TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

Oleh 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... Lebih Banyak

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 22

2.8K 278 26
Oleh 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

               22

Acen ma hakan ce ta kasance, zubewa tayi tana rero uwar gaisuwa

"Allah ya taimaki mahaifiyar me mulkin masarautar Hankaka, Allah ya k'ara girma, ina neman afuwan rashin zuwa in gayar dake kwana biyu, jiki da jini ciwo nayi" Murmushi tayi

"Babu komai 'yata, hakan ma ba laifi bane ki huta shine fatanmu, karki wahalar da jikinki" Murmushi tayi ta sadda kanta k'asa tana me jiran k'ara cewarta.....kyautata mata wurin zama akayi aka wadata gabanta da kayan ciye ciye, ba laifi tad'an tab'a abubuwa sannan tanemi yi mata sallama, ajikinta ta kula kullum zoben hannunta yana nan ko wancen zuwa haka t tarar amma laifin liqawa a wurin wataqil dashi take wanka, Harta mik'e ta k'ara zubewa

"Hajiyar mu aduk b'angaroran masarautar nan nakula nan ne kurun yakeda cikar abubuwan k'awata d'aki na gargajiya, wani lokacin idan na k'ara zagowa zanso kuyangi sumun iso inga kayan tarihi" murmushi Hajiyar rusau tayi

"Da zaki iya k'ara lokaci aida na rakaki da kaina yanzu" k'ara duk'ewa tayi k'asa hannayenta biyu asaman carpet datake zaune  tana me k'ask'antar da kanta

"Ban isa na saka mahaifiyar Hankaka kaf d'inta zagaye ba, tuba nake hajiyar mu, a had'ani da kuyangi" murmushi tayi ta mik'e ta rik'o hannunta ta mik'ar da it tsaye sannan tace

"Nice nake sha'awar yin hakan, kodai kishine abin, kuma me gidan aiya tafi abinsa" murmushi Meenal tayi suka rankaya don zagayen wurin seda suka zaga sosai sannan ta kaita d'akinta cenne yafi abun kallo na gargajiya wannan matar akwai tanadi, duk dukiyar daka b'angaren Dakuna biyune da parlor biyu kcal keda kwalliya irinta zamani duk sauran gargajiya ce, hannunta takai wurin wani abu da ake kira lefe ta shafeshi tare d'ana 'yar matashiyar recoder a d'akin, wacce bazakayi saurin gane waba

"Hajiyarmun ina san wannan abun" murmushi tayi

"Wannan kakatace ta bani akwai wanda mahaifiyata ta bani kizo muje zan baki"

"Laa ba komai hajiya shima me muhimmancine ki ajiye" Batai maganaba suka fito daga d'akin a d'ayan d'akinma tayi nasarar mannawa har wuri biyu

Haka tayi mata sallama sannan ta koma b'angarenta.

************
   Zirga zirga Nusy keyi  tsakiyar d'akinta tamkar me yunk'urin nak'uda tana tunanin yanda akayi Meenal ta ganta, kodai tasan wani abune game da ita? Kai ina bazata sam komai ba, tanayin komai ne cikeda nazari, to kodai kurun taganine btasan ko meye? To ina zata sani tunda ba kowa yasan abunba ma wannan sokuwar, koda yake har yau tana tunanin inda tasan yarinyar kman ta santa, bata tunano komai ba, yanzu ina zata k'ara d'ana masa tracker? Motocin hawan takawa sunkai sha biyar yana masifar san  mota, to Amma akwai motr excort nashi dasam baya fita seda ita haka zatayi, ajikin motar zata saka kurun sabida tanada buk'ara yin aiki a b'angaren sa, dole t d'ana bama bamanta bataso meenal tayi wani dogon sabo da Takawa daze kaita ga kasa  aiwatar da shirinta akan ta, matakin su na farko ze soma aikine daga yau sabida tsaro.

***********
   Washe gari shirin asuba tayi ta jere kuyangi zuwa b'angaren Takawa, Excort nashi ta tarar da fadawansa, malmo ce tace

"Asanar wa Takawa Sawunsa tana nan iso sarkin fadawan Takawa" wani security ne yace

"Yace ya dawo sallah kar wanda ya tashesa se sanda ya fito" Shiru sukayi Meenal kuwa ta taka har inda yake tace

"Zan shige bani hanya" Kwarjini ta masa amma be d'aga ba tace

"Acikin biyu wanne ka zab'a, kawa Takawa rashin kunya ka hanata hanya kokuma kabarta ta shige ta kareka akan ita ta matsa" kalon juna sukayi shida d'an uwans suka janye wasu dogwayen takubba na mayak'an da dasuk gitta ta shige seda tad'an taka sannan ta waigo tace da kuyanginta

"Kuje ko wacce ta kaiwa waninta ziyara adawo k'arfe sha biyu na rana"  godiya sukayi sannan suka juya kowacce dama tana jiran irin wannan  damar tayi abinda take ganin shize fitar da ita....

  Kai tsaye inda take tsammnin nanne bed room d'insa ta nufa, da sallamar ta ta shiga sedai ta tarar ya rage hasken fitilar d'akin se deem light kurun alkyabbar jikinta ta zare ta rage kayan nauyi tukunna ta shige ban d'akin sa, Ba laifi akwai wadatacciyar tsafta k'ara gyarawa tayi sannan ta wanke wasu tsirarrun boxers da singlet data gani da wasu handkerchiefs ta shanya awurin dataga an tanada donsu, fitowa tayi tashige duka sauran d'akunan ta gyare ko ina sannan ta shiga kitchen tasha dariyar ganin yanda yake a harkitse tasha wahalar gyaranshi sosai seda taga komai k'alk'al sannan ta juya gefen kayan abinci duk wani abu daya lalace t cireshi a fridge dasu albasan dasuka rub'e ta jefar  a wani buhun semo ta zuba komai ta bud'e k'ofa ta baiwa wasu Fadawansa su zuba, lokacin sha d'aya tayi ta shige kitchen d'in ta masa lafiyayyan girki sabida komai akwai a part d'in abu d'ayane ya takura gidan shine rashin mace aciki, ga alama ko girkin namijine keyi da kansa,seda ta jere komai a dining sannan ta koma d'akin wanka tayi har lokacin bacci yakeyi kayan data cire ta mayar sannan ta koma b'angarenta lokacin k'arfe d'aya na rana tayi ma.

    Koda ya farka seyaji k'amshin dayasn ba nasa bane amma yakanji jiyo k'amshin jikin wani makusan cinsa kodai mafarki yakeyi?, mik'ewa yae zuwa ban d'akin nanma yasha mamakin ganinsa k'alk'al  ko ina yayi fesfes ga k'amshi me ratsa zuciyar me shak'ar sa ya kwantar masa da hankali...yaga kayansa asaman hanger a shanye yasan yace kar wanda ya shigo masa zazzab'in mura yake fama dashi, magani yasha mesa bacci shisa yaketa bacci tamkar gawa, ya gayawa Amoh ta dena turo masa komai daya shafi kuyangin nan kar suyi poisoning nashi, ya iya  girkinsa daidai gwargwado ze iya d'an gyaran gidan sabida tsaro.....wanka yae sannan ya fito daga d'akin yasha mamakin ganin komai qalqal idanshi na kaishi dining ya gano k'amshin abincine yakeji, k'ofa ya bud'e  kira wani daga cikin bayinsa

"Waya shigo nan part d'in? Ya buk'aci sani

"Sawun takawo ce ta kawo ziyara kuma bamu isa mun hanata shiga ba" Jinjina kanshi yae yana murmushi, aranshi yace wato tanan ta b'ullo abincin ya bayar duka sannan yasha tea daya had'a da kansa, yabar gidan...

********* wuraren k'arfe biyar aka aiko tafiya da sawun takawa b'angaren sarauniya hassy, yana kallon sanda suke wucewa yae murmushi danshi bega amfanin wannan ba, Acen kuwa wanka akai mata da ruwan turaruka masu tashin hankali, bayan nan aka cika wani tsohon baho da ruwa aka sakata, yasha flowers masu alasin k'amshi da dad'i, tayi awa d'aya aciki harta k'osa a fitar da ita, hankalinta sosai yake a tashe jin abinda tajiyo datake sauraren recordings na duk maganar da akeyi a inda takai abin recording d'inta, acikin ruwa take amma gumi sosai take had'awa sabida tsoro, ta tabbatar masarautr nan akwai munak'isa acikinta, wanda kakewa kallon masoyinka ma bakasan meyake maka tanadi ba, tabbas makashinka na gindinka.

An shirya sosai Nakai amarya d'akin mijinta, an gama shirya komai shima kuma yasha shiri sosai zuciyar sa ba dad'i se baya take kaishi yana tunano angwancinsa da Salma abar sonsa ko guntun murmushi babu  fuskar sa....

************
   "Na gama shirya komai, daga zaran an kaita ka aika message d'in kakuma dinga kiranta kamar ba gobe, tuni anyi saving number wayarta As Maryam acikin wayarta, yanda ze k'ara yadda b'oye lambar tata takeyi" Wata dariya wanda ake gayawa maganar yae

"Bakida matsala hajiya wannan duk me sauk'i ne zanma k'ara da maganganu masu rikitarwa sabida tada hankalin 'yan mazan, tun yaushe muke jiran wannan chance aikoda wasa bazanyi wasa da wannan damar ba" Murmushi sukayi du kansu kansu ajiye wayoyinsu.

***********
    Se wuraren k'arfe goma na dare sannan aka kaita d'akinsa, Tunawa tae da maganar sarauniya Hassy sanda ake shirin fitowa da ita

"'Yata ki rik'e martabarki karkiga kamar ba daga wata masarautar kike ba kije ki aikata abinda 'ya'yan talakawa ke aikatawa, ki nutsu sosai komai yawan abinci da aka kai maku karki ci, al'dace shima kanshi mijinki ze duba wannan martabarki ta k'aru agunsa, shisa kikaga seda nacika miki cikinki tukunna" Murmushi tayi ita kanta k'amshin jikinta yana mata dad'i  amma tana cikeda fargaba, gyaran zamanta tae acikin alkyabbar data mana nauyi tasha zinarae tako ina, sanda tajiyo sallamar sama sadda kanta tayi a k'asa ya zauna, Kalolin abincin da aka jere masa yake kallo, harga Allah yunwa yakeji, kallonta yae

"Daga B'angaren wa wannan abincin yake" kasa bud'e bakinta tayi tae magana, se kai data gyad'a masa kurun alamun bata saniba" zama yae ya soma k'ok'arin zuzzuba abincin don yaci, kallonta yae yaga har lokacin kanta a k'asa, ya kula gumi ma se d'igowa yake daga cikin hular alkyabbar ta, yama zata cewar kuka takeyi

"Meenal kukan me ne kikeyi kuma, sakko kici abinci" batace masa komai ba, tadai sauke hular alkyabbarta ta k'ura masa ido, lomar farko dayake shirin kaiwa ta rud'ar da ita, da sauri ta sakko ta rik'e hannun sa tana kuka

"Abu Hidar dan Allah karkaci wannan abincin" kallo ya bita dashi na mamaki

"Ina cewa malmo tayi daga b'angarenki aka kawo? Kuma na tambayeki ke kince baki sani ba, sa'an ku neni dazaku rainan hankali?"

"Kayi hakuri amma dan Allah karkaci"  mamakinta yakeyi yakai cokalin ya ajiye, cafko hannunta yae iya k'arfin sa

"Baki isaba wlhy, akawo abincin daga wurinki sannan kice dani kar inci, me kika sakamun aciki?" Kukanta ne ya k'aru

"Haba Takawa tayaya zanyi yunk'urin cutar dakai kuma na hanaka ci?" Wayartace tayi k'ara abinda ya d'auki hankalin dukkansu, su kuma harinsu dake kallonsu kai tsaye ta CCTV Camera sukaji wani sanyin dad'i, lokaci d'aya suka sauya akalar zancen dazasuyi a waya, k'in d'agawa tayi har kira n biyu ya shigo a wayan, kai hannunsa yae ya d'auki wayar yana nanata sunan aranshi

"Wacece Maryama?" Ya buk'aci sani yana kallonta,, screen d'in ta wurgawa kallo

"Maryama?" Ta nanata  sarari cikeda mamaki, batayi saving wannan number a wayarta ba itakam, bata bashi amsaba har wayar  ya yanke, mutanen dake cikeda haushi tak'i d'agawa suka kalli juna cikeda takaici, macen ce tace

"Ka k'ara kira mana" shi kuma Takawa yace

"Ehnhmmm inajinki,gayamun wacece maryama?"  Muryarta har rawa takeyi sanda ta furta

"Wlhy Allah Takawa banyi saving wannan number a wayana ba, yanda ka gani haka na gani" kan yae magana kira ya k'ara shigowa a wayar, d'agawa yae batare da yayi magana ba, su kuma dama haka sukeso suka d'aga juna babban d'an yatsa  suna murmushi

"Ki tabbatar yaci abincin nan fa, dan kinsan gubar me tsada ce" Da sauri takawa ya kalleta

"Kindai jini ko, inba haka ba wlhy sekin dawon da miliyan biyar d'ina babu abinda nakeso irin inga Takawa ya mutu" Zuface tashiga ketowa Takawa ya katse kiran tare da cilla mata wayarta

"Haba Ameena? Menayi miki? Mesa kikeso ki kasheni?" Kukan ma ya gagareta tace

"Haba Takawa wai mezesa idanka ya rufe ne? Tayaya zan so cutar dakai haka kawai kuma sena dawi in hanaka cin abu?" Cikin k'araji ya mik'e ya furt

"Ro ta yaya kikasan da guba abincin? Mesa wannan ze kira yace karki musu wasa da guba, akan miliyan biyar Ameena?" Kukanta ta karawa sauti

"Wlhy tallahi sharri akamun ka saurareni" Tsaki yaja

"Shine kuma kike b'oye sunan namiji zuwa maryama?"

"Ka yarda dani wlhy bani nayi saving ba" Takaicine ya sanyashi wanketa da kyakyawan mari

"Wlhy sena d'aukar wa wannan abun naki mataki, dama kinshigo rayuwatane sabida kawai ki kasheni muguwa, barinje in kirawo Guads d'ina yau a underground cell zaki kwana wlhy" rik'o masa hannu tayi

"Bari in tabbatar maka cewar sharri akamun bari in nuna maka cewar niba matsiya bace dazan kashe koda kiyashine akan kudi bare mutum,kan yayi wani yunk'uri ta kaiwa abincin cafka ta soma ci, kallonta yakeyi hartakai loma ta biyar, hannunta ya rik'e

"Ke kina haukane?" Cikin kuka tace

"Ka barni in mutu in huta, zargi na kake akan zan iya kisan kai, menayi maka kakeso ka cutar dani, mena yi maka ka raboni da kwanciyar hankalin zuwa wannan gidan me kamada mak'abarta, wlhy an cuceni Allah yana kall.....se tasoma tari kuma kan kace meye wannan tasoma aman kumfa idanun nan sun birkice zuwa fari tas babu baqin idon ko kad'an...hankalinsa ne ya tashi yasom jijjigata, malmo ya k'wallawa kira ta bazamo da gudu

"Ke gayamun Gaskiya daga ina wannan bincin ya fito, wlhy gunduwa gunduwa zanyi da naman jikinki idan kikamun k'arya" Muryrta na rawa tace

"Sarauniya ce tace akawo, ace daga b'angaren Sawun Takawa ne sabida tawaka yae murna amarya ta shirya masa abinci,kuma ta hore mu kan karmu gayawa kowa" k'ara me girma ya k'walla ya kwashi Meenal dake kwance lifeless.....

   Meena l duk taji tuggun da Sarauniya ke shiryawa ta hanyar recoder d'in nan, akan su kashe shi akan ya tra da wata, ya haifi wani yaron bazasu bari wani ya mulki masrautr hankaka ba se Hidar konan gabane, idan akace abincin daga hannunta yake dole ita za'a zarga amma idan akace meenal ce fa?? Wannan ne ya sanya ta hanashi cin bincin.

~kosu waye suke shirin wancen kiran waya dansu kashewa Meenal aure? Ko meenal zata mutu?~

Mom Nu'aiym.....

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

609K 1K 22
Smexy One shots😘 Got deleted twice 3rd times a charm🤦🏻‍♀️😭
37K 2.9K 60
Hamza Siddiqui- The new student in the school, whose smile made every girl lose her heart but he is a cold , ruthless and rude demeanor person Fiza...
186K 6.9K 13
2 tom dylogii ,,Agony"
39.6K 1.3K 17
18 year old Ymir grew up on the outskirts of a small Romanian village. On her 18th birthday she sought out to run away from home when things haven't...