NISFU DEENIY.......!

By deejasmah15

1.2K 117 25

She was exactly opposite of what he wants in a wife,,,he vowed not to be with her but fate has its own way as... More

PROLOGUE ( TEASER)
CHAPTER ONE (REJECTION)
CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO)
CHAPTER 3 ( MY PRAYING POINT)
CHAPTER 4 ( HOW I WISH....)
CHAPTER FIVE (MEETING.. ).
CHAPTER 6 ( MISFORTUNE....!)
CHAPTER 7
CHAPTER 8 ( HIS VISIT)
CHAPTER 9 ( THE RIDE)
CHAPTER 10 ( SHE'S BACK)
CHAPTER 11 ( SHE'S BACK II)
CHAPTER 12 ( DAYS TO GO.....)
CHAPTER 13 ( #BECOMINGMRSBAY)
CHAPTER 14 ( DAY ONE)
CHAPTER 15 ( HONEYMOON)
CHAPTER 16 ( A_RIDE_TO_YERWA)
CHAPTER 17 ( LIVING WITH HIM)
CHAPTER 18 ( HER EFFECT)
CHAPTER 19 ( SICK)
CHAPTER 20 ( SHE'S TO SOFT)
CHAPTER 21 ( GETTING TO KNOW HIM)
CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)
CHAPTER 23 ( DAY AFTER )
CHAPTER 24 ( GETTING ALONG OR GETTING APART?)
CHAPTER 25 ( SETTING THE GROUNDS)
CHAPTER 26 ( SACRED TRIP)
CHAPTER 27 (THE PERFECT HER)
CHAPTER 29 ( MILESTONE)
CHAPTER 30 ( HURRICANES)
CHAPTER 31 ( MEETING II)
NISFU DEENIY 32 (BROKEN)
CHAPTER 33 ( BROKEN 11)
CHAPTER 34 (DAY-OFF)

CHAPTER 28 ( PROUDLY HIS❤)

52 5 0
By deejasmah15

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 28 (Proudly his❤)

And today a queen was born, happiest birthday Deejasmah❤

" kar ki damu wife, nan fa gidanki ne so kina da right da duk wanda ya ga dama zai iya kawo mana ziyara as long as bai sab'awa sharia ba. So, calm down go and meet your friends but get ready for me idan sun tafi" ido ta rufe tana murmushi cikeda kunyar abinda yace.

Sake ta yayi ta sake lafewa a jikinshi cike da kunya, duk'awa yayi saitin kunnenta yace " seems like you want it right now, okay bari in ce musu su jira mu kawai ko?".

Ai da sauri ta janye jikinta tana cewa " sai ka fito Yaa" murmushi kawai yayi ya bita da idanu, yana tariyo yanda ya hango damuwa a idanunta a kan zuwan k'awayenta. Is he that special to her or she's just so perfect and unique a cikin mata da ba ta son damuwar shi ko kad'an ko kuma dai tsabar tsoronshi da take ji ne?.

San da ta fito parlorn suna zazzaune abunsu hankali kwance, suna ganin fitowarta suka fara mata tsiya Sophia tace " matar nan kiji tsoron Allah, wa to har da safe ma kina hanyar turaka".

"Ba ga shi nan kina gani an samo tsarabar turakar ba" cewar Ayush tana dariyar mugunta Heedayah ce tace " haba ku kuwa aikin Allah ne fa take yi, ya zaku saka ta a gaba ne ".

Kallonsu tayi tana cewa " wallahi yaran nan kun lalace tabbas, sai fatan shiriya".

"Su waye yaran?" In ji Jam-Jam cike da taajibi, Deeyah tace " ba dole a ce muku yara ba ta shiga in da ko a mafarki ba ku tab'a shiga ba, Allah na gode maka muma nan da 2 months an wuce wurin" kasancewar itama bikinta kafin babbar sallah ne.

Shewa suka saka gabad'aya kamar wasu manyan mata, Nadeefah tace " oho dai ai mun rigaku shiga d'in". Cewa tayi " abinda ita dai turaka ba ta da gwani? K'arshenta dai a labor room ake k'arewa kema kin kusa ai ga su Nana can anyi haihuwar asuba".

"Dan Allah dai, Nana ta haihu? Yaushe?" ta tambaya don ba ta sani ba, ta dai san tana da ciki don ma tayi b'ari sai wannan ne ya tsaya da yanzu ai tayi kusan 3 months da haihuwa tunda an riga bikinta da su.

"Ai ke yanzu kin zama sai Allah ya kawo d'auki kawai, yau da asuba ta haihu Baby girl mai kyau wallahi" In ji Sophia, cewa tayi " Allah sarki Nancy, lemme call her now".

"Ki dai bari zuwa anjima don yanzu dai tana bacci ne, d'azun ma Saudah muka yi magana da ita wai ta ji jiki ne sosai wajen haihuwar" Cewar Deeyah. Cikeda tausayi tace " Allah ya bata lafiya, wayyo Nanata mai sona".

"Saura ke ai kina zare idanu, zaki ga k'arshen so ai ".

"Ku bakinku bai da kyau wallah, sai mugun fata kukewa mutum thank god dai ban da komai balle ku saka ni a ashanar tashi".

Sophia ta bud'e baki zata ba da amsa kenan suka jiyo sallamar Burhaan a parlorn, dukan su natsuwa sukayi suna gaishe shi amsawa yayi a d'an sake ba yabo ba fallasa. Sai dai har da tambayansu ya suke, daga haka ya koma ciki dama bai zauna ba. Bin shi a baya tayi don ya mata alamun fita zai yi, a k'ofar fita ta garage ta gan shi kuwa gabanshi ta k'arasa tana cewa " zaka je gidan Umma ne?".

"Gidan Yaa Budu zan je, sai ki shirya in sun tafi sai ki kirani mu je gidan Adnan ".

"Okay Yaa sai ka dawo Allah ya tsare hanya" Ameen ya amsa sai da yayi kissing d'in ta kafin ya wuce, komawa parlor tayi tana blushing ba ta ko zauna ba ta shiga kitchen ta fara serving d'in su samosa ta d'an sa a mai ta soya ta kawo shi a plate d'in shi daban. Barin su tayi suna ci suna hira ita kuma ta koma kitchen d'in tana d'aura girki fried basmati rice ta musu da dama shi tayi tanadin yi yau yaji vegetables sosai yayi kyau ta zubo ta fito da shi, daga nan suka dasa hira don an dad'e ba a had'u haka ba tun zuwan da suka yi washe garin aurenta. Sauran had'uwar sai a office d'in ta ko ta bi su gidansu don ba laifi tana da zumuncin k'afa sai kuma ta waya.

Sallah ne yake tadasu daga hirar ba ta yi wasu bak'i har zuwa bayan Asr da suka fara haramar tafiya, transfer tayi musu na kudi wai in ji Burhaan wanda ba sata yayi ba ita ce tayi don kankaro masa mutunci a wurinsu and she actually succeeded don sun tafi da ganin mutuncinshi sosai dama suna girmama shi but ya dad'u ainun duk da ba wacce bata fi k'arfin duka kud'in ba a cikinsu but alkhairi komin k'ank'antarshi yana da dad'i.


Har parking lot ta rakasu suna tafiya ta shiga tayi wanka ta cire lace d'in jikinta ta sanya atamfa, nan ta sake bak'i 'yan maaikatarta ne su kusan 7. Ta ji dad'in zuwansu ainun inda ta dinga hidima da su ainun, ba su wuce 1 hr ba suka tafi bayan sun sake tayata gyaran gidan suma ta sa musu kud'in barka da sallahn su ta account. Su na fita ta kira Burhaan cewa sun wuce bai dawo gidan ba sai magrib don haka sai da suka yi sallah kafin su ka wuce gidan Adnan da yake Malali layout can ciki. Yau ne karon farko da ta fara zuwa gidan ya had'u shima ainun ga shi yana samun gyara daga matar cikinshi, an musu tarba ta musamman a gidan in da ba su suka baro gidan ba sai after 10 su ma ko da suka koma Burhaan bai ko d'aga mata k'afa ba kamar yadda ya fad'i sai da ya sarara over kafin ya rangwanta mata in da sai da zazzab'in daren da take fama da shi ya sake tashi.


Washe gari ko da k'yar ta iya ta shi tayi ayyukan gida 11am ta shirya cikin atamfa embellished super riga da skirt da suka mata tsam kamar kullum tsadadden lafaya mai kyau da ya k'ara k'awata cikar kamalarta ta d'aura a kai ta had'a da jaka da matching wedge shoes na Zara suka nufi Yerwa in da yau suke yin na su taron, a nan Yerwa Hall suka had'u. Ba a tattauna komai ba sai hira da suka yi ta yi da juna kowa da circle d'in shi aka ci abinci 2 bayan an yi azuhur kowa ya watse ya tafi gidan shi itama gidan Ummu ta gudu ko zama ba ta yi ba ta wuce d'akinta rigar jikinta ta zare da skirt bayan ta warware nad'in lafayar jikinta daga ita sai under skirt ta haye gado ta ja bargo ta rufe kan ta. Ba ta ko dad'e da kwanciya ba barci ya kwashe ta ba ita ta iya tashi ba sai bayan Asr, shi ma Ummu ce ta kad'o ta tashi tayi cikin shagwab'a tana d'an tab'a fuska.


Ruwa ta watsa a jikinta ta fito kayanta ta mayar tayi sallah, fitowa tayi zuwa parlor babu kowa a parlorn sai ta nufi part d'in Abbu inda can ta iske su har da ElSadeeq.

Gefen Ummu ta je ta zauna tana gaisawa da Sadeeq d'in tare da tambayarshi Suliem, da kulawa ya amsa yana mai cewa " tana gidan Mommy, ba ta wani jin dad'i a kwanakin nan ma".

"Allah sarki my baby Mama, Allah ya rabasu lafiya".

"Ameen" ya amsa fuskar shi ta d'an nuna damuwa na tausayin matar ta shi, Ummu ce tace " ai sai a hankali dama, ka san wasu matan ba su cika ciwo ba sai a third trimester da ta haihu kuma shikenan".

"Gaskiya ko Suleim is one of them Ummu, yanzu fa ko bacci ba ta iyawa ta dad'i ga ciwon baya and joints ".

"Baiwar Allah ga shi duk ta kumbure, Allah ya bata lafiya da ladan rainon ciki ya kuma hore mata k'arfin shayarwa" nan ma ya k'ara amsawa da Ameen.

Abbu ne yace " Allah ya k'ara sauk'i, tana haihuwa in shaa Allah za ta samu sauk'i don't worry ok?" Ok ya amsa masa shima. Kallonta Abbun yayi yana cewa " you also look unwell, ko kin yi ciwo ne?".

"Gajiya ce kawai ke damu na, Ummu ne bata tab'a gaya min haka ake gajiya da sallah ba. Ehh duk da fa an taya ni amma na ji a jikina ga shi ma ina kan ji ". Dariya suka sanya mata don sun san za a yi hakan saboda muguwar rakinta, k'aramin aiki za tayi a gidan sai kowa ya san tayi don ma Ummu ba ta mata wasa ta wannan b'angaren don duk da kasancewarta jinin sarauta ba ta saki jiki tace komai sai an mata ba kuma ba ta raine su dukansu a haka ba.

ElSadeeq yace " in da ke kada'i kika yi aikin nan da ai sai Burhaan ya toshe kunne da rakinki na tsiya" tab'e baki tayi tana cewa " Allah Yaa don ba ka san wahalar aikin ba ne shiyasa" a zuciyarta ko tace " ai ko a jikin Burhaan in dai kan aikine sai dai in zai kashe ni, ya kashe ni kowa ya huta".

Abbu yace " ai tabbas Burhaan ya na k'ok'ari da Lele, yarinyar da ko allura ya caketa sai tayi jinya kamar an yankata da wuk'a?". Dariya suka sanya Ummu tace " ai ka kai da nisa, matar da ko tsintsiya ya bige ta yini take yi a kwance. Ai tabbas Islaam yana k'ok'ari sai ma a bashi endurance award".

"Ni dai za a bawa endurance award ba shi ba, don k'ok'arina ne za a yaba ba na wani ba". Ta furta da iyakar gaskiyarta don in da wanda yake enduring wani abu to ita ce ba wani Burhaan ba, ta jure halayyarsa, aikin gidansa, buk'atunsa da ma zama da shi, shi fa mai yake jura a gareta? D'an kuskure k'arami za ta yi sai ya nuna a fuska, ga shi ba a birge shi balle a iya masa.

"Ba wani nan in yazo anjima ma da kaina zan ba shi award d'in" Abbu ya fad'i da dariya, kusa da shi ta dawo tana cewa '' Allah Abbu ni ya kamata a bawa, in kuma za a ba shi then you must give mine to encourage and support me besides ba ma ku ba ni barka da sallah na ba".

"Beggie-beggie garl". Cewar Sadeeq.

''Ko ma menene a kirani but sai an ba ni, balle ma ba rok'o nake yi ba tuna muku nayi".

"Tunawa a ina? Ce miki aka yi an manta da sai kin tuna mana?".

"Kun manta mana, a k'aida da an dawo eid nake jin alert but yau har third day of sallah ba a da niyyar ba ni bari ma su twins su dawo su ma su bani nawa kason".

" Ashe ko zaki bushe kina jiran su, mutanen da suka had'u da su Safwaan da Lameen suna zaga gari da 'yan matan ne zaki gani a gida?".

"Eh lallai su Tayyib an fara girma, toh ai in dai ba kwana zasu yi ba nan zasu zo su same ni".

"Da yake ke kwanan zaki yi ko?".

Tura baki tayi tana cewa " yes, sai gobe zan koma gida". Ok yace mata kawai su ko su Ummu ba su bi ta kan maganar ba thinking that wasa take yi, su ka d'auko wata hirar da kiran sallah ya tada su a wurin.


Bayan idar da sallahr ne ta tuna da tunda ta shigo ba ta yi amfani da wayarta ba ne ya sanya ta zaro shi daga jakarta, misscalls biyu ta gani daga infinite love. Da sauri tayi unlocking wayar tana mai mamakin kiran na shi don bai kira more than once in ba su Umma ba may be, amma ita bai tab'a kira ya fi haka ba.

Sai da wayar ta kusa tsinkewa ya d'aga yana cewa "ki na ina?". Amsawa tayi da " gidan Ummu" ok ya furta bai ko jira cewarta ba ya katse wayar yana mai barinta da shi sak'ale a hannu, sai kuma ta tab'e baki ta ajiye wayar.

Sauka tayi daga gadon tana magana a zuciyarta kan zuwa gidan Hajjah sai kuma tace "tun da ina nan ai gobe sai in je gidan in wuni". Ta na fita daga d'akin yanzu kam wurin Ummu taje in da suka dasa hirar uwa da 'ya cikeda so da kulawa, rabin hirar bai wuce a kan zamantakewar aure da rayuwar duniya baki d'aya ba. Ba ta ko binciki zamantakewar su ba don ko makaho ya shafa Nadeefahn ya san tana samun kulawa daga mijinta balle ita kuma mai idanu, ga kuma alamun ciki da ya gama bayyana kan shi a jikinta nan.

A nan ta yi ishai kafin suka d'unguma zuwa parlor, lokacin Abbu ya dawo daga masjid a nan suka ci abinci same plate da hannu ba kuma da cokali ba da suka gama ta kai kitchen ta gyara wurin maids kuma suka wanke kayan da aka b'ata. Kafin ta dawo ta zauna gefen Abbu kamar yadda suka ci abincin kai kace zata koma cikinsu a sake haifota, su ko ba su damu ba sai ma sake tarairayota da suke yi suna biye mata tana abunda ta ga dama.

Abbu ne ya dubi agogo yana cewa ''wai Islaam ba zai zo ku wuce gida ba ne, dare sai sake yi yake fa''. Tura baki tayi tana mai cewa "ni fa a nan zan kwana Abbu" kallon you no well yayi mata yana cewa " ki kwana a ina?".

"A nan mana Abbu"

"Saboda ga mu shashai ko? Ki kwana ki mana mene a gidan nan?".

"Abbu wai laifi ne kwana a gida? Na fa yi missing d'inku ne''.

"Missing ko? Da yake a na wasa da ke ne, shi Burhaan d'in ne ya yarda ki kwana a gidan?" cewar Ummu tana mata duban tsanaki, shagwab'e murya ta yi tana cewa " No Ummu please ki kira shi ki gaya masa zan kwana".

"Tun da ba mu san abinda muke yi ba ko? " in ji Abbu, Ummu ko ta cab'e shi da cewa "ba mun zama irinta ba? Ai sai mu biyeta ".

Za tayi magana Abbu ya katseta da harara, ya janyo wayarshi dake gefe ya na dannawa Burhaan kira ya na mai cewa "ba ri ma in kirawo shi ya zo ya d'auketa su wuce ban son sakarci ".

Ringing biyu ya d'aga cikin ladabi yayi sallama, amsawa yayi da murmushi yana mai amsa gaisuwar da yake masa. " Islaam kai ma na lura ba ka tsoron yin dare a hanya ko?" Ya furta bayan ya amsa gaisuwar ta shi, murmushi yayi yana cewa " A'a Abbu muna nan da su Yaa Hafeez ne amma in shaa Allah yanzu zan zo ".

"Aa toh ayi zumunci ai yana da kyau amma a dinga duban time don yin dare bai da gaisa sam".

"In shaa Allah za a kiyaye".

"Abbu don Allah ka ce zan kwana" ta furta a dai-dai sanda Abbun ke cewa " hakan yana da kyau ai, Allah ya muku albarka ka gaida 'yan uwan naka".

Daga can jinjina kai yayi wa maganar Nadeefahn don sarai ya ji ta, yana kuma jiyo Abbun na cewa "ki kiyayeni Nadeefah". Murmushi kawai yayi yana cewa " Ameen Abbu, sai mun zo" daga haka suka yanke wayar, komawa yayi ciki inda suke fira da mazan familyn wacce rabi kan siyasa, k'wallo, economy da sauran topics masu muhimmanci na dai maza masu ilimi da wayewa ba kan abinda bai da amfani ko yin gulma da yi da wani ba.

Bai iso gidan ba sai to 10 da ya zama constant a duk zuwansu gida, ko jiya ma da daren su ka dawo daga gidan Adnan. A nan parlorn ya iske su zaune, shi ma zama yayi a k'asa duk yanda Abbu yayi da shi akan ya hau sama k'i yayi. Gaisawa suka yi cikin girmama juna da mutuntawa kafin shi ma ya d'an tsoma baki a hirar da suke yi, bai fi minti sha biyar ba Abbu yace "ai sai ku zo ku tafi ko dare yana ta k'ara yi".

"Toh Abbu" ya furta kan shi k'asa still yana a inda ya ke bai ko motsa ba, kallonta yayi ta mik'e tana tuttura baki cikeda shagwab'a. Ummu tace " sai bakin ya tab'o ceiling zamu san kina fushi, in ba sakarci ba wa zai bar ki ki kwanar masa a gida?".

Murmushi yayi yana cewa " Ai Ummu da an bar ta ta kwanan".

"Au kai ma ka zama irinta ne? Don na san ba haka ka ke ba". Cewar Abbu yana murmushi, ita dai Ummu tashi tayi ta wuce kitchen. Bayan kamar 3mins sai ga ta ta fito daga d'akin rik'e da jakarta, har yanzu bakin nata a ture yake sama ba ta zauna ba ta coge a jikin kujera.

Abbu ne ya dubeta yace " Mamana ba dai fushi kike ba? Zo nan in ji wa ya b'ata miki rai" kamar k'aramar yarinya ta nufi inda yake ta zauna gefenshi, lallashinta ya fara ita kuma sai zuba kukan tab'ara da babu ko hawaye take yi.

Ummu ta fito da k'atuwar leda a hannunta itama tsayawa tayi tana kallonsu kamar yanda Burhaan shi ma yayi kasak'e yana enjoying abinda yake gani, sosai uban da 'yar suka burgeshi and one funny thing is yanda kukan da take yi yake kai wani sak'o ga can southern hemisphere d'in shi don kukan daban ne da kowani irin kuka. A da mugun haushin shagwab'a yake ji but yanzu da ya san falalarta ne ya gane he's way a shagwab'a freak, don tana mai abu ta narke fuskar nan yake jin ya manta komai a that time sai ita.

"Ko dai zai tafi ne ya bar ta a nan ta kwanan ne kawai?" Cewar Ummu baki sake, dariya yayi ya janyeta yana cewa "ai ta hak'ura ko? Yanzu za ta tafi ba maganar kwana kuma".

"Aa da dai an barta ta kwanan sai a sa mata nappy, don alamu ya nuna ba a gama rainonta ba ".

"Wani irin nappy kuma a na zaune lafiya, sai kace yarinyar goye".

"Zaujus-salih ai alamu ya gwada yarinyar goyen ce, wannan in ta haihu kasa bambance ita da yaranta za ayi ".

"Kayya dai Mar'atul Jannah".

Dariya suka sanya jin Abbun ya rasa bakin magana, ita ko gabanta ta zo ta tsaya tana cewa " kai dan Allah Ummu, wai sai ki dinga ce min na girma duka nawa nake? And besides a gabanku ai nake ko min tsufana ai still your baby".

"Ai in dai magana ne bakinki zoin, toh na ji amshi ledan nan and find your way out a gaida gida".

"Kai Ummulkhair....."

"Don't start that, a tafi gida maza". Tura baki tayi ta amshi ledar tana nufar k'ofa bayan tace musu goodnight, tashi yayi yana cewa "sai da safe Ummu and Abbu" a tare suka amsa ya nufi k'ofa yana murmushi jin Abbu yana cewa " kin ga kin sake b'ata mata rai an samu ta daina fushin".

"Ai dama kai kake b'ata ta Zaujul-Khair, ta je tai ta fushi in dai fushin Nadeefah ne mara tushe da kanta za ta sauka".

"Wai ina b'ata ta bayan kowa ya san ke ta gado da wannan shagwab'ar, ko har kin manta ne Khairun-Nisa'?".

"Kai Abbu" itama ta amsa a shagwab'ar tana buga k'afarta a k'asa, da sauri ya k'arasa fita daga gidan yana gulma a ranshi " wato duk girman da mace za tayi halinta bai tab'a canjawa, haka kuma duk tsufan masoya kullum jin su sukeyi kamar yara".

A take mood d'in shi ya sauya a fili ya furta "if only i was given a chance to marry someone i love i for enjoy my marital bliss like or more than them, ya rabbi". A haka ya k'arasa inda take tsaye a jikin motar shi, ba tareda ya dubeta ba ya bud'e motar zagayawa tayi ta shige passenger sit ta zauna bayan ta ajiye ledar da Ummu ta ba ta a baya.

Tafiya suka yi in silence zuwa gida don haka nan mood d'in shi ya lalace shiyasa ko sau d'aya bai kalleta ba, ita ce ma time-time take kallonshi tana mamakin sauyin mood d'in shi don ta hango shi yana murmushi sai kuma kafin ya k'araso gabanta har b'acin rai ya bayyana a fuskar tashi.

A cikin garage ya yi parking ita ta fara fita daga motar bayan ta d'auki ledarta, kafin shi ma ya fito. Key ya sanya ya bud'e k'ofar tana biye da shi a baya har ya kai k'ofar bedroom d'in shi tace " akwai abinda kake buk'ata ne?" Waigowa yayi yana kallonta kamar zai ce wani abu sai kuma ya girgiza kai yace "nope, good night''.

Gyad'a kai kawai tayi ta wuce ciki, wanka ta samu tayi da d'an ruwa mai d'umi saboda zazzab'in da take ji yana shirin rufeta. Ruwa ta fita ta d'auko a kitchen ta sha paracetamol ta kwanta bata wani dad'e da kwanciyar ba bacci ya samu nasarar kwasheta.

Zaune take a dadduma bayan idar da sallahr asuba tana azkar aka turo d'akin, bata waigo ba dukda taji bud'e d'akin da kuma niimtaccen k'amshinsa da ya gauraye d'akin. Wuri ya samu a bakin gado yana jiranta ta d'an jima kafin ta idar, hijabin ta zare a jikinta ta ajiye shi a inda ta saba kafin ta nufo inda yake zaune.

Zama tayi nan gefenshi tana cewa "good morning Yaa". Dubanta yayi da kyau yaga tayi masa fayau kamar mara lafiya ya amsa da "morning, are you sick?".

Girgiza kai tayi tana cewa " i'm fine gajiyar sallah ne kawai ba komai ba".

"Wannan ba gajiya ba ce kawai Wife, you look so pale and sick me yake damunki?".

"Fever ne kawai, shi ma da dare ne yau ne ma na tashi da lower abdominal pain which is nothing but menstrual cramps ".

"Menstrual cramps kuma? Dama kina yin menstrual cramps ne?".

"Yeah every month sai na yi".

"But kin dad'e ba ki yi cramp d'in ba ko " ya furta caressing her cheeks.

"No, ko last cycle d'ina nayi fa".

"And when was that?".

Shiru tayi tana tunanin last cycle d'in nata, a nan ne kuma tunaninta ya tsaya cak don gabad'aya ma ta kai kusan 3 months ba tayi period ba. No, rabonta da shi tun kafin su d'an shirya d'in nan wanda ta dinga faking sa pad. Zaro idanu tayi tana kallonshi cikeda damuwa tace "Na shiga ukuna Yaa, ban da lafiya? Na dad'e ban yi period ba".


"Shi ne yake nuna ba ki da lafiya? Uhmm".


"Could it be hormonal imbalance?, Innalillahi!!" Ta k'arashe tana kuka sosai don ita har ga Allah ta manta akwai wani dalilin da zai sa ka yi missing period in ba cuta ba.

"Heyyy calm down mana, ba yanzu kina expecting period d'in ba ne?".

Kai ta gyad'a masa a razane tana mai cewa " what if bai zo ba?" k'ureta yayi da idanu a k'asan ran shi yana sak'e-sak'e 'could it be that she's pregnant?' Ya tambaye kanshi, tambayar da ya sanya shi mik'ewa a d'okance yace" bari in miki wani test mu gani, ko zan iya sanin me ke damunki in na kasa then we should go to the clinic a gwadaki da kyau".

Bai ko jira cewarta ba ya fita daga d'akin ya barta da tagumi tana mai adduar Allah ya sa lafiyarta k'alau, ita fa tunaninta is far from pregnancy ba wai ba ta so ta samu ciki ba ne Aa ba ta kawo wa ranta shi ba ne shiyasa ma take ta ma mutane musu in suka ce mata tana da shi.

D'akinshi ya shiga yana d'auko pregnancy kit d'in da ya ajiye tun kafin tafiyarsu Saudi, bai kuma san dalilinshi na siyanshi ya ajiye d'in ba sai ga shi yau zai yi masa rana.

A yanda ya bar ta haka ya tarda ta da taguminta, k'aramar containern ya mik'a mata ya cewa 'fitsari kad'an zaki yi a ciki, like 3drops or so'. Kai kawai ta gyad'a masa ta wuce toilet d'in, ba ta dad'e ba ta fito da kwalbar ta mik'a masa amsa yayi ya d'auki stripe d'in dake nan kaman biro wanda tana ganinshi ta zaro idanu da kyau don ta san amfaninshi tunda ta na yawan gani a movies da dramas haka.



Sai dai ba ta tanka ba illa tsura masa idanu da tayi, yana saka kan a ciki ya zare kafin ya gama reading ya tafi da containern yayi discarding a waste bin ya dawo ya zauna. Dukansu su biyu suka zuba ma strip d'in idanu, har ya gama reading layi biyu ne suka fito b'aro-b'aro da ya sanya ta daka tsalle.

Rik'eta yayi zuwa jikinshi yana cewa "be careful" a d'an razane ta fara magana "Yaa, I'm pregnant!! My Allah I'm pregnant!". Zura mata idanu yayi yana kallon yanda take magana with full excitement, which shows her out must love for babies. Don har da long sujud tayi tana cewa " Alhamdulillah I'm gonna be a mom, I'm grateful ya rabb" rasa abun cewa yayi sai kawai ya janyota jikinshi yana had'e bakinsu wuri d'aya.

Da same energyn da yake kissing d'inta itama take maida masa da martani, wanda ko da ba su fad'i ba celebrating suke yi. They are all happy zasu rik'e first child d'in su a tare, lamarin ya kankama sosai don sai da gari yayi haske sosai kafin suka rabu da juna ba kuma rabuwar suka yi kai tsaye ba. D'aukar abunshi yayi zuwa toilet inda a nan ma sai da suka gama shiriritarsu, in da a banza ne da yanzu Lele tana k'orafi but da yake tafe take a kogin k'auna ga uban ciki da shi kan shi cikin ya sa bata ganin kowa no one matters a lokacin but her Baby daddy. Faranta masa is her own priority then anything else, saboda kalar gajiyar da tayi ya sanya suna fitowa daga wankan ba su bi ta kan komai ba sai bargo da suka shige wani bacci ya kwashe su k'ank'ame da juna kamar zasu goma cikin su zauna da babyn nasu har zuwa sanda zaa haifeshi.

Sosai suka yi bacci har rana ta fito ta hantse kafin ta tashi, yana nan a gefenta bacci yake peacefully kamar ba Burhaan rigima ba, pecking cheeks d'inshi tayi ta zare jikinta toilet ta fara wucewa gyara shi tayi ta wanke tsaf kafin ta fito. Half gown ta nema ta zura ta nufi parlor, gyaran gidan tayi kamar yadda ta saba kullum har da part d'in shi ta baza turare. Ta nufi kitchen breakfast mara nauyi ta had'a musu, tana jerawa a dining ya fito sanye da boxers kawai yana ta mik'a.


Tsayawa yayi ya k'arewa parlorn kallo da ita kan ta ma'abociyar parlorn. Murmushi tayi tana cewa "good morning". Cewa yayi "morning" daga haka bai sake magana ba ya wuce d'akinshi, murmushi tayi ta k'arasa had'a dining d'in da abubuwan buk'ata kana itama ta wuce nata d'akin. Zagewa tayi ta gyara shi tsaf ta baza k'amshi sai lokacin ne ma ta ga strip d'in da suka yi gwajin, murmushi tayi ta d'auke shi ta adana a cikin drawer ko ta kan wayarta ba ta bi ba ta wuce toilet wanka ta yi ta fito kasancewar ta kwana da son zuwan gidan Hajjah ya sanya ta shirya cikin simple doguwar riga da ya mata daidai ga kuma colorn da ya sake fito da haskenta kasancewarshi bournvita color mai touches na sage green da kuma tumeric. Sage green veil ta ciro sai takalmi tumeric da bag ta fito zuwa parlor bayan ta d'auki wayoyinta. Zama tayi a cikin kujera bayan ta ajiye kayanta a kujerar, wayarta ta bud'e a notification box ta ci karo da miss calls.


Da sauri ta bud'e wayar don duba calls d'in suwa tayi missing, Sadeeq ne da 2 miss calls wanda ta san bai rasa nasaba da barka da sallahn da ya tura ma ta jiya ba kuma ta kira ta sanar masa ta gani ba balle a kai ga batun godiya. Dialing number tayi sai dai bata kai ga shiga ba aka shaida mata da yana waya, sai kawai ta juya alak'ar kiran ga Zulfaa da ita nata miss calls d'in sun fi biyar.

Ita dai tayi sa'a ya shiga tana d'agawa tace "ke kam ina kike ajiye waya ne? A yita kiranki ki k'i d'agawa?.

" Kin haihu ne halan?".

"Eh gashi nan a gado kizo ki gan shi".

"Labari ne wannan".

"Haihuwar tawa ce labari or what''.

"Haka ake haihuwa ne madam? Kin ji muryarki fa zak'wai kike wani cewa kin haihu, da haka ake haihuwar ba wahala ai da kowa yayi".

"Banzaaa, Allah ya shiryeki".

"Ameen, so what's up ?".

"Guess what?!".

"What's this abegg, in zaki gaya min ki gaya min meye wani guess what a na zaman lafiya?".


"Ke fa ta wani lokacin a birkice kike wlh, common guessing kin kasa?".

"Naji d'in yanzu dai zaki gaya min ne or in kashe wayata?".


"Ki kashe mana wa ya rasa?".



"Zulfaaaa!!"

"Kar ki k'arar min da suna ko ki fasa min kunne madam don na lura abunda kike shirin yi kenan?".


"Ni dai ki gaya min kawai, ban son rough play ".

"Kayan takaici kawai".

"Na ji d'in ".

"Toh Suliem ce ta haihu mace, yanzu haka muna gidan Mommy".


"Wata Suleim d'in Zulfaa?".


"Hala kin san wata Suleim d'in ne bayan ta Sadeeq, ke ni ba da ni zaki yi shiririta ba sai anjima".

"Ki tsaya mana......."

Sai tsit ta ji alamun an katse wayar, tsaki tayi ta bud'e wayar tana kiran Ummu. Daga yanda ta ji muryarta ta tabbatar tana cikin farin ciki ainun, gaisawa sukayi ta yi mata barka inda Ummun ce take shaida mata wai ashe tun kusan 4am suke asibiti sai 9 kuma ta haihu. Ta tausaya mata inda ta tabbatar mata da yanzu za ta taho.


Kashe wayar ta yi ta nufi room d'in Islaam, ta na murd'a knob d'in shima ya murd'a cire hannunta tayi ya bud'e ya fito. Daga yanda ya gan ta ya san an shaida mata da haihuwar, ita ko rungume shi tayi tana cewa " Suleim ta haihu Yaa".


"Uhm yanzu Sadeeq yake gaya min Allah ya raya ".

"Ameen ya rabb Yaa, yanzu nake son wucewa wai da ".

"Ki bani abinci in ci, sai in yi dropping d'in ki when I'm done". Ok tace cikeda zak'uwa tayi serving d'in shi shi kad'ai ban da kanta don a yanayin d'okinta ba zata iya cin komai ba, sai da ya nuna mata in bata ci ba ba inda zata je.

Hakan ne ya sa ta d'an iya shan plain black tea da coconut cake k'waya biyu kacal wainda ma take jin su kamar ta cusa ice a bakinta, da sauri ta gama shi ko yau sai da ya gama baza yangarshi kafin ya tashi suka wuce.


A gidan Mommy dake cike da 'yan barka ya sauketa bai ko shiga ba ya wuce sabgarshi ita ko tana shiga aka yo mata caaa a kai, ita ko baki abun magana sai biye musu take yi haka taje kan bed gefen Suleim da duk ta sauka dama har da ciki a k'ibar tata tana mata shak'iyanci har da cewa "wai akwai wahala ko babu".

Cije baki tayi tana cewa "ai da yake ma kema kin kusa haihuwar zaki san akwai zafin or no, gwara ma kowa da kowar wake".



Murmushi ta saki a fakaice ta shafa cikin tana mai jin wani shauk'i a ranta wai yau d'an Burhaan ne kwance a mararta lallai Allah alhakeem ne kuma fiyayyen masu kyauta. In ba shi ba wa ya isa ya dasa iri a gonar da ma'abocinta bai so ?............


Ya rabbi bacci nake yi ina typing idanuna suna rufewa sosai, I thought zan iya kai wa inda nayi niyya unfortunately i couldn't meet my budget wanda bai rasa nasaba da zaryar sallahn nan da ya saka mu a gaba kamar wainda suka shiga k'ungiyar 'yan tafiye-tafiye.

Manage please I'll try my best in yi wani kusa kafin komai ya daidaita in dawo normal posting d'in da nake yi in shaa Allah.

Ai na bayar da barka da sallahn da nayi alk'awari plus my birthday gift to you all😂, ohhh ana bawa celebrant gift but you guys na the celebrant dey give you gift una weldon naaa😂🌚.

Deejasmah ✍🏼

Continue Reading

You'll Also Like

190 49 5
In a village where female empowerment has never been heard of,a village where girls are married off to men old enough to be their fathers once they s...
454 64 44
Labari ne maicike da tausayi izaya makirci da kuma soyayya da sauransu
1.6M 111K 166
Choose me or Lose me ? I don't want to be your second CHOICE ! Start Date : 4th Feb 2022 End Date : 4th Nov 2022
2.7K 1.2K 31
𝗖𝗼𝗺𝗽𝗹𝗲𝘁𝗲𝗱!!♡ a kookv [ or taekook, whatever you like] fanfic~ Top kook~ Bottom tae~ . . promises are made to keep right~? or are they made...