Heart attack

632 61 5
                                    

_The secret issues_
*💖JUYAYI💖*

*20-21*

*WATTPAD*
  Nimcyluv

*Telegram*    https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ     _Masoyan *NIMCYLUV* ga mahajarmu na telegram yana da kyau kuyi join domin samun littafai cikin sauƙi da kuma amfanuwa da_
   *programs* _ɗin daza muna gabatarwa kuma dukkan wani posting ɗina zai kuma can zai zama VIP group ɗina na musamman kuyi share zuwa wasu groups ɗin dan nuna ƙauna dan Allah._

    
    
           
                ......Jinin dake fita ta hancinsa da bakinsa ne yasa Ammi saurin fasa ƙara tare dayin kansa tana zuwa ta durƙushewa gabansa ta shiga girgizashi tare da kiran sunnansa "Faisal" Faisal"..ganin ko mutsi ba yaye bare ta saka ran zai buɗe idanunsa har yay magana.
Da gudu tayi waje tana rabza kuka ganin halinda ɗan nata ke ciki tana ƙoƙarin ficewa daga parlon domin ta samu ta kira mai gadi ya taimaka mata,a nan sukayi karo da Papi wanda ke ƙoƙarin shiguwa.
Ganinta a rikice ne ga kukan da take ya sashi saurin sakin jakarsa tare da jawota jikinsa,kuka ta fashe dashi tare da faɗin.
"wacce uwace ni?ina ƙoƙarin kashe ɗana da kaina wlh.."kukan da yaci ƙarfinta ne yasa bata samu damar ƙarasa abinda tayi niya ba.
Bayanta ya shiga bubbugawa tare da jijjigata,shi kansa tun safe  ba dai² yake jinsa ba fargaba tsoro bugun zuciya faɗuwan gaba shine abinda yake damun ransa dalilin hakan ya tattaro kayansa zuwa gida,cikin dauriya yace.
"lafiyanki ɗaya wannan kukan duk na mene?".
Cikin firgici ta shiga bashi labari ai bata ƙarasa ba yasa hannu ya tureta da gudu yay flat ɗin faisal,yana shiga ya ganshi yashe a ƙasa bai tsaya jiran komai ba ya sunƙuci ɗan nasa yay waje.
Hijab Ammi ta ɗauka tare da rufa masu baya cikin sauri ta shiga motar da wani irin speed Papi yaja motar daman tuni mai gadi ya buɗe get cikin sauri ya halba hancin motar kan titi.
Lokacin kaɗan suka isa Amino kano teaching hospital,suna zuwa ma'aikantan asibiti sukayo kansa a haka aka ɗurashi zuwa bed ɗin marasa lpa akai cikin emagency room dashi.
A nan ƙofar emagency ɗin suka shiga zirga-zirga sosai zallar tashin hankali ya bayyana kan fuskar Papi tym to tym yakan girgiza kansa tare da fesar da numfashi.
Sun ɗauki wajan 1hour kafin likitocin su fitu da sauri Papi yay wajan babban likitan tare da faɗin.
"Dr meke faruwa da lafiyan ɗana?"
Gomi Dr ta ya share kana ya kalli Papi yace.
"follow me" yana hakan ya juya zuwa cikin office ɗinsa,jiki babu ƙwari suka rufa masa baya,glass ɗin idanunsa ya zare kafin yaja numfashi yace.
"tunda na ganka nasan ciwon Faisal yayi tsauri kusan kullum yana zuwa amsar magani"cikin rashi n fahimta Papi yace.
"kullum fa Dr ka sani a fargaba pls meke faruwa?".
Tausayin Ahalinne ya kama Dr numfashi ya ƙara kafin ya maida glass ɗinsa yace.
"ciwon zuciya ya kama Faisal kuma ciwo mai tsanani irin na lokaci guda ɗinnan,yanzu mun ɗurashi bisa magana kamar su,H2Blockers,
Lisinopril
Perindopril
Quinapril
Trandolapril
Angiotensin,ya buƙaci kada na sanar dakai sabida yana saran samun lafiya nan kusa,amma abin mamaki kullum Faisal cikin ƙunci da damuwa haɗi da tunani nayi nayi ya faɗamin damuwarsa yaƙi,yanzu haka zuciyar sace ta buga bashi da wani sauran lokacin sai wanda ya ubangiji ya tsara masa but i'm sorry to say zai wahala ya tashi zuciyansa yaje matakin ƙarshe ta tashi daga aiki".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shine kawai abinda Papi ya shiga faɗa gaba ɗaya jikinsa rawa yake kansa ya ɗura kan table ɗin dake kusa dashi idanunsa na fitar da wasu ƙwalla na tausayin kansa da kuma ɗan nasa.
Ammi kam tsoran da yay mata yawa ne yasa yawa ne yasa ta kasa cewa komai kukanma ya tsaya gaba ɗaya sai kanta data ɗaga sama tana tunani.
Miƙewa Papi yay kai tsaye special room ɗin da aka kwantar da Faisal ya nufa yanz ya gansa kwance flat gaba ɗaya jikinsa na'oruri ne sai ƙara suke hannunsa ɗaure da drip,zama yay gefen bed ɗin tare da riƙe hannunsa cikin muryar kuka Papi yace.
"Son kada kayimin haka dan Allah ka tashi ka faɗamin damuwarka wlh wlh na ɗauki alƙawarin cika maka ita da dukkan aƙarfina lafiyata aljihuna dan Allah ka tashi na tsani ƙwanciyar nan"ya faɗa lokacin da kuka ya ƙwace masa,ƙansa yaji an dafa hakan yasa Papi saurin ɗaguwa cikin farin cikin ganin Faisal na mutsa hannunsa,hannun ya kama ganin rubutu a tafin hannunsa ya sashi riƙe hannu abinda yaga an rubuta ya sashi saurin runtsa idanun ko shine ya nuna masa ba dai ba,a fili Papi ya ƙara duba rubutun.
"I want see her,my eyes want to see my Lili,i knew she's alive itane damuwata pls".
Cikin damuwa da kuma aro jarumta Papi yace.
"tabbas tunda zuciyanka yaƙi  baka Lubna ta rasu babu shakka akwai wani ɓoyayyen sirri akan hakan,zanje insha Allah zanyi ƙoƙarin naga na haɗaka da muradin ranka"yana faɗin hakan ya fice daga cikin room ɗin.



 JUYAYINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ