page 14

3K 266 11
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

             14
Kai tsaye masarautar sa ya wuce, Manya manyan sassa ne agidan masu girman gaske, wanda suke k'ofa k'ofa har k'waya hudu, masarautar Hankaka masarauta ce me girman gaske, danku tafiya a k'afa sekayi ta awa d'aya tsakanin kowace k'ofa da 'yar uwarta, idan amota kakr kuwa sekayi mintuna goma sha biyar koma sama da haka, k'ofar gabas itace k'ofar sarki anan fada take, nanne isashen mulki yake da tak'ama kuma anan ne Sarki Muzammil yake da ahalinsa....yayinda sassan  dasuka saura ma jinin sarautane da hadimansa ke rayuwa aciki, k'oafr gabas anan ne shima TAKAWA Yake, inda tsakanin sa da sashen sarki ma tafiya ce wacce seya hau mota shikam, sekuwa idan yayi ra'ayin rage nauyin jikinsa......

   Takawa haifaffen d'ane awurin Me martab'a sarki Abduljalal d'nd'an sarki Mu'azu jikan Sarki Musa me walaha. Ya kasance jinin sarauta ne gabansa sarauta bayan sa sarauta...Mahaifiyarsa 'yar sarki ce agarin agadez dake Niger wanda  awurin wanintaro mahaifinsa ya had'u da ita dayaje Niger itace sarauniya a garin, ita da k'anwar tane a wannan lokacin, seya nemi aurenta aka kuma aura masa, yanada k'aninsa dayake ubansu d'aya shima seya nemi auren k'anwar ta dasuke uba d'aya aka bashi, Amma seda aka kusa shekaru biyu sannan aka d'aura na k'anin nasa da k'anwar mahaifiyar TAKAWA.

   Sarautar masarautar hankaka sarauta ce me cikeda nuna isar mulki da ji dashi, sam su basa d'aukar rainin talakawa.

Sarki Mu'azu shine mahaifin su sarki Abduljalal da k'aninsa Abdulra'uf, yanada mata uku da k'wara k'warai da dama, acikin matansa Sarauniya Daurama itace uwar gidansa, kuma itace me yara da yawa amma dukansu matane kusan susu bakwai, seme binta Hajiyar kilisa wacce itace tauraruwar sarki Mu'az itace kuma ta haifi Abduljalal tunda kuma ta haifesa bata k'ara samun haihuwa ba, Gimbiyar Rusau kuwa itace da haihuwar Abdulra'uf da k'aninsa mata susu biyu gimbiya salima da kuma gimbiya Huraiyya.

   Babu shakka wannan masarautar cike take da tsoron adilin sarkin ta wato sarki Mu'azu, ya gada tun kaka da kakanin karamci da mutunci, yana kuma da tsauri sosai, yana taimakon talakawa sedai baya d'aukar musu raini ko nan da cen, Asalin sunan ta ya samo asaline tundaga yanda suke d'aukar wanda ba nasu ba nasu, komai k'ask'ancinka suna sanya ka ajiki tun kaka da kakanni, wannan dalilinne ya sanya ake kiranta da suna *Masarautar hankaka maida d'an wani naka*......

Sarauniya daurama macece me asalin kirki da kuma karamci sedai fa sam bata k'aunar abinda ya tab'a mata yaranta, dukda zamtowarsu mata ta d'aukaka darajar su a wannan masarautar da hanyar dako sarki baya samun irin kulawar dasuke samu, tana son mulki tana kuma k'aunar mulki, a yanzu haka 'yarta Gimbiya sailuba tana aurene a wata masarauta me girma, kana tana da yaro acen, sedai kuma shine na kusan uku a family d'in kuma sarauniya daurama ta kudiri aniyar seya mulki masarautar Hankaka, acewar ta ya gaji uwarshi.

Babu wani imani a tsarinta duk kirkinta batasan Allah ba, bakuma ta k'aunar d'an wani, ita dai nata kacal!!!!.

Hajiyar kilisa kuwa itace mahaifiyar Abduljalal, itace kuma sarki yakeji da ita fiyeda sauran matayensa, wanda kowa yasan da hakan, da wannan ta kafawa kanta k'iyayyar dabame santa, gashi ko a cikin 'ya'ya yafi nuna kulawarsa akan Abduljalal sabida koba komai shiyake kallo a matsayin magajinsa wanda ze gaje sarautar garin ko bayan ba ransa.
     Hajiyar kilisa macece me nagarta sosai, tanada kirki, tana asali me kyau dankuwa 'yace aka d'akko daga wata masarautar zuwa wannan, tanada halaye na gari kuma kowa natane.

********
   Gimbiyar Rusau mahaifiyar Abdulra'uf kuwa bazaka iya fassara halayenta ba, bazaka san gabanta ko bayanta ba, bata shiga mutane batada fara'a batada kuma bak'in rai, bata magana sam kullum kum kum, yarantama koda wane lokaci suna gu d'aya ta kame su ko amasarautar bako ina kake ganin suba.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt