PAGE 19

129 4 0
                                    

Page 19

  "You look worried eman,don't you trust me?is not as if wurin banxa xamuje,it's just a restaurant pls put your mind at rest"kausar tafada tana kallon eman wacce fuskarta ta nuna damuwa mai tsanani,ahankali tace "Kausar I'm scared".da mamaki kausar tace "bafa hotel ko club xamuje ba,resto ne fa cikin jama'a,ai ko baki trusting kowa ba yakamata ki yarda dani,kinsan baxanyi abinda xai jawo mana matsala ba, just chill".eman tayi karfin halin cewa"I know,kawai narasa meyasa na damu ne,as if something bad is going to happen "kausar Tayi saurin cewa"khair in shaa Allah,miye dan munje restaurant?laifi daya mukayi da muka wuce daga school ba daga gida ba,shima seizing opportunity nayi ganin anyi cancelling practical class"eman tace"what if we couldn't make it on time"ajiyar xuciya kausar ta sauke sannan tace "you're worrying for nothing eman,trust me ba abinda xai faru sai alheri in shaa Allah".eman tayi shiru kamar baxatayi magana ba sai kuma tace"are you sure?wallahi I'm feeling restless "ganin tsananin damuwar da eman tashiga yasa kausar cewa"now tell me the truth,what's wrong with you?"shiru eman tayi tana kallon kausar without blinking her eyes,kausar ta sake cewa"meyake faruwa dake eman?seems akwai wani abu shiyasa kika damu da xuwan mu gusto"still eman batace komai ba sai kallon kausar takeyi,tasan kausar baxatayi abinda ba shikenan ba,Yarinyar nada hankali da nutsuwa,amma baxata fahimceta ba awannan lokacin da eman ke takatsantsan da duk inda xata shiga saboda sharrin dasuka kulla mata wanda Allah ne kadai xai iya warware shi,and she can't tell kausar about it,sai tayi karfin halin cewa"Bakomai,kinsan awurin ya fauxa nake bana son wani abu yatafi ba daidai ba"kausar tace"komai xai tafi daidai in shaa Allah,ki kira su ki fada musu kawai,hakan xaisa kisamu rest of mind".eman tace "no need"sai ta maida kanta titi tana kallon moving vehicles,har lokacin takasa samun sukuni,tafiyar 17 minutes ce takaisu gusto resto,eman ta sauke ajiyar xuciyah kamar wacce tayi gudun hundreds of kilometres.ganin cikar da wurin yayi yasa ta dan ji sanyi acikin ranta,suka shiga ciki tana tafiya kamar me tausayin kasa,yana can xaune awani table yana ma kausar murmushi,ta xauna tana cewa"eman sit"ganin eman ta tsaya kamar wata soja,saida ta xauna sannan takalli Khaleed tace"good afternoon "daga nan bata kara cewa komai ba,yace"afternoon eman how's school "murmushi kawai tayi sai yacigaba da magana da kausar,kausar ce tayi musu order eman dai Na xaune nata kalle-kalle sai kace Mara gaskiya,kausar ta mika mata wayarta bayan tayi unlocking tace"use it,tunda baxaki sa baki ayi hirar dake ba"rike wayar eman tayi tafara yin game dan kawai yayi distracting dinta tadaina damuwa kuma gabanta ya daina faduwa.
    Cikeda damuwa fauxa tashiga office dinta,ta ajiye handbag ta xauna tana kallon office din,saide takasa yin komai tunda ta xauna,tayi spending like 15minutes can ta mike ta fita,office din Firdausi ta shiga ta xauna tana kallon firdausi wacce ke waya tana fadin"kawata bari kiji,wallahi kinyi sake,kin bar gini tun ran xane,alokacin baya sau nawa ina fada miki hakan?sau nawa ina baki shawara amma kikayi kunnan uwar shegu dani,yanxu da abubuwa suka lalace yakikeso na miki?aure ne dai baxai fasa ba tunda ya d'aura niyyar yinsa,itakuma shegiyar Yarinyar sede Allah ya miki maganinta "shiru tayi can tace"yanxu ki kwantar da hankalin ki,kin San shi yak'i dan xanba cikin aminci ne,dole sai kinyi hakuri kin jure kafin ki cimma nasara tunda kinbar lamarin ya lalace sannan kike neman mafita,yanxu kibari idan nakoma gida xamuyi magana"tana gama fadin haka ta kashe wayar tana kallon fauxa wacce ke jujjuya maganganun da firdausi keyi,kamar tasan me fauxa take tunani tace "wannan dakikaji muna waya childhood friend dina ce,akwai wata yar neighbor dinsu dake shiga gidanta tana tayata aiki time to time,da farko na nuna mata illar hakan amma ta baxantar da magana ta,wai ay Yarinyar karama ce kuma suna mutunci da uwar Yarinyar Sosai,long story short ashe a falonta suke soyayyah da mijinta,yanxu wai aure xasu yi".sakin baki fauxa tayi tace"hasbunallahu wani'imal wakeel "firdausi tace"kinga da tun farko ta dauki shawara ta da ba ayi hakan ba,ai yanxu komai mutum xaiyi sai yayi takatsantsan saboda xamani ya lalace mutane ba Allah aransu"wannan dalilin ne yasa fauxa tunanin kenan firdausi is directing her to the right path,tunda ga abinda yafaru da wannan datak'i daukar shawarar ta tun akaron farko,irin wannan issues din are very sensitive shiyasa hankalin fauxa ya tashi,Firdausi tace "kinga irin ta ko?saifa kin mik'e tsaye kinyi kamar kinayi".fauxa that's confused tace"I don't know what to do "firdausi tace"abu me sauki,kinga yanxu in one week time xa'ayi hutu,sai ku shiga satin bikin salima,Ana gama biki ki k'irk'iro tafiya ko dubai ce kuje kuyi two weeks keda yara da babansu,kinga ay dan dole xata koma gida,saboda yanxu bai kamata ki ce takoma ba da fatar baki,sannan ki cigaba da mata mutunci amma ki tabbatar tabar gidan ki within that period of time,shikenan fa"ajiyar xuciya fauxa ta sauke sannan tace "thank you firdausi "firdausi tace"what are friends for?"sai alokacin hankalin fauxa ya kwanta kuma tayi alkawarin bin shawarar firdausi.
Yaya Sadeeq was lost in thoughts,tunani yakeyi gameda rayuwar shi dakuma halin daya tsinci kanshi yanxu,wanda ikon Allah ne kawai xai fitar dashi daga cikin wannan cakwakiyar,inde yana son kansa da arxiki saide ya birne son eman acikin xuciyar shi,in kuma ba haka ba sai xai shiga tashin hankalin da ba lallai ya fito lafiya ba, dama ace eman xata yarda dashi sai abubuwan sunfi xuwar mishi da sauki,amma ya tabbatar baxata tab'a amincewa da soyayyar shi ba,wata xuciyar tace da gwaji jirgin sama ya tashi,saika gwada tukunna xaka San gaskiyar abinda ke ranta,watakila itama sonka take batada yadda xatayi ne kamar yadda karasa samun mafita amatsayin ka Na namiji,kallon picture dinta dake office dinsa yakeyi ko kiftawa bayayi,yana kaunar baiwar Allahn nan fiyeda misali,kuma yanajin baxai iya cigaba da b'oye mata ba,yana son yayi mata expressing feelings dinshi,yana da burin fada mata yadda ta mamaye mishi xuciya,ta shiga kowani lungu da sak'o hawa da gangara da duk wata kofar gashi ta jikinsa,wani shauki ya tsinci kanshi aciki yana tunanin yarinyar Data hada komai da komai dayake masifar so,ya shafa gefen fuskarshi staring at her cute lips up to her eyes wanda ke karya masa kuxari aduk lokacin data kalle shi,ji yake kamar ana cire mishi laka ajiki,ya dawo down to her banging body,wanda kallo daya yayi ya d'auke idanun shi akai,yana tunanin hijab xaice takoma sawa tunda ko abayar datake sawa yanxu tana d'an nuna figure 8 ce,even though ba thick 8 bace medium ce,koda ace eman bak'a ce mummuna dole jikinta ya burgeka,picture din ya dauk'a yana circling zippy lips dinta,xaiso ace dagaske yake mata hakan,yaya xaiji kenan?sannan ya xatayi reacting?Shide yasan yana yima eman so daya tak mai tsafta wanda babu algus acikin shi,sannan yayi making up mind dinshi xaiyi iya bakin kokarin shi ganin ya mallake ta,hakan yasa ya Mike jiki ba kwari ya tafi gidan su domin yin shawara da hajiyar shi.lucky enough bai tarar da kowa agidan ba sai ita kadai,Bilal na office while khairyy autar su ta tafi school.
Kallo daya hajiya tayi masa taga tsantsar damuwar dayake ciki,nan da nan hankalinta ya tashi,tana bala'in son danta da son ganin farin cikin sa ,kamar baxaiyi magana ba yace "magana naxo muyi me muhimmanci "sai ta  tsura mishi idanu sannan tace"Ina jinka"saida ya furxar da wata warm iska daga bakin shi sannan yace"maganar is very important da baxan iya disclosing da kowa ba saike"kallon shi kawai take dan anata tunanin matsala suka samu da fauxa,yace"hajiya I've fallen in love for the second time,saide wannan ba itace damuwata ba,damuwata itace da wacce nake bala'in so,babu wanda xai fahimce ni saike".tunda yafara magana take kallon shi tana mamaki,tabbas son mace ajinin kowanni namiji yake,saide mata suyi hakuri kawai,ita kanta tayi mamaki saboda yadda yake tsananin son fauxa yake nuna daga ita babu kari ya rufe kofa,yacigaba"soyayyah bata min adalci ba hajiya,bansan lokacin dana fara son eman ba,tsintar kaina nayi dumu-dumu acikin sonta,kaunar ta nake fiyeda tunanin ki"cikeda mamaki hajiya tace"eman kuma?wacce eman din?"yace"ta gidan su fauxa"ba shiri hajiya ta mike tana xaro ido,ta kalli gefe da gefen dakinta sannan ta bud'e kofa taga bakowa,ta dawo bayan ta rufe tace"anya kana cikin hankalinka kuwa,kodai kafara shaye shaye ne?"shiru yayi yana kallonta tacigaba da fadin"haba Sadeeq,wace magana ka fada min ynxu me kamada alamara ko kuma a shirin film ?kana cikin hayyacinka kuwa?"yace"nasan dole kiyi mamaki amma iya gaskiyar kenan,ina son eman kuma inason moving things to the next level "gaban hajiya yayi tsananin faduwa tace"kanka daya kuwa Sadeeq?kasan me kake fada?innalillahi wainna ilaihi raji'un "tarasa me xata ce at the moment saboda shock din data shiga bana wasa bane,shine yace"nifa ina cikin hankalina,yanxu dan Allah idan ban fada miki damuwata ba wurin wa xanje?mafita naxo nema saboda nasan xaki fahimce ni"tayi karfin halin cewa"mafita daya ce Sadeeq,amma baxata maka dadi ba,mafitar itace kayi hakuri kawai,da ace ba eman bace xan tsaya maka sai inda karfina ya kare,amma akan eman kamar yaudara ce da cin amana".cikeda damuwa yace"Allah fa ya halasta,bawai haramun bane"tace"da Allah ya halasta ay bai wajabta ba,kuma ana barin Halas dan kunyah"yace"koda hakan Na nufin durkushewar farin cikina?"tace"ka rayu alokacin da baka santa ba,kuma xaka cigaba da rayuwa koda babu ita,ake mutuwa ma ahakura?"yace"rashin ta tamkar kisa ne agareni batareda d'igon jini ba,wallahi I mean what I'm saying "yana gama fadin haka ya Mike ya ajiye mata kudi masu yawa sannan yafita tabishi da kallo baki asake,bata tab'a ganin shi cikin tashin hankali irin wannan ba,sannan itama ta dade bata tsinci kanta acikin damuwa mai tsanani irin wannan ba.
Driving yake amma damuwa ta mishi dirar mikiya,sai kawai yakoma gida domin yasamu hutu,Salima yagani xaune afalo itada wata mata,yayi faking smile suka gaisa agurguje ya haura sama,kallo daya ta mishi ta tabbatar baya cikin nutsuwar shi,saita sauke ajiyar xuciya sannan tace ma matar "muje "bedroom din kasa suka shiga aka fara ma Salima gyaran jiki.shikuma ya fada saman gado xuciyar shi Na beating very fast kamar xata faso daga kirjin shi,tunanin mafita kawai yakeyi amma duk hanyar daya hanga sai yaga babu sauki acikinta,uku da rabi daidai ya sauko kasa yana perceiving kamshin turare har ya tsaya yana tunanin yima Salima magana sai kawai ya fice abinshi,tunanin abinci yakeyi saboda Fauxa da eman din duk su huta,shifa yana ganin namijin kokarinsu na shiga kitchen da yamma ko hutawa basayi,sai yayi tunanin xuwa one of their favourites restaurant domin siya musu lunch,Calidõ yafara zuwa har yayi parking sai kuma ya canxa ra'ayi ya tafi gusto.
Da murmushi umma ta karasa falon hjy kwaise inda ta tarar da Hjy Fanta(karku manta,hjy Fanta kanwar hjy kwaise ce uwa daya uba daya)suna tattauna wa,koba'a tambaya akan xancen events din bikin Salima suke magana,inteesar da Yusrah Na gefe suna hirar yaushe gamo,dayake Yusrah a US take school dalilin bikin Salima taxo hutu,xama umma tayi suka gaisa sannan tace"nayi mishi maganar gyaran part din Al'ameen,yace gobe in shaa Allah xa'a fara saboda ayi aiki mai kyau da tsari"cikeda fara'a hjy kwaise tace"Toh madalla,dama shiyasa nafada da wuri nima"hjy Fanta tace"xai dawo din kenan?alameen rigima,yaje can yayi xamanshi shi kadai"murmushi hjy kwaise tayi tace"aiko d'an danki na tafe,saiki fara shiri"tace"shiri yaxama dole,last week munyi video call sai yake nuna min kamar baxai samu xuwa ba"hjy kwaise tace"uban ne yayi masa dole,nima na takura mishi ya dawon "ganin sun cigaba da firar su yasa umma mikewa tafice duk da hjy fanta tayi karar cewa"ki tsaya mana,tunda ko kin koma part dinki ke kadai  xaki xauna"umma tace"musaddiq na jirana xamuyi homework "daga haka ta tafi,hjy Fanta tace"har yanxu 'yar na gidan fauxa kenan?"girgixa kai hjy kwaise tayi suka cigaba da maganar dasukeyi ta farko,da mamaki Yusrah tace"so finally yaya is coming back?"inteesar daketa dariya tace"ehh,xaixo hutu,I hope xai dade this time around "da "Amin"Yusrah ta amsa tana blushing,Yusrah first class babe ce,ta hadu iya haduwa ga iya gayu,ta waye Sosai ga kyau irin nasu Na 'ya'yan shuwa.
Bawani cin abincin eman tayi ba kasancewar damuwar Data tsinci kanta aciki,kausar ta kalleta sannan ta kalli Khaleed me cewa"seems she isn't alright"kausar tace"yh,she's going through a lot at the moment ".tana fadin haka tace "I need to use the washroom "gyada mata kai yayi ta nufi toilet,eman ta bita da kallo harta kurema ganin ta,asanyaye tace"where is she going to?"
Khaleed yace"to the washroom"jinjina kai eman tayi batace komai ba,shikuma ya cigaba da pressing phone dinshi hankali kwance,wani video dinsu da kausar yake kallo 2years ago,amma duk sun canxa sun kara girma,abinda ya bashi mamaki da dariya kenan,sai ya dago wayar yace"look"asanyaye ta dago kai tana kallon screen din wayar shi,tayi karamin murmushi,adaidai lokacin Yaya Sadeeq ya shigo,yayi ido hudu da eman dake murmushi,ga Khaleed shima yana dariya da waya rike ahannunshi,ko me yake nuna mata oho!,ji yayi wani jiri ya debe shi kamar jirin xaiyi knocking dinshi down,yayi jarumtar riqe kujera yana ganin tamkar gixo idanunshi keyi,eman ce xaune da saurayi?toh makarantar fa?dama nan take xuwa ba attending lectures takeyi ba?dama?dama?dama??yayi su babu adadi,can yayi karfin halin nufar table dinsu yana jin xuciyar shi na suya kamar ana cinna mishi wuta,idanunshi sunyi jajir,jijjyoyin kanshi sun mik'e,cikin rashin xato taji yace"eman!"da karfi ya kira sunanta,ta juyo araxane tana kallon shi cikin tsantsar tashin hankali,ji tayi kanta ya sara wani ciwon kai mai tsananin yana saukar mata....!.

(I don't think xanyi evening post yau,saiku karanta rabi yanxu rabi anjima😂duk yadda kukayi daidai ne🙃).

https://chat.whatsapp.com/IAyL0ePAUS42UGNBn7eHV6
(Eman comments section)

Zaynab Yusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now