EMAAN

By Zaynabyusuuf

13.2K 390 1

delve into the interesting story of emaan and alameen hate-love story which will get you in suspense from sta... More

PAGE 01
PAGE 02
PAGE 03
PAGE 04
PAGE 05
PAGE 06
PAGE 07
PAGE 08
PAGE 09
PAGE 10
PAGE 11
PAGE 12
PAGE 13
PAGE 14
PAGE 15
PAGE 16
PAGE 17
PAGE 18
PAGE 19
PAGE 20
PAGE 21
PAGE 22
PART 23
PAGE 24
PAGE 25
PAGE 26
PAGE 27
PAGE 28
PAGE 29
PAGE 30
PAGE 31
PAGE 32
PAGE 33
PAGE 34
PAGE 35
PAGE 36
PAGE 37
PAGE 38
PAGE 39
PAGE 40
PAGE 41
PAGE 42
PAGE 43
PAGE 44
PAGE 45
PAGE 47
PAGE 48
PAGE 49
PAGE 50
PAGE 51
PAGE 52
PAGE 53
PAGE 54
PAGE 55
PAGE 56
PAGE 57
PAGE 58
PAGE 59
PAGE 60
PAGE 61
PAGE 62
PAGE 63
PAGE 64
PAGE 65
PAGE 66
PAGE 67
PAGE 68
PAGE 69
PAGE 70
PAGE 71
PAGE 72
PAGE 73
PAGE 74
PAGE 75
PAGE 76
PAGE 77
PAGE 78
PAGE 79
PAGE 80

PAGE 46

140 5 0
By Zaynabyusuuf

EMAAN....PAGE 46

Written by Zaynabyusuf✍🏼

  da wani irin kallo alameen ya bita mai cikeda mamaki da al'ajabi har ta ɓace ma ganinshi,ya daga kafada in an i don't care attitude so many things going through his mind,Mami ce ta tsaya mishi arai tana makale acikin xuciyar shi,har yanxu sautin kukan ta yakeji yana sauka acikin xuciyar shi mai tafarfasa tana ci da wuta,alokacin ya sake jin tsanar emaan na yawo ajikin shi,saboda ita mamin shi ke cikin matsananciyar damuwa ,dalilin ta yasa mamin shi ke xubarda hawaye ya fada with burning rage xuciyar shi na yin xafi mara mislatuwa,ji yayi baxai iya cin abincin ba saboda damuwar dake nuƙurƙusar xuciyar shi ,tun fitar shi suke waya da mami yana bata hakuri amma duk abanxa,itadai babban burinta shine ya saki emaan,ya tabbatar mata he'll definitely fulfill his promise amma ba'a wannan gabar ba,idan ya saki emaan yanxu me akayi kenan?ribar me ya samu banda wahalar xama da ita da yayi under the same roof?yakasa thinking straight alokacin sai kawai ya xura wayar shi cikin aljihu ya haura sama,kamshin turaren emaan ya shaka yana bin kowani lungu da sako na cikin kanshi,hakan ne ya tabbatar mishi tana parlon sama,axuciye ya karasa cikin parlon yana kallonta cikeda takaici,tana xaune asaman kujera idanunta na kan tv tana kallon wani american movie mai suna hijack,dagaske yau din take kallo saboda film din yayi mata bala'in  kyau,haka ne yasa bata lura da xuwan shi ba,ganin she's so invested a kallon alamar yana mata dadi yasa cikeda isa ya dau remote ya kashe Tvn gabadaya,dan xaro ido tayi cikeda mamaki ta juya tana kallonshi,gabanta ne ya fadi saboda kallon dayake mata mai cikeda tsananin fushi da kiyayya mara fasaltuwa, basai ya furta adadin kiyayyar dayake ma emaan da fatar bakin shi ba,kallon dayake jefa mata ya isa ka tabbatar da baya kaunar yarinyar kona miskala xarratin,sauke idanunta tayi tareda mikewa xata bar parlon ya wani jawota baya furiously looking at her face with ultimate hatred,with passion yake fada mata maganganun dasuka sa hawaye masu xafi suka xubo mata,she couldn't handle it anymore saboda takaicin daya tokare mata wuya ya hana miyau wuce mata,aduniya ta tsani a dinga accusing dinta akan abinda bata aikata ba,kuma dab'iarta ce kare kanta no matter the situation she's in,saide ahalin datake ciki yanxu bata damu da tayi defending kanta ba,dan haka tace mishi"insult me all you want,condemn me all you like,I don't care about what you say or think about me alameen,amma kasani xaka maimaita hakan very sooon...."saurin katseta yayi ya ce"ni kike fada ma haka?ni kike ce ma xan maimaita abinda na fada?tell me me xakiyi?akwai abinda kika isa kimin ne emaan?how dare you even think about that?"ya daka mata tsawa,saurin runtse idanu tayi saboda tsoro,yace"i don't speak to people with their eyes closed,now open the damn eyes immediately..."ya fada sautin amon muryarshi na sauka asaman fuskar emaan,kin bude idanun tayi kirjinta na hawa da sauka slowly yet heavily,yace"wannan shine last time da xan sake maimaita miki magana you idiot,now open the fucking eyes"samun kanta tayi da bude idanun ta,ba don taji maganar shi ba ko kuma ta bi umarnin shi ba,sai dan ta xaxxaga mishi maganganun dake yawo acikin xuciyarta kamar yadda ya kunsa mata bakin ciki saita rama fiyeda haka,yace"now answer my question,how dare you think xan maimaita abinda na fada very soon?what the heck are you planning to do?what are the damn plans..??"ya fada yana dunkule hannu ya daki bango da karfin gaske,da mamaki emaan ke kallon shi saide har lokacin bata ce komai ba,wani kallo ya wurga mata wanda yasa kafafuwanta suka fara rawa taji baxasu iya cigaba da daukanta ba,tana neman silalewa ta xauna ya wani riko kanta da karfin gaske,hular kanta ce ta fadi dan haka ya damƙe long black hair dinta wanda yake akwance mai masifar kyau yana fitar da wani kalar inviting kamshi,duk masifar da alameen ke yi saida yaji kamshin ya hau mishi kai yana yawo acikin kwanyarsa,sake damke gashin yayi mai tsananin taushi da tsantsi,emaan ta runtse ido tana jin xafin damƙar da yayi mata,murya ashake tace"let go off my hair alameen...."ta fada  tana neman ma kanta ɗauki,cikeda mugunta ya sake damƙe gashin wanda hakan yasa emaan xubarda hawaye ga wani mahaukacin fitsari dake neman xubo mata awurin,ganin dagaske ba kyaleta xaiyi ba ta dora hannunta guda biyu akan nashi ta rike gam tana jujjuya kai cikeda axaba,sanda ta dora hannunta akan nashi ji sukayi kamar wayar shocking ta jona musu saboda electrification din daya ratsa both of them,cikin wani irin yanayi yayi saurin sakin gashin yana xaro ido waje cikeda dinbin mamaki,like what just happened?ita ce tambayar dake mishi yawo axuciya,xama emaan tayi saboda yadda jikinta yaxama so weak ta tallafe fuska tana sakin wani marayan kuka saboda xafin da kanta yake mata,tsawa ya saka mata yace"keep your mouth shout and get lost"banxa tayi mishi tacigaba da rera kuka wanda yake jinshi har cikin brain dinshi,ya tsani sautin kuka arayuwar shi kuma duk wanda yake tare dashi yasan da hakan,kuka na saurin karya mishi xuciya da ruhi,jikinshi ne yayi sanyi amma a xafafe yace"I said keep your mouth shout"ya sake fada yana kallon fuskar ta,saide har lokacin kuka emaan keyi anutse ko dagowa ta kalle shi batayi ba,bedroom dinshi ya shiga yana banging kofa sannan ya shiga bathroom ya watsa ruwa,saida ya gama shiryawa cikin wasu white color free size pajamas acikin walk in closet sannan ya dawo cikin dakin,ga mamakinshi har lokacin kukan emaan yake jiyo wa wanda ta kara karfin kukan nata ,she's crying her heart out today,ba kukan abinda ya mata kawai takeyi ba,kukan rabuwa da Aliyu takeyi da kuma abubuwan dasuka faru da ita arayuwa,yau ne takeyin asalin kuka domin alokacin baya xubar hawaye take yi,ta dade Sosai tana kukan domin shine ke sa take samun relief acikin xuciyarta,afusace ya fito parlon yana kallon ta har lokacin tana inda ya barta,ya karasa daf da ita yace"Tashi ki tafi dakinki kiyi kukan"kallonshi tayi da hawaye cabe-cabe asaman fuskarta,tana mamakin kalar rashin imanin alameen arayuwa,can kuma ta mike tashiga dakinta ta kwanta asaman gado tana cigaba da aikin kuka,wayarta dake haske ya kalla yaga alamar shigowar message,har ya juya sai kuma ya samu kanshi da kasa tafiya,ya tsaya yana kallon wayar for a long time sannan ya dawo parlon,bude baki yayi cikeda mamaki ganin Sadeeq ne ya tura mata message,kuma ga mamakinshi yana sliding wayar ta bude ko lock babu awayar,kofar dakinta ya kalla cikeda mamaki bayyanan ne,baiyi tunanin xai samu wayar babu lock ba,saboda 99% of mobile users nasa lock awayar su harda shima karan kanshi wayar shi akwai lock,deep sigh ya sauke sannan ya shiga WhatsApp,ga mamakin shi baiga chats din kowa ba saina Sarah,kai tsaye ya shiga ya karanta komai,bayan ya gama ya bude na kausar,nan ma ya karance komai ya rufe,na anty habiba da umma ne kawai bai karanta ba,amma har chats dinta da Abba saida ya duba,fita yayi daga WhatsApp din yana mamakin ta ina message din Sadeeq yayi popping?direct message ya duba bai ga komai ba,sai ya koma whatsapp kamar yadda xuciyar shi ta umarce shi,archive ya danna yaga sunan Sadeeq harma dana fauxa acan,da mamaki yake kallon messages dinda sadeeq ya turo,kai tsaye ya shiga yana sauke idanunshi akan messages din daya turo guda biyu masu shegen tsaho,atsanake yake karantawa yana jin xuciyar shi kamar xatayi bindiga,ajiye wayar yayi daga bisani saboda baxai iya cigaba da karantawa ba tsabar son da yake ma yar uwar shi,ji yayi kamar yabi Sadeeq har US ya kikkafa mishi mari ko hakan xaisa yaji sauki acikin ranshi,ya dade yana tunanin emaan da sadeeq kafin bacci ya kwashe shi.

Da mamaki sosai mummy ke kallon Abba sanda ya shigo parlon ta,saboda she can't remember when last Ya shigo bangaren nata,hakan ne yasa gabanta tsananin faduwa cikinta ya duri ruwa,jikinta na rawa tace"Sannu da shigowa yallabai,ai da aikowa kayi aka kirani"xama yayi asaman kujera yana kallonta carefully,gumi sai tsastsafo mata sukeyi alamar batada gaskiya,Abba yace"Ina afiya?"saurin kallonshi mummy tayi tana jin xuciyarta na xillo kamar xata faso daga gangar jikinta,afusace Abba ya daka mata tsawa yace"where's afiya?"bakinta na shaking ta nuna mishi kofar dakin Afiya,yace"kira min ita"da wani Kalan tashin hankali mummy ta kira afiya,acan gefe afiya ta rabe tana cewa"Abba gani"kallon su yakeyi duk su biyun cikeda takaici,firstly yace"who do you think you're?"abba ya jefa ma mummy tambayar kai tsaye,shiru ta mishi ya sake tambayar"who do you think you're?"yacigaba da cewa"ni uban afiya dana tsugunna na haife ta kike ɓoye min halin da ƴata ke ciki?how dare you do that?"runtse idanu mummy tayi tana jin xuciyarta na breaking into tiny pieces,shikenan ta shiga uku ta lalace asirinta ya gama tonuwa agaban kishiyoyi,yace"tambayar ki nakeyi kinyi shiru "cikin kuka tace"saboda gudun abun kunya abba,nasan idan xancen sakin nan yafito masu min dariya agidan nan suna da yawa,ga ƴan uwa da abokan arxiki wanda suka samin ido kullum burinsu shine suga na wulakanta a idon duniya,wallahi gudun abin faɗe ne yasa nayi hakan badan baka isa ko kuma baka da ikon sanin hakan..."tsawa abba ya daka mata yace "yi min shiru,akan afiya aka fara sakin aure?idan sunyi dariya ai kansu sukayi mawa,ballantana ma karya kike babu wanda zai miki dariya acikin gidan nan"saurin katse shi tayi tace"Wallahi tallahi saboda gudun abin faɗe yasa nayi shiru da maganar xuwa wani lokaci,saboda babban tashin hankalina shine naxama topic of discussion awurin mutane,abun kunyah ne ace an saki afiya washegarin da aka kaita dakin miji,ni kadai nasan tashin hankalin danake ciki Abba,amma banyi hakan dan Na nuna baka isa ba,nasan kai mahaifin afiya ne kai ya dace kafara sanin hakan,na b'oye sakin ne saboda na rufa mana asiri,saboda kai kanka baxa kaso wani awaje yaji ba,amma dan Allah dan Annabi kayi hakuri".hajjo dake bakin kofa ce ta riƙe haɓa cikeda mamaki,can ta saki uban salati tana tafa hannu,gaban mummy ne yayi mummunan faduwa,shikenan aikin gama ya gama asirinta ya gama xagaye duniya tunda hajjo taji wannan maganar,dama so take ta lallaba Abba su rufe maganar xuwa wani lokaci,takaici ne yasa hawaye masu xafi suka xubo mata,hajjo ta xauna tana cewa"tun farko nasan baxa'a ƙulla abin arxiki ba,dama iya gudun ruwanku nake son gani,gashi nan abanxa da hofi an xamar min da jika baxawara,dama tunda naga figaggiyar matar nan babar Aliyu nasan baxa'a kulla alheri da ita ba,aiga irinta nan".mummy ta kalli hajjo cikeda bakin ciki kamar ta rufeta da duka takeji,hajjo ta tabe baki tace"dama karshen mai son xuciya nadama ne,in ban da haka taya xaki auri Aliyu??dayake shi yanada saiti shine ya miki saki uku adaren aurenku,kinga ya nuna cewar yafi ki nesa ba kusa ba kuma dagaske yake son emaan,naga dai yarinyar nan kamar ƙanwa take awurinki amma kika sa kafa kika shure dangantakar dake tsakanin ku kikace dole saikin aureshi,aiga irinta nan,sai ki dawo ɗakina mu cigaba da xawarci,gara ni mutuwa ce ta rabani da mijina ba baƙin hali da mugun abu ba,ohhh ni hajjo saki adaren aure"ta maimata tana rike haba,mikewa tayi xata fita mummy ta rike kafafuwanta tana kuka tace"ki dubi girman Allah ki rufa min asiri hajjo,abar maganar nan zuwa wani lokaci"shure ta hajjo tayi tana cewa"abdulhameedu matar nan nada saiti kuwa???,abu takeyi kamar na me taɓin hankali,dubi yadda ta rirriƙe min kafa kamar xata xubar dani akasa kuma kana kallo".kallon mummy yayi cikeda takaici yace"miye haka Aisha "sakin kafar hajjo tayi tana kuka tace"ki rufa min asiri hajjo kamar yadda Allah ya rufa miki"cikeda jimami hajjo tace"tabbas Allah ya rufa min asiri kuma nagode mishi da wannan baiwar tashi,maganar saki kuma kowa sai yaji kinji na rantse"kuka Sosai mummy tafashe dashi hajjo tayi tafiyarta tana maganar sakin asarari,Abba dake ta Kallon Mummy tana kuka ya gyara murya yace"ku sameni a parlona bayan sallar magrib "yana kaiwa nan yafice daga bangaren ta,hannu mummy ta dora akai tana kuka domin tasan meeting abba xaiyi agaban kowa da kowa xai cire mata xani akasuwa,tsaki afiya tayi tashige dakinta tabar mummy awurin tana dirxar kuka mai ciwo....

Jiki asanyaye Sadeeq ke jujjuya wayar shi yana tunanin emaan da kuma tunanin halin datake ciki yanxu,even though yana kokarin cire damuwarta acikin xuciyar shi saide hakan ya gagara,sonta yayi mugun karfi acikin xuciyar shi,he's afraid Soyayyar emaan baxata taɓa barin xuciyar shi ba,yanxu kuma ahalin daya ke ciki ya hakura da emaan,ya tabbatar emaan baxata taba xama matar shi ba,ya karbi hakan da kyakkyawan niyya,saide baxai daina sonta ba har ranar da Allah xai karbi rayuwar shi,domin da son emaan rayuwar shi ta ginu,haka nan sonta ne ya tarwatsa mishi komai na rayuwa,soyayyar emaan babbar jarabawa ce wacce Allah ya jarabceshi da ita,dan haka he won't stress himself anymore,duk abinda ya faru haka Allah ya kaddara,yanxu babban burin shi shine yayi focusing akan cikin Fauxa da ita kanta fauxa da kuma ƴaƴanshi,duk da yasan rayuwar shi baxata taba dawowa daidai ba,hawaye masu xafi ne ke xubo mishi sanda ya shiga gallery yana kallon pictures din emaan masu yawan gaske,tun daga wanda take karama har ixuwa yanxu data girma,ya dade yana tara pictures dinta a wayar shi,saboda ya dade yana jin yarinyar acikin xuciyar shi,xaman ta awurinsu ne ya tabbatar da yana mutuwar kaunar ta,pictures dinta kawai yake kallo yaji sanyi aranshi yanxu,shigowar fauxa ne yasa yayi saurin fita daga wurin yana shiga WhatsApp kai tsaye,agefen shi ta xauna tana kallon wayar tashi dayake pressing hankali kwance,kanta ta dora saman shoulders dinshi sannan tace"nagama hada kayan mu"kissing forehead dinta yayi yace"ok baby"ya fada yana kife wayar tashi looking at fauxa closely,murya can kasa yace"what's wrong with you?",kallon kwayar idanunshi takeyi without saying a single word,haka ne yasa ya xagaye waist dinta yana dora fuskarshi akan tata,goshinsu,hancinsu da bakinsu ya hade dana juna,pecking lips dinta yayi still suna kallon juna saide har lokacin babu wanda yace komai acikin su,hannun ta Sadeeq ya rike gam tareda dorawa asaman kirjinshi saitin xuciyar shi,wacce a badini yake bugawa da sunan emaan,axahiri kuma yace"listen carefully my love,xakiji tana kiran sunanki"ya fada yana danna hannunsu akirjin nashi,slowly Kuma romantically yayi owning lips dinta,with passion and everything they got suke kissing juna kamar yau ce rana ta karshe da xasu kasance da juna,kowanne acikinsu najin wani abu na xarya acikin xuciyar su,beneath his breath yake furta"I love you fauxa,I love you so much....."hawaye ne suka gangaro mata tana feeling every touch of his without saying a single word,yace"fauxana!matata!...."ya fada yana sake rungumeta kamar xa'a kwace mishi ita,sake shigewa jikinshi tayi har lokacin bata ce komai ba duk da akwai tarin maganganun dake cikin xuciyarta,murya can kasa yace"muje kada muyi missing flight,tun daxu su Abba ke jira "xuciyarta bata so ba ta gyada mishi kai saboda ji tayi kamar su dawwama ahaka,rai bai so ba suka wuce Orlando airport,makale mishi tayi agaban surukai wanda hakan ke musu dadi fiyeda misali,tabbacin Sadeeq yana samun kulawa awurin matar shi,few hours later suka sauka a john f Kennedy international airport dake New York,hotel suka sauka saboda sai nan da 2 days xasu wuce nigeria saboda akwai abubuwan da xasuyi a newyork din,itadai fauxa she made sure tayi rekindling wannan chemistry din na amarci mai tsayawa arai da zuciya.....

Sai past 10 emaan ta bude idanunta ahankali tana yin mika feeling so weak,fatar idanunta sunyi mata nauyi saboda kukan data yi jiya,kuma har lokacin kanta bai daina mata xafi ba,siririn tsaki ta saki lokacin data tuna dalilin ciwon kan nata,wanka ta tashi tayi daga bisani ta shirya cikin off-white tummy skirt da Prada shirt,vintage scarf ta daura sannan tafita daga dakin nata asanyaye saboda ta gaji da fita siyan abinci harga Allah,kawai bata da yadda xatayi ne,kamar kullum yau ma yana xaune a parlour,plate din abinci ya ajiye asaman table yana ci yana waya cikeda nishadi,kallo daya ta mishi ta kawar da kanta gefe yayinda shikuma ya bita da kallo har ta fita daga parlorn,nearest restaurant taje tasiya abinci sannan ta karbi numbarsu domin su rika kawo mata abincin har gida ta huta da fita kullum,ko 30 minutes batayi ba ta dawo still yana xaune a parlo kasancewar yau Saturday babu aiki,da sallama ta shigo ya amsa mata ciki-ciki kamar wanda akayi ma dole,asaman dining ta ajiye abincin tana duba wanda xataci yanxu da kuma wanda xataci anjima,without twice thought tayi making decision ta xuba sauran abincin a fridge, plate ta dauko ta xuba abincin aciki tana mamakin wanda ke wankewa,saboda ita tunda taxo gidan ko spoon bata tab'a daurayewa ba,asanyaye take cin abincin tana danna wayarta,chatting takeyi da sarah wacce tace xata kawo mata ziyara gobe,dan bude ido emaan tayi kamar xatace mata a'a sai kuma tace mata babu damuwa,daga bisani kuma ta tura mata da address din su tana satar kallon alameen,bata wani ci abincin da yawa ba ta mike xata hau sama,yadda taga ya taso yayo kanta gadan-gadan ne yasa gabanta faduwa,ta dan xaro ido tana ja da baya tana tunanin maketa xaiyi,yace"wa kika mayar mai aikinki?ni?"ya fada yana pointing kanshi,wani irin kallo ta mishi tana bama kanta amsar tambayar da xuciyrta ke mata daxu,ashe shine ke wanke plates din da take batawa,rolling eyes dinta tayi ta daga mishi hannu alamar no offence sannan ta shiga kitchen ta wanke plate din,har kuma tafito yana tsaye a dining yana kallon kitchen din,samun kanta tayi da kasa motsawa daga wajen,hakan yasa ta tsaya tana kallon shi kamar yadda yake kallonta,sun dade ahaka sannan ya girgixa kai ya koma parlour yana mike kafa asaman centre table,ita kuma ta hau sama ta xauna a parlo ta dauki remote tana duba abinda xata iya kallo,saboda ranta da zuciyarta a cunkushe suke kuma bata san kara ma kanta damuwa wurin tunani,wani Indian movie tasamu sukeyi mai kyau alokacin,ta sauka kasa ta dauko bowl yana kallonta ta hau sama dashi,dambun naman da Umma ta bata ta xuba aciki dama already ta dauko chilled mango juice da bottle water,tana cin dambun tana korawa da ruwa da lemo mai sanyi ga film din yana mata dadi kasancewar maddd love dinda akeyi aciki....ta dade tana kallon film din sannan tafara jin takun tafiyar shi yana hawowa saman,tsayawa yayi yana kallonta tana munching meat floss din hankali kwance,ya kalli bowl din ya kalleta sannan ya karasa cikin parlorn,dakin shi ya shige baice mata komai ba,yana shiga ya shirya cikin ash color versace outfits,ya feshe jikinshi da turarenshi mai sanyin kamshi sannan yafito yana kada car keys dinshi wanda yayi drawing attention din emaan ta dan juyo ahankali idanunsu ya sarke acikin na juna,kamar wanda take controlling ya tsaya cak tunda tafara kallon shi ya rasa kuxarinsa,bai dawo daidai ba saida ta kawar da kanta ta mayar ixuwa Tv shikuma ya sauka yana mamakin wannan lamarin......

Umma ce tafito daga bangarenta sanye da dogon hijab da car keys ahannu alamar fita xatayi,mami dake xaune a main parlor abin duniya yayi mata yawa ta dago tana kallon umma cikeda takaici,jin tsanar umma takeyi tana yawo acikin jikinta,saboda ta tabbatar umma ce ta hada shegen auren nan wanda sauran kiris ta murkushe igiyar shi,cikeda fara'a umma ta karasa tana cewa"barka da rana mami"banxa mami tayi mata tana kallon direction dinda Tv yake,hakan yasa umma juyawa tafita compound abinta domin abubuwan mami sun fara yawa,ita kuma hakurinta ya fara xuwa karshe,gudun kada su samu matsala shiyasa umma tayi tafiyar ta bayan taga alamun Hajia kwaise ba amsa gaisuwar ta xatayi ba,ita badon komai take gaisheta ba balle tayi tunanin saboda yanxu su in-laws ne shiyasa take son shisshige mata,gidan anty habiba umma ta tafi domin tasamu saukin abinda ke damun xuciyarta,bata san meyasa kwana biyu take having wasu irin feelings ba akan emaan,gabadaya hankalinta atashe yake duk da emaan nace mata she's fine amma xuciyarta ta kasa samun nustuwa,tana wannan tunanin ta karasa gidan anty habiba wanda bashida nisa dasu Sosai ....

Continue Reading

You'll Also Like

3.5M 148K 61
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...
3.3M 187K 77
Nobody ever loved him; she was the first who loved him. He did not have a family and then one day she entered into his life and became a world for h...
1.1M 28.4K 45
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
11.4K 1.3K 20
The romance between two high school sweethearts. Two people who have hurt each other so much and yet want no one else but one another. Munayah is a s...