NISFU DEENIY.......!

By deejasmah15

1.2K 117 25

She was exactly opposite of what he wants in a wife,,,he vowed not to be with her but fate has its own way as... More

PROLOGUE ( TEASER)
CHAPTER ONE (REJECTION)
CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO)
CHAPTER 3 ( MY PRAYING POINT)
CHAPTER 4 ( HOW I WISH....)
CHAPTER FIVE (MEETING.. ).
CHAPTER 6 ( MISFORTUNE....!)
CHAPTER 7
CHAPTER 8 ( HIS VISIT)
CHAPTER 9 ( THE RIDE)
CHAPTER 10 ( SHE'S BACK)
CHAPTER 11 ( SHE'S BACK II)
CHAPTER 12 ( DAYS TO GO.....)
CHAPTER 13 ( #BECOMINGMRSBAY)
CHAPTER 14 ( DAY ONE)
CHAPTER 15 ( HONEYMOON)
CHAPTER 16 ( A_RIDE_TO_YERWA)
CHAPTER 17 ( LIVING WITH HIM)
CHAPTER 18 ( HER EFFECT)
CHAPTER 19 ( SICK)
CHAPTER 21 ( GETTING TO KNOW HIM)
CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)
CHAPTER 23 ( DAY AFTER )
CHAPTER 24 ( GETTING ALONG OR GETTING APART?)
CHAPTER 25 ( SETTING THE GROUNDS)
CHAPTER 26 ( SACRED TRIP)
CHAPTER 27 (THE PERFECT HER)
CHAPTER 28 ( PROUDLY HISโค)
CHAPTER 29 ( MILESTONE)
CHAPTER 30 ( HURRICANES)
CHAPTER 31 ( MEETING II)
NISFU DEENIY 32 (BROKEN)
CHAPTER 33 ( BROKEN 11)
CHAPTER 34 (DAY-OFF)

CHAPTER 20 ( SHE'S TO SOFT)

39 4 0
By deejasmah15

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Alhi wattpad sannunku da k'ok'ari tunda 'yar comment da vote d'in ma kun daina sai dai reads but ba kwa rating storyn mutum, shiyasa ma nayi posting 17 na manta da ku, a dai gyara gaskiya ko in k'yaleku in dawo WhatsApp in tare abuna.

Wannan shafi tukuici ne ga all team Nadeefah living out there, make you guys make some noise let's scare team Burhaan, wato soyayyarku daban take ita ce ma ke bani energyn typing ko ban shirya ba💖.

Na san page d'in nan yayi kad'an in zayyano kalar so da k'aunarku but i'll take my time and start appreciating your efforts daga chapter 21 da zai zo anytime soon but kafin nan ku had'u k'asan page d'in nan ku wataya😘😂.

CHAPTER 20 ( She's too soft)

A firgice ta bud'e idanu jin saukan wani abu mai d'umi da danshi akan lips d'in ta, nan tayi arba da fuskar Burhaan da ya lumshe idanu yana k'ok'arin kissing d'in ta. Janyewa ta fara k'ok'arin yi ta hanyar matsar da fuskarta baya, amma unfortunate for her ya riga da ya dafe kanta ta baya bud'e baki tayi da niyyar magana ai ko hakan ya zama tamkar wani dama ta bashi don ko claiming bakinta yayi da kyau yana yanda ya ga dama da ita.


Tun tana mutsu-mutsun k'wacewa har ta saduda ta zurawa sarautar Allah idanu, yayinda hawayen da ba ta san ko na menene ba suka hau aikin zarya akan kuncinta suna sauka akan lips d'in ta. D'and'anonsu da yake ji bai sa shi janyewa ba sai ma manne mata da ya sake yi, sai da yaji kamar numfashinsa zai d'auke ne sannan ya janye gasping for air. Time d'in ita ai nata yayi k'aura har ya dawo ba tareda ta sani ba, yana sakinta ko ta fad'a kan gadon lak'waf don tuni ya riga ya rabota da kan stool d'in da take zuwa kan jikinshi.


Maida numfashi sukeyi ita da shi kamar wainda sukayi gasar tsere, sun d'auki lokaci mai d'an tsayi a hakan kafin ya bud'e idanun shi da ciwo da jaraba ya sauya kamanninsu ya dubeta. Ware idanu yayi ganin har lokacin hawayenta suna zuba, hannu ya kai ya tab'o su sannan ya bud'e muryar da ta riga ta canja kamar ba tashi ba yana cewa.

"Wannan dai kukan munafunci kike ba komai ba, abinda fa kika dad'e kina kwana addua shi na yi miki then what's the big deal ko dai kukan murna ne kike yi?" Da sauri ta bud'e idanunta tana kallonshi da mamaki, waro mata mayun idanunshi yayi ya sake furta '' yes you've been praying for this very moment, ga shi kuma na baki abinda kike son. So you should be thankful to me for that don na baki cikon burinki kin ga ko yanzu kika mutu you are contented, so chill taimaka miki nayi ". Daga haka ya sauka daga gadon with zero to little energy ya nufi hanyar toilet, da idanu ta rakashi cikeda alajabi.


Sai kuma ta saki murmushin tuno kalamanshi, wai taimaka mata yayi ko dai ya taimakawa kan shi?. Ta san tabbas tana son shi tana kuma adduar daidaituwar zamansu cikin lokaci k'ank'ani but bata tab'a exceeding limit d'inta ta hanyar tunanin kasancewarsu a yanayin d'azu ba, abu ne da ya fi k'arfin tunani ko lissafinta yau sai gashi ta farka cikinshi amma kuma ya wani lak'a mata. Cije leb'e tayi tana sake zurfafa a tunaninta kan shi da lamarinshi, hakan ya sa bata san fitowarshi ba sai saukar ruwa da taji a kan fuskarta.

Da sauri ta kalle saitin da ruwan ya feso mata, shi ne tsaye shamelessly sanye da towel fari k'al. Yana jifanta da wani irin kallo saurin kawar da fuskarta tayi, shi ko tab'e baki yayi cikin ko in kula yace " wai ke hala ba kya sallah ne? Tun d'azu muka tashi amma kina kwance sai juyi kike akan gado. Bayan kin gama cin barci kamar ba jinyar mutum kike yi ba har shi patient d'in ya riga ki, ko haka ake jinya a garinku oho ". Ya k'arashe yana mai juya mata baya, kallon agogon dake mak'ale a bango tayi 6:28 da sauri ta tashi tana mai istigfari a ranta.


Fita tayi zuwa room d'in ta tana mai cigaba da shafa wuyanta da sai yanzu ta sake jin rik'ewar da yayi, wanka ta yi a gurguje ta d'an gasa wuyan a cikin toilet d'in ta lakaci neurogesic ta shafeshi da kyau kana ta fito. Doguwar riga ta zura tana tada sallah ko da ta idar ta d'an d'auki lokaci mai tsayi tana lazumi, sannan ta ajiye hijabin. D'akin ta fara gyarawa ta kimtsa shi thanks to her vacuum cleaner da mop d'in ta, sanna ta fito zuwa parlor shi ma gyarashi tayi ta shiga kitchen.


Ruwan zafi ta fara sakawa ta had'a masa tea da yaji kayan k'amshi, ta lura yana son milk da yawa hakan ya sa ta zuba masa a wasu containers masu kyau da sugar ta nufi d'akin na shi. A parlor ta sameshi kwance dafe da kanshi, jiri yake gani ga kuma yunwa. Sannu tayi masa ta gaisheshi a d'an dake ya amsa, bata ko kula ba ta ajiye masa trayn da ta sako ruwan zafin akai tana mai tambayarshi " what do you want for breakfast?".

Kamar ba zai amsa ba don har sai da ya had'a tean shi dai dai yanda yake so, kafin yace " anything". Gyad'a kai tayi kawai ta tashi komawa kitchen d'in tayi tana lissafin abinda za ta had'a masa, tuno jawabin Dr tayi "banda abu soyayye for now". Sai kawai ta d'ebo irish ta fere ta yayyanka, porridge ta had'a mai wanda ta ji ganye da hanta a ciki.


Bai wani d'auketa time ba ta kammala a cikin bowl ta sanya masa, ta d'aura akan tray ta nufi d'akin nashi. Har yanzu yana a kwancen don sosai bai jin dad'in jikinshi dauriya kawai yake yi, ajiye masa tayi ta nufi cikin d'akinshi. Gyarawa tayi da kyau har da canja masa bedsheet ta wanke masa toilet da kyau, fita tayi ta d'auko burnernta guda d'aya da humidifier ta sanya turare a ciki ta turara masa d'akin. Kana ta dawo parlorn nan ko ta tarda ya ci sosai kam har ya ture, hamdala tayi ga Allah ganin yaci d'in sai dai kuma yana yin na shi ya d'an razanata ba kad'an ba.

Cewa tayi " a sake kiran Yaa Adnan d'in ne ko kawai mu tafi asibiti ne?". Girgiza kai yayi yana cewa " no need, don suna hanya yanzu haka zasu kawo min magani ".  Tace " toh, ko zaka shiga ciki ka kwanta kafin su zo d'in ?" Ok yace, yanzu ma ita ta taimaka masa ya shiga ciki ya kwanta yana lumshe idanun don sosai yanayin d'akin yayi masa dad'i kashe AC tayi ta masa lullub'i ta fita. Gyara masa parlorn tayi ta koma ta ciro burnern da humidifiern shi ma ta sanya masa k'amshi, sake lek'ashi tayi ta tarda yana bacci silenty ta rufe d'akin ta koma tana k'arasa gyaran parlorn. Tana yi tana duba shi har ta kammala, saida ta kammala har da wanke kayan da ya b'ata musu ita da shi a daren jiya da amai babu k'yama ko wani abu.


San da ta kammala komai ne taji wata iriyar gajiya ta sark'afeta ashe aikin gidan ba kad'an ba ne, dole a ce za'a kawo mata 'yar aiki amma kuma ya zata yi tunda mai gidan ba ya so.


Canja kaya tayi zuwa doguwar rigar atamfa mai bud'ad'den k'asa, simple d'aurin d'an kwali tayi ta fito zuwa parlor. Baiwar Allah sai lokacin ta samu sukunin yin breakfast da sauran porridge d'in da ta had'a masa ta sha tea, wayarta ta d'auka tana mai tunanin sanar da gida sai kuma ta kwab'i kanta gudun a samu matsala sanin halin kayanta.


Kiran wayar da ta saba a kowace safiya shi tayi musu, ta kira Ummu sun d'an dad'e suna hira kafin ta katse. Kana ta kira Abbu shi ma sun dad'e da shi yana ta tsokanarta kamar wani kakanta, murmushi tayi kawai tana masa shagwab'a. Kamar yadda ya saba tambayarta ko tana cikin matsala ko damuwa haka yau ma yayi, sai dai amsar d'aya ce ba ta da damuwa nasiha ya sake mata kafin sukayi sallama. Lumshe idanu tayi tana mai jin kewar gidansu na kamata, kamar ta bud'e idanu ta ganta a Abujan haka taji sai dai babu dama.

Hajjah ta kira tana d'agawa tace " 'yar tusa wai da gaske k'auran kika yi ne?'' Cewa tayi " girma dai nayi ina adduarku kenan in girman?". Dariya ta sanya tana cewa " addduar ta mu ta amsu kenan? Ai ko bari in kirawo Tayyib in shaida masa a fara shirin siyan miki shoprite d'in ".


Juya idanu tayi tana cewa " sai kin dawo " dariya ta sanya jin yadda take maganar ba a sake da ta saba ba kamar dai da damuwa a harshen nata, cewa tayi " Lelena, kina lafiya kuwa?".

''Yes, lafiyata k'alau me kika gani?'' Ta amsa cikin son daidaita maganarta. Cewa tayi " ba dai lau ba, akwai abinda ke damunki ne?". Cirgiza kai tayi kamar tana gabanta tana mai cewa " babu" a takaice ta amsa, tashi zaune tayi tana cewa " Burhaan ne?". Shiru tayi tana mai tunanin gaya matan ko A'a, jin shirun nata ya sanya ta zargin ko wani abun Islaam d'in yayi mata hakan ya sa ta cewa "Nadeefah!! Kina jina kuwa".

A d'an fisge ta amsa da cewa " uhmm, ina lafiya kar ki damu ". Cikin rashin yarda da maganarta tace " kina ina ne haka?" Amsa ta bata da " gida''. Gyad'a kai tayi tana cewa " ok, ki huta sai anjima ko?". Ba ta kawo komai ba tace "toh Hajjah, zan sake kiranki in na gama aiki " daga haka ta kashe wayar ta nufi side d'in Islaam don duba ko ya tashi.


Ita ko Hajjah tana katse wayar, number drivernta da ke nan zaune ba kullum yake aikin ba saboda rashin fita mai nisa da sukeyi. In ma fitar ta kama dole sai dai cikin 'ya'ya ko jikokin wani ya fitar da ita ba dai driver ba, ta doka ma kira yana d'agawa tace " ka shirya kazo ka kaini gidan Lele". Cewa yayi " toh, Hajjah".

Gyara zaman lafayarta tayi tana mai k'osawa ya iso su tafi, ko 'yan uwanta su YaMara ba ta kira ba. Ya d'auki kusan one hour kafin ya iso ta ko kirashi a waya yafi sau uku kafin Allah ya kawo mata shi, yana isowa ta shige bayan ta gama zazzage masa kwandon k'orafi aka Yana ta bawa sallahun in an zo wurinta ta ce ta fita.

Sanda ta shiga d'akin ya tashi, tambayarshi tayi ko yana buk'atar komai. Ce mata yayi Aa sai dai tambayar ko su Adnan sun zo, cewa tayi " ba su k'araso ba tukun". Yace " ok mik'o min wayata " mik'a masa tayi ya fara dokawa Adnan d'in kira, ringing biyu ya d'auka yana cewa " ka cire wayar a DNDn kenan?".

Cewa yayi " eh, ya na ji ku shiru ne?" Yace " yanzu zan taho, result d'in ne bai dad'e da fitowa ba don ma Ade d'in da kanshi yayi running test d'in but gimme just 5 minutes zan zo gidan ". Ok yace kawai bai ko jira jin mai zai ce ba ya kashe wayar, yana mai bin ta da kallo k'asa-k'asa ba ta ma san yana yi ba sai ma fidgetting yatsunta da take yi kanta a k'asa feeling so uncomfortable and unease.


Suna zaune kamar kurame ba mai cewa wani ko uffan, Adnan ya k'araso. Ta main entrance ya shigo parlorn babu kowa, sai kawai ya nufi k'ofar parlorn sai knocking suka jiyo. A tare suka mik'e zuwa parlorn, fitowarsu tayi dai-dai da shigowarshi cikin parlorn. Bai yi zaton samunsu a tare ba, musamman wai daga cikin bedroom sai dai ganin nasu a tare bai sa ya nuna mamaki ko al'ajabi ba. Mazewa ma yayi yana zama gefen da Burhaan d'in ya zauna, yayinda ita kuma ta zauna a d'ayan kujerar.


Gaisawa sukayi a mutunce shi da Nadeefahr inda yake tambayarta mai jiki, cewa tayi " da sauk'i, Alhamdulillah" masha Allah ya furta yana mai duban Islaam da yayi cid'in-cid'in da fuska, Gyad'a  kanshi yayi yana mai jinjina halayyar Burhaan d'in. Kace baka son mace amma kuma kana d'an karen kishinta kamar me, cewa yayi " How far Man ya jikin?".


Da sauk'i ya furta yana mai duban gefen Nadeefah ya jefa mata kallo mai d'auke da sak'on da ita ta gane abinda yake nufi, wato ta fita. Mik'ewa tayi tana excusing kan ta zuwa waje, tana fita ko ya d'an marairaice fuska yana mai cewa " wai ina maganin ne, i'm dying jiya da k'yar na kai safiya".

"So sorry" ya furta yana ajiye masa ledar a gabanshi, mik'ewa yayi zuwa kitchen d'auko ruwa yayinda shi kuma yake ciro magungunan. Da mamaki yake kallonshi ganin har da maganin low sugar, kafin yace " me ya had'ani da low glucose level kuma?" Cewa yayi " abinda result d'in ya bada kenan, i'm sure ka san abinda yayi causing maka shi Burhaan ka azabtar da kanka da yawa da rashin cin abincin nan bayan ka san ba juriyar yunwa kake da ita ba". Ya k'arashe yana zama ruwan ya mik'a masa, drugs d'in ya b'alla masa dai-dai dose d'insu ya ba shi. Sha yayi cikin sanyin jiki shi kuma ya fara had'a allura, a cikin canula ya tsira masa kasancewar ta jijiya ce kafin yayi discarding ya dawo yana zama.


Kallonshi yayi jin yana cewa " but ai shi low blood sugar ba rashin cin abinci bane yake kawoshi, haka shi ma ulcern ciwuka ne masu zaman kansu ". Gyad'a kai yayi yana cewa " yes, ba yunwa ke kawosu ba amma yana triggering d'in su tunda shi blood glucose is dependent on both the  hormones responsible for glucose delivery and digestion, da enzymes da kuma precursor na samar da shi glucose d'in wanda kasan ta diet ake samun shi ".


Ya nisa kadan kafin yace " haka za shi ma ulcern, ka san dai kamar ciwo ne a cikin ciki ko hanji shiyasa ma hausawa kan kirashi da gyambon ciki. Abinda yake kawo shi ko guda uku ne, ko dai hyper secretion na acid d'in ciki wato gastric hydrochloric acid, ko cinyewar gastric mucosal barrier sai kuma infection by bacteria. Wanda ka san rashin cin abinci a lokuta da dama kan sa ulcern ya tashi which is a long mechanism da ba sai na tsaya maka bayani ba so bai kamata ka na tantama akan ciwukan naka and their relationship to food. Tukunna ma me yake hanaka cin abinci?".


Shiru yayi yana Digesting maganganun da ya fad'i which ya san gaskiya ya fad'a ba komai ba, sai kuma ya kyab'e bakinsa yana mai cewa " banda appetite ne" a dunk'ule. Gyad'a kai yayi yana cewa " ai ko ga shi nan ya kusa costing rayuwarka, that aside sai maganar tsakaninka da matarka meyasa ba zaka sauke hak'kinta da Allah ya rayata a wuyanka ba?".

"Malam wannan ba huruminka ba ne, ko k'arata ta kawo maka ne wai ?". Ya furta a d'an hasale don ma muryar ta disashe, cewa yayi " sai ta kawo min k'ararka? Bayan is so obvious ba ka bata hak'kinta?".

"Ban sonta ne shiyasa ko zaka tursasa ni ne? A na dole ne?". Girgiza kai yayi yana cewa " na san ka sani, kawai take sanin kake yi amma babu had'in hak'kinta da so ko k'iyayya in Allah ya tashi kamaka da shi ba zai duba wannan ba tunda iyakarsa ta shallake nan ko so kake taje waje ta nema ne? Besides kai ma fa kana so tunda ga shi nan kana shirin gangarawa akan haka and tablets d'in da kake sha don suyi suppressing maka desire are killing you and kai ma kasan da hakan ka kuma san solution d'in is non but embracing your wife shegen pride d'inka da k'in gaskiyarka ne suke rufe maka idanu. Ni mai sonka ne shiyasa nake maka nasihar ka rungumi matarka ku gina gidanku cikin aminci da soyayya tunda Allah dai ya k'addara Suliem ba RABONka ba ce ita".

"Naji ka Malam, Kayi abinda yake gabanka please kadaina damu na kana sa mun ciwon kai" girgiza kai kawai yayi yana mai kallonshi.

Ta gefen Nadeefah kam ko a jikinta wai an tsinkari kakkausa, don ko ita ba ma ta san wainar da suke toyawa ba. Tana kitchen tana shirin d'aura girki, traditional jollof rice mai wake take son had'awa. Allah ya taimaka tana da jan wake packed one da yake zuwa a gyare wankewa kawai zaka yi ka zuba ga su manya shar abinsu sai ta wanke ta d'aura kafin ta fara had'a kayan da zata buk'ata na girkin.


Tayi nisa taji motsin bud'e gate ta kitchen d'in ta lek'a nan ta hango masu shigowa, zurawa motar idanu tayi ganin kamar motar Hajjah har suka gama shigowa. Shigowarsu ya sanya ba a gani don parking lot d'in yafi kusa da main entrance sai kuma na Burhaan dake part d'in shi ta baya, tab'e baki tayi don ta san Hajjah ba zuwa za tayi ba sai dai in ko sak'o ta bayar a kawo mata.



Cigaba tayi da aikinta kawai, kamar a sama ta jiyo muryar Hajjahn tana k'walla sallama ai da sauri ta fito parlorn ko hannunta ba ta wanke ba. Turus ta tsaya da farko sai kuma ta ruga da mugun gudu ta d'aneta tana sakin mata kukan shagwab'ar da ya sake rikita Hajjah don ita na ta tunanin wani abun ne ya sameta.


Jan ta tayi zuwa kujera mafi kusa tana lallashi ita ko tana k'ara sautin kukan na ta, da babu ko d'igon hawaye sai tab'ara da ta cikata. Sai da ta gaji don kanta sannan ta tsagaita, sai kuma ta mik'e tana ''oh my Allah, yau Hajjah ce a gidana me zan kawo miki? Tukunna ma why don't you tell me that you are coming?". Ba kuma tare da ta jira amsarta ba ta nufi kitchen da saurinta, fridge ta bud'e duk wani abu na sha ta kwaso ta d'aura a tray da su snacks sannan ta fito tana cewa " ai da kin gaya min zaki zo da na shirya miki kayan tarba kala-kala".



Ita dai idanu ta zura mata ganin ta ajiye mata kaya a gabanta kamar su goman nan ne suka zo gidan, ga kuma ganinta lau da ita amma ta d'aga mata hankali cewa tayi " duk ina zan kai wainnan abun da kika ajiye".

"Toh ai ke ce baki gaya min zaki zo ba" ta furta kamar zata yi kuka, Hajjah dake binta da idanu ne tace " ai ke d'in ce kika d'aga min hankali, shiyasa na fito ". Dawowa tayi kusa da ita ta zauna tana cewa " da nayi me kenan Hajjah?". Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa " muryarki mana da muna waya kamar kina cikin damuwa, da fatan k'alau kike da shi Islaam d'in?". Shagwab'e fuska tayi tana cewa " ashe har yanzu ana sona, in da na sani da tun tuni na kiraki na miki kuka kin ga ai kya fito don dole. Ni ina lafiya ai, shi d'in ne dai bai jin dad'i har ruwa aka k'ara masa jiyan wallahi ".


"Subhanallahi, Burhaan d'in? Shi ne baki gaya min ba?" Hajjah ta furta a d'an rikice tana mik'ewa, cewa tayi " to ai ko ruwa baki sha ba, ina kuma zaki je?".


"Kai ni wurinshi kin ji, zan sha ruwan yanzu dai kai ni in ganshi ". Diddira k'afafunta tayi a k'asa alamun shagwab'a tace "toh mu je". Tana rik'e hannunta zuwa part d'in shi, da sallama ta shiga suna a zaunen da suke suna d'an tattaunawa k'asa-k'asa kamar basu suka gama halak'ok'o ba.



Ware idanu yayi ganin Hajjah, ita ko sosai ta tsorata da yanayin shi. Duk yayi laushi fuskar nan ta fad'a abinka da mai ajiyan gashi da gemu ga saje ga kuma dak'walan idanuwa duk sai suka sa fuskar ta sake zurmawa kamar yayi watanni yana ciwo. Zama tayi tana salallami tana tambayarshi jikin, yana amsawa da lafiya ta gefe yana hararar Nadeefah a tunaninshi ko ita ta fad'a mata. Gaisawa sukayi da Adnan inda yake tambayarta " da fatan kin taho ma majinyaci da danderu?". Murmushi tayi tana mamakin soyayyar Adnan da danderun da kullum ya ganta sai ya tambayeta, tace " ina fa, ai ban san bai da lafiya ba wannan uwar shagwab'ar ce ta d'aga min hankali da kukanta na taho ba shiri". Ta k'arashe tana dungurin Lele da ke tura baki, Allah sarki Adnan ya furta yana murmushi. Tashi tayi ta barsu nan ta koma parlor kayan da ta ajiyewa Hajjah su ta d'auko ta kai musu can kana ta koma kitchen kan girkinta, don har ta manta da abinci Allah ma ya taimaketa ba ta sakin masa wuta ba da sai ya k'one.



Sanda ta koma har Pepper soup d'in da ya kammala, while shinkafar kuma kad'an ya rage ta k'arasa albasa ta zuba a kai tana sake rufewa. Sanin Hajjah tana son sobo ya sa ta had'a musu mai pineapple da cucumber har da lemon juice a ciki, sai ta had'a normal salad na cin abinci ta kashe gas d'in don ya riga ya kammala. Kallon agogo tayi after one tayi ajiyar zuciya don ta samu ta kammala a kan lokaci, dishing abincin tayi na Burhaan da shi da Adnan a same food flask ta d'aura a tray da acrylic plates da cups da jug d'in dake d'auke da sob'o da spoon da sauran kayan cin abinci su tissue da tooth pick.



Sai nasu ita da Hajjah da ta sa daban ta fara kaiwa parlornta kafin ta d'auki nasu zuwa part d'in shi, tarda su tayi suna ta hira har da k'yak'yatawa lallai an samu duniya duk da dai Adnan ne da Hajjah suka fi k'arfin zancen. Shi bai fi d'aya zuwa biyu yake chirping in ba, ajiyewa tayi Adnan yana mata sannu da aiki murmushi tayi kawai shi ko gwaskan sai binta da idanu da yake yi ba tareda ya tanka ta ba.


Kwashe wainda ta fara kawowa tayi ta kama hannun Hajjah zuwa na ta part d'in, suna tafe tana mata hira ita ko sai murmushi takeyi. Suna zama akan couch ta bi parlorn da idanu tace " ahh Álà kámbò ( Allah mai girma) lallai Leleta ta girma, yanzu duk ke kike gyaran gidan nan har ki gama kiyi girki da sauran hidimar gida?". Murmushi tayi tana cewa " toh Hajjah me ye a cikin gidan nan, da dai ba a yi maka training bane sai kace zai yi wuya amma ni yanzu ai har na saba"


Ta k'arashe da k'aramar ajiyar zuciya tabbas ta san tana k'ok'ari a yanayin tashinta na ba ta san wahala ba,tsintsiya wannan wani lokacin sai ran Hajjahn ya b'aci kafin ta kawar in ba ta so bane. Duk da wasu lokutan ita da kanta take sa kanta yin ayyukan kamar gyaran nata d'akin da na Hajjah, girki ma tareda Yana sukeyi. Har ma tafi yin aiki a Abuja don Ummu ba ta cika entertaining son jiki ba, amma yanzu kamar ba ita ba ta riga ta rungumi ayyukan gida kamar wacce ta saba a yau kam da kanta ta san tayi k'ok'ari don shi ne ranar farko da ta fara aikin ya kai yawan haka ga shi kuma ta gama a kan lokaci.

Gyad'a kai tayi tana cewa " sai kace wacce take yi da d'in, ni fa daman damuwata kenan har nacewa Yana ta nemo min wata ta dinga tayaki sai Ummanku tace wai ke da mijinki kunce baku so ". Cewa tayi " ba gashi nan ba kema kin gani da idanunki, duka fa aikin bai da wani yawa har mutum ma zai kwanta in yaso. Ni dai yanzu kici abinci ko sai kin yi sallah ne?".

Tace " ba zan wuce Zuhr a gidan nan naki ba ai, sa min abincin kad'an sai ki sawa Mele ( Idris/drivernta) ki mik'a masa "  Toh tace kawai tana mik'ewa.


Sosai taji dad'in zuwan Hajjahn gidanta, don tare sukaci abincin duk inda ta motsa albarka kawai take sa mata da addua "Álà bárgà njó" ( Allah miki albarka) kawai ke tashi ita ko sai amsawa take yi da Ameen. Ba ita ta bar gidan ba sai kusan 3 bayan ta kirasu Abba ta shaida musu da ciwon Burhaan d'in kamar an saka ta, sai da ta sake lek'ashi ta duba jikin da masa sallama kafin ta tafi. Tana shiga cikin mota Nadeefah ta sanya mata k'atuwar leda cikeda kayyaki duk da ko ta san tana da su amma ba ta damu ba, ai ko ta rik'e hannayenta tana cewa "Nyiro askǝrngǝna,
Álà bárgà njó ". Tura baki tayi tana cewa " ni dai ki daina min godiya, tunda kink'i yini a gidan" ta k'arashe k'walla na taruwa a idanunta, cewa tayi " ai zan dawo wata rana kin ga ko gidajen 'yanuwanki ban je ba nan kawai na zo, zan dawo muku zuwa na musamman ranar a nan zan yini kin ji?". Ok tace tana share hawayenta, lafayarta ta gyara mata ta ja baya Mele ya ja motar suka bar gidan ita kuma ta koma cikeda kewa kamar ba yanzu ta fita ba haka take ji a duk randa wani nata ya zo gidan.

Da yamma Suliem ta sauka gidan don ta dubata a office yau ba taje ba, ta kuma mata dropping message a WhatsApp amma bata duba ba ta kuma kirata a waya tace mata zata duba amma shiru har to 4 ita kuma urgent take son reply saboda order sukeyi na kayan baby toh duk ta kasa zab'a saboda ruwan ido irin nata shi ne take son ta tayata zab'e.

4 dai-dai ta tashi nan gidan ta nufo kai tsaye, a entrance na waiting room ta had'u Adnan yana fita gaisawa sukayi sama-sama don ba wani saninshi tayi ba shi ko sai da ya bita da kallon mamakin wai saboda wannan matar ne Burhaan bai son Nadeefah. K'wafa yayi kawai ba wai ba ta da kyau ba ne but ko kusa da Nadeefah ai bata kai ba a komai,ga kumburin ciki da take fama da shi. Sai ji da kai da take da shi irin na Burhaan d'in wanda ya tabbatar inda itace a gidan ko halayyar Nadeefah irin tata ne toh da Burhaan sai yaji a jikinshi a k'asan ran shi kuma yace " da ai ya shiga hayyacinshi yanzu, ba zai na wannan iskancin ba". ( ohh Adnan ana tafe ana gulma a rai, ko wa ya sashi k'arewa matar wani kallo oho).

Ita ko bata ma san yana yi ba wai kunu a wani gida shiga tayi da sallama Nadeefah dake wanke-wanke a kitchen ta amsa sai kawai ta nufi can kafin ita ta fito d'in har ta shiga ciki tana cewa " ko yaushe Lele the artist ta ajiye paints da brush ta rungumi tukunya jamaa?". Girgiza kai tayi tana cewa " the same day da Suliem Yerwa ta ajiye fashion designing ta rungumi cikin gabanta". Dariya tayi ta d'aka mata duka a gadon baya tana cewa " wato ke ba a cinki a magana ko ?".

Sosa inda ta dake ta tayi tana cewa " cikin nan ya koya miki mugunta wallah, wayyo Yaa Islaam nah!!". Jan kujera d'aya tayi a cikin kujerun dining d'in kitchen d'in tayi ta zauna tana ajiyar numfashi, tace " zaki kira ma Yaa Sadeeq ba Yaa Islaam ba kawai". Goge hannunta tayi da kitchen towel tace " ai shi wannan sai dai ya goyi bayanki, shi yasa na kira mai goyon min baya kuma wanda yake kusa da ni ".

Cewa tayi " yau har ya dawo aikin kenan?" A hankali cikin rausayar da murya tace " yana gida ai, bai da lafiya bawan Allahn". Cikin d'an nuna concern kad'an tace " Allah sarki shiyasa baki je office ba yau kenan, Allah ya bashi lafiya. Ke ni fa yunwa nakeji mee kike da shi na ci?".

"Akwai ragowar abincin rana, rice ne ".

"Sa min abeg".

Ok ta furta ta d'auko saucer ta zuba mata a jiki da salad d'in ta ciro mata zobo a cikin fridge, tana ci suna tab'a hira har ta kammala wanke-wanke. Sai lokacin suka gaisa ta nuna mata kayan tareda bata wuk'a da nama ta zab'i wainda suka fi kyau, zab'ar mata ta fara yi ba tareda tabi k'yale-k'yalen kayan ba mafi inganci and unique ones ta zab'a mata sai ga shi abinda ta gaza Nadeefah ta mata shi a cikin minutes dukda ko ita d'in kaya take saidawa.

Tana gamawa ko ta mik'e tana cewa " toh bari in yi na gida kafin babe ya dawo".

"Amma ba abu mai wuya zaki dafa ba yau kenan?".

Tab'e baki tayi tana cewa " wannan Yayan naki mayen abincin ne zai yarda in dafa normal food? Ga muguwar son k'walama? Ai wuya yake bani ina gaya miki ".

Dariya ta sanya don ta san halin kayanta tace " i thought housegirl d'in ki ita ke girki ". Harararta ta tsaya yi sai kuma tayi k'wafa tana cewa " magana dai kike son sakani, waye zai bari housegirl ta dafa masa abinci? Ai lalacin nawa bai kai nan wajen ba 'yanmata, ko ma dai nima irin rice d'in nan taki zan dafa ne?".

"Awnnnn, ashe ba oga wife bace ".

"Ba zan biye miki ki sabautani a cikin gidanki ba, ni zan tafi Hajiya".

"Au haka zaki tafi baki duba Yaa Islaam d'in ba?".

Dafe kai tayi don ita kam har ga Allah ta manta da wani bai da lafiya amma sai ta waske tana cewa " ni na isa, muje in ga Aortan naki ". Girgiza kai tayi suka fita zuwa room d'in na shi, baya parlorn ya shiga watsa ruwa. Zama tayi yayinda ita ta shiga ciki, a kan gado ta same shi sanye da shorts kawar da kai tayi gefe tana cewa " Suliem za ta gaisheka, tana parlor".

Daga haka ta juya ta koma, da idanu ya bita yana mai jin kamar kar ya fita sai kuma ya mik'e ya ja jallabiyarshi dake kan hanger ya zura.

Zama yayi a kujera one sit yana kallonsu, Suliem ce ta d'an saki fuska tana cewa " Ina wuni Yaa, ashe baka ji dad'i ba Allah ya k'ara sauk'i". A jere ta fad'i maganar, d'an kallonta yayi a sace ta k'ara girma alamun masu ciki duk ya bayyana a fuska da jikinta. Nan take yaji kishi yana taso mai d'an daurewa yayi yace " da sauk'i, thanks" mik'ewa tayi kawai don ta san halin wulak'ancin kayanta, yayinda ita ko Lele lura da yanda ya tab'e fuska alamun bai jin dad'i ya sa ta cewa " har yanzu jikin ne?" Da idanu ya amsa mata, marairaicewa tayi tana cewa " so sorry,bari in kai ta in dawo " ok kawai tace suka mik'e har da shi, shi ya koma ciki ita kuma suka fita zuwa parking lot suna tafe tana ba ta labarin halinda suka shiga jiya da dare sosai ta nuna tausayinta da adduar neman sauk'i gareshi don ta san ba k'aramin ciwo bane zai wa Burhaan fyad'a irin haka ba.

Motar ta taja zuwa gida ita kuma ta shige ciki ta koma bakin aiki, tunda ta zama daga kitchen sai parlor ta bakin Suliem d'in. Tana gama girkin dare ta watsa ruwa taje ta watsa ta sanya wata abaya ta fito a part d'in shi tayi sallahr Magriba

Bayan ishai sai ga su Umma, da Abba da Safwaan. Sun tausayawa Burhaan d'in musamman Umma da ta sake yarda da hasashen da suka yi ita da Ya Budu na cewa Nadeefah ciki ne da ita, musamman da ya dinga lissafo symptoms d'in shi na low apetite da kuma jiri amai da sauransu. Suna gidan sai ga su Farhaan, ElSadeeq, Suliem da Zulfaa har da wasu d'ad'daikun familyn. Babu dad'ewa shi ma Adnan yazo yi masa allura da Salmah da d'iyarsu, nan fa d'akin ya kacame da hira kamar ba mara lafiya suka zo dubawa ba.

Ai ko ya shiga takura iya takura don shi bai son surutu yayi yawa ga su zuriaar gidan Yerwa akwai k'ara da kara'di in dai suka zo wuri sai kowa sani don addaba ce da su sosai, ba manya babu k'anana sai tsaki yake saki k'asa-k'asa yana mai jifar Lele da harara ganin muryarta yafi na kowa a wurin ga uban shagwab'ar da take ta yi a jikin Umma. Ba su suka bar gidan ba sai kusan 10pm shi ma don suna tausaya masa ne, tattara kayan dubiyan da aka kawo tayi tayi shirin bacci ta dawo d'akin. Ranar ma a nan ta kwana sai dai sab'anin jiya yau a kan sofa ta kwanta, duk da haka duk motsinshi tana kulawa da shi sai kusan 12 ta samu bacci inda Allah ya taimaketa kiran sallahr asuba a kunnenta har tayi ta fara gyaran gidan bai farka ba sanda ya tashin ko ba ma ta part d'in na shi sai mayataccen k'amshinta da kuma ruwan wankan da ta riga ta tanadar masa duk ko halin ko in kulanshi sai da ya yaba da yadda take bashi kulawa kamar wani k'wai.

Zuwan su Umma shi ya fallasa ciwon Burhaan a cikin familyn, nan ko aka fara zaryan zuwa dubiya kamar ba gobe. Dama ga shi nan cikin unguwar suke, ai ba 'ya'yan ba ai har iyaye haka gidan zai cika da jama'a kamar suna biki. Wainnan na fita wasu na shiga su tarda wasu, Hajjah ma ta dawo ita da su YaMara da Ya Madari a nan ma suka iske su Zulfaa hakan ya sa ma basu je can gidan nasu ba.



Safwaan kam kullum in ya dawo daga office nan yake zama sai bayan ishai yake tafiya, ba kasafai ake zuwa gidan da safiya ko rana ba don kusan dukansu maaikata ne sai in sun dawo daga office kafin suke zuwa nan gidan a k'arasa dare. Hakan ya sa take d'an samun barci da safiya in ta gama aiki, don shi ma time d'in barci yake yi sai rana ta fito kafin ta tashi d'aura abinci. Cikin 'yan dubiyar harda maaikatanta da su Baba Sule, sosai taji dad'in zuwan nasu tayi ta musu hidima da su kamar zata goyasu sai magrib suka wuce.


Yau Saturday kusan kowa na familyn ya had'u a gidan nata duba jikin Burhaan, hakan ya sa yau take d'and'ana wurin aiki duk da ko ba da wani mugun wuri suka zo ba. Sai ma bayan la'asar d'in da suka saba zuwa bambancin kawai yau collectively suka zo kamar sun had'a baki Allah ma ya taimaka d'azu tayi baking cupcakes sai kawai ta fito da shi da drinks duk wanda ya zo ya ci. Yau a living room suka sauke dabar har da shi Burhaan d'in, muryoyi kawai ke tashi a na ta nishad'i da dararraku.


"Ke da ya kamata a ce ke ke ciwo amma saboda rashin zuciya sai mijinki ne ke yi, toh ke sai yaushe zaki fara naki ciwon da zamu zo dubiya?" Aunty Ainah ce ta furta hakan kusan da wasa a harshenta tana kallon Lele, amma duk mai hankalin da yake wurin ya san ba wai wasa take yi ba in ko wasan ne ya fi kama da 'Bad Joke'.


Kallon Lelen da ke zaune gefen Aunty Najwah yayi duk ta muzanta da maganar yet, murmushin nan nata dake k'awata fuskarta ne shimfid'e kamar ba da ita take yi ba. Yayinda duka d'akin ya d'auki tsit kamar irin mutuwa ta kawo ziyara sai kace ba su ne suka ishi mutane da surutu ba, gyad'a kai yayi yana maida kallonshi ga Ainah dake murmushin nasara.

Murmushin mugunta ya saki yana mai cewa " ko meye damuwarki da ciwon nata da har sai kin zo dubiya oho?". Juyowa tayi tana kallonshi kafin ta samu zarafin amsawa Ya Budu tace " kai ma dai ka tayani gani Islaam, duk ta bi ta saka damuwa a ranta ta kuma damu Nadeefahr kai kace a kanta take ".


"Ohh ki ce ba wannan ne na farko ba, haba Hajiya Ainah saurin me kike yi ne har haka? Ko ke kika auro min matar ban sani ba". Ya furta studying her don yaga reaction d'in ta, d'agowa tayi ta kalli kowa taga kallonta suke yi ta ce " daga tambaya har za a kaini tashar da ban kai ba? Toh Allah ya baku hak'uri" ta furta tana kauda kanta gefe.


Murmushi ya sake yi yana cewa " ai there's actually nothing wrong in minding your own business, and it doesn't cost a dime ". Ya k'arashe sarcastically, Ya Budu ko ta taya shi da cewa "ai kuwa dai, in kuma kika sa hak'uri shi waken nan in dai kina da rai sai kin ga bayyanar shi don ba a cin shi a zauna lafiya ".

"Ai kin san ba kowace mace ke da lafiyar fidda tsiron waken ba, wasu sai dai suyi ta tusa " ta amsa mata cikin hausa kamar wata cikakkiyar bahaushiya, ita ma cikin salon hausar tace " ai lafiya ke sa ayi tusar musamman ma mai k'ara, na san kuma baki tab'a samun labarin a kaf zuriar Tar Goni Yerwa akwai wanda ya gagara yin tusa ba ". Ta k'arashe da murmushi sannan cikin yare tace " ki kwantar da hankalinki, ya kusa fashewa ". Kawar da kai kawai tayi tana jin ba dad'i don ba haka ta so ba, so tayi a biye mata a wurin ta samu abin magana amma kuma kowani lokaci in dai abinda ya shafi Nadeefah ne kaf ahalin Yerwa ba su had'a shi da na biyu.

Su fa irin su Aunty Ainah akwai su a kowace family no matter how civilized and educated they are, su dai burinsu a yi gulma ya kuma zama topic d'in da suka kawo ne yake trending  ba su iya minding business d'in su ba ko kad'an sai in abu ya juye su fake da su fa wasa sukeyi.  Ba kuma wai tsana ba ce take sa su irin wannan abun Aa, toxicity ne yayi musu yawa ba komai ba Allah ya raba mu da irin halayyarsu da gyara mana zuciyoyinmu Ameen.


Yak'e kawai ta saki inda ta canja maganar zuwa ga Aunty Fadwah tana tambayarta farashin takalma don ita sana'arta kenan footwears both elegant handmade da kuma na k'asashen turawa you can check IBN_EMPIRE and ALKAAY_FOOTWEARS don su suke had'a mata takalman da farko kafin ta bud'e nata companyn ta zuba maaikata a ciki suna had'a mata nata na kanta. Hakan da tayi ya sa kowa ya bar maganar a wasa amma banda Lele, Islaam da Ya Budu kai har ElSadeeq ma bai dawo dai-dai ba. Ba ma ta k'ara ko 5 mins ba ta musu sallama ta tafi, nan sauran ma a hankali kowa ya zame ya wuce aka bar Ya Budu kawai.

Ita ta taya Lele gyaran gidan tsaf kafin ta fara haramar tafiya, Burhaan ne ya rakata wurin mota nan suka yi magana akan Ainahn da lamarinta da kuma yanda take takurawa Nadeefah kan maganar ciki. Gyad'a kai yayi kawai yana cewa " zan taka mata birki, tayi gulmarta can amma banda ni ". Dariya Ya Budun ta sanya tana cewa " wai kai ma ka san gulmar Ainah?" Cewa yayi " ai babu wanda bai san halinta ba, sai dai in bak'o ne a familyn nan ". Tace "toh Allah ya shiryata " Ameen yace sai da suka sake wata maganar kafin suka rabu shi masallaci ma ya wuce don yanzu kam yana zuwa ita kuma ta wuce gida.

Da ya dawo masjid d'in ne wurin 9pm da Nadeefah ta kawo masa tea ne don yanzu ta daina kwana sai dai in ta ajiye masa abinda ya buk'ata ta koma nata d'akin. Ta ajiye mai kenan ta juya zata fita har da doguwar good night d'in ta ya dakatar da ita ta hanyar cewa " it's high time da zaki daina barin kowa yana baje kolin cin kashinsa a kanki, ba Ainah ba kuwa ko da ko waye ". Juyowa tayi ta kalleshi tana cewa " how bayan ba sa'a ta bace ita?". Cewa yayi "ok jira kike ni in gaya miki yanda zakiyi da critics or what? Ba zaki tsaya firmly akan k'afafunki ba sai an miki abu ki dinga washe bakinki kamar sun baki kyauta ko ? Okkk yayi miki kyau wuce ki bani wuri ". Sorry kawai ta furta tayi wucewarta, a ranta tana mai cewa in yaji haushin maganar Ainah to ya kawo k'arshen abun. Shi ko da wata muguwar kallo ya bita har da tsakinshi, wannan sanyin nata da son maida komai ba komai ba yana d'aya daga dalilan da ya sanya bai sonta tun farko he wants a woman of action and words shiyasa har gobe ya kasa cire Suliem a ranshi cos ita ce dai-dai da tsari da halittar rayuwarshi. Uhmm wai inji mai ciwon hak'ori.

Ranar haka ya kwana tunani da takaicin  maganganun Ainahn, sai dai kuma duk lissafin yanda zai cusa mata bak'in ciki ya rasa wanda ya kwanta masa a rai kamar na ya nuna mata cewa Nadeefah ba juya ba ce kamar yadda banzan tunaninta yake ba ta. A zahirin gaskiya ba kuma wai zai yi hakan don ita Ainahr bane kawai Aa shi ma fa a k'asar ranshi yana da buk'atar matarshi don har yanzu da azabar ciwon ciki yake kwana, musamman in ya farka tsakar dare ya hangota duk'unk'une akan sofa tana bacci ga shegen turarenta da har ya kama d'akin nashi.




Kai komai nata is remarkable kama daga tafiyarta, maganarta musamman muryarta dake tada masa da tsigar jiki har yanda take lumshe idanuwanta a yayin maganar zuwa yanda take lak'wasa harshenta wurin maganar. Uwa uba shagwab'arta da ya zame mata halitta ko yace yana cikin features d'in ta masu shiga rai, ga kuma in ta kawo masa abinci tana mai lallashinshi yaci.

Ta kuma kwalliyarta mai sauk'i da aminci duk kayan da ta sanya suna karb'ar jikinta ko don yanda ake mata d'inkin ne ko a halittarta ne hakan shi ma?. She's so free haka take rayuwarta ba ta da abokin rikici ko musayar yawu, she's a darling abar son kowa a ciki da wajen Yerwa. Most importantly ba zai manta kulawarta gareshi ba, ba ta da rik'o don ko bata tab'a duba cewa he doesn't treat her right ba tana kulawa da nuna damuwa akanshi kamar ko ma fiyeda yadda za tai ma kanta. Matsala d'aya shi ne bai sonta amma hakan ba shi zai saka ya kasa fad'ar kyawawan qualities d'in da take da shi ba, ba ta da cikas sai na rauninta shiyasa yake ganinta kamar ba zata iya da shi ba he's cold while she's soft.


A haka ya kwana yana mai tunani akanta wanda bai k'are masa ta dad'i ba don ko da muguwar buk'atarta ya kwana ya sha magani a banza it even lead him ya tsira ma kanshi allura amma bai samu sukuni ba don ko yana rufe idanu hotonsu na randa sukayi sharing kiss ne yake replaying a idanuwanshi. Yayi wanka da ruwan sanyi kusan sau uku sai can tsakiyar dare bacci ya sace shi, shi ma kusa it doesn't help matter tunda intimate dream ya samu da ita.


Haka washe gari ya tashi cikin sanyin jiki, duk inda ko tabi yana binta da idanu kamar zai cinyeta. And the more he look her the more yana sake samun urges a kanta, ita dai da ta ga kallon yayi yawa babu kuma magana sai ta tattare kanta ta koma tsaginta ta barshi nan yana fama.

Monday ko yana tashi yayi shirin office tunda ya samu sauk'i kuma zaman gidan ban da cutarshi ba abinda yake yi, ta shigo part d'in na shi gyara ta iskeshi a shirye yana d'aura necktie. Gaisheshi tayi ya amsa da d'an sakin fuska ba tareda ya kalli gefen da take ba gudun kar a warware masa tufkar da yayi, Allah ko yas taimake shi don ko short gown d'in ta ta sanya maroon da ya d'an kamata ba laifi fita tayi ta had'o masa tea mai d'an kauri da cake.

Amsa yayi har da mata godiya, zama yayi yana sha ita kuma ta wuce ciki ta gyara tsaf. Tana gyaran gadon ya shigo briefcase d'in shi ya d'auka a hankali ya furta 'sai na dawo' Allah ya tsare hanya ta bishi da shi, a ranta tana mamakin k'in rufe k'ofarshi yau. Ba ta d'auki wani lokaci ba ta fita bayan ta gama gyaran koina ta baza turare ta koma ciki, yau kam bacci tayi sosai ko breakfast ba tayi ba sai to 1pm lallai akuyar d'aure an samu sake.




5 ya dawo gidan da d'an kuzari compared to yanda ya fita da safe, ya ko tarar ta ajiye masa favorite d'in shi pounded yam da egusi ya ko ci yayi k'at kafin ya fita zuwa masjid.

Haka suka cigaba da rayuwa kullum yana tafe da damuwa k'asan rai, hakan ya sa jikin nashi k'in dawowa yanda yake kamar da don ma yana samun abinci mai kyau mahad'in ruhi kawai ne ya rasa wanda shi d'in ne ya so ba wani ba. Kwana biyu tsakani ta koma office tana kuma k'ok'artawa wurin tabbatar da breakfast d'in shi akan kari haka za dinner don 4-5 take dawowa while shi wata rana yakan kai har Magrib bai dawo ba.


Yau da ciwon mara na menstrual cramps ta dawo gida, tun kusan 2 ta gudo jin babu na alamina. Da ta dawo hot water massage ta yi ta sha ruwan zafi da magani ta kwanta, sanda ta tashi ta d'an samu sauk'in ciwon don ya riga da yazo wanka tayi ts kimtsa jikinta ta fita.

Da d'an k'arfin da ta samu ta had'a masa dinner mai d'an sauk'i wanda ba zata takura ba sai blueberry blast da ta had'a masa, a parlorn shi ta ajiye don ba tare suke ci ba kowa na shi yake ci da ban ta koma d'akin tana sake kwanciya don shi kawai take so.


San da ya dawo a na sallahr Magrib a masallaci hakan ya sa ya tsaya sallatar Magrib yayi da ishai kafin ya shiga gidan. Gidan tsit ya tarar da shi amma yana jiyo muryar TV ta d'akinta alamun tana kallo ne, rufe main entrance door yayi ya kashe wutar waiting room kana ya wuce room d'in shi. Wanka yayi jikinshi har rawa yake wanda bai rasa nasaba da abinda yake ji yinin yau ya kuma yi alk'awarin fitar da shi ya huta, da ya fito shorts kawai ya sanya bayan ya shafa cream ya nufi parlor. Abincinshi yaci yana korawa da ruwan blast d'in da ta had'a masa, bai wani saki jiki yaci da yawa ba ya koma ciki toilet ya shiga ya sake brush kafin ya fito bayan ya gama checking kan shi from head to toe.


Zama yayi a gaban mirror yana shiryawa turaruka ya dinga fesawa tun daga na armpit, har joint bai bari ba sannan ya fesa mouth fresher-anti bad breath mai k'amshin mint. Kana ya koma parlorn wayarshi ya d'auko yana mai nemo numberta, a WhatsApp ya duba don bai yi saving ba.


Tana kwance akan gado da shirin bacci, k'aramar rigar bacci ta sanya kalar black mai santsi da ta manne da kayan jikinta. Ba ta jin bacci a time d'in amma kuma ba abinda yake mata dad'i ko abinci ba ta ci ba fruit kawai ta sha shiyasa kawai ta kwantan da adduar Allah ya kawo mata bacci da gaggawa sai ga k'arar wayarta.


Lumshe idanu tayi ta bud'e a kasalance ta janyo wayar daga bedside inda take charge, infinite love da ta gani yana yawo akan screen ne ya sanya ta jin fad'uwar gaba. D'agawa tayi a d'arare kafin ta kai ga furta wani abu ta tsinkayo muryarshi yana cewa "to my room" daga haka ya kashe wayar ya barta sage da waya a kunne, the last time da ya fara kiranta ranar da ta tura masa message d'in son shi da take yi ne and da irin wannan tone d'in yayi mata magana hakaza 2 words kawai ya furta ' i'm outside' yau kuma only 3 ya furta.

Dafe k'irjinta tayi tana addua don ji tayi har k'asar ranta kiran bai kwanta mata ba amma ya ta iya? Gudun yin laifi ya sanya ta mik'e da saurinta hijabi ta yaya ta fita. A zaune ta tarda shi kan kujera k'afa d'aya kan d'aya, babu riga sai shorts bak'i.

Kasa k'arasawa tayi ta coge a bakin k'ofa kanta a k'asa, kallonta yayi da wani irin yanayi yana mai extending hannunshi gareta alamun ta zo. Ba ta ma gani ba sai da ya tafa hannun, d'ago kai tayi tana kallon hannun da ya mik'o mata.

Cikin sanyin jiki ta matso tana mai shirin tsayawa a gefe, ba kuma tareda ta kama hannun ba. Sai ji tayi ya fusgeta ita da hijabin nata zuwa kan cinyarshi zare idanu tayi a d'an tsorace yayinda bakinta ya hau b'ari tana son yin magana amma ko kad'an ta kasa don babu sound d'in da yake fita.

Yatsar shi sabbaba ya sanya yana zagaye bakin nata da shi cikin wani murya yace " ji bi yanda kike bud'e baki kamar mai jin tsoron wani abu, bayan abinda kika dad'e kina nema zan baki you should be jubilating and celebrating as I'm giving you the most precious gift and that's my own self a daren nan...." Baki ta bud'e da niyyar shaida masa she's on bayan haka ma she's no way ready for this night sai da ya hanata hakan don yatsarshi ya d'aura akan lips d'in shi "shssssssss" ya furta leaning in a style yana mai...................

Kuyi manage banda charge wayata d'aukewa zata yi any moment, cika alk'awari ne ma ya sanya na tura muku. Ina sonku da yawa😍💖.



Deejasmah ✍🏼

Continue Reading

You'll Also Like

510K 7.5K 32
Rajveer is not in love with Prachi and wants to take revenge from her . He knows she is a virgin and is very peculiar that nobody touches her. Prachi...
2.7K 1.2K 31
๐—–๐—ผ๐—บ๐—ฝ๐—น๐—ฒ๐˜๐—ฒ๐—ฑ!!โ™ก a kookv [ or taekook, whatever you like] fanfic~ Top kook~ Bottom tae~ . . promises are made to keep right~? or are they made...
628K 14.4K 30
I looked out of the window. The huge window had bars on it. It was designed in a way only I could see outside world. That's what I could only do. I c...
4.2M 266K 102
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...