NISFU DEENIY.......!

By deejasmah15

1.2K 117 25

She was exactly opposite of what he wants in a wife,,,he vowed not to be with her but fate has its own way as... More

PROLOGUE ( TEASER)
CHAPTER ONE (REJECTION)
CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO)
CHAPTER 3 ( MY PRAYING POINT)
CHAPTER 4 ( HOW I WISH....)
CHAPTER FIVE (MEETING.. ).
CHAPTER 6 ( MISFORTUNE....!)
CHAPTER 7
CHAPTER 8 ( HIS VISIT)
CHAPTER 9 ( THE RIDE)
CHAPTER 10 ( SHE'S BACK)
CHAPTER 11 ( SHE'S BACK II)
CHAPTER 12 ( DAYS TO GO.....)
CHAPTER 13 ( #BECOMINGMRSBAY)
CHAPTER 14 ( DAY ONE)
CHAPTER 15 ( HONEYMOON)
CHAPTER 16 ( A_RIDE_TO_YERWA)
CHAPTER 17 ( LIVING WITH HIM)
CHAPTER 18 ( HER EFFECT)
CHAPTER 19 ( SICK)
CHAPTER 20 ( SHE'S TO SOFT)
CHAPTER 21 ( GETTING TO KNOW HIM)
CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)
CHAPTER 23 ( DAY AFTER )
CHAPTER 25 ( SETTING THE GROUNDS)
CHAPTER 26 ( SACRED TRIP)
CHAPTER 27 (THE PERFECT HER)
CHAPTER 28 ( PROUDLY HIS❀)
CHAPTER 29 ( MILESTONE)
CHAPTER 30 ( HURRICANES)
CHAPTER 31 ( MEETING II)
NISFU DEENIY 32 (BROKEN)
CHAPTER 33 ( BROKEN 11)
CHAPTER 34 (DAY-OFF)

CHAPTER 24 ( GETTING ALONG OR GETTING APART?)

42 5 1
By deejasmah15

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Hello my people, how una dey ya ayyuka da alamura? Ina ma su son sui glowing kamar yadda Lele take yi or fiye da ma yadda take? Ina wainda suka ji ina ma zasu mori Ramadan promo da take yi? Toh ku matso kusa ku ji don kuwa Deedee organic skincare products ta shirya muku wannan na kwana uku kacal, inda zaku samu discount a duk package d'in ta da kuka siya and akwai free shower milk ga duk wanda ya sai package d'inta.

Ya zaku samu wannan discount d'in?

Wannan ba abu bane mai wahala just DM her at  +2348080932163

Kaya ne fa na yan kwalisa wallah nima can nake shirin kwasar kayana in koma don na ga kayan nata da rahusa kuma fa har adashe take yi ga wainda ba su da halin siya a nan take.

Za su fara Ramadan promo on February 25th-3rd march while delivery start on 10_13th March

20k promo bag
45k promo bag

Idan bazaki iya sayan promo bag ba akwai adashen promo bag na Ramadan din su.

Zakisamu:

Oil 30ml
Soap 250g
Scrub 250g
Face soap small
Lotion 100ml

Da free whitening milk shower gel

5k Zubi weekly for 4weeks kwasa products 20k.
1k daily kwasa skincare  product 20k after 20 days.
Kar ku bari a baku labari.
Location:Kaduna
Nationwide delivery

CHAPTER 24 ( getting along or getting apart?)



Idanuwansu ya rufe ruf ba su ji kuma ba su gani, sai abinda zukatansu suke raya musu akan lokacin. Sai da tafiya tayi nisa tayi ana shirin sake kusantata da azabar da ta fuskanta a daren jiya and it wasn't like ta warke daga na jiyan ne, ya sanya ta fara k'ok'arin janye jikinta.

Ture shi tayi a rikice sannan ta ja duvet ta lullub'e jikinta tana mai maida numfashi, hannu ya kai da niyyar sake janyo ta cikin fitar hayyaci don yau ma ya kai gejin da ba zai iya jurewa ba. Sake k'ank'ame jikinta tayi shi ma ya sake matsowa jikinta yana maida numfashi, shiru sukayi shi da ita kowa yana sauraron bugun zuciyar d'an uwanshi na mintoci sai da ya d'an samu natsuwarshi ta d'an dawo amma har lokacin babu mai kuzari a cikinsu bud'e idanunshi da har sun canja kala yana cewa " Awiro? (Why)".

"Tiy ni kuttu, (i'm sick)" ta amsa a shagwab'e,hannu ya kai ya dafa kanta yana cewa " me yake damunki?".

"You know naa".

Zare idanu yayi yana sake shige mata yace " but you didn't tell me so, mu ga wurin". Zare idanu tayi tana cewa " kaiii!! Haba Yaa" cewa yayi " meye a ciki, bud'e in gani ".

Da mugun sauri ta janye jikinta daga gareshi, tana shirin dira daga gadon ta ma manta that she's shirtless shi ma towel d'in an yar da shi a toilet cikin zafin nama ya rik'ota kan gadon ya dawo da ita yana cewa " ashe ma kin warke kenan, since you've gat a lotta energy".

"Ni ban warke ba ai" ta furta tana kwab'e fuska, cewa yayi " shi ne sai kin ji ma kanki ciwo, or make the one a jikinki to be more severe?". Shiru kawai tayi ba ta tanka ba sai duk'ar da kai da tayi, d'an murmushi ya saki ganin yanda ta tsume yace " in ta ni ne ba sai na duba ba, na bari ok? Hope ciwon ba sosai ba ne or mu je asibiti?".

"No need of that it'll heal in shaa Allah".

"Alright " ya furta yana mai tsura ma jikinta idanu, sai lokacin ne ta tuna ba ta da riga ai ko da sauri ta duk'e a cikin gadon tana sake jan duvet har kan ta, tab'e baki yayi in an effort to suppress his laughter komawa yayi gefenta ya kwanta haske ya kai hannu ya kashe bai kuma sake attempting tab'a ta ba har bacci ya kwashe shi a wurin. Jin numfashinshi yana sauka a hankali ya sanya ta sauka daga gadon, da wayarta ta haska ta nemo wata sleeping dress ta zura toilet ta shiga ta gyara wurin alwala ta sake d'aurawa kafin ta fito shigewa tayi jikinshi ta lumshe idanu a haka har bacci ya d'auketa.


Tun daga ranar bai sake nemanta ba duk da a d'aki d'aya suke kwana wato d'akinta ko na shi amma tsakaninshi da ita wasanni ne, as in dai yana gida he can't keep his hand off her amma bai tab'a crossing limits d'in shi da ita don ya fi son ta warke sosai kafin ya k'ara ziyartan ta.

Ya jure na tsawon kwana biyar inda ita a tun rana na uku ta koma office don tana jin ta normal, har girki ranar tayi musu ai ko a ranshi kamar ya goyata but ko a fuska bai nuna ba sai kwasar girkinshi da yayi ya cika ciki. Ta sha ko zai nemeta a ranar amma bayan normal romance da ya saba bai k'ara a kan hakan ba, though bai k'are darenshi ta dad'i ba sai haka dai ya sake jurewa ya k'ara mata kwana biyu akai ranar ko ko k'afa bai d'aga mata ba k'afa ba sai da ya huce takaicin kwanakin da yayi cikin kad'aici.

Shima dai second encountern nasu she feel pain, but ba kamar wancan ranar ba and bai sake d'aga mata k'afa ba ya cigaba da abinda ya fara. Tun tana raki har ta saba itama ta fara fiddo da nata salon more than he even expected from her, toh ai haka ake so bayin Allah.

A kullum kwanan duniya sake samun kusanci sukeyi da juna, sabo musamman wurin bacci yana sake shigarsu but one weird and funny thing is that akwai k'arancin sakewa, shak'uwa haka soyayya a tsakaninsu.

It might sound somehow tunda akwai sabo me ye ya hana shak'uwa mai k'arfi a tsakaninsu, wannan ba komai ba ne face rashin fira ko in ce har da rashin sanin mai d'an uwanshi yake ciki. Rayuwarsu a zahiri ma'aurata ne toh amma maaurata ai akwai yarda da kuma fahimtar juna tsakaninsu da ba da shawara ko, toh a gidan BAY dai babu don kowa kamar zamanshi yake yi magana in ba ta kama ba ne basu cika yi ba.

Duk da ko yanda Nadeefahr take k'ok'ari wajen ganin an samu wannan a tsakaninsu, tana yawan jan shi da hira but yana yawan katseta a tsakiya haka in shawara ne ma yana bata masu fissheta musamman a business but ba kasafai ya cika ba sai in ya ga dama. A lokacin ita ta k'ara saninshi amma shi bai ba tab'a zurfafawa ga sanin nata ba, ko nuna mata bai yi ya gano ita wacece ba ( Nadee's Arts da yake nema ba). Ran da tayi masa kyautan wani frame da tayi na zanenshi he's so excited inside, amma a fili ko thank you bai ce mata ba sai "it looks good" kawai yace mata kawai. Ita ko she don't care ko yace thanks d'in ko akasin haka don ta fahimci cewa he's really impressed kawai yana k'yashin fad'in hakan ne, besides ta sha kamashi yana k'arewa zanenta kallo a kullum ya shiga parlornta shine ma dalilin da ya sa ta dage ta zana masa duk da she's getting lazy to draw sai tayi da gaske take iyawa.

A haka har aka fara shirin azumi, a tsukin she's very busy da ayyukan rabon da zata yi. List tayi na wainda zata fara ba ma wa da kuma mutanen Yerwa complex za ta fara, a na saura sati d'aya aka kawo motar kaya guda aka ajiye a tsakiyar wajen tunda ga staffs har security kai har mabaratan da kan zo cikin complex d'in da masu shige da fice sai da suka samu na su kason su kuma nata staffs d'in tayi musu k'ari akan salarynsu.

Ranar har neighboring plazas da suke wurin sai da suka shisshigo suka amsa, da yake akwai security ya sanya ba a wani yi rikici ba kowa yazo zai amshi card mai number a jiki. Kana zuwa wajen amsa ka bada card d'in zasu yi signing su saka a cikin wata box sai baka package d'in mai d'auke da kayan masarufi mai d'an yawa, har wasu daga wani wuri can sun zo sun amshi na su ana ta shi ma mai rabon albarka.


Duk da ko ba wanda ya san waye don tayi gargad'i mai k'arfi akan hakan, ranar ko ma office ba ta je ba tana gidan Hajjah. Haka ko a social media ba su sanar ba, mutane ne ma suke ta aikin yad'a maganar ka san duk yanda aka yi da mutanen zamaninmu sai sun yi posting abu a media balle na rabo irin wannan. Su ma kuma Yerwa Group suke ta sawa a matsayin wainda sukayi aikin, ai ko ranar an yi ruwan godiya da sanya albarka a garesu. Yayinda aka dinga tagging manyan k'asa tun daga kan 'yan siyasa da 'yan kasuwa akan suyi koyi da abinda sukayi, ba a tsaya nan ba har gidajen TV da radio sai da aka dinga shela through nan ne aka wasu ma suka sake sani sai dare kafin motar ta wuce tunda kayan sun k'are hakan ne ma ya sa mutanen suka fara watsewa.

Washe gari kuma suka tafi orphanage da gidajen gajiyayyu aka kai musu na su har da kayan sawa, ba su tsaya nan ba har prison da rehab centres. Sai fatan Allah ya k'ara arzik'i kawai ake yi.


Yau da mugun gajiya ta dawo gida ga yunwa tana ji don ko breakfast ba tayi ba ta fita, wanka ta samu ta watso ta samu wuri akan sofa ta kwanta ko ta kan abincin ba ta bi ba don ba ta shi take ba gajiyar da tayi ma ya isheta. Agogo ta kalla 5:15 ta san ko bacci tace zata yi yanzu ba wani dad'inshi za ta ji ba, amma tana buk'atar hutu ko jikinta zai sake she's overstressed fiyeda kowace rana sauk'inta ma daga yau shike nan sai kuma shirin tarban azumi da ake yi nan da kwana biyu.

Hamma ta sake yi a karo na barkatai wayarta ta janyo tana dialing numb Hajjah, tana shiga ta d'aga da kulawa tana cewa " Lele yanzu nake zancenki a raina wallah, kin koma gida dai ko?". Ajiyar zuciya ta sauke tana mai cewa "uhmm gani nan ma kwance ga yunwa ga gajiya, and i can't cook" ta k'are tana k'wal da idanu kamar za tayi kuka kai ka ce tana gabanta ne, cewa tayi " Sannu diwu, ai aikin lada kike yi Allah ya karb'a yayi miki albarka yanzu ya zaki yi da abincin ko zaku siya ne kawai?".

"Uhm uhm, ni naki nake so bari ma in kirashi yazo ya amsa kawai ".

"Ya zo ya amsa tunda d'anki ne ko? Bari in kira Mele ya kawo miki tunda kin ga wurin ba kusa ba ".

"Toh Hajjah, a saka nama da yawa please ".

"Ba zan saka ba 'yar nema mara naman zan aiko da shi in kinga dama kar kici".

"Ki bar kayanki kawai mijina zai siya mini, don ma kin samu ana son aci abincinki ".

Dariya tayi tana cewa " ai ban kiraki na rok'eki ki ci ba, ba mijinki zaki kira ba ki kira na gabanshi in kin isa kafin ma ki san zaki yi shi mu har mun yi namu balle wai ki cusa mana takaici kuma soyayyar da muka ci ko rabinta ba zaku iya ci ba".


"Wai Hajjah kuma lokacinku ana soyayya ne? Like auren soyayya kuma kuka yi? I thought fa ladan noman nan aka muku da shi".

"Ina fa ake soyayya a lokacinmu? Ai soyayya sai gidan su Nadeefah da Burhaan, dalilinsu ma aka haifeta wasu ma tabarraki suke dangwala balle kuma mu da aka yi wa auren biyan bashi ba ma ladan noma ba".


Dariya ta k'yalk'yale da shi tana cewa " ni fa na ga alama ashe ba ma na ladan noma ba ne bashi aka biya, Amarya kuma Uwargidan Aji Garwa".


"Wallahi Nadeefah ki kiyayeni" ta furta tana murmushin halin Nadeefahr ita kowa bai tsira da tsokanarta ba, daga su kakanni har iyaye.

Cewa tayi " Hajjah Nadeefah fa kika ce? Ina Lelen ya tafi?" Ta k'arashe tana fashewa da kukan shagwab'a, " za ma kiyi ki gama ne amma na cire Lelen ban kuma kira " ta furta tana gimtse dariyarta.

"Ki yi hak'uri toh Ka'a, zau yaye".

"Uhm tohm, sai anjima " ta katse wayar kamar da gasken tayi fushi, amma tana ajiyewa Mele ta dannawa kira akan yazo tana nemanshi. Da yake yau ya fito gida tun safe ya sa da sauri don gudun rikicin Hajjah, ga kuma ba a dad'e da musu rabon azumin ba su ma infact ba su kad'ai ba har danginsu don kowa wakilcin unguwarshi aka ba shi. Kafin ya zo ta sa Yana ta shirya musu abincin a kwanukan acrylic masu kyau, an kuma cika mata naman da ta neman yana zuwa bai ko zauna ba ya kwashi kayan zuwa gidan Lelen.


Ita ko su na gama wayar murmushi tayi ta ajiye wayar, ta san halin Hajjah ba wani fushi da tayi ta dai fad'i ne kawai. Mai da kanta tayi inda yake ta sake kwanciya ba tayi baccin ba, sai ma kallo kawai da ta kunna abinta duk da ba wai tayi focusing completely kan kallon ba ne kawai dai saboda kar zaman ya gundureta ne.


Gab da Magrib Mele ya kawo sak'on, bell ya tab'a ta taso a gajiye tana d'aukar hijabi ta d'aura a kan denim gown d'in da ta sanya. Armless ce kuma short don iyakacinta guiwa akwai kuma tsagu a gefe da gefen rigar, fita tayi ta ganshi zaune cikin kujerun waiting room d'in.


Gaisawa sukayi a mutunce sannan ta amshi kayan ta koma ciki bayan ta shaida masa ya gaida Hajjah, tana shiga ta dire su a dining cupboard ta bud'e ta d'auko plates da spoons  ta d'auraye kana ta shiga kitchen ta d'auko ruwa da drink ta dawo ta zauna.


Serving kan ta biskin da miyar ganyen tayi wanda har da yankakkiyar kub'ewa a ciki ta zuba nama ta yawa, ta ci sosai ko dan tana jin yunwa ne oho sai da ta tattabar da cewa cikinta ya d'auka kafin ta tashi a wurin lokacin ma ana kiran Magrib.

Ba shi ya shigo gidan ba sai bayan ishai as usual da ledarshi, ajiyeta yayi a parlor yayi wanka first kafin ya wuce d'akinta jin shiru. Ai ko a kan gado ya tarda ta ta shige cikin bargo tana son yin bacci, ganinshi ya sa ta kwab'e fuska don ta san me zai biyo bayan shigowar ta shi.


Zama tayi tana cewa " Welcome home, Yaa".

"Uhmm thanks wife, ba dai bacci ba?" Ya tambaya yana zama a gabanta, gumtse bakinta tayi daga blushing d'in kiranta wife da yayi a shagwab'e tace " Allah ya na gaji ne ".

Cewa yayi " ai kwana biyun nan you are always tired, da mutum ya tab'a ki ki fara raki ".

Rufe idanunta tayi a kunyace tace " kai Yaa".

" Ba wani kai Madam, mu je in ci abinci and better be ready for me tonight". Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye yana extending mata hannunshi wai ta kama, nata hannun ta sanya cikin na shi da kanshi ya d'agata sai sake narkewa takeyi. Sai da suka je dining ya zauna kafin ya saki hannayen nata, serving d'in shi tayi ta na bashi labarin Hajjah ce ta aiko mata da shi kan shi ya gyad'a yana jinjina irin matsayinta a wurin Hajjahr in da wata ce ma fad'a zatayi mata akan k'in yin girki amma da yake ita ce sai ma aka kawo mata.

Bai ce uffan ba ya fara cin abincinshi, yayi dad'i don yana gwana ce wurin girki amma shi dai bai wani ci da yawa ba don in ba abincinta ba bai iya sakin jiki ya ci da yawa ko da na Umma ne kuwa. Turewa yayi gefe ya na goge bakinshi da tissue, tattara wurin tayi ta kai sauran kayan kitchen ta ajiye komai a inda ya dace kafin ta fito. A tsaye ta tarda shi ya kullo k'ofofin gidan ya dawo, ajiyar zuciya ta sauke tana bin shi a baya sai da ya shiga toilet d'in ta yayi brush kafin ya hau gadon yana janyota jikinshi kamar dai yadda ya fad'in bai ko d'aga mata k'afa ba har sai da ya samu natsuwar da yake buk'ata nan wani gajiyar ya sake sark'afarta haka ta koma gefe tana numfashi.


Washe gari kam k'in fita tayi don ta gaji da yawa, a yanzu kam ta tabbatar tana buk'atar mai taya ta aiki balle kuma ga azumi yana zuwa taa tabbatar cewa aikin zai fi haka amma kuma ta ina zata fara tunkararshi da maganar shi ne ba ta sani ba. Lumshe idanu tayi tana lissafin ko dai Umma za ta kira ne kawai? Amma kuma ai zai iya zama rikici a tsakaninsu don ta tabbatar d'an sakin fuskar da yake musu zai iya dainawa completely, in ma bai wulak'anta ta irin na baya ba so yanzu kwanciyar hankalinta da shi ya fiye mata komai amma kuma gajiyar mafita ce a gareta bayan ba ta tashi taga ana wahala a gidansu ba a k'asan ranta ta furta ' i'll then have to talk to him first, in ya yarda toh if he says otherwise kuma i'll be left with no choice than to respect his decision'.

Wayanta ta janyo tana sake tuna wa wainda zasu kawo package d'in da tayi order, sun bata assurance yau da yamma za a kawo godiya ta musu tana sakin murmushi ta tabbatar cewa it will impressed him even more. Kamar an tsikareta ta tashi da gudu ta nufi artroom d'in ta, cikeda k'warewa ta fara design d'in calligraphyn da take son had'awa a cikin package d'in shi ne ma ya d'auke mata hankali ta ma nemi gajiyan ta rasa.

Ayar " sharur-ramadhanal-lazhi-unzila-fihil-quran" ta rubuta da larabci ta kuma yi translation d'in sai can k'asan ta rubuta Ramadhan-Mubarak Habibie, tayi mai kyakkyawan wasali da khad'd'i mai d'aukar hankali. Rufe rubutun tayi da plain paper tayi spraying da gold kana ta bud'e, gyara inda bai samu ba tayi sai shi kuma rubutun ta sake tracing da bak'in kala mai k'yalli. D'an 3D finishing tayi da bak'in shi ma ta sake embosssing rubutun da glitters shi ma, ja da baya tayi tana sake kallon design d'in yayi mugun kyau. Wasu k'ananun abubuwa ta sake gyarawa har yayi mata yanda take so kafin ta fara framing a wani gold resin frame mai matuk'ar kyau anyi customizing wata a ciki da taurari, lumshe idanu tayi ta bud'e tana cewa " cute and unique, like my man ".

Sai ta saki murmushi as usual sai da tayi snapping da videos kafin ta d'auka zuwa parlor, a kan dining ta ajiye ta zauna cikin kujera tana jiran masu kawo sak'on duk ta k'agara. Ba su suka kawo ba sai 3:15 ita ta fita ta amso tayi signing kafin security suka shigo mata da shi cikin gida, bud'e package d'in da akayiwa kyakkyawan wrap tayi komai da tayi order an saka tunda ga carbi da customized pray mat mai taushi ga mug, k'urani har da trainers da track suit farare na Puma a ciki a ciki. Murmushi tayi ta maida ta d'aure da kyau yanda aka kawo ta had'a da frame d'in ta nufi ciki da shi, sallah tayi kana ta fito kitchen.


Yau tuwo tayi musu na shinkafa da miyar egusi, da assorted meat traditional drink tayi masa na pineapple, ginger da kuma coconut both milk d'in da fruit. Shirya komai tayi a dining sannan ta shiga d'aki, wanka ta shiga ta dad'e kafin ta fito haka ta sake zama a gaban madubi light makeup tayi da nude lips sai kuma smoky eyes. Roller ta d'auka tayi rolling gashin kanta da kyau yayi kamar spagetti making her look so sexy and beautiful red hair color ta fesa a k'arshen gashin ba tareda ta d'aure shi ba turare ta shafa a gab'ban jikinta kafin ta nufi closet shiryawa tayi cikin wata double slits straight gown na Giorgio Armani emerald color.



Wanda ya amshi jikinta sosai musamman ma 'yar kib'ar da tayi da ta k'ara k'awata jikinta, tsayawa tayi a gaban madubi tayi juyi 360 har ta d'auki wayarta da niyyar shiga snap sai kuma ta fasa don ganin rashin kyautuwar hakan. Hijabi ta d'auko ta hau kan dadduma tana tada sallahr magriba, kamar yadda ta saba yau ma bata tashi ba sai da ta gabatar da sallahr ishai. Turare ta k'ara a jikinta ta d'auki wasu shegun stilettos na kamfanin Fendy kamar mai zuwa party kafin ta fita parlor, a daidai k'ofar shigowa part d'in ta taci karo da Burhaan zai shigo.

Don ya shigo gab da Magrib ya ji k'arar ruwa a toilet d'in ta kasancewar yayi alwala kuma fita zai yi zuwa masallaci ya sa bai shiga toilet d'in ba don he's very sure sai ya karya alwalarshi in ma bai yi missing sallahr a jam'i ba. Ya sanya ya ja 'yanmatan k'afafunshi zuwa masallaci, yanzu ma da ya dawo ya ji shirun yayi yawa ya sanya ya biyota tunaninshi ko dai ba lafiya ba. Kyakkyawar ganin da yayi da ita ya sanya shi sandarewa yana binta da kallo sala-sala, bai tab'a ganin mace mai kyau da kwalliya yake wa mugun kyau kamar Nadeefah ba. Smoky eyes d'in da tayi ya sake fito mata da hazel eyes d'in ta masu girma da kyau ga su kusan kullum a lumshe kamar na mai jin bacci, miyau ya had'iye starring at her lips da suka ji lip gloss mai k'yalli yana imagining taste d'in su and the wet lips ya k'ara maida su so luscious and tempting.


Cikin muryarta mai sanyi, taushi da kwantar da hankali tace " Yaa ka dawo?".

Lumshe idanu yayi ya bud'e a kanta yana cewa " yeah, ya kike?".

"I'm good, ya aikin?".

Kasa amsawa yayi ya matso gabanta yana sake kafe lips d'in ta da idanu, saitawa yayi yana k'ok'arin had'ewa da na shi. Zillewa tayi cikin salo tana cewa " i'm sure you are hungry, come lemme serve you". Da wani kallo ya bita da hooded eyes d'in shi, cije baki yayi yana bin bayanta idanunshi k'yar a kan kwankwasonta da take juyawa yana rhyming da tafiyarta na catwalking.

Kafin ya iso ta ja masa kujera zama yayi ita kuma ta fara serving d'in shi, kafin ta saka wa kanta itama spoon ta ba shi ta san yafi ci da shi ita ko hannunta ta wanke ta sanya a ciki. Gutsura tayi d'an dai-dai tana kaiwa bakinta, yanda ta sanya hannun kamar da wani salo sai da ya sake motsa masa da magudanar jinin jikinshi. Balle da ta tsotse yatsun tana lumshe idanu tana gyad'a kai alamun abincin is giving, lashe na shi bakin yayi so naughty and kinky yana had'iye yawu. Har sai da tayi loma uku kafin ta lura bai cin abincin cewa tayi " Yaa ka k'oshi ne or baka so in sama maka wani abun?".

Girgiza kai yayi ba tareda yace uffan ba ya fara cin abincin bai ko sake dubanta ba, don she's tempting him in ya biyewa kallonta kuma zai iya yin abinda bata tab'a zata ba. Shi fa ma bai san what's getting over him a kanta ba? In dai zai ganta ko da decent kaya ne sai yaji shaawarta balle kuma yau that's she's looking like a goddam b**ch kuma ko ta nuna ta san abinda yake faruwa. God knows wannan na d'aya daga cikin weakness d'in shi he wants a decent girl with a touch of Cardi B musamman a bedroom and Nadeefah is actually perfect or more than he's asking a d'iya mace. Da haka aka k'are cin abincin having the worst tutor of lifetime, shi ya fara tashi don yadda take cin abincin kamar yaron goye dake koyan cin abinci kan couch yaje ya zauna ya sake kafa mata idanu kamar tsohon maye irin na Soban nan masu gani har hanci.



After what seems like an eternity or so aka samu ta kammala cin abincin, hannunta ta ja tissue ta goge da bakinta kafin ta tashi. Wanko hannun tayi ta kwashe kayan kan dining d'in ta goge, ta dad'e a cikin kitchen d'in hakan ya kawar masa da hankalinshi daga kan ta zuwa TV. Wanke-wanke tayi ta goge koina ta tsane kayan, kafin ta maida su inda ta d'auko kamar ba a yi amfani da su ba.


Wuceshi tayi ta kinkimo package d'in ta zo gabanshi ta zauna, a kan cinyarshi ta ajiye caressing him a cinyar k'adan da akaifarta masu d'an tsawo but well cut ba yanda zai ji ma mutum ciwo ba. Kallonta yayi da idanu ya tamabyeta ko na menene, itama da idanun ta nuna masa ya bud'e kawai. Tab'e baki yayi ta bud'e cak ya tsaya ya kalli cikin box d'in ya sake dubanta, murmushi tayi kawai ciro kayan yayi ya bubbud'e originals d'in ne kuma masu tsada ba wai gama gari ba.


Had'asu yayi da trainers d'in kana ya zaro daddumar itama mai mugun taushi an rubuta Habibie a kai, haka mug d'in da customized Quran notebook shi customized da pen sai casbaha mai kyau bak'i na maza sai wani k'aramin alarm clock. He can't help but smile san da ya d'aga box d'in idanunshi ya sauka akan frame d'in da yake da tabbacin ita ta zana shi, he's an art lover hakan ya sa yafi jin zanen a ranshi fiyeda komai.

Mazewa yayi yana b'oye excitement d'in shi yace " what for?". Murmushi tayi tana cewa " it's my Ramadan gift to you Yaa, Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi".

"Ameen, but wife you don't have to do it because.....?"

"Ba ka so na so bai cancanci ka amshi kyauta daga wurina ba ko? Nima i'm not forcing you to do so but can you accept it as a gift from a lil sister to her elder brother?".

"Wife.....!".


"Issokay if you don't want, Now i gat it". Daga haka ta tashi controlling her tears ta shige cikin d'akinta banging the door, da idanu ya rakata yana mai jin ba dad'i a abinda ya faru. Wai shin ma menene tayi masa da zafi haka da har ya sa bai iya bata regards d'in da ya kamata? She loves him and wants things to settle between them but shi me yake yi apart from shunning her away da kuma nuna mata cewa ba ta kai matsayin wacce zai iya rayuwa da ita ko son ta ba.


Ba laifin shi ba ne Allah ma ya sani, yana iyaka k'ok'arinshi a kanta he hates been mean and cold towards her amma zuciyarshi ta k'i ba shi had'in kai. Does that means he's a monster or bad person? In many scenarios the answer is a big and fat YES. Shi mugu ne tunda ya kasa tank'wara zuciyarshi ga son wacce ta cancanci a so ta a kuma kula da ita, bai kuma tsaya a nan ba sai ya nuna mata cewa her presence bai da wani muhimmanci a gareta sai ta wajen shimfid'a.

Wannan kuma is an insult to her saboda Nadeefah daban ce a cikin mata ta tara dukkan abinda yake so " amma kuma ta zubda ajinka wajen fad'a maka tana sonka" zuciyarshi ta furta masa cikin son sake nuna masa cewa ita d'in tayi k'aranta da yawa but does that means she's cheap like how he thought in the first place answer shi ne NO, she's way more than that she's a priceless jewel ya kuma san da haka sai dai hange-hange irin ta zuciyarshi ya hanashi kamuwa a cikin soyayyar tata kuma bai son saka mata rai ta hanyar mata cewa he's cool and ok with har ma ta fara tunanin cewa ya fara sonta ne don duk ran da ta gane bai son ta d'in that thing will definitely break her completely abinda kuma bai so ko fata ne har abada musamman a yanzu da ya san muhimmancinta tarkata kayan yayi ya bi bayanta da sauri.


Ba ta bedroom d'in da ya saba shiga ciki, bud'e Amish one d'in da ke dama yayi ba ta ciki shi ma na hagun ya bud'e wato mai shabby chic design nan ya tardata a swinging chair da ke gefen ta zauna ta tura k'afafunta cikinta ta kuma d'aura kanta a kan tank'wasassun guiwoyinta hakan ya ba wa gashinta bajewa a gadon bayanta da ma fuskarta. Gabanta ya k'arasa yana mai k'ok'arin d'agata k'wacewa tayi in da ta kusa fad'uwa saboda kujerar dai lilo take yi ga uban pillows a ciki da kuma shape d'in ta, saurin rik'ota yayi cikin jikinshi yana bubbuga bayanta alamun rarrashi yana cewa "shhhhh......I've got you".

Banza tayi masa tana mai jin d'aci a ranta da kuma takaicin kanta da kanta, Allah ya sani ba ta tab'a nadamar son Burhaan ba haka har yau ba ta dana sanin furta masa abinda ke cikin zuciyarta amma kuma a yau taji haushin abinda ya faru fiyeda komai. Wanda ba komai ya assasahi ba face ganin darajarta yayi fad'uwar bak'ar tasa a idanun Yaa Islaam da yake ganin duk wani da zata yi masa don karkato da hankalinshi ne kanta, wanda in da dan hakan ne ai ba abun kunya tayi ba Aa she's playing her duty right as a wife amma ita ta na yi ne saboda kyautatawar miji da mata ba don komai ba. Kuma ko bai aurenta ai d'anuwanta ne so ba shi kyautar da duka ba ta fi 200k ai ba wani abu ba ne da har zai iya k'in amsa saboda ba ta kai matsayin ba shi kyauta ba.


Janta yayi zuwa kan carpet yana mai cewa "ki daina kuka, kanki zai yi ciwo".

Cikin rad'a-rad'a da muryar kukan tace " i'm sorry I'm forcing myself on you, in shaa Allah ba zan kuma ba".

"I should be the one sorry not you wife, and who says you are forcing yourself ehnn kar fa ki manta ni mijinki ne fa".

"But it's like I'm overdoing it, ka yi hak'uri ba zan sake ba ".


"Shhhhhhh you are just overreacting over what just happened, like i wasn't expecting that from you that i felt shame of myself da ban tab'a baki kyauta ba amma ke kinyi tunanin ba ni ".

'' Ni ban baka ko dan tunanin komai ba,Yayana na bawa in dai ina da wannan matsayin a wurinka you won't hesitate in collecting a gift from me ".

''Kin fi gaban nan ma Wife, ki daina kuka kin ji " ajiyar zuciya kawai ta sauke tana janye jikinta daga gareshi, toilet d'in room d'in ta wuce wanka tayi tana shilla kayan a laundry ta fito yana inda ta bar shi ko mai bata shafa ba nightie ta zura kawai ta haye gadon har yanzu k'irjinta na suya. Da idanu ya rakata ganin tana ta sauke ajiyar zuciya kuma hawayen bai daina zuba ba, ta lallashi kanta a toilet a kan kukan but tana ganinshi suka sake zubowa "so she's a fool and stupid in front of him, well that's good" yanda tayi makes her look like a barbie, tasowa yayi ya hawo gadon a bayanta ya kwanta yana janyota jikinshi cije baki tayi yau kam ko yafi k'uda kwad'ayi ba ta ba shi sai da ya karb'a ta k'arfi wato ba ta da matsayi a idanunshi da ya wuce plaything toh yau zai ga tsiya don zata nuna masa itama mace ce kuma mai zuciya. Shi ma ko kamar ya san me ke zuciyarta bai ko nema ba tunda ya rungumeta cikin k'irjinshi ya tafi tunanin rayuwa sun dad'e kafin bacci ya kwashe su.


Da asuba yana tashi sallah ya kwashe kayan ya closet d'in shi ya adana, ita ma sallahr ta yi ta kwanta sai lokacin take scolding kan ta akan kukan da tayi. Taune lips tayi tana cewa "ai yanzu sai ya sake raina mu ke da kan ki kikayi alk'awarin daina masa kuka akan soyayya and here we are" ta k'are tana tsaki, jan duvet tayi cikeda nauyin zuciya har kanta ta lumshe idanu tana tunanin mafita................

Toh Allah ya wanye mana🌚.

Jama'a a samu wani yayi ma NEPA magana mana, suna azabtar da bayi da yawa nan nace zan yi typing Friday. Toh ba su ba mu wuta ba sai da dare, dai jiya na samu nayi typing ban ma gama da wuri ba dare yayi sosai shiyasa na bar shi sai yau. Da fatan za kuyi maneji a d'an yi adjusting da yanayin da muke ciki, zan samu nan kafin Wednesday in sake dropping another update d'in in shaa Allah.

Deejasmah ✍🏼

Continue Reading

You'll Also Like

2.9M 71.5K 22
"Stop trying to act like my fiancΓ©e because I don't give a damn about you!" His words echoed through the room breaking my remaining hopes - Alizeh (...
2.6M 150K 48
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
190 49 5
In a village where female empowerment has never been heard of,a village where girls are married off to men old enough to be their fathers once they s...
1.2M 63K 59
π’πœπžπ§π­ 𝐨𝐟 π‹π¨π―πžγ€’ππ² π₯𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐑𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐒𝐞𝐬 γ€ˆπ›π¨π¨π€ 1〉 π‘Άπ’‘π’‘π’π’”π’Šπ’•π’†π’” 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ✰|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...