NISFU DEENIY.......!

By deejasmah15

2.1K 188 40

She was exactly opposite of what he wants in a wife,,,he vowed not to be with her but fate has its own way as... More

PROLOGUE ( TEASER)
CHAPTER ONE (REJECTION)
CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO)
CHAPTER 3 ( MY PRAYING POINT)
CHAPTER 4 ( HOW I WISH....)
CHAPTER FIVE (MEETING.. ).
CHAPTER 6 ( MISFORTUNE....!)
CHAPTER 7
CHAPTER 8 ( HIS VISIT)
CHAPTER 9 ( THE RIDE)
CHAPTER 10 ( SHE'S BACK)
CHAPTER 11 ( SHE'S BACK II)
CHAPTER 12 ( DAYS TO GO.....)
CHAPTER 13 ( #BECOMINGMRSBAY)
CHAPTER 14 ( DAY ONE)
CHAPTER 16 ( A_RIDE_TO_YERWA)
CHAPTER 17 ( LIVING WITH HIM)
CHAPTER 18 ( HER EFFECT)
CHAPTER 19 ( SICK)
CHAPTER 20 ( SHE'S TO SOFT)
CHAPTER 21 ( GETTING TO KNOW HIM)
CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)
CHAPTER 23 ( DAY AFTER )
CHAPTER 24 ( GETTING ALONG OR GETTING APART?)
CHAPTER 25 ( SETTING THE GROUNDS)
CHAPTER 26 ( SACRED TRIP)
CHAPTER 27 (THE PERFECT HER)
CHAPTER 28 ( PROUDLY HIS❤)
CHAPTER 29 ( MILESTONE)
CHAPTER 30 ( HURRICANES)
CHAPTER 31 ( MEETING II)
NISFU DEENIY 32 (BROKEN)
CHAPTER 33 ( BROKEN 11)
CHAPTER 34 (DAY-OFF)
CHAPTER 35 ( HIS WIFE)
Chapter 36 ( HIS WIFE II)
CHAPTER 37 (LIVING WITH HER).
CHAPTER 38 ( SOMETHING'S IN THE AIR)
CHAPTER 39 ( HIS💜)
CHAPTER 40 ( MINE🎭💜)
CHAPTER 41 (THEN)
CHAPTER 42 ( ALL OF A SUDDEN)
CHAPTER 43 ( WHAT WENT WRONG?)
CHAPTER 44 ( WHAT COULD IT BE)

CHAPTER 15 ( HONEYMOON)

38 3 0
By deejasmah15

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 15 ( Honeymoon).

"Beautiful nonsense " shi ne kalmar da ya jefeta dashi yana k'wata, ruwanshi ya shanye yayi jifa da gorar kafin ya nufi d'akinshi. Wanka yayi ya fito yana kallon time, ganin da d'an sauran lokaci kafin magrib ya sanya shi zama a gaban mirrorn. Dangwale-dangwale ya din ga yi, ya mittsikka wancan ya goga wancan. Sai da ya gama kafin ya nufi gadon da towel d'in jikinshi ya kwanta ba bacci yayi ba, dogon tunani ya tafi na rayuwa.

Kiran sallah ne ya katse mai tunanin da ya keyi, toilet ya koma ya d'auro alwala kafin ya fito ya shirya cikin jallabiya. Turare ya fesa ya fita daga d'akin zuwa masallaci.


Masalllacin a nan farkon street d'in su yake, kusan 'yan familyn ne suka cika masallacin sai na d'aid'aikun mutanen da suke zaune a unguwar. Duk da gidajen layout d'in yawanci mallakin 'yan Yerwa ne but kasancewarta sabuwar unguwa ya sanya suka sai da filaye da yawa ga sauran jama'a bayan an cirewa duka mazan filin da zasuyi gini in sun tashi aure kuma har yanzu suna kan siyarwa don unguwar babba ce sosai duk da bata kai Yerwa estate girma ba shi ma ba isu-isu bane akwai wasu jama'ar da aka zama kamar 'yan uwa.

Basu baro masallacin ba sai bayan ishai, bayan fitowarsu sun jima a tsaye suna tsokanar junansu shi da su Farhaan. In da suka d'an gaisa da yayyinsu da suma sun zo masallacin kafin su rankayo zuwa gida, suna tafe suna cigaba da hira tsayawa sukayi wurin mai tsiren dake gaban masjid d'in kad'an Farhaan ya siya musu kowa leda d'aya kafin suka wuce zuwa gida.

Na shi part d'in ya shige sai da yayi al'adar rayuwarshi kafin ya kwanta bacci, yau ma dai tunanin Suliem ya hanashi runtsawa sai da ya had'a da istigfari kafin baccin ya d'aukeshi a wahale cike da sak'e-sak'e.

Ita ma dai yau da sak'e-sak'en ta kwana, a jiya ba ta da damuwa gani take kamar hak'arta ya kusa cimma ruwa. Amma a yau reality ya sark'afe ta, ta wartaske daga tunanin da anyi aure shikenan. Ta gane ashe da sauran rina a kaba, da kuma buk'atar ta natsu wurin shiri mai kyau a zamantakewarta da shi. A yau ta amince ba ya sonta kuma k'ok'arin cusa masa sonta ta k'arfin tsiya ba shi ne mafita ba it requires patience and determination, wanda take fatan ya zame mata makami mai k'arfi wajen yak'i da k'iyayyarta. Yanzu lokaci ne da zata fahimceshi da abinda yake so, but how? Shi ne abinda bata sani ba sai dai kuma zata bi shi a yanda yake so d'in taga mai hakan zai haifar.
'Uhmmm' wai in ji mai ciwon hak'ori.

Washe gari haka ta tashi wasai abunta, bak'i ta cigaba da yi kamar yadda gidan amarya yake tarawa. Har su Abba da Umma sun zo gidan, time d'in baya nan dama Abban yace ba wurinshi yazo ba ai ko ta sha gata ranar Abba ya sake jaddada mata akan in yayi mata ba dai-dai ba ta sanar masa. Umma kuma tace " zata kawo mata 'yar aiki" toh kawai tace haka suka tafi suka barta cikeda kewa, haka su Safwaan da sauran samarin familyn su Maheer, Zaheer da sauransu duk sunzo. Suma sun dad'e suna shak'iyancinsu kafin suka tafi sai sauran matan masu aure da kusan a nan unguwar suke zaune.

Abbu ma yazo shi da su prof da Daddy senator da sauran iyayensu maza, basu wani dad'e ba nasiha sukai mata kowa yana maimaita mata muhimmancin hak'uri da kawaici. Hakaza sauran iyayen nasu mata ba su dad'e ba suka tafi suka bar ta a gidan mijin nata.


Two weeks later.

Rayuwarta take ita d'aya kamar ba ya gidan, kamar yadda ya fad'in mata, hakan ko ya sama mata salama a rai da zuciyarsta. Ba ta san fita ko shigar shi ba don ta k'ofarshi yake hidimarshi, though ta kan ji shi a main parlor yana kallo ko wasu ayyukan. Ta kan kuma tararda takeouts d'in shi idan tazo shara da safiya meaning shigo da abinci yake yi hakan ne ma ya sanya dakatar da Umma daga kawo musu.



Duk abinda zai had'a ta dashi ta gujeshi, hasalima ta daina zama a main parlorn balle su had'u da shi. Kullum tana na ta shiyyar in ta gama gyaran gida ta d'an dafa abinda take muradi, wata rana tayi kallo watarana kuma tana artroom d'in ta a can take yini sallah ne yake fito da ita. Ta ko yi zanuka da dama, frames tayi order aka kawo mata har gida nan ta sanya arts d'in a ciki tayi hangin d'insu a room d'in ta. Abunku da mayyar Burhaan sai da ta zana fuskarshi a yana yin murmushi, gemunshi da sajenshi ya fito sosai zanen yayi kyau ainun tayi retouching da finishing da kyau a k'asa tayi inscribing " loving you isn't my choice but living with you is the best decision ever, you're my own priority no one matters but you". Da allusry style tayi rubutun, Frame ta samu mai mugun kyau ta sanya a ciki a bedside ta ajiyeshi.

Ta so zuwa gida sanda su Ummu zasu koma, Ummun ce ta hanata wai bata dad'e ba. Ai ko ta kira Hajjah ta sa mata kuka, sai da ta tsagaita don san ranta kafin Hajjahr tace " ai dama na gaya miki, ke da fita sai bayan wata biyu don haka kuyi sallama ta waya ".

Kukan ta k'ara tana cewa " ni ba zan yarda ba, in yi ta zama kamar wata tsohuwa". Dariya hajjahr ta sanya tana cewa " toh ki fito yau kawai sai ki ga yanda zanyi dake mai taurin kan tsiya kawai ". Yanzu kam kukan gaske ta sanya ba na shagwab'ar ba, tausayinta ne ya kama Hajjahr don haka tace " To yi shiru ki daina kukan, ai su Sameehan zasu zo".

"Don Allah ? Ita da Abbu? Hajjah don Allah ke ma kizo". Ta fad'i a jere kamar yarinya " suma sai su fasa zuwa, ashe kukan naki na k'arya ne". Diddira kafa ta farayi tana cewa " wallahi ba k'arya bane Hajjah, ki zo ki gani ma yanzu". Girgiza kai tayi kawai bata ce komai ba, cewa tayi " Hajjah kema zaki zo please?".

"Aa Lele sai in kunzo mana sallama kya zo da shi d'in" Hajjahn ta furta, da sauri tace " sallama in zamu je ina kuma Hajjah?". Cewa tayi " nima ban sani ba fa, sai anjima ". Ok tace tana ta jujjuya maganar, sai kuma ta tab'e baki ta barta nan hasalima kiran Ummun tayi da zumud'i tana mai tambayarta yaushe zasu zo, Girgiza kai Ummun tayi tana cewa " anjima zamu zo da su Tayyib".

"Abbu fa?" Ta tambaya da d'oki, cewa tayi " yace ba zai zo ba, wait ba sun zo ba". Tura baki tace " Abbun da bai dad'e ba ya tafi". Murmushi tayi tana mai jinjina rigimar Lelen tace " Toh da so kika yi ya kwana a gidan ko me?". Tace '' at least dai" Ummun tace " ni dai sai munzo bye " ta kashe wayar ba tareda ta jira rigimar Lelen ba. Itama ajiye wayar tayi ta tashi ta nufi kitchen don shirya musu kayan tarba.

Bayan zuhr sai gasu nan sun iso gidan, suna shigowa ta ruga da gudu a parking lot ta tare su. Su Tayyib suka sanya mata dariya ita kam ko kulasu ba tayi ba ta rungume Ummu tana fashewa da kukan shagwab'a.

Sai da ta gama kukan nata kafin ta sake ta, kana ta rik'o hannunta sai lokacin ta kalli Talhat tana mai cewa " Yaa naa". Harararta yayi cikeda wasa yana cewa " sai da kika gama tsallen ganin Mamanki kafin kike tunawa da ni ko?".

"Kai ka gode an ma kalleka ni ne banza ko inda nake ba a kalla ba". Tayyib ya furta cikeda basarwa " ni Nadeefatou k'anwar 'yan biyu ina na isa in manta rabin raina ai nafi missing d'inka fiyeda kowa".

"Story for the gods" ya furta har da murgud'a baki, sakin hannun Ummu tayi tana kama na shi tace " Allah fa abokin fad'a". Fisge hannunshi yayi yana mai cewa " in na yarda in b'ele, ke ni na ma fasa shiga cikin gidanki inda na fito zan koma since I'm not welcome ".

Da gudu ta d'afeshi tana mai cewa " wallahi ba inda zaka je sai ka shiga cikin gidan nan". Dariya Ummu ta sanya ita da Talhat tana cewa " kana son wahal min da yarinya ko Tayyib?". Talhat ya bige kanshi yana cewa " get in my friend". Sake shi tayi suka rankaya zuwa cikin gidan.

Rasa in da zata saka su tayi, parlornta ta kaisu a can ta dire musu abincin da ta tanada domins. Daga nan kuma tazo ta nanik'ewa Ummu, ko da tayi serving d'insu a plate d'aya tare suka ci su duka da suka gama suka natsa ne Ummun tace " Bibtie ina Islaam d'in yake?".

Dafe kai tayi tana cewa " ya fita office tun safe, da kuma kuka ce zakuzo ban ma gaya masa ba". Tayyib yace " Allah sarki, har ya koma kenan? I thought sai kun dawo zai koma ai ". Kallonshi tayi cikeda mamaki tana mai cewa " in mun dawo daga ina?".

Talhat yace " wa ya sani? K'ila maganannen can zai aikeku ne". Kai this can't be a mistake, meyasa ake ta mata maganar tafiya ne kam? Tukunna ma ina zasu je. Kallon Tayyib d'in tayi tana cewa " ni dai gaya min kaji Sahibiy, ina zamu je?".

Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa " wai baki gane mai ake nufi da tafiya ba? abinda muke nufi fa in kun gama amarcin gabad'aya sai ku koma bakin aikin a tare tunda kin matsa sai anyi miki explanation a gaban Ummu".

Ido ta rufe tana dariya, duk da bata yarda da maganar ba but zancen ya mugun sata a kunya. Shi ko Talhat kallon gargad'i yayi masa daga haka suka ci gaba da hirarsu. Gab da la'asar suka shirya tafiya, nan fa y'ar rigimar ta sa rikicin wai basu dad'e ba duka-duka yaushe suka zo. Tayyib ne yace " ashe dai bs ranar da zakiyi hankali Lele, thought in kika yi aure zakiyi but I was wrong ". Harararshi ta tsaya yi ba tareda tace uffan ba sai Talhat ne yace " toh abinka da wacce take bin Tayyib Yerwa " ai ko tai masa gwalo shi ko kallonshi yayi a harzuk'e sai Nadeefah yayi l worsening maganar da cewa " shi ya sha rage min hankalin ba?" Kunnenta ya kama zai murd'a Ummu tace " kul! Ka biyota gidanta ka ci zali". Talhat yace " da kin bar shi ai ya bar ganin shi Yayanta ne, ba shi zai hana Yaa Islaam ya lakad'e shi ba ". A haka dai suka rabu cikeda kewa kamar kai a rabun, suna fita ta ja jiki zuwa ciki kukanta ta sha ma'ishi cikeda jin da ma bata yi auren ba ( yoh in ba dole ba mai ya isa ya d'auke yarinya daga gidan iyayenta, ita dasu sai dai ziyara in ba lalurar da ba a fata bane ta gitta Allah ya tsaremu da ita). Ta d'an kwana biyu tana fama da kewar kafin ta wattsake abinta ta cigaba da harkoki.


Kamar kullum yau ma tsaye take a art room d'in ta tana zane, kasancewar ta tashi da ciwon mara ya sanya ba ta shigo da wuri ba sai bayan la'asar haka nan taji shawaar zane. Tea splash style takeyi, hannu ta zana rik'e da mirror a mirrorn ne ta fara zana fuskarta a ciki. A wurin gashi sai tayi mata zanen kitson Liberian weavon, hannu ta cusa cikin gashin kanta tana murmushi.

A take taji sha'awar yin kitson a kanta, " zan samu in fita dai in je office a min kitso ko kuma in kira a min home service ne?" ta k'arashe hannunta a cikin tulin gashin kanta da ke gyare tsaf, saboda lokacin da take warewa gyaran kan nan ba k'arami ba ne. Ga shi nan yana ta shining na mai ga kuma hair color da yau a gaba ta shafa ta gefen hagu kasancewar ba ta d'aura d'ankwali akan straight gown d'in da ta sa mai slits biyu ta gefe-gefe ba rigar da kad'an ta wuce gwuiwa ga kuma wuyar da ta kasance open neck so rabin k'irjinta a waje yake. Ba tayi kwalliya ba bayan kwallin da ta zizara, sai powder amma tayi kyau ainun kamar ka saceta ka gudu.

Abun Allah har murjewa tayi da haske da ta k'ara yoh zama wuri d'aya da zero tension. Ko mak'iyi ya ganta sai ya yaba da yanda ta koma balle masoyanta. Ta wurin colorn ta shafa gashin tana cewa " yin kitson dai shi ne yafi ".

"Gaskiya kiyi kitso Bibtie" aka furta ta bayanta, ai da mugun sauri ta waigo tsayawa tayi turus ganin Suliem da sauri ta yo kanta. Rungumeta tayi tsam don rabon da su ga juna tun randa aka kawosu gidajensu, sai ta video call da voice call wai mazajensu sun ce suna hutawa ba zasu fito ba ita dai tazo shiga gidan sai dai rashin ganin Islaam ya sanyata hak'ura kawai.

"My best " ta furta still tana rungume da ita d'in, zareta daga jikinta tayi tana mai bin room d'in da kallo wani mai sky da bishiyoyi ta nuna tana cewa " ni dai wannan ni ke so ". A hankali tace " baki da case bari in sa a kawo frame ".

"Thanks babe, wannan karon ma zakije art exhibition program d'in ne?". Tab'e baki tayi tana cewa " yeah zan je though ba da kaina zan je may be zan bada ne kawai ". Kallonta tayi da kyau tana mai cewa " you know that this is not the first time da kike k'in zuwa, baki tunanin this is the right time da zaki bayyanawa duniya who you are ba Nadee's Arts ba?". Dariya tayi ta kama hannunta tana cewa " ai ko aina I'm Nadee so shi ma wani identity ne". Tace " Nadee can be any name like Nadeeyah or so, why not ki koma amfani da NYY d'inki kamar yadda kike yi?".

"Akwai bambanci tsakanin personal arts d'ina wanda ban bawa kowa sai irinku, su ne nake sa NYY while Nadee's Arts is my public name so ba zasu had'u ba ". Tab'e baki kawai tayi ta san halin Nadeefahr da mugun naci ba yau suka fara haka ba. a hankali tace " toh ki ajiye zanen nan muje parlor, my husband is there waiting".

Tsalle ta sa tana mai cewa " Allah sarki Yaa Sadeeq d'ina " rakota tayi a baya, bedroom ta shige a saman rigar jikinta ta d'aura wata Abaya k'irar Bahrain Burnt orange sai black veil da ta d'aure gashinta turare ta k'ara tana fitowa lokacin har Suliem ta koma parlorn.

"Shi ne aka wani yi zuwan bazata" shi ne jumlar da ta shigo dashi parlorn sounding excited, Zulfaa dake zaune gefen Suliem tace " baki gode ba kenan?". Waro idanu tayi tana mai cewa " I'm more than grateful babe, it's just that I was unprepared".

Gefen mazan ta kalla za tayi magana idanunta ya fad'a cikin na dodon nata, ita fa ko k'amshinshi bata jiba sai yanzu. D'an daburcewa tayi sakamakon idanunshi masu kaifi da ya kafa mata cikeda kallon gargad'i, kawar da nata idanun tayi tana mai fad'ad'a faraarta.

Tace " kaga mijin Zulfaa " ta furta referring to Farhaan, juya idanu yayi yana cewa " fad'i ki k'ara matar Islaam". Murgud'a baki tayi tana mai cewa " dama ai kowa ya sani I'm his wife". Da same tone yace " ni ma haka kowa ya san I'm Zulfaa's husband" Kallon Yayanta tayi tana cewa " Yaaa naaa". Murmushi yayi mata yana extending hannunshi, kamawa tayi ta rik'e a nata sai kuma ta sa dariyar shak'iyanci.

"Lallai Babe ta iya kiwo, kaji yanda hannunka yayi lukuti kuwa?". Ta furta tana cigaba da dariyarta, gabad'aya dariya suka sa wai hannunshi yayi lukuti Farhaan ne yace " ke dai 'yar nan Allah ya shirya ki dama k'iba har a hannu akeyi?". Murgud'a baki tayi tana shigewa kitchen bayan tace " ai kai naka a kunne kayi, rashin ji sai abinda yayi hali ". Wani sabon dariyar suka sakeyi shi ko cewa yayi " ba dake zan yi ba yarinya da mijinki zan yi, shi ne dai-dai ni ".

Kamar a bazata yace " b'acewa zakayi Malam, don ko ita tafi k'arfinta bare ni ". Dariya matan suka saka k'asa-k'asa su ko mazan musu suka sa shi Farhaan harda cewa 'a gwada a gani". Sadeeq na zuga shi, d'auke da tray ta fito a gaban mazan ta ajiye ta koma ba tareda tace uffan ba.

Kamar an tsikari Burhaan ya tashi ya bita, Farhaan ne ya sa dariya da cewa " dama tun d'azu kake son bin ta, sai ka dawo ". Bai tanka ba su ko yana shigewa harda gulmanshi oho bai ma san sunayi ba, wai kunu a wani gida.

Ta kammala yanka vegetables d'in da zatayi using a cous-cous d'in da zata had'a musu sharp-sharp, sai ta d'auki next tray da ta jera ruwa, exotic da small chops d'in da take ajiyewa domin kanta da bak'i. Juyawan da zatayi taga mutum a tsaye a jikin k'ofa, da sauri ta rik'e trayn hannunta da kyau don jin ya tafi kamar zai fad'i.

Gyaran murya yayi yana takowa gabanta, miyau ta had'iye jin ya d'aura hannunshi a kan nata dake shaking. Cikin dakakkiyar muryarshi yace " Magana nake son yi da ke ".

Bata samu zarafin amsawa ba sai kai da ta gyad'a mai, tana mai jan iska a hankali bai ko kula da yanayinta ba ya ci gaba da maganarshi. " Ina son idan sukayi miki magana akan honeymoon, ki nuna ba kya ra'ayin zuwa no matter how you'll put it just convince them that you are not interested that's all".

"But why?" Ta tambaya kamar an fisgi maganar daga bakinta, murmushin mugunta yayi yana cewa " Ba kya ganin honeymoon na masoya ne, while we are not one? tafiyarmu will just be waste of time and resources ko ba haka ba". Da sauri ta kalleshi jin abinda ya fad'in, ko a jikinshi ya maimaita tambayar tashi " ko ba haka ba?".

"Haka ne, in gaya musu hakan kenan?" Ta tambaya itama cikin son controlling hawayenta, cewa yayi " you can tell them that babe, your words not mine". Daga haka ya zare trayn daga hannunta yayi ficewarshi, sakar masa tayi cluelessly.

D'ukawa tayi a gaban kitchen island d'in tana fashewa da kuka, sai da tayi maishinta kafin ta tashi. Tap ta bud'e ta wanke fuskarta kana ta fito, suna zaune suna ta hirarsu kamar ma an manta da ita nan ko ganin idon Islaam ne ya sa sukayi shiru daga gulmar da sukeyi. A gefen matan ta zauna sai lokacin suka gaisa da juna cikeda shak'uwa, sannan suka d'aura da hira.

Shi dai Islaam ya zama d'an kallo a wurin don yanda suke hirar ya nuna ba k'aramar shak'uwa bace a tsakaninsu duka, wanda shi bai da ita. Iyakanshi d'an murmushi in ta kama shi ma ba sosai ba, har lokacin basu sako maganar honeymoon d'in ba excusing kanta tayi ta koma kitchen.

Fried cous-cous da taji vegetables da liver ta had'a musu, tayi kyau sosai ta juye a wata kyakkyawar elegant warmer. Sai ta had'a apple and grapes mocktail ta yi dressing da whipping cream da sprinkles. Sai salad da ta had'a na chicken nuggets da yaji milk da mayonnaise sosai.

A babban vanity tray ta jera komai ta nufo parlorn dashi, tana fitowa Farhaan da k'amshi ya isa ya tareta kamar zai amsa yana cewa " kaga k'amshin Yerwa mai abun ban mamaki". Dariya kowa ya sanya ta jefeshi da hararar wasa tana mai cewa " ai kai in dai kwad'ayi ne ka d'aure masa k'ugu, ka goyashi a baya ".

Zulfaa tace " don't forget that I'm a professional chef, balle ki ce bamu iya ba ake yabon naki ". Farhaan yace " tell her dai babe, tama godewa Allah za a taimaketa a ci abincinta".

"Ahh toh may be ma fa k'amshin ne kawai ba dad'i" ta tareda fad'i shewa ta sanya tana cewa " and who's begging you to eat? Ai sai ki tashi ki shiga kitchen d'in Aunty cook". Ta k'arashe da ajiye trayn a dining, Zulfaa tace " taimaka miki zamuyi muci, we don't want to turn you down besides if we don't eat..." Farhaan ya katse da cewa " who go eat this food? Mu ma ai saboda 'yanuwantaka zamu ci ".

"Na ga irin naku, yanzu ta hanaku a tafi da ita a bakin duniya ana cewa tayi rowa leave them babe yau sai dai matarshi ta masa girki". Burhaan ya fad'i yana k'arasowa dining d'in, d'ago kai tayi tana kallonshi ido ya kashe mata kawai. Sauran ne suka taso suma Farhaan yace " ai wallahi ba wanda ya isa ya hanani cin abincin nan, kai ne dai ba zaka ci ba".

" Dama ni ba yanzu zan ci ba, duka yaushe ne Babe ta cika min ciki da lunch wannan naku ne kuyi manage nawa sai anjima" ya furta yana zama a kujera, suma zama sukayi tayi serving d'insu har da kanta don bata ci komai ba tun breakfast. Burhaan yana kallonsu suna ci suna zuba santi ga k'amshi ya takurashi amma pride ya hanashi cin abincin itama dama har ga Allah ba ta dafa da shi ba. Haka suka cinye abinsu Farhaan harda k'ari yana kaiwa ciki yana cewa " Allah Bro yayi dad'i fa, ka ci kaji ". Tab'e baki yayi yana cewa " ni ko na san da hakan, don komai za ta dafa dole ya zama mai dad'i  ". Sai lokacin Suliem tace " Alhaji angon chef ai bai kamata kaci abincin nan ba fa, da ka bari madam ta dafa maka" harararta yayi yana cewa " ba zata dafa ba d'in, ina ruwanki ma?" Sadeeq yace " har da tsakinta, ka kuma daina harararta ke Madam chef ki sawa mijinki waigi kar ya fad'i " dariya suka fashe dashi har da ita, shi dai bai tanka ba sai da ya cinye wanda ya k'ara d'in kafin yace '' toh ki gode mana madam, mun taimakeki baki b'ata abincin ba da fa sai dai a zubar toh abinka da 'yanuwa ".

''Yanzu ma ai zubarwan a kayi don ba bolar da ta kai taka d'iba" ta furta tana murgud'a baki, me zasuyi in ba dariya ba murmushi yayi sai yanzu ya lura da wasan dake tsakaninsu ba komai bane face 'yan mace da 'yar namiji da sukeyi ba wai soyayya yanda ya zata ba. Tashi sukayi suka koma parlor matan suka gyara wurin sukayi wanke-wanke, kiran sallah ne ya sa suka shige ciki kawai su kuma mazan suka tafi masjid.

Basu dawo ba sai bayan ishai, su ko hirarsu ta yaushe gamo aka sha. A nan Suliem ta sako zancen tafiyar tasu zuwa k'asashe uku wanda Daddy Senator ya d'auki nauyinta, da private jet d'in shi ma zasu tafi. Lumshe idanu tayi ta bud'e akan Suliem d'in tana cewa " sai kun dawo kam, don ba damu za ayi wannan tafiyar ba".

"Why?" Zulfaa ta tambaya tana kallonta " aikinshi mana, kin san dai likitoci basu da lokacin pleasure aikinsu yafi komai". Ta bata amsa a hankali, Suliem ta bita da kallon tuhuma tana mai cewa " ni ban gane inda kika dosa ba, shi yace ba zaku ba or who?". Girgiza kai tayi tana cewa " basu bashi hutu bane, duk yabi ya damu akan haka shi ne nace ya barshi kawai in an samu hutu sai mu je ko Umrah ne".

"You must be sick in the head Lele, ku zauna kuyi uban me a gidan?" Zulfaa ta furta cikeda masifa " dariya ta kwashe dashi tana mai cewa " calm down madam, muyi namu honeymoon d'in mana ai a koina akayi indai an samu satisfaction d'aya ai ta biya, besides I'm against the idea of that honeymoon thing ".

"Wonders shall never end" in ji Suliem tana mai rik'e baki, Zulfaa tace " wallahi k'arya kikeyi that must be the reason da ya sa kuke fad'a dashi kenan ". Waro idanu tayi cikeda mamakinta tana cewa " fad'a kuma? Ni da wa muke fad'an?". A harzuk'e tace " shi Yaa Islaam d'in mana a parlor fa muka iske shi zaune ya zurawa k'ofarki idanu cewa ma fa yayi mu shiga kina ciki sai Suliem tace bari ta kiraki and kin fito yana ta yin abu da rawan jiki kamar ba Yaa Islaam ba".

"Sai kuma aka ce fad'a sukeyi kenan? In ma suna fad'an sai ya zamana akan honeymoon sukeyi? Mata da miji kan samu sab'ani akan abu k'arami ma kawai basu cika bari yayi nisa ba so fad'ansu ba huruminmu bane ki bari yanzu dai ba zakije honeymoon ba right?".

"Ba zamuje yanzu ba sai time d'in da ya samu hutu shi ma Umrah zamu je, I also wish that mun tafi tareda ku I know it will be fun". Ta furta da murmushi cikeda son kawar da damuwarta, gyaran muryan da akayi a bayansu ne ya ankarar dasu shigowarsa. Tun d'azu ya shigo ya kuma ji duk hirar da sukayi da ita, waigowa sukayi a tare suna kallonshi bai ce komai ba ya dai tsaya a k'ofar hakan ne yasa su fita zuwa parlor aka barsu su biyu.

Kallonta yayi da kyau yana cewa " you did well, dama you are good at creating stories I can applaud you for that yanzu saura kiji da Daddyn kawai ". D'ago kanta tayi jin yanda ya kirata mak'aryaciya kai tsaye, kuma a hakan yake nufin tayi magana da Daddy lallaima. "Ba zan iya gaya musu hakan ba wannan kuma aikinka ne ni nayi nawa". Ta furta tana mai shirin zagayeshi ta fita, janyota yayi baya ya tsayar da ita a gabanshi yana mai cewa " banda aiki akan haka, ke zakiyi abunki ki gabad'aya besides taimakon kanki zakiyi don kika sake aka tursasa ni tafiyar nan dake na rantse miki sai kinyi nadamar tafiyar tamu. Don depression sai ya kama ki shiyasa nake guje miki hakan amma in kin shirya toh ga hanya nan sai kin dawo". Daga haka yayi ficewarshi ya bar ta a wurin, ajiyar zuciya ta sauke tana mai bin bayanshi da idanu ita dama ko giyar wake ta sha ba zata bi shi ba balle da hankalinta bin bayanshi tayi zuwa parlorn inda ta tarda suna hirar tafiyar Zulfaa tana basu labarin wai tace ba zasu je ba.

Zama tayi tana mamakin yanda suka d'auki abun suka sa a ka, sai kace honeymoon d'in ne gaba da komai ko don shi ake auren. Ba komai bane face d'abbaka sunnar turawa, and it's not like she's against it Aa itama ta dad'e tana burin yinsa da mijinta abun k'aunarta. But kamar yadda ya fad'i tafiyar masoya ne and they are not one, gaskiya ya fad'i amma abun yayi mata ciwo fiyeda yanda kake zato.

Tana jin shi yana ma su bayani akan dalilin da ya sa ba zasu je ba, wai akwai patients d'in shi da aka kawo daga yak'i shi yake musu physio ba zai yiwu ya barsu wurin wani ba bla bla bla ita dai jin su takeyi kawai bata tanka ba. Ba su dad'e ba sukayi haramar tafiya gida, har gate suka raka su don a k'afa suka zo tunda gidajen babu wani nisa tsakaninsu.

Suna shiga ta rufe main door na entrance ta waiting room ta kashe hasken kana ta rufe na living room, ba ta kashe hasken ba ganin Burhaan ya shiga kitchen da takeaway pack alamun zai yi microwaving. Wucewa tayi zuwa nata wutan koina ta kashe ta shiga bedroom, bata zauna ba ta shige cikin toilet wanka tayi ta gasa jikinta sosai sannan ta kimtsa jikinta da kyau kana ta fito. Nightie ta nema mai kauri ta sanyi bata shafa komai a jikinta ba ta kwanta, wayarta ta janyo nan ta tarda miss calls bud'ewa tayi tana duba kiran. Daddy ne sai Abba rasa wa zata kira a cikinsu tayi kiran Abba da ya sake shigowa ne ya katse ta da sauri tayi picking tana mai sallama a hankali.

Amsawa yayi yana cewa " ya kuke ya gidan?" Alhamdulillahi ta iya cewa tana mai lusmshe idanu " Lele wai kece kika ce ba zakije tafiyar da daddynku ya shirya muku ba?" ya furta plainly and straight forward, girgiza kai tayi kamar tana gabanshi tace " Ba haka bane Abba dama ka san yanayin aikinshi, ba hutu suka cika samu ba...."

"Mun san da hakan ai, da kaina nace zan nemi hutun sai kuma ga maganarki ta fito shi yace ki fad'i hakan ko?". Ya katse ta, da sauri tace " Aa Abba shi ma yana son tafiyar ganin ya damu ne ma nace a bar shi kawai besides ba wajibi bane zuwan Abba kuma a lokuta da dama rashin zuwar yafi zuwan faidah ".

"Ohh really?" ya tambaya cikeda mamakinta, ita ko bata kula ba tace " Allah Abba, koyarwar turawa ce fa ba wai ina condemning tafiyar bane but ni dai ba wani son shi nake ba shiyasa ma nace in ya samu hutun muje Umrah ". Murmushin manya yayi cikeda jindad'in hangen nesa irin tata wato dai ba zata iya fitowa fili tace mai ba zata je ba shi ne ta bi ta haka, dama kowa da nashi ra'ayin and he loves and respect hers fiyeda tunani. Don haka yace " Allah yayi muku albarka I'll talk to your daddy about it, Be safe okay?". Murmushi tayi tana cewa " Ameen ya rabbi Abbanmu sai da safe". Kashe wayar yayi itako runtse idanu tayi sai lokacin take tunanin maganganun Burhaan d'in, sai kuma tayi murmushi tana mai ce "mu ba masoya bane right? Oya naa time will tell......"

Oya naaa we shall see Lelen Yerwa🌚

Deejasmah✍❤🦋

Continue Reading

You'll Also Like

218 49 5
In a village where female empowerment has never been heard of,a village where girls are married off to men old enough to be their fathers once they s...
4.3M 236K 49
"Stop trying to act like my fiancée because I don't give a damn about you!" His words echoed through the room breaking my remaining hopes - Alizeh (...
967K 30.1K 61
Dans un monde où le chaos et la violence étaient maitre, ne laissant place à ne serrait ce qu'un soupçon d'humanité. Plume était l'exception. Elle...
671K 96.9K 37
Yaduvanshi Series #3 it is a book under yaduvanshi series. But it could be read as standalone too. Nitya Raghavendra is a telugu businesswoman earnin...