RIKICIN MASOYA

Von Ruky_i_lawal

225 16 6

labari ne na wasu masoya guda biyu masu matukar k'aunar junansu duk da yawan Rikici da rashin fahimtar juna d... Mehr

page 31
page 32
page 32
page 33
page 34
page 36
page 37
page 38

page 35

10 0 1
Von Ruky_i_lawal

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

DEDICATED TO: BESTIENA MARYAM NASIR(MANAB YAR BABA) & SISTER JANNAT M NASIR

WANNAN PAGE KAM NAKU NE SAI YANDA KUKA SO YI DASHI.

BESTINA MANAB INA MIƘO GAISUWA TA MUSAMMAN, DA FATAR ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKI YA TSARE MUN KE A DUK INDA KIKE.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣5️⃣

Afrah ce ta shigo falon da yake cike da mutane.

Bayan y'an gaishe-gaishe tsakaninta da mutanen falon, ta wuce kai tsaye zuwa ɗakin Sabreen.

Isarta ya yi dai-dai da lokacin da Anty Jidda ke ƙoƙarin fitowa riƙe da roba wacce take ɗauke da kayan gyaran jikin amarya a hannunta, ga dukkan alamu gyaran jikin ta gamawa Sabreen.

Gaisawa suka yi da Antyn sannan ta shige ciki.

Can ta hango Sabreen ta kifa kanta a kan gado, ta na kuka mara sauti, da ya ke dama ta na zaune ne a gefen gadon.

Ƙarasawa Afrah ta yi haɗe da dafa ta, a ɗan razane ta juyo don ganin ko waye.

Ganin Afrah ce ya saka ta juyo gaba ɗaya tare da saka tafin hannunta ta goge hawayenta.

Zama kusa da ita Afrah ta yi gami da riƙo hannunta ta ce "Ki yi haƙuri ƙawata,  insha'allah komai zai zo ya wuce kamar ba a yi ba, kuma insha'allah za ki tsinci farinciki a rayuwar aurenki nan gaba kaɗan."

Zare hannunta ɗaya ta yi ta kai saitin fuskarta tare da ɗauke guntuwar ƙwallar da ta zo mata ta ce "Dole na yi kuka ƙawata, ni da kaina na rusa farincikina, ban taɓa tsammanin soyayyar Asim ta yi girman da za ta iya saka ni cikin irin wannan gagarumin tashin hankali ba, sai yanzu da na rasa shi, na san ba zan taɓa samun nutsuwa ba in ba shi, ni fa ina ji da an ɗaura auren nan mutuwa zan yi..."

Hannu Afrah ta kai ta yi saurin rufe mata baki, ta na faɗar "Kul, kada ki sake zancen mutuwan nan, insha'allah ba za ki mutu ba sai mun ga ƴaƴanki ke da Asim."

Y'ar dariyar jindaɗi ta yi, duk da ta san cewa Afrah ta faɗi hakane don ta faranta mata.

Nan da nan kuma fuskarta ta sauya zuwa damuwa kamar ba ita ce ta gama dariya yanzun nan ba, ta ce "Don girman Allah Afrah ki taimaka min, ina son sanin halin da Asim ɗina ya ke ciki, domin na ga tashin hankali ƙarara a fuskarsa a ranar da na masa gani na ƙarshe, ki taimaka min ki haɗa ni da shi asirrance."

Ajiyar zuciya Afrah ta sauke sannan ta ce "ya na asibiti fa, bari mu gani ko zan same su."

Wayarta ta ciro da zimmar kiran mijinta, kawai sai ga kiransa ya shigo, sai dai vidio call ne da yake ta manta datar ta abuɗe shiyasa.

Ɗagowa ta yi suka haɗa ido da Sabreen, sannan ta mayar da hankalinta kan wayar.

Bayan ta ɗaga sun gaisa ne ya ke cewa "Wifey don Allah ki kaiwa Sabreen wayar, Asim ne ya dame ni da cewa na taimaka masa ya ji muryan ta na ƙarshe, ya na so su yi bankwana ne."

Afrah ta miƙe zuwa ƙofa ta na faɗar "Ni ɗin ma wannan roƙon ta gama yi mun har zan kira ka sai kuma ga kiranka."

Ta na gama faɗa ta saka kubar ɗakin sannan ta dawo inda Sabreen take ta miƙa mata wayar ta na faɗar "Ga shi Asim na nemanki."

Ai tun bata gama rufe baki ba Sabreen ta warce wayar.

Ya na ganin ta karɓi wayar ya miƙawa Asim wayar, ya zagaya ta bayansa ya saka masa filo a bayansa, yanda zai ɗago sosai ya ji daɗin hirar.

Fuskar Asim ta bayyana a screen ɗin ya yi baƙi ya rame duk ya fita a hayyacinsa, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai don zuciyarta ta tsinke har ta fara hawaye.

Cikin matuƙar ƙarfin hali Asim ke kallon yanda kyakkyawar Babynsa ta sauya cikin ƙanƙani lokaci, shi da kansa ya tabbatar cewa ita ma ta na cikin matsananci tashin hankali.

Aka rasa wa zai fara yin magana a cikinsu, zuwa can Asim ya ce "Babyna baki da lafiya ne? Na ga kin rame?"

Bata ba shi amsa ba, kawai sai ta fashe da kuka ta na faɗar "Don Allah Asim ka yafe min, na cuci kaina na kuma cutar da kai, duk da kai ne silar faruwar komai, amma zuciya ce ta ɗebe ni ta saka na yi gangancin amincewa da abinda ya saka ni a garari, ka yafe min masoyina ka yafe min, har abada ina sonka Asim."

Shima ƙwallar ce ta fara gangaro kallonta kawai ya ke, sai da ta dire zancenta sannan ya ce "Ba ki mun komai ba Babyna, asalima ni ne mai laifin, ni zan nemi yafiyarki, don Allah ki yafe mun, ba na so na tafi da haƙƙin kowa akaina musamman ma ke, domin ina tabbatar miki ana ɗaura auren nan za ku rasa ni, mutuwa zan yi ba zan iya jurar ganinki a gidan wani ba..."

Ya na kainan kuka ya ci ƙarfinsa, akan dole ya yi shiru.

Itama kukan ta ke sosai ta ce "Na yafe maka masoyina, har abada ka na raina, ko da ya aure ni, tabbas gangar jikina ya aura domin ruhina ya na tare da kai."

Numfashi ta sauke da ƙarfi sannan ta cigaba "Don Allah kada ka mutu, ka bani lokaci, sooner or later zan dawo gareka, ni kaina ji nake kamar zan mutu...."

Ita ma bata yi nasarar ƙarasawa ba, saboda kukanta da ya tsananta.

Afrah ce ta taso ta ƙwace wayar tare da katse kiran, ganin abun ba na ƙare ba ne, ga shi ta ji a na ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

Ai kuwa kamar ta ce Sabreen ta ƙara volume, Nan ta ware iya muryarta ta na kuka tare da bubbuga ƙafa kamar wata jaririya.

Sosai kanta yake matsanancin ciwo saboda kukan da ta sha.

Rarrashinta Afrah ta yi akan ta daina kukan saboda jama'a dake falo, sannan ta rage volume.

Afrah ta je ta buɗe ƙofar tare da ficewa daga ɗakin tun kafin wani ya zargi wani abu.

©©©©©©%%

Ana saura kwana uku bikin Umma ta tattara amarya da tarkacen ƙawayenta, ta tura su gidan Baba Babba dake sharaɗa da yake can za su zauna har agama bikin saboda gidansu ya yi kaɗan da biki, can kuwa babban gida ne sosai.

Ba wanda a ka bari a mai dile sai Umma da ƙawayenta da y'an uwanta da suka zo taya ta murna.

An so a yi shagali sosai a bikin,amma ganin cewa amarya bata cikin walwala ya saka a ka taƙaita, kamu kawai aka yi, nan ma sai da a ka sha gwagwarmaya kafin Amarya ta yarda ta je gurin taron, amma duk da haka sai da ta ɓata musu biki, domin ta yi abinda kusan kowa ya fahimci ba ta son auren nan a bayyane.
@@®®©©©©©

Ranar ɗaurin aure da safe, Sabreen ce zaune a ɗakinsu Mubeena(ɗaya daga cikin ƴaƴan baba Babba) y'an mata uku sun saka ta a tsakiya, sai tsiya suke mata iri-iri, ita kuwa ko kallo basu ishe ta ba damuwa ta mata yawa, fatanta kawai su bar mata ɗakin.

Zee(ƙanwar Lily) ce ta ce "Habah! Anty Sabreen ki saki ranki mana, ni fa ban taɓa ganin amarya na baƙin rai ba sai a kanki." Ta ƙarashe zancen ta na Yar dariya.

Suma sauran y'an matan dariya suka yi ba su ce komai ba.

Mubeena ce ta sauko daga kan gadon ta na faɗar "Uhmm! Ni ba amarya ba sai zama da yunwa, bari na tashi na je na nemo abinda zan sakawa cikina." Da fara'a a fuskarta take zancen, ta na gama faɗa kuwa ta fice ba tare da ta jira cewar su ba.

Zee ta kalli a gogon dake manne a ɗakin tare da ɗan fito da ido ta ce "Lah! Wai har tara ta yi? Cab bari na tashi na je zuwa shirya abincin angwaye, kafin ya Lukman da yaya Jb su zo su balbale ni da masifa." Ita ma miƙewa ta yi ta fice a hanzarce.

Yanzu ya rage saura Saliha da Sabreen a ɗakin, Alla-Alla Sabreen take Saliha ta fice daga ɗakin kafin sauran su dawo amma shiru bata da niyyar tashi.

Sun fi mintuna goma zaune a hakan ba mai cewa wani uffan, can Saliha ta miƙe kamar an tsikare ta komai ta tuna oho, kawai sai ta fice daga ɗakin a hanzarce ba tare da ta samu damar yin magana ba.

Ai kuwa Sabreen ta miƙe da sauri ta je ta saka kubar ɗakin, dama jira take su gama ficewa.

Ta na sakawa ta dawo kan gadon ta yi rashe-rashe ta na ruzgar kuka a take kanta ya fara ciwo mai tsanani.

Ta ma rasa tunanin me za ta yi ta ji daɗi, duniyar gabaki ɗaya ta fice mata a rai.

©©©©©©©

Kowa ya shagala sai hidima ake, ba wanda ya san halin da Sabreen take ciki.

Ƙarfe goma dai-dai na safe a ka ɗaura auren Lukman Zaid da amaryarsa Sabreen Salis Mu'az, a ƙofar gidan Baba babba.

Zo ka ga farinciki a gun Lukman abun ba a cewa komai, yaya Jb ne ya kira Ummansu don sheda mata ɗaurin Auren.

Kabbara Umma ta yi ta ce "Allahu Akbar! yau dai Allah ya cika min burina na aurar da ƴaƴana ga junansu, wannan Albishir ne mai daɗi idan hankali ya kwanta Jabir ka zo ka karɓi tukuicinka."

Dariya Jb ya yi ya ce "Allah umma? Da gaske wai za ki ba ni tukuici?."

"Ƙwarai da gaske kuwa Jabir, sai ma ka zaɓi abinda ranka ya ke so, irin wannan Albishir haka?." Ta faɗa cikin tsananin murna.

"Wow! Shikenan Ummarmu sai na zo." Ya na gama faɗa ya kashe wayar ya nufi cikin gidan.

Jb ne ya shigo gidan, a waje ya tarar da Mubeena gun murhu ta na duba abincin da ke kan wuta, ya kalle ta ya ce "Sannu da aiki yayar amarya kuma ƙawar amarya?"

Dariya ta yi sosai ta ce "Yawwa sannu babban yayan Amarya."

Y'ar dariya ya yi shima sannan ya ce "Ina amaryar tamu ne?, je ki fito mana da ita za mu yi hotunan tarihi.

Sai a lokacin ta tuna  ta bar ta a ɗaki tare da su Zee domin ita tun da ta fito bata koma ɗakin ba.

Cikin hanzari ta nufi ɗakin ta murɗa handle ɗin kofar, sai dai me? Ƙofar a rufe take ruf, da alama an saka kuba daga ciki, ga shi ta na jiyo sheshsheƙar kuka a ciki.

Ɗaga muryarta ta yi ta ce "ya da rufe ƙofa kuma, Amarya buɗe mun, an ɗaura auren fa, ku fito za a yi hotuna da angwaye."

Ai kuwa Sabreen na jin zancen ɗaura aure ta miƙe zumɓur daga kwancen da take ta fara ihu tare da fashe-fashen abubuwa tamkar hauka sabon kamu.

Jin ƙarar fashewar abubuwa ya ankarar da su Zee da suke shigowa yanzu, da gudu suka ƙaraso ƙofar su na faɗar "Mubeena me ke faruwa? Waye a cikin ɗakin."

Ita ma tambayar ta watso masu "Yaushe kuka fito daga ɗakin? Hakan na nufin Sabreen kaɗai a ka bari a ciki? Ba shakka ita ce, Saliha kira mana su hajiya, mun shiga uku."

Hankali a tashe take zancen, su ma hankalinsu ya tashi, jin abun na ƙara yawa sai ƙarar ƙumuwar abu da bango suke ji, ashe kanta take bugawa da bango tun ƙarfinta.

Da gudu Saliha ta wuce ta kira su Hajiya Babba, sai ga su tare da yaya Jb sun iso gurin a guje.

Nan fa a ka shiga roƙar Sabreen a kan ta buɗe ɗakin, amma ko saurararsu bata yi ba, sai ihu take kamar zararriya ta na sambatu kala-kala.

Faɗar ta ke "Ni ku ƙyale ni ku bar ni na mutu, tunda ba ku damu da rayuwata ba, kun fi son Lukman a kaina, masoyina ne ya na can zai mutu amma don rashin imani ba wanda ya damu da rayuwarsa a cikinku."

Ganin tashin hankalin ba mai ƙarewa ba ne yasa Hajiya ta kirawo Abba da su Baba Babba, shiko Jb ya kira Umma hankali tashe ya sanar mata.

A na cikin hakane shi ma Lily ya shigo ciki a ruɗe domin labarin ya je kunnensa, nan fa tashin hankali ya dawo sabo domin shima zubewa ya yi a ƙofar ya na roƙonta da ta buɗe ya na kuka faɗar yake "Don Allah my angel ki buɗe ƙofar, me ya yi zafi haka? Ki buɗe ka da ki illatar mun da kanki, ba zan iya jura ba, duk abinda na yi na yi ne saboda soyayyarki da ƙaunarki, ba zan iya zuba ido wani banza ya zo ya aure ki ba bayan ina sonki, duk abinda na yi na yi ne tare da taimakon Umma da take goyon bayana a lamarin."

Nan fa kallo ya koma sama, duk a ka zuba mi shi ido a na kallonsa ya na ta tona abinda ya yi.

Daga ciki Sabreen ke faɗar "Da kyau! kun kyauta, yanzu ai ga ni sai ka ci uwar da za ka ci da ni, amma ina mai ƙara jaddada ma, gangar jikina za ka aura ruhina ya na tare da Asim, Kuma Ina ma kashedi na ƙarshe ka da ka ƙara kiran masoyina da Banza shi ba banza ba ne."

A dai-dai Lokacin Umma ta iso ƙofar ɗakin da yake dama ta na hanyar zuwa Jb ya kira ta.

A ruɗe ta isa gun ta na faɗar "Don girman Allah Sabreen ki buɗe ƙofar nan, duk iyayenki ne a nan, gamu mun taru muna roƙarki shin ba za ki haƙura ba?"

Ɗaga murya ta yi sosai, dai-dai yadda Umman za ta jiyo ta da kyau, ta ce "Habah Umma! ya da roƙona haka? Kin manta ke kika yi ruwa ki ka yi tsaki a auren, duk da kin fi kowa sanin ba na so? Me Asim ya tsare maki da ba kya sona da shi? Tarbiyya ce ba shi da, ko kuwa ya maki wani abun ne da ni bansani ba shiyasa kika tsane shi? Umma bakya sona tunda har bakya son abinda nake......."

Follow me on Wattpad @ummu inteesar.


UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Weiterlesen

Das wird dir gefallen

215K 10.3K 55
My name is Alex Cruz, I'm a omega, so I'm just a punching bag to my pack. But Emma, Queen of werewolves Sam, queen of dragons Winter, queen of vampi...
16.4K 704 8
Oc female Jackson x Hermes x Apollo x Ares
8.4M 502K 64
The fiery sequel to Death Is My BFF Rewritten and 2016 WATTY AWARDS winner... The book you should read before this one is "Death is My BFF Rewritten...
15.2K 294 7
Meri nayi nayi shadi hui hai. main 19 saal ki hu. mere sasural wale bohot shareef hai lekin na jane kyu kuch dino se badal se gaye hai.