaninki take bugawa,ina nan ina zaman jiranki daga nan har ƙarshen rayuwata,kece farin cikina muradin raina da sonki nake ƙwana nake tashi i luv u i luv the rest of my life i luv soo much i'm always be ur side my Bby boo mu'ahh💋_

Wani ƙyaƙƙyawan murmushine ya suɓucewa  Najma cikin farin ciki tace "Mutuwarki ya zama abu na farko daya sanyaya miƙe daya daɗe yana damuna shekara da shekari kin ƙwace komai nawa ƙyau ilimi farin jini gata muradin raina hankali nutsuwa komai dai kin ƙwace why Lubna i lost everthing because of u pulish gril i hate u tsana mai yawa,koda baki mutu ba na ɗauki al'ƙawarin ra baki da ranki kamar yadda kika rabani da dukkan wani farin cikina zuwa now he is mine for rever and ever".


*** ***
Abuja.
Idan tace abun duniya bai isheta ba tayi ƙarya gaba ɗaya cikin firgici take kullum a tsorace take,ita kanta bata san meke damunta amma ƙasan ranta tana ji akwai wani baban kuskure data tafka kullum ciki tunani da zullumi take yayinda a koda yaushe ƙyaƙƙyawar fuskarsa keyi mata gizu a cikin dara-daran manyan idanunta waye shi?a ina yake wannan shine tambayar dake damunta wacce a kullum take son furtawa wa wani ko zata samu sauƙi a ranta amma babu dama,babu wanda zata gayawa taji daɗi,Yusrah da take matsayin ƙanwar wanda zata aura ko kuma Momma dake matsayin uwa a wajansa ko kuma shi ɗin kansa zata tambaya tace zuciyarta wani take muradi bashi ba? Lumshe idanunta tayi hakan ya bawa hawayen cikin idanunta damar sakkowa daga cikin idanunta zuwa kan fuskarta,lumshe ido ta ƙara cike da muradin son ƙara ganin fuskarta duk da har yau ba full face ɗinsa take gani ba amma ganin fuskar tasa ya fiye mata komai a yanzu domin sosai takesa zuciyarta nutsuwa da kuma dai² tuwar bugun zuciyarta,ɗan cije lips tayi ganin ba taga abinda take muradin gani ba hakan yasa ta fashe da wani irin kuka haɗi da cusa kanta cikin fillow ta shiga rera kukanta,sai yaushe ne zata daina jin abinda ta keji a cikin zuciyarta,yaushe ne zata daina kukan rashin Ahalinta?mai yasa ƙaddara take juya rayuwarta kamarta samu ƙwallo a cikin fili.
Bata ji a wannan karan zata iya rauninta domin damuwar sosai take son fallasa abinda yake cikin zuciyarta cikin sauri ta miƙe tare da sakin siririyar ajjiyar zuciya,Tunawa da yayarta ta ya zama wani garkuwa a gareta ya kuma zama wani farin cikin daya samu gurbin raƙe mata damuwar ranta.
Ƙatun hijab ɗinta ta ɗauka tare da kallon madubi ya mutsa fuska tayi ganin yadda fuskarta  ta faɗa sai idanunta daya ƙara girma ga ƙyan fuskarta ya ƙara fituwa babu abinda ke birgeta a fuskarta sama da cute peach lips ɗinta daya ƙara ɗan tudu da kuma sharning sosai take samun kulawa wajan Momma da kuma gogan nata Sufyan.
Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi parlo a nan ta tarar da Momma sai Sufyan da shiguwarsa kenan sosai yay kyau cikin shigar blue ɗin t.shirt sai long dark black jeans dake jikinsa yana zauna yana danna waya,ƙamshin turarenta ya kawowa hancinsa ziyara lumshe idanunsa yay tare da buɗesu ya mannasu akanta sosai tayi masa kyau yana jin ina babu Momma awajan da babu abinda zai hana ya shaƙi daddaɗan ƙamshin turarenta.
Jikin Momma taje ta lafe tana ji tamkar a jikin Mamynta take  bakinta na rawa tace.
"Momma ina neman izinin zuwa kano wajan sister na tuna da ita ina buƙatar ganinta".
Kanta Momma ta shafa tare da faɗin "Lubna kin faɗa a ƙorarran lokaci gashi jibi jirginmu zai tashi suwa bikin ƴar uwar mijikin a can za'a haɗa ai naki keda Sufyan"
Turo baki LILI tayi tare da ƙara shigewa jikin Momma ta shiga sauke numfashi ita sam ta manta matsayin uwar miji take,cike da zallar shagwaɓa tace.
"pls Momma i want see her ita ɗaya nake da"murmushi Momma tayi tare da zare jikinta daga na Lili tace.
"babu damuwa kuyi magana da Sufyan gobe da safe saiya kaiki"gdy tayi mata.
Miƙewa yay ya dawo inda take zaune kallonta yay sosai kafin ya maida idanunsa kan lips ɗinta ganin ya fara fita on his mood domin sosai ƙamshin turarenta yaƙe ƙara masa wutar sha'awarsa harya matsu sati ya zagayo domin ta zama mallakinsa.
Miƙewa yay tare da kallonta yace "7 zamu bar gida so don't keep me waiting"yan faɗin hakan ya shige cikin flat ɗinsa jin wani hurt feelings ɗinta na tasu masa.

 JUYAYIजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें