NISFU DEENIY.......!

By deejasmah15

1.2K 117 25

She was exactly opposite of what he wants in a wife,,,he vowed not to be with her but fate has its own way as... More

PROLOGUE ( TEASER)
CHAPTER ONE (REJECTION)
CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO)
CHAPTER 3 ( MY PRAYING POINT)
CHAPTER 4 ( HOW I WISH....)
CHAPTER FIVE (MEETING.. ).
CHAPTER 6 ( MISFORTUNE....!)
CHAPTER 7
CHAPTER 8 ( HIS VISIT)
CHAPTER 9 ( THE RIDE)
CHAPTER 10 ( SHE'S BACK)
CHAPTER 11 ( SHE'S BACK II)
CHAPTER 12 ( DAYS TO GO.....)
CHAPTER 13 ( #BECOMINGMRSBAY)
CHAPTER 14 ( DAY ONE)
CHAPTER 15 ( HONEYMOON)
CHAPTER 17 ( LIVING WITH HIM)
CHAPTER 18 ( HER EFFECT)
CHAPTER 19 ( SICK)
CHAPTER 20 ( SHE'S TO SOFT)
CHAPTER 21 ( GETTING TO KNOW HIM)
CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)
CHAPTER 23 ( DAY AFTER )
CHAPTER 24 ( GETTING ALONG OR GETTING APART?)
CHAPTER 25 ( SETTING THE GROUNDS)
CHAPTER 26 ( SACRED TRIP)
CHAPTER 27 (THE PERFECT HER)
CHAPTER 28 ( PROUDLY HISโค)
CHAPTER 29 ( MILESTONE)
CHAPTER 30 ( HURRICANES)
CHAPTER 31 ( MEETING II)
NISFU DEENIY 32 (BROKEN)
CHAPTER 33 ( BROKEN 11)
CHAPTER 34 (DAY-OFF)

CHAPTER 16 ( A_RIDE_TO_YERWA)

28 2 0
By deejasmah15

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Da yawan mutane are either tired of canned drinks ko basu son su sbd kullum taste Daya ne ga health issues kullum kullum ☹️
Wasu kuma basuson gas din da keh a ciki ne 😏
Wasu kuma kawae basa burgesu ne sunfi son natural abubuwa😗

Ko kunsan wann matslar duk ta rashin iya mocktails haddadu ne?😱 Made from natural abubuwa irinsu Mangoes, Strawberries, Pineapples etc
Wanne ne yasa na shirya mana shararraren CLASS da zaki koya hadaddun mocktails to replace those drinks 🥳💃🏼💃🏼💃🏼

Zaki koyi....
📌Ynda Ake hada Pineapple spritzer🍹
📌Ynda Ake hada Watermelon wonder🍸
📌Ynda Ake hada Mongo mojitos🍹
📌Yanda Ake hada Virgin Kiwi🍸
Wann class da Harshen Hausa ne, kuma KYAUTA. Yes FREE
Join through the Link👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.me/message/W56IOTHO6JIJB1

CHAPTER 16 ( The_ride_to_Yerwa).

Daga ranar basu sake had'uwa ba har su Suliem suka d'aga suka bar k'asar, ta so yi musu rakiya sai dai ba ta samu damar hakan ba don an dakatar da rakiyar kowa daga su sai drivern da ya kai su. Tayi takaici ta ciji yatsa musamman da Aunty Fadwah tace mata wai ai saboda ita ne aka hana, a lokacin ta fara gajiya da kad'aici ga Hajjah da ta kasa ta tsare ta hanata zuwa gida. Ga meeting da ake shirin yi nan da kwana biyu, ga kewa ita d'aya. Yau kam da tunanin gidan ta tashi, ko breakfast ba tayi ba ta kwad'a kiran Hajjah tana mai shirin sa mata kuka.

"In ni ba zaki bari in fito ba ai sai ke kizo ko? Haba don Allah ". Ta furta tana kukan rigima, murmushi Hajjahr tayi tana cewa " in ce ke kika zab'i zama a gidan ke d'aya da yanzu ai kina can kina yawatawa ". Tura baki kawai tayi jin maganar Hajjahr dama ga su Suliem kullum cikin tashin kanta sukeyi a story, tace " ni dai ba wannan maganar ake yi ba Allah Hajjah ina son in fito ke kuma kullum cewa kikeyi ba yau ba".

"Maganar nan dai da ba kya so ayita Lele dole ita za ayi, shin kin manta da abinda na fad'a miki ne? Na gaya miki yawan kusanci a tsakaninku shi zai harfar da shak'uwa mai k'arfi har soyayya ta shigo ciki amma me kika yi Lele? Fatali fa kikayi da damar da aka baki ". Ta k'are da k'wata, ajiyar zuciya ta sauke ta san maganar Hajjah gaskiya ne amma kuma ta ina za ta fara mata bayanin shi wanda akeyi don shi ne yace bai buk'ata? Bayan da kanta tayi shelar ita ce bata da ra'ayi?.

A hankali tace " Ai a gidan ma ana samun shak'uwa ba sai an fita wajen ba, besides ma ai zamu je umrah. Yanzu ni dai ki sa a kawo min car keys d'ina zan zo in ganki duk da dai na lura kin daina so na".

"Ban daina sonki ba Lele saiti nake nemar miki a gidan aurenki ba komai ba, key kuma sai in kin zo ki tafi da kayanki". Tab'e baki tayi tana mai jin kamar ta sa kuka, dabara ce ta fad'o mata murmushi tayi ta katse wayar ba ta ko yi sallama da Hajjahr ba. Number Umma ta lalubo tana danna mata kira.

D'agawa tayi cikeda soyayya tayi sallama, amsawa tayi a kunyace tana mai cewa " ina kwana Ummanah?". Murmushi tayi tace " lafiya lau my daughter, ya gidan?".

"Alhamdulillahi Umma, ya su Abba da Yaa Safwaan?". Ta tambaya tana saukar da murya, amsawa tayi da kulawa " suna lafiya ya naji muryarki so low kina lafiya kuwa?". Murmushi tayi tace " Allah lafiyata k'alau Umma kawai dai kewarku ce ba komai ba ".

Murmushin manya tayi tana cewa " gida kike son zuwa Lele?". Shiru tayi bata iya amsawa ba, sake cewa tayi " toh kiyi wanka ki shirya zaki zo gida yau okay?". K'iris ya rage ta sa ihu sai dai ta daure ta hana kanga yi tace " toh Umma nagode sosai ".

"Yawwa Allah yayi miki albarka, je kiyi wanka ki shirya". Toh ta furta tana ajiye kan wayar, tsalle tayi ta sauka daga sofar da take kwance tun bayan kammala aikinta. Tayi wanka amma da yake hajiyar zumud'i ce ita sai kawai ta ruga zuwa toilet don sake yin wankan.

Ya na kwance a kujera yana dafe da ciki, tun asuba yake fama da azababbiyar ciwon ciki yanzu ne ya d'an samu ya lafa. Kira ne ya shigo wayarshi, tsaki yayi shi fa yau ba inda zashi sai masallaci. Duk da akwai aiki amma shi bai cika fita Friday ba yakan huta abinshi ko da ko ya fita d'in ba office yake zuwa ba yawo ya kanyi ko yaje BAY clinic. Yau kam ba ma zai lek'a can d'in ba sai bayan jumaah, janyo wayar yayi don ganin mai kiran.

'Umma nah' dake yawo akan screen d'in ne ya sashi murmushi yana katse kiran, a ranshi ya na ayyana ' ta huce kenan'. Kiranta ya fara yi back, ringing biyu ko ta d'aga. Sallama yayi cikeda natsuwa, itama ta amsa shi. Gaisawa sukayi inda take tambayarshi gidan da iyali Alhamdulillahi ya furta yana sosa kai, cewa tayi " ka fita ne?".

"Aa Umma kin san yau Friday ". Ya furta a hankali, tace " afff na sha'afa ne, dama 'yata nake son ka kawo min gida in ga abuna tunda na lura kai ba sanin kawaici kayi ba". Shiru yayi yana juya maganar na ta, in ya fahimci mai take nufi dai-dai Nadeefah take son ya sa a motarshi ya kaita gidan toh ba akwai motocin ta a gidan ba?

"Kana jina kuwa?" Ta katse masa tunanin da ya tafi da sauri yace "Aa Umma, amm me kika ce?". Cewa tayi " Nadeefah nake so ka kawo gida, tunda kai tunda akayi bikin ba ka san ya kamata ka kaita gida ba sai kai ne kullum ka ke jelen hanya ko gidan Hajjah ban tsammanin taje ma don in da tazo za tazo nan gidan. Ba dai kulle kake mata ba Islaam?".

Cewa yayi " ni Umma ba ruwana ita ce bata tab'a ce min za tazo gidan ba ai". Tafa hannaye ta fara yi tana cewa " yau naga abinda ya fi k'arfina ni Sato? Gidan ne sai tace maka zata sannan zaka kai ta? a karan kanka ba ka san ya kamata ba?".

"Kiyi hak'uri Umma za a gyara in shaa Allah ". Ya furta cikin k'asa da murya, cewa tayi " a gyara a nan gaba ni dai yanzu ka kawo min ita gida yanzun nan".

"Yanzu kuma Umma?" Ya tambaya a hard'e ai ko ta jeho masa zagi da kanuri " karam, karamka nace. Zaka kawo min ita ko in aiko driver ya d'auko min ita?".

"Zan kawota in shaa Allah bari in tashi yanzu " ya furta cikin saurin murya, tace " ina jiranku, sai kun zo". Daga haka ta yanke wayar ba tareda ta jira cewarshi ba, lumshe idanu yayi yana cizon baki.

Tsaki kuma yayi yana mik'ewa tsaye, har ya nufi hanyar bedroom d'in shi da niyyar yin wanka sai kuma ya fasa ya k'ara jan tsaki tuno bai sanar da abokiyar tafiyar tashi ba. Hanyar main parlor ya nufa yana mai hura hanci kamar shi da wani, tsayawa yayi yana k'arewa living room d'in kallo tas yake yana ta k'yalli da shek'in gyara alamun anyi dusting d'in shi da kyau ga k'amshi mai sanyi na turaren wuta, incense sticks, ga room fresh dake tashi a humidifiers wanda ya had'e da rab'ar dake sauka daga split ya haifar da wani yanayi mai sanyi.

Tab'e baki yayi dukda room d'in ya k'ayatar dashi ainun, amma sai ya kasa yaba mata cewa ma yayi " not bad, though ba ita tayi da kanta ba har da taimakon vacuum cleaner da dustern dake ajiye a laundry". Tsaki yayi yana mai dosar k'ofar part d'in nata, knocking yayi bai jira an ba shi izinin shiga ba ya murd'a k'ofar ya shige.

K'amewa yayi yana mai bin parlorn da kallo, yau ne karon farko da ya fara shigowa sashen tunda aka kawota gidan and he's quite impressed not by tsada ko kyan kayan but by the uniqueness da tsarin mamallakin parlorn. Daga kan cushions d'in da suke two colors , Guda biyu dark blue biyu kuma sky blue har zuwa ga rug d'in d'akin shi ma sky blue da dark blue. Kan shi center table ne sky blue da gold.

Ya d'aga idanuwanshi zuwa bangon da ke zagaye da curtains skyblue da ma abun d'auresu gold. Shi ma curtain rod d'in da holdern gold ne sai inner d'in su blue. A sauran sashen babu wasu tarkace sai kayan kallo da aka k'awata side d'in da French styled wall dark blue da skyblue pattern. Sai drawer da a k'asa kalar centre table d'in, a sauran sassan parlorn kuma art designs ne da aka jera a walls na nature design da kuma mandala art zare idanu yayi yana matsawa gaban arts d'in.

"Lallai ma! Ina yarinyar nan ta samu zanen arts by Nadee? Not one but har uku a wall d'aya?". Ya furta da mamaki yana shafa zanukan, ya san tsada da kuma wahalar da yake dashi samun zanen k'wararren artist d'in da aka kasa sanin inda yake kuma wani jinsi yake. Ya dad'e yana bibiyar artist d'in though ba following d'in shi yakeyi ba amma duk inda ake art exhibition da ya san zai yi displaying arts d'inshi sai yaje amma abun haushi bai tab'a samun dacen siyanshi ba sai sau d'aya ya siya ya manna a bedroom d'in shi na gidan Abba bayan biki kuma yaje d'auko kayanshi ya tarda babu yayi masifar har ya gaji haka ya hak'ura tunda su ma 'yan gidan basu san wanda ya d'auka ba sai ga arts har uku a parlorn Nadeefah tabbas in da wani ne yake da shi da ya rok'e shi ya bashi amma Lele ce fa ina Allah ya kyauta ai sai ta saka masa doka ko ta fara mai iyayin tana da abunda yake so.
( Hausawa suka ce a rashin sani kaza ta hau kan dami ta kwana da yunwa, in ba rashin sani ba ga mutum a gidanka kana can kana bulayin nemanshi ko da kud'i?. )

Tab'e baki yayi yana sake kallon design d'in d'aya na waterfall mai mountain da dogayen bishiyoyi sai d'aya na Sahara da caravan na african marchants a kai sai rana da take shirin fad'uwa. Na tsakiyar kuma mandala art ne mai kala uku dark blue, skyblue sai gold kalan ya matuk'ar hawa da parlorn sosai.

Mai da idanuwanshi yayi kan k'ofofin parlorn, sak irin setting d'in nashi ne amma kuma rooms d'in parlorn da alamu sun fi nashi yawa don shi 2 bedroom ne sai home office a d'ayan gefen ita kuma 3 bedroom ne sai d'aya a ta d'ayan gefen " may be ita ma office take da shi" yana tab'e baki.

D'akin farko ya fara bud'ewa babu kowa a ciki sai dai a gyare yake, sai k'amshin da ke tashi kamar parlorn ma. Next door ya tura, a nan yayi kyakkyawan gani da surar Nadeefahn dake tsaye a gaban mirror sanye da bathrobe sai towel da ta d'aure gashinta tana shafa moisturizer a fuska.

Tsayawa yayi cak yana kallonta, everything about her is absolutely perfect. Daga kai kuwa har k'afafunta haka ya bisu da kallo, shakkah babu fara ce tas babu d'igon bak'i a jikinta in ka d'auke moles d'in da take da su a fuska, wuya da k'irji ta inda yake iya gani.

Saurin kawar da kanshi yayi zuwa kan gadon dake gyare tsaf, zuwa ga sofa da bangonta mai d'auke da arts suma. Mai da idanuwanshi yayi zuwa kanta tana shafa cream.

Haka nan jikinta ya bata ana kallonta, ga kuma k'amshin turarenshi da yake kawo ziyara a k'ofofin hancinta sai kuma fad'uwar gaban da take kasancewa a cikinshi idan suka kusanta da juna. Da sauri ta waigo zuwa saitin k'ofa, da sauri ta dafe k'irji ganin wanda ke tsaye a wurin kamar an dasa shi fuskar nan babu yabo ba fallasa sai wani kallo mai hargitsa k'wak'walwa da yake bin ta da shi.

Tsaki ya ja yana mai kawar da idanunshi, ganin yanda ta ja towel d'in kanta tana rufawa a kafad'arta. Cikin rawar murya tace " Good morning Yaa", kai ya gyad'a yana cewa " morning,,,,am ki shirya zan ajiyeki gidan Umma ". Daga haka ya juya abinshi yana yatsina fuska kamar ya ga kashi, tsalle tayi tana juyi farinciki yana mamaye ranta ga na fitar da za suyi ga kuma na shigowarshi cikin d'akin da kuma maganar da yayi mata yau ba tsawa.

Cigaba da shiryawarta tayi cikin natsuwa, Atamfa ta sanya chiganvy mai dusty rose da sage green sai ratsin black a jiki d'inkin Abuja gown akayi mata. Veil ta d'auko medium sage green na Asma da bag da kuma flat shoe na Vinci. D'auri ta kafa a gaban goshi na Zara Buhari da ya hau da d'inkin, sosai tayi kyau musamman da ta shafa shiny lip gloss sai glowing take yi da cika idanu.

Wayarta ta d'auko a hannu bayan ta feshe kanta da turare, jakarta ta d'auka sai kuma taji kunyar zuwa gidan wayam ba komai. Cije yatsa tayi tana mai jin da ma ba ta ce yanzu za ta je ba da ko gobe in ta bari tayi wani abu mai muhimmanci ta kai, fitowa tayi parlor ta jiye jakarta, da veil d'in ta nufi kitchen. Tattara duk snacks da small chops d'in dake kitchen d'in tayi sai ta ga sun mata kad'an ga kuma shi ba wani zafi ne da shi ba balle ta kai musu.

Bud'e fridge tayi tana dubawa, samosan da tayi ajiye ta ciro ba laifi da d'an yawa tayi ordern 50 pics kuma sau biyu ta soya. Ajiyar zuciya ta sauke ta ajiye a gefe sai whole chicken guda 3 da tayi marinating da niyyar gobe tayi using d'in su ciresu tayi suma ta d'auko a apron da gloves tana sanyawa.

Griller ta kunna ta jera chicken d'in a cikin rack sannan ta sanya su ciki, sai ta kunna gas tana sa mai a kai. A tsanake ta soya samosan tsaf, ajiyesu tayi a gefe ta ciro vegetables ta yayyanka. Sauce tayi mai d'an yawan ta ciro cikin d'in ta da suka fara gasuwa ta d'aura akan foil paper ta zuba sauce d'in sosai a kai sai ta maida su oven d'in ta da tun d'azu tayi heating d'in shi. Fifteen good minutes suka d'auka a ciki kafin ta ciro su, a separate vanity dishes ta jera kazar, da spring rolls d'in sai cupcake da take ajiyarsu kullum. Sanyasu tayi a buffet bag tayi ziping kafin ta d'auka d'aya bayan d'aya ta kai parlor, tana yi tana duba agogo gudun kar ya fito ba ta gama ba.

Cire gloves d'in tayi tai discarding sannan ta nufi store, ruwa ta d'auko da sosa drink each Hajjah kuma ta kai ta had'a mata da malt. Ajiye su tayi a parlorn tana ajiyar zuciya, komawa tayi kitchen d'in ta gyara komai da ta b'ata ta kimtsa shi da kyau. Murmushi tayi ta fito parlor ta zauna as kujerar tana mai da nishi kamar wacce tayi gudu, kallon k'ofar side d'in shi tayi tana mai mamakin rashin fitowar ta shi.

Shi ko bayan fitowar shi daga d'akin nata, sashen shi ya shige yana mai jin yanayin d'azu yana mai bijiro masa. Zama yayi a cushion d'in parlorn na shi, yana runtse idanu kamar almara surar Nadeefah ne yake masa gizo a idanunshi. Bud'e idanun da har sun kad'a yayi yana cizon baki, tun yana jin abun da kamar wasa har abun ya nemi fin k'arfinshi.

Kifa cikinshi yayi ya kwanta kawai yana nishi sama-sama, da jera duk adduar da tazo bakinshi. Yafi 30 minutes a haka amma bai samu sauk'i ba sai ma hauhawa da yanayin yake yi, k'arin haushin hoton surar Lele da yake gani ne tun daga gashinta da ya lek'o daga towel d'in da ta rufe kanta zuwa fuskarta dake shek'i, wuyanta, cinyoyinta and everything.

Sake tsaki yayi yana mai k'ok'arin korar yanayin, ganin in ya zauna a haka zai iya wafati ba tareda wani ma ya sani ba ne ya sanya shi mik'ewa. A hankali ya nufi cikin bedroom d'in shi, bedside drawer ya janyo yana bincike wani magani ya d'auko daga ciki. B'allan guda biyu yayi ya afa a baki, ya sha ruwa. Runtse idanu yayi ya kwanta kamar d'azun d'in a kan cikin.

Ya d'auki almost 30 minutes kafin ya samu sauk'in abinda yake ji, toilet ya shiga yai wanka ya fito tsayawa yayi a gaban mirror ya goge jikinshi. Shafa yayi a natse, ya taje gashin kanshi ya shafa hair cream na Tom Ford har da wata powder ya shafa a fuskarshi. Closet d'in shi ya nufa ya nemo kayan sawa, Ash colored shaddah ya sanya da black hula dara.

Bak'ak'en tuxedos half covers ya sanya sai agogon Graff bak'i da ya d'aura a tsintsiyar hannunshi da glass d'in Prada mai bak'in kwalba,  ya feshe jikinshi da turare ya fito daga d'akin. Car key ya d'auka a drawer ya kashe haske da electronics d'in d'akin AC kawai ya bari a kunne har ya nufi k'ofarshi dake sa da shi ga garage kai tsaye sai kuma ya tuna da Nadeefah za su fita .

Iska ya fesar daga bakinshi yana tsaki sai ya rufe k'ofar ta ciki, ya bud'e k'ofar part d'in na shi ya shiga living room. Fitowarta daga part d'in ta kenan bayan ta gaji da jiranshi ta d'an koma ta sake kimtsa jikinta ta fesa turare and coincidentally ta sanyo  photo chrome glasses na Bose da ya k'awata fuskar tata, tana rufe k'ofar ya fito bai tanka ba ya nufi hanyar bita.

Murmushi tayi tabi bayanshi don har ta kira security ta intercom sun fitar mata da kayanta sun ajiye a garage, black Cadillac ya nufa yana mai bin kayan da aka ajiye da kallo. Ta lura da tambayarta yake son yi sai dai yadda bai tanka ba itama bata tanka ba sai ma shirya kayan da ta fara yi a back seat, beeping d'in ta yayi ta d'ago tana kallonshi.

"The boot is open ki sa a ciki " ya furta a dake yana warming motar, cije baki tayi ta maida kayan boot kafin ta d'auko jakarta dake bayan Tundra d'in dake wajen. Shiga ciki tayi da sallama, a k'asan mak'oshi ya amsa sallamar yaci gaba da abinda yake yi tada motar yayi suka bar gidan.

Sun d'an fara tafiyar ne ya d'an dubeta ya na mai jin yanayin da dama ba tafiya yayi ba yana k'ok'arin dawowa, cije baki yayi yana mamakin abinda yake damunshi d'in bai tab'a kasancewa a haka don yana tareda mace ba amma me yasa yau yaji haka a kanta alhalin da kayanta a jiki balle yace ko nakedness d'in ta ne yayi triggering abun?. Katse shirun yayi ta hanyar kunna Diwani Wasiqtu bi Mahi daga bakin Muhammad Hadi Sha'aban Ghana, sautin yake bi cikeda natsuwa.

Tana daga gefenshi tana kallonshi a kaikaice, haka nan tana mai sake godiya ga ubangiji na samunshi da tayi a matsayin miji. Like he's all she prayed for abu d'aya ne ya rage mata wato samun soyayyarshi, karatun da yake bi ba k'aramin burgeta yakeyi ba.

Kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata kallonshin da takeyi, d'aga wayar tayi ganin daga Auckland ake kiran kuma face time ne murmushi ta sanya tana picking.

"Garba jikan Garba, Habu na Habu " shi ne abinda ta fara fad'i a dai-dai time d'in da fuskar Sadeeq ta bayyana akan screen d'in ta. Zaune yake a wani park da k'atuwar jacket a jikinshi alamun suna k'arbar sanyi, dariya ya sanya yana cewa " Allah ya yafe miki Lele ".

"Ameen ya rabbi, angon Honeymoon sai yau aka tuna damu?". Ta tambaya tana shagwab'e murya da fuska. Gira ya d'aga mata yana cewa " ba ga shi nan zaki fita yawo ba".

"Ni 'yar yawo? Tun fa da aka kawo ni unguwar nan ban fita ba sai yau, Hajjah ta kasa ta tsare wai ba yanzu ba ".

"Ba gobe za ai meeting ba? Da kin bari sai goben kuka fita"

"Waye? Meeting d'in da aka ce ba damu za ayi ba? Ka manta ance sai next month zamu fara attending, this month ma sunday zasu yi meeting d'in kamar gobe akwai wani d'aurin auren da zasu je".

"Ohh yes bikin gidan Gangarida ne, ya kike ya gidan? Kuma honeymoon d'in zaku fara yau ko kuma outing zaku fita da sassafe ke da likitan naki?".

Tura baki tayi cikeda kunya tace " gidan Umma zamu je yawon jumaa ina Rabin Raina?''.

"Ga ta nan ta matsa min in bata" ya furta yana kai hannu ya ture hannunta da take k'ok'arin amsar wayar, cewa tayi " ayya ka bata mana, yanzu ma da daren nan mai kukeyi a waje to 11 fa".

"An ce miki irin k'asarku ne da 10 kowa ya rufe gida? 24/7 ake gaya miki yanzu ma munzo wani eatery ne zamu koma condo d'in mu ". Ya amsa mata yana nuna mata eatery d'in ta hanyar sa shi ta back camera.

"Abinci by this time? Ko shi a can ba matsala bane?". Ta k'arashe da tsokana " Babe ce take k'wadayin Hot dog shiyasa ma muke fito, ki sa min mutumina mu gaisa kafin in bawa wannan 'yar nacin".

Kallon side d'in shi tayi da tunda suka fara wayar har slowing down yayi tsabar hankalinshi na kanta, tace " he's driving". Ya cab'e da cewa " kuma ban cin mik'e, bai san ya kirani bane sai da ya kiraki tukunna?".

"Ka dai ji shi ko?" Ta tambaya cikin k'ok'arin suppressing dariyarta, dariya ya sanya yana cewa " ho d'an rigima marad'inka baya jin kunya I sha know say u must say this".

Bai tanka ba yaci gaba da driving d'in shi, cewa yayi " sa min a yanda zan ganshi kin ji 'yar k'warai". A selfie stand d'in dake motar ta d'aura wayar, Sadeeq d'in ne yace " Don ubanka ka dinga ganin mutuncina else in sa k'anwata ta koya ma hankali". Murmushi yayi ya d'auki wayar dai-dai shi yace " wannan ne kuma ba ka isa ba don yanzu na fika kusanci da ita " Sadeeq d'in ne yace abu ya bashi amsa amma bata jin mai suke cewa don rage voice yayi su biyu kawai suke jin abinda suke fad'i.

Suliem dake d'ayan side d'in ta gaji da k'walelen da ake mata, bayan ita ta matsa a kirawo Lelen ne ta matso da fuskarta tace " Barka da safiya Yaa Islaam ya gidan ". Runtse idanu yayi yana mai jin yadda voice d'in nata ya shiga har cikin zuciyarshi ya tab'o inda yake tunanin ya mutu ashe likimo yayi, a hankali ya bud'e su yana kallonta.

Maimaita gaisuwar tayi ya amsa da dauriya yana cewa " na san dai wannan gaisuwar ba ta gaskiya bane k'awarki kike son a ba wayar toh ga ta nan ". Kafin tayi wani abu ya ajiye mata wayar akan cinya ya tsurawa hanya idanu with a heavy heart.

Ita ko d'auka tayi tana cewa " My Rabin Rai ". Cewa tayi " Oporrr babe ji yanda kika yi kyau". Harararta tayi tana cewa " Ji mata don kawai kin ganni a haske ne, it's but a sun kissed".

"Ko ba sun kiss ba madam kin yi kyau wallahi matar Yaa Islaam ko mun samu k'aruwa ne?".

"K'aruwa ai sai ku masu fita neman hot dog 11 pm, Ina Zulfaa?". Ta kawar da maganar ganin Yaa Islaam na wurin itako cewa tayi " 'yar sharri ba a fita neman abu sai da dalili?". D'aga mata gira tayi tana cewa " Ana yi mana amma wainnan shegun cravings d'in ai sai Babynmu".

"Allah ya shiryaki, Zulfaa mun barsu a nasu unit d'in".

"Mara M tun ranar fa ko ta neme ni, ita 'yar miji ko za a dawo a sameni yaushe zaku bar Auckland d'in?".

"Jibi in shaa Allah daga nan kuma sai Hawaii ".

"Awnn Allah ya kaimu, mu ma gamu nan zamu Yerwa".

"Mu kam ai sai mun dawo yaushe zaki shiga complex ne duk da ana tura min report akwai ma kayan da nayi order zasu iso amma ina son sanin ya yake going ". Inji Suliem d'in, d'an kallon side d'inshi tayi tana cewa " Monday in shaa Allah zan koma, Zan duba muku duka offices ni ma na san ana buk'atata a wurin ".

"Yawwa Babe you are a darling " d'an hira suka yi tsakaninsu, har sai da suka doso gate d'in shiga estate d'in kafin suka yi sallama. Kallonta yayi da mamakin yadda both ita da Suliem d'in basu gajiya da magana ji dai yanda suke ta zuba ca-ca-ca kamar tsinkakkun carbuna.

A dai-dai gate d'in gidan Umma yayi honk, securitynsu da kamar jira yake ya bud'e gate d'in ya shigo da motar. Parking yayi a bakin entrance bai ko daidaita ba ta b'alle motar, yatsina fuska yayi yana jinjina rawar jikinta.

Yana fitowa tana shirin d'aga boot, bud'ewa yayi da kanshi yayi ma securityn da ya biyo shi alamu da hannu akan ya d'auka kayan. Nuna mai wanda za a fitar tayi ya ciro suka nufi k'ofar shiga ya biyosu a baya.

Su na shiga Umma dake fitowa daga kitchen ta taresu, hannu ta warewa Lelen ai ko da sauri ta fad'a jikinta ta rungumeta tsaf. Hard'e hannu yayi yana kallonsu da mamakin kalar bond d'in dake tsakanin Lelen da alummar familyn,Umma ce tace " sai kuma ka tsaya a nan baka k'araso ba?".

Tura baki yayi yana cewa " toh ai naga ba tani ake ba ta 'yar ki kike shiyasa ". Dariya tayi tace " ba dai kishi ba?". Zama yayi yana mai cewa " ai Umma in ma nayi ba laifi bane, besides ba ma kishin nake yi ba".

Dariya sukayi su duka zama tayi ta sake jawota jikinta, gaisawa sukayi da juna Umman tana tambayarsu gida da hanya. Rabin hankalinta na ga Lele da ainun taji dad'in yadda ta ganta. Ta k'ara haske ga shi ta murje, da alamun sun had'e kansu ko wannan ma ya isheta komai.

Nan aka cika musu gabansu da kayan tab'awa, Umman da kanta tayi serving d'in Lelen. Har ya mik'e da niyyar ya bar musu d'akin sai ga Safwaan ya shigo da sallama sanye da k'ananan kaya, bai san ma da zuwan nasu ba sai da ya shigo.

Tsayawa yayi yana cewa " Amarya ce yau a gidan namu?". Tura baki tayi tana cewa " Ni dai na gaya maka ban son wannan sunan ko Yaa Safwaan". Gwalo yayi mata yana cewa " ai ko ba zan kiraki da sunan da kike son ba Allah ya kyauta in ce miki Aunty".

"Girma ai Allah ne ya bata kuma dole kace mata ". Cewar Umma, gwalo ko tai masa tana cewa " see?". Zama yayi yana cewa " ke ko baki da kunya, ko d'an karar ganin Umman nan ba zaki yi ba ance kinyi aure harda wani murmushi ".

"Toh had'a su ka kasa rabasu duk yaushe akayi hakan i na ina kuma?". Inji Umma tana rik'e baki, cewa tayi " ai ki k'yale Yaa Safwaan Umma abokin sharrinshi ya jima da mutuwa". Dariya ya sa mai k'arfi yace " sai yanzu kika san da hakan?".

Sai ya juya kan Burhaan dake zaune " Brother good morning". Tab'e baki yayi yace morning haka nan yake jin haushin wasanninsu musamman ma na yau, ba su ko kula da yanayin ba aka cigaba da hira.

A tsakiyar hirar ne Safwaan yace " wai shi wancan Buffet d'in da ruwan dake wurin wa ya kawo su?". Da sauri tace " laaa mu muka kawo fa". Ai ko da sauri ya tashi ya nufi wajen, Bag d'in da ya d'auko first da Sosa drink d'in ya kawo gaban Umma sannan ya koma ya d'auko ruwan shi ma ya ajiye.

Umma tace " Allah yayi muku albarka abun har da d'awainiya haka?". Shi ko sai k'ok'arin bud'ewa yakeyi,Umman ne ta bige masa hannu tana cewa " cire hannunka a kai, ba kai aka kawowa ba ".

Ya shagwab'e fuska yace " Allah sarki Mum, muma fa k'iris ya rage a fara kawo abu ana cewa daga gidan Safwaan Abdullah aka girko ko Yaaa?" Harara ya jefa masa yace "baka da kunya ai kai ". Cewa yayi " kai Yaa mai kuma nace? " sai kuma ya nufi cupboard dake dining plate ya d'aako da spoon ya d'auraye kafin ya dawo parlorn yana mai cewa " Allah umma save a life ko breakfast banyi ba".

Umman ce ta bud'e ta sa masa Samosas d'in a plate ta yanka masa kazan tana cewa " ai akwai abun breakfast, kaci wannan sai ka k'ara ka kuma ci naka ". Yace " haba Umma ayi min rai mana, Auntyna yaushe zanzo ki min nawa special eh". Ya k'arashe yana d'aukon hot milk d'in dake gabanta, cewa tayi " ko ba Aunty ba?".

"Auntyna kuwa, kin ga wannan ba zai isheni ba ko ki bani key kawai zan je in d'auko " Umma tace " ai kai dama hankali har na siyarwa kana dashi". Shi dai bai tanka ba sai ma magiyar da yayi mata ta k'ara mai, ya kuma had'awa da peppered soup d'in da aka ajiye musu yaci ya k'oshi.

Umma ne ta dubesu tace " ke ma ya kamata ki fara fita office ai, akwai yarinyar da na sa a kawo min saboda tayaki 'yan ayyuka da sauransu so that ba zai miki yawa ba".

Da sauri ta kalli gefen Burhaan da yake zaune, shi ma kallonta yake yi. Idanu suka had'a ya jefa mata wata zazzafar gargad'i da idanun na shi a take ta tuna da maganar da ya gaya mata akan 'yar aiki don haka tace " laa Umma ai ba sai kin damu ba, duka aikin ai bai da yawa ba zai gagareni ba".

"Wani irin bai da yawa Lele ko dai baki so ne bayan duk 'yan uwanki suna da mataimaka?" Ta tambaya da kulawa, girgiza kai tace " ba haka bane Umma, na ga aikin duka bai da yawa ne ban kuma san in saba da langab'e jiki tun yanzu zuwa gaba dai idan buk'atar hakan ta taso zan yi magana sai a kawo ".

"Ai Umma mun ma yi maganar da ita tuntuni ta nuna ba ta ra'ayi, kuma nima ganin ba wani aiki bane mai yawa in ya fara yawa ma I won't let her da kai na zan sa a nemo mana" Ya furta da sauri yana dubanta, murmushin manya Umman tayi tace " da alamu dai dukanku ne baku son mai aikin sai ta sha zamanta, daman Fadwah tana nema wai tata za tayi aure sai a turata can ku in kun shirya a nema muku".

Ajiyar zuciya ta sauke tace " Yawwa Umma, a aikawa Uomm Nihilan kawai" cewa tayi " case closed".

Sun jima a gidan sai 1 suka bar gidan, basu had'u da Abba ba dan sun fita duba gidan gona shi da Baba Tijjani. Kayan spices Ummahn ta had'a mata masu yawa ba laifi, har mota ta rakasu sai da suka bar gidan kafin ta koma da murmushi har da Hamdalarta.

Gidan Ummu ya kaita daga nan, shi ko ko parking bai ma kai gayi ba ta b'alle k'ofa zata fita. Unexpectedly ya rik'o hannunta yana cewa " careful!". Kallonshi ta tsaya yi, kawarda fuskarshi yayi ya yai parking tareda sakin hannunta.

Girgiza kanta tayi ta bud'e da sauri, tun daga entrance take k'walla kiran Ummulkhair kamar yadda ta saba idan ta kwana biyu ba ta ganta ba. Ba ta parlor don haka ta nufi bedroom d'in ta tana mai cigaba da kiran sunan, can ma bata ciki da sauri ta fito tana kwab'e fuska kamar za tayi kuka.

A parlorn ta tarda tana kallonta da murmushi, rungumeta tayi tana sa mata kukan shagwab'a. Dungure kan ta tayi tace " ke dai Bibti ba kya girma". Tura bakin tayi tana cewa " ai na yi missing d'inki ne Ummu, kuma ma ai lallshina ya kamata kiyi".

"I've missed you too Bibtie, but da haka ake sabawa ai muma haka muka baro namu k'asar muka zo taku ga shi nan har mun saba".

"Uhmm Allah Ummu it is not easy,musamman ma da ya zama an hanani zuwa inda kuke" ta k'are da shagwab'a, cewa tayi " toh bibtie miye na k'orafi ba gashi nan kin zo ba". Uhmm tace tana janyewa, a lokacin ne Ummun ta lura da Islaam d'in.

Cewa tayi " au tare kuke kenan da ranar nan?" Sosa kai yayi yana cewa " eh wallahi Ummu, mun same ku lafiya" ya k'arashe yana rusunawa. Fuskarta yalwace da murmushi tace" lafiya lau, ya kuke?".

Zama yayi suka sake gaisawa, itama sosai taji dad'in ganinsu. Sanda tace a kawo mai abun tab'awa ne yace " ahh Ummu don't mind I'm okay, daga gidan Umma ma muke". Murmushi tayi kawai, ita dai tana jikinta tana zuba mata tab'ara tana biye mata.

Bai jima ba ya mik'e don za shi masallaci lokacin jumaah ya gabato, kallonta Ummun tayi tana mata alamar ta raka shi. Tura baki tayi ta bi shi a baya, bayan sun yi sallamar da Ummun.

Ko da ta fito bai ce mata uffan ba sai bud'e boot da yayi ya dire mata duka kayanta dake ciki. Ya ja motarshi ya bar wurin, dariya tayi ta d'auko bag d'aya zuwa ciki.

Sauran su Maids d'in Ummu ne suka shiga dasu ciki, ware na Ummun tayi ta ajiye na Hajjah a dining. Sosai taji dad'in zuwa gidan, har room d'in ta ta shiga ta din ga juyi akan gado haka nan sai taji kewar d'akin ya kamata. Ba ita ta bar gidan ba sai to 5 da k'afa ta shiga gidan Hajjah su Iyami suka rakata da kayanta.

A can tayi kyakkyawan gani da su Yamara da Ya Madari sun zo wurin Hajjahn, su ta gaisar sukayi 'yan wasanninsu kafin ta zauna tana zumb'urawa Hajjah baki.

" Y'ar nema in kina fushi ai ba sai kin zo ba dama ni ban neme ki ba". Ta furta tana dariya, Cewa tayi " ai nazo ne in nuna miki na fito d'in, na kuma gama kulle Hajjah ".

Yamara tace " ahh abun azimun ne amma Hajjahn ki bata kyauta ba". Cewa tayi " Wallahi fa Yamara, ai ni car keys d'ina na biyo if not for that da ba zan zo ba ". Ya Madari tace " ai ba mai shiga tsakaninnu, kema Yamara kar ki zak'e anjima su kware miki baya".

Ai kuwa yadda ta fad'an ko minti biyu ba tayi ba, ta shige jikin Hajjahn tana mai sa mata kuka. Cewa tayi " ke dai yau so kike hawayenki ya k'are, kin yi na safiya yanzu kuma da almuru kin dasa".

"Allah Hajjah baki san yadda nayi kewarki ba ne, yau ma ni a nan zan kwana". Ta furta a sakalce, cewa tayi " ai shiyasa nace kar ki fito, in ba shirme ba ki kwana ki min me?". Tale baki tayi tana cewa " da can d'in da nake kwanar me nake miki?".

Dariya suka sanya Yamara tace " ahh dole a ce ki sha zamanki wannan shiririta da me tayi kama?". D'aga baki tayi sama tana janyo buffet d'in da suka shigo da shi tace " ga shi nan dai ku ci ku more tsufa, Hajjah ba kiyi ajiyar danderu ba?".

"Ba a rasawa, Ahh Leleta tayi hankali har da tsaraba". In ji Hajjahr ita dai bata tanka ba, wucewa tayi zuwa kitchen don neman abun sa wa a baki. Don duka gidajen da taje ba wani abun kirki ta ci ba, a plate ta sako sinasir k'waya d'aya da danderu ta fito nan ta tarda su suna cin kazar da ta kawo a kwano d'aya murmushi tayi tana jinjina girman shak'uwar dake tsakanin bayin Allahn nan su uku. Ba 'yanuwa bane na jini kowacce daga dangi na daban aka aurota amma sun had'u, sun had'a kansu wuri d'aya ba suyi kishin balbelu da mata kan yi yanzu ba sun kuma raini yaransu a matsayin abu guda in ma ba an fad'a maka bane ba ka sanin waye d'an wannan duk da ko kasantuwar ba gida d'aya suke rayuwa ba ga shi kuma sun tabbatar da auratayya a tsakankanin y'ay'ayen nasu har ya zamana babban abun koyi a tsakanin 'ya'yan sun zama tsintsiya mad'aurinki d'aya ba kuma sa nuna bambanci a tsakaninsu.

Murmushi tayi tana mai adduar Allah ya sa suma su gida zuria kamar yadda suka yi ko ma fiye don tabbas sun musu gini mai k'arfin da ba zai tab'a rushewa ba har abada.......

Deejasmah✍❤🦋

Continue Reading

You'll Also Like

4M 168K 63
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally โฃ๏ธ Cover credit...
2.6M 151K 48
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
11.6K 886 54
Note:I do not own the quotes,They belong to their rightful owners.and credits to them