Sun ɗan jima a gidan kafin su ɗauki basket ɗin tare da yiwa Fauwaz sallama suka koma gida.
Da kuka Afnerh ta shiga gidan tana zuwa ta faɗa jikin Mama tare da fashewa da kukan cikin kiɗima ta fara tambayar abinda ya faru,cike da nutsuwa Fannerh ta shiga gawa Mama komai har rashin ko in kula daya nunawa Afnerh ɗin.
Da ƙyar Mama ta rarrashi a Afnerh tare dayi mata alƙawarin ita da kant zata amsar mata soyayyarsa.

*** ***
   Wajan satin Najma uku kenan gidansu Faisal dukkan wani jin daɗi Ammi na bata shi,amma batun farin ciki wajan Faisal babu shi kullum rashin kulawarsa gareta ƙara yawa yake.

Misalin 7 na dare shiguwarsa daga sallah kenan ya zauna a babban parlon gidan tare da kunna karatun Sudais cikin suratul Maryam,sosai karatun yake masa daɗi kuka yake sashi nutsuwa domin baƙin ciki da damuwarsa suna nan kwance ƙasan zuciyarsa saima abinda ya ƙaru.
Lallai Ƙur'ani haske ne aduk zuciyar data ƙawatu da son karanta shi kuma dukkan wanda ya dogarar da alƙur'ani bazai taɓa taɓewa ba.

Ƙamshin turaranta daya daki hancinsa shine kawai ya tabbatar masa data ƙarasu parlon ganin tare suke da Ammi ne ya sashi sakin fuskarsa tare da zubawa abin idanu gani yake kamar yau ya fara ganinta idanunsa da suka cicciko da hawayene yasa yay saurin ɗauke kai tare da faɗin"barka da dare my luv"cikin so da ƙaunar ɗan nata ta zauna gefensa tare da shafa sumar kansa tace"yawwa yaya aiki?"..."mungode Allah" shine kawai abinda yace..ɗaga kai Ammi tayi tare da faɗin Najma zauna ma..ruwan hawayen data gani kan fuskar Najama shine ya hanata ƙarasa abinda tayi niya cikin kulawa tace"lafiyanki lau?"wasu hawayenne suka ɓalle mata ta shiga girgiza kanta kafin ta durƙushe gaban Ammin tace"Ina son komawa gidanmu domin na gaji da zama da Faisal,banyi iskanci tun ina budurwa ba haka bazanyi ina matar aure ba,amma yasan da cewa nima mutumce kamar kowa kuma dole akwai haƙƙina daya rataya a wuyansa,bansan mai nayi masa amma baison haɗa gado dani😳hakan kuma illah ce wa rayuwata koda ace bashi da lafiya ya kamata ace ya faɗamin tunda niɗin matarsace bawai zaman dadiro muke dashi ba".

Ai maganarta tamkar saukan ruwan dalma haka yake jinsu cikin zuciyarsa baƙin ciki takaici ladama na aurenta babu wanda baiyi ba,hakan kuma ya tabbatar masa bata da kunya ko kaɗan sannan ita ɗin ba matar sirri bace,cikin ɓacin rai Ammi ta kalli Faisal wanda idanunsa yake a rufe ruf tamkar maiyin bacci tace.

"ka tabbatarmin niɗin ban isa da kai ba kuma baka ɗauki maganata da muhimmanci ba,ka sani indai ni nayi cikinka nayi naƙudarka kuma na shayar dakai ruwan nono a yau basai gobe ba nakeson ka bawa Najma dukkan wani haƙƙinta da yake kanka idan kuma ba haka ba wallahi Faisal zan sallamawa duniya kai badan kaga mahaifinka baya nan ba kakemin wannan abun to kaje dani dakai za'aga wanda zaici riba".

Idanunsa ne yay jajur tamkar gauta sosai kalaman Ammi suka daki ƙawon zuciyarsa meyasa Ammi ba zatai masa uzuri ba?mai yasa ba zata fahimci zafi da raɗaɗin abinda yake damunsa ba? Mai yasa ba zata fahimci abinda zuciyarsa da gangar jikinsa suke muradi ba? Runtsa idanunsa yay da ƙarfi tare da miƙewa cikin zafin rai ya kalli Ammi yace

"zanyi dukkan abinda kikeso koda bakan zai baƙanta raina,zanyi abinda kikeso Ammi koda zuciyata zata buga,zanyi abinda kikeso koda hakan zai zama sanadiyar rasa raiana,tabbas inajin hakan shine ƙaddararta kuma shine silar rasa raina,zanbar duniyar kamar yadda Lubna da iyayenta suka bari inaji a raina I think my Lubna is calling me, I think it's time to go  tabbas lokacina na zuwa wajan mahaliccina yay Ammi kuma insha Allah indai kece kike haifeni kika kula dani da yardar ubangiji bazan bar duniyar nan ba saina tabbatar maki da kalamanki zanyi tabbas zanyi abinda kikeso Ammi"

Yana faɗin hakan yasa hannu ya riƙe Najma tare da janta da sauri a haka suka ƙarasa flat ɗinsu,tsoro da fargaba gaba ɗaya sun cika zuciyar Najma babu kalaman da suma tsaya ma sai "tabbas zabar duniyar kamar yadda Lubna da iyayenta suka bari"me hakan ke nufi wace duniyar zai bari? Ina zaine'inane inda Lubnan da iyayenta suka tafi"tambayoyin da suke zuciyanta kenan amma babu wanda zata tambaya ƙara ta saki sabida cillata da yay kan gado kanta ya daki fuskar bed ɗin a zafafe ya cire rigar jikinsa tare da long jeans ɗin dake jikinsa ya rage daga shi sai boxer cikin saurin ya faɗa kan gadon,babu ɓata lokaci ya zare zanin dake jikinta babu wani romance haka yay bisimillah tare dayin Addu'a ya shiga jikinta.
Zafin da raɗaɗin da ta jini yasa ta fasa wata mahaukaciyar ƙara ta shiga ya ƙushinsa tare dayi masa Allah ya isa ganin hakan bazai mata ba ta shiga cizonsa tare daya ƙushinsa.
Faisal bai rabu da ita ba saida yay mata lilis yay mata fata-fafa sannan ya zare jikinsa tare da sakin wani mahaukacin kuka kamar mace sunayen Allah ya shiga kira tare da salatin Annabi hannunsa dafe da saitin zuciyarsa wata bugawa da zuciyarsa tayine yasa shi faɗin "La'ilah ha'illahu  Muhammadur Rasulillah" wani gudan jinine ya fitu ta hancinsa da bakinsa lumshe idanunsa yay yana mai ƙara jadadda sunayen Allah a zuciyarsa,dai² lokacin da Ammi ta buɗe ƙofa ta shigo yay dai² da lokacin daya saki wata shaƙuwa mai ƙarfi.
  

    *Dan Allah dan Annabi kuyimin share dan Allah wlh bbu lokaci groups sunmin yawa sai kuna taimakawa🥰👏🏻luv u all*

Team Najma
Congratulations🤾🏻‍♀️💃🏻

 JUYAYIWhere stories live. Discover now