Numfashi ya fitar tare da ɗaure fuska ganin kallon da take masa,lumshe ido yay sosai maganar da yay tayi masa kafin ƙara saki numfashi tare cije lips kana ya ware laɓɓansa tare da faɗin.
"mai yasa kika zama mai butulci wa Ubangiji?ya baki komai na rayuwa sai ɗan wani buri dake banne a zuciyarki amma ki kasa yiwa ubangiji tasbihi da kuma neman sauƙi daga wajansa,nayi tunanin kina da hankali ashe sakalyace?kulna ƙarajin kuka domin baya maganin damuwa akwai dubban mutanan da suka fiki shiga damuwa da kuma ƙuncin rayuwa su kuma suce me?idan mutum bai gode ni'imar Ubangiji ba amma ya gode azabarsa,ki zama mai ta wakkali kuma me yarda da ƙaddara ki ɗauki hakan matsayin ƙaddararki da ubangiji ya jarabceki da ita danya gwada imaninki kinji ko?

    Ajjiyar zuciya ta shiga saukewa tare da zure jikinta waje guda tare kafa masa idanunta tana ji dama ta dauwama a haka tana kallon baiwar zati da kuma surar da ubangiji yay masa.
Raguwar ruwan daya zuba mata ya kafa a bakinsa ya shiga ƙwanƙwaɗa saida ya shanye tas sannan ya cire gorar ruwan daga bakinsa.
A fili ya saki ajjiyar zuciya sosai ruwan yay masa daɗi maƙoshi tare da magana a zuci"Rabbi ka shayar damu ruwan alkausara".
Cikin nutsuwa ya juya tare da zama a kan duguwar sofa ganin gaba ɗaya ya gaji ga wani bacci daya keji ne ya sashi ware idonsa tare da mannasu a kan Fannerh wacce ta zubawa Afnerh ido domin sosai ta kejin tausayin ƴar uwarta ta, saukar muryarsa data jine ya sata ɗago kai tare da zuba masa ido dan baza taɓa iya cewa taji abinda yake faɗa ba.
Ya tsuna fuska yay tare da ɗauke kai ya maida kallonsa wa Afnerh wace take zauna ko mutsi ba tayi sai ajjiyar zuciya take saukewa a kai²,Tausayin tane ya kamashi cikin taushasshiyar murya yace.
"mai kuka aban abinci ina jin yunwa"cikin sauri Afnerh ta miƙe jikinta har rawa yake dan ba tayi tunanin hakan a wajansa ba,kallo ɗaya tayi masa ta fahimci shiɗin mutum ne wanda bai damu da magana ba sannan shiɗin miskiline uwa uba girman kai amma sam bata damu da hakan ba indai zai nuna mata ƙauna zai zauna da ita zata iya jure duk wata halayya tashi.
Basket ɗin abincin ta ɗauka tare da ƙara sawa inda yake zauna tana zuwa ta zauna ƙasan sofar  tare da ɗaukan plate ta buɗe wata wamer nan ƙamshin abincin ya daki hancinsa cikin saurin ya lumshe idanunsa wanda hakan ya zame masa ɗabi'a.
Zallar chips ɗin tare da ɗaukan wani glass cup ta  siyaya masa fruit salad ɗin,cikin rawar murya tace"gashi"yi yayi kamar baiji abinda ta faɗa domin ya fahimci itama bata son magana sosai.
Turo baki tayi kamar zata fasa ihu tace"the food is ready"ware manyan dara-daran idanunsa ba tare daya kalleta ba ya zamu da ƙafarsa ƙasan sofar tare da sakkowa ya zauna a kan capert bai damu da zaman da yay kusa da ita ba,dan ko ajikinsa impact  bai ɗauketa wata babbar macen dazai damu kansa danya zauna musanta halima shi mata duk kallon maza yake babu wata macen da zaiji wani feelings a kanta.
Zamansa kusa da ita yasa taji wani mugun shock ya kamata take wutar sonsa da ƙaunarsa ta ƙara huruwa cikin zuciyarta,tabbas ya cika namijin da dukkan wata ƴar mace ta ganshi za taji ƙaunarsa a lokaci guda,ware ƙofar hancinta tayi tana ƙara shaƙar ƙamshin dake fita daga jikinsa a sanyaye tayi magana yadda shine kawai zai iya jin abinda ta faɗa banda Fannerh da take tsaye sai kuma Fauwaz wanda zuwansa gidan kenan.
"kai ɗin gwarzu ne"
Girgiza kai kawai yay tare dayin bisimillah ya saka zara-zaran ya tsunsa tare da fara cin abincin,Fannerh tunu taja basket ta zubawa habibinta abinci sunayi suna shira.

Fahad bai wani ci abincin da yawa ba ya ture ko fruit salad ɗin bai sha ba ya miƙe tare da shigewa cikin toilet ya ɗauki lokacin kafin ya fitu suna zaune ya fitu sanye da bathrobe jikinsa na ɗigar da ruwa a haka ya ƙarasu wajansu tare da kallo Fauwaz taɓe baki yay shi a dole soyayya yake cikin ransa"ƙaddararka soyayya da underage"a fili kuma yace "boddy goodnight"ɗaga kai Fauwaz yay tare da murmushi kafin yace"Na ɗauka zakuyi hira da Afnerh"kallonsa yay da alamar tambaya sai kuma yace"wani abune haka?"dariya Fauwaz yay tare da kallon Afnerh wacce take turo baki gaba tare da fidda wasu sabbin hawayen ɗauke yay tare da faɗin"eh wata abace gata nan a bayanka ai"tsaki Fahad yaja dan ardy yasan wace Afnerh ɗin tun ɗazu yaji sister ɗinta na kiran sunanta,baice masa komai ba ya juya zai shige bedroom ɗinsa tayi  saurin miƙewa tare da sakin kuka danji take zuciyarta kamar  zata fashe,waro manyan idanunsa yay ganin kuka baya yi mata wani ƙawataccen murmushi yay lokacin daya tuna da Lili ko magana ce bata gamsheta ba yanzu zata saka maka kuka harda birgima bare kuma faɗa cije lips ɗinsa yay tare da ware laɓɓansa a fili yace"i'm still waiting for u my sunshine bby"jin haka yasa Afnerj da katawa da kukanta tare da zuba masa idanu ta gefenta ya huce ko ƙara kallonta baiyi ba.

 JUYAYIWhere stories live. Discover now