PAGE 07

158 5 0
                                    

Eman...🥀

Page 7

  Agefen gado ta zaunar dani tareda rik'o hannuna tana murzawa with so much care,tace"kiyi hakuri eman ki fawwalawa Allah komai,kowa da irin tashi k'addarar kuma mafi kyautuwar d'abi'ar musulmi kuma mumini shine mai yadda  da kaddara aduk yadda tazo mishi ,Ke musulma ce kuma kinyi imani da k'addara,ki ajiye abinda ya faru dake abisa k'addarar ki wacce Allah ya rubuta tun kafin zuwanki duniya,zan baki shawara wacce idan kika bi zaki samu risslama acikin zuciyar ki".tacigaba da cewa"damuwa,kuka da tunani bazasuyi miki maganin matsalar kiba,sai dai su haddasa miki wani ciwon Na daban da k'ananun shekarunki,har ynzu ke yarinya Ce Eman,kyakkyawa son kowa k'in wanda ya rasa,kuma mai jini ajika,bari nafada miki miji ma saikin zaba,dan haka ki fitar da damuwar komai daga ranki kiyi facing future dinki which is the most important,tunanin abubuwan dasuka faru dake abaya bazai haifar miki da d'a mai ido ba,ki yawaita karatun AlQuran da istigfar in shaa Allah zaki samu sassauci acikin rayuwar ki,sannan ki saki jikinki saboda yar uwa ta jini na d'aukeki,kiyi duk abinda kikeso acikin gidan nan,duk abinda kike bukata in shaa Allah zan miki,ga Baban Anum ma in shaa Allah zamu tsaya miki".
Girgiza kai Ya Sadeeq yayi sannan yace"fatan mu shine kidaina wannan damuwar ki dawo Eman dinki ta asali".
Damuwar su akan lamarina yasa na daina kukan inata sauke ajiyar zuciyah,Ya Sadeeq yace"yakamata abata wani abun taci,ki dafa mata ko noodles ce".da toh Ya Fauza ta mike suka fita atare gwanin ban sha'awa,hakika sun dace da juna,saina samu kaina da kallon fitarsu har suka kurewa ganina,jiki ba kwari Na mike na ciro pajamas dina pink color,saida nayi wanka nasa kayan ina cikin sanya turban Ya Sadeeq ya shigo dakin hannunshi d'auke da madaidaicin tray,saurin sunkuyar da kaina nayi nace"thank you ".Ina mamakin tsananin kirkin shi,saida ya rungume hannunshi ya Daidaita idanunshi akaina sannan yace"you're most welcome eman,maza tashi kici".duk yadda naso cin abincin kasawa nayi,cakalar shi nayi Na sha ruwa da drink masu sanyi,tray din na dauka nakai kitchen ina kara kallon gidan Ya Fauza wanda kyan shi ya wuce misali,saida Na wanke plate din sannan nafito,afalo naga ya Sadeeq yana pressing phone,gabadaya hankalin shi ya tattara akan wayar da ko motsi na baiji ba saida nazo daf da wucewa daki,ahankali ya dago da kanshi tareda zubamin madaidaitan eye balls dinshi yace"har kin gama?".gyada kai nayi kamar bazance komai ba nace"Ina Ya Fauza?".
Karamin murmushi yayi wanda yayi ma fuskar shi kyau yace"ta kwanta".
"Ok"kawai nace mishi sannan nashige daki,koda ban juya na kalleshi ba jikina ya bani cewar  da rakiyar idanu ya bini har na shige daki.
Ya Fauza ce ta tasheni sallar asubah,na dade banyi bacci me dadi ba irin na ranar,tun lokacin da kundin kaddarata ya bud'o mini wani shafi mai tsanani,nasihar Ya Fauza ta shigeni ba kadan ba,na tabbatar dole na ajiye damuwar abinda ya faru dani agefe kodan nasamu nutsuwar zuciyah ta,shigowar Anum ce tasa Na d'ago kaina ina sakin karamin murmushi,ta tsugunna har kasa tace mini "Ina kwana Ya eman,yaushe kikazo ".
Nace"jiya da daddare lokacin kunyi bacci".gefen da akwatina yake ta Kalla sannan tace"Ya eman kin dawo gidan mu?".asanyaye na gyada mata kai nace"zan muku kwana biyu".cikeda farin ciki ta mike tana murna har dasu rawa,ta fita domin fadama Asad,tare naga sun dawo bakinsu a washe sai murna sukeyi,Kasancewar acikin Weekdays muke yasa basu koma baccin safe ba,shirin school sukayi Ya Fauza Na shirin nata office din da Ya Sadeeq,Sosai naji dadin yadda zasu rik'a barina ni daya agidan,gabadaya bana son shiga sabgar mutane yanzu sai ya zama dole,even though nima ina missing school Sosai,saide banda courage din tambayar umma makomar karatuna.
  Ina cikin wannan tunanin Ya Fauza tashigo sanye da wata sky blue din atamfa anyi mata dinkin kaftan,da sauri sauri tace min"zamu tafi,akwai komai ki dafa duk abinda kikeso",tana gama fadin haka tafita,samun kaina nayi da bin bayanta na tsaya a window ina kallon su tashiga motarta,yaran kuma da Ya Sadeeq suka shiga motar shi suka fita.
Zuwana gidan Ya Fauza bema umma dadi ba ko kadan,gani take can ma wata maganar zan janyo mata,zamana awurinta yafiye mata kwanciyar hankali domin koba komai ita mahaifiya tace sannan duk maganar dazan jawo a iya kanta zai tsaya,amma batada yadda zatayi da umarnin Abba,dole ta ja bakinta tayi shiru kamar yadda Hjy kwaise tayi badan tanaso ba,itafa zuwan Eman gidan Fauza bai zauna mata ba ko kadan,Sosai tashiga damuwa wacce tafi ta baya,hankalinta yakasa kwanciya,runtse idanu tayi tana jin zuciyarta na shirin tarwatsewa akan tunanin Eman,gashi anty habiba ta tafi balle su tattauna maganar da ita duk da anty habiba taji dadin hukuncin da Abba ya yanke,shigowar Abba ce yasa ta sauke ajiyar zuciyah,bata San saka shi da kanta acikin matsala,shiyasa ta tattaro duk wani courage da Allah ya bata tace"kana ganin Zaman Eman agidan Fauza daidai ne?".
"Ki furta alheri ko kuma kiyi shiru,haba fatima wacce irin magana ce wannan?banda gajeran tunani irin naki me zai faru?dole ce tasa nace taje can din, kin takure ta anan kina gana mata azaba,gara dai ku bama juna space duk ranar dakika sauko daga fushin dakika dauka da ita saita dawo, bazan iya zuba ido ba kiyi ruining life dinta da kalamanki marasa fa'ida wanda kike furtawa acikin fushi"cewar Abba yana tsareta da idanu,tace"hankalina yakasa kwanciya tun bayan tafiyar su".karamin tsaki Abba yasaki tareda ficewa daga dakin ya tafi part dinshi,ajiyar zuciyah umma ta sauke tana binshi da rakiyar idanu.
Ya kasa tsayawa ya fahimce ta bare yayi nazari,ya kamata ya saurareta amatsayin ta Na wacce ta haifi Eman tafi kowa sanin halinta,sannan tana gudun matsala ne Dan ta tabbatar baza'a wanye lafiya ba, ayanzu bata hango matsala ba amma tana iya hango faruwar wani alamarin nan gaba,duk da abinda Abban yayi shine daidai,kawai tana gudun matsala ne.
Afalon shi ya tarar da hjy kwaise ta zabga uban tagumi,shi lamarin su ma haushi yake bashi,ya tabbatar akan zuwan Eman gidan Fauza take tunani,wuceta yaso yi domin baya son jin komai akan hukuncin daya yanke da farar aniya dakuma farar zuciya,bayason su tofa magana mara dadi kuma hakan takasance gaskiya,bai San meyasa suke da matsala ba,"Sannu da zuwa abba"tace tana mikewa tabi bayan shi cikin bedroom,da "Yawwa" kawai ya amsa yana tsare gida,bayason tamishi maganar amma saida ta samu hanyar cewa"Abba akan zuwan Eman..."saurin katse mata hanzari yayi yace"meyasa bakwa nufin wannan hukuncin nawa da alheri sai sharri? yanzu fatima tagama questioning hukuncin dana yanke akan Eman,meyasa kuke haka ne?".
Shiru hjy kwaise tayi tanajin wani iri,idan har umma bataso tayaya zaayi ita taso?yarta Na zaman lafiya da mijinta zaa kai musu matsala.karamin tsaki ta saki sannan tafita daga dakin,abakin kofa suka ci karo da mama ta kawo mishi fruit salad,ko kallon mama batayi ba tayi wucewarta hakan yasa mama yin karamar dariya.

Dogon tsaki mummy taja sanda takalli gefen da yaranta suke,rafee'ah da sadeeya suka had'a baki wurin cewa"mummy lafiya?".kamar jira take tafara sauke musu kwandan masifa,"ace yara sai shegen bakin jini kamar wanda suka hada jini da jab'a?wannan wacce irin masifa ce tasameni ni Sa'adatu,yara kowacce takawo girma amma babu saurayin arziki?ni zaku tonawa asiri?duk burin dana ci akanku acikin kawaye da dangi?ga kyau ga diri Allah ya baku ina tutiya dashi amma har yanzu babu wacce takawo mini miji?so kuke kishiyoyi da kawaye su mini dariya?"tafada tana zuba tagumi abin duniya duk ya isheta,ta manta duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tashi ko dumi bazatayi ba.Rafee'ah wacce sam bata biyo halin mummy ba tace"mummy shifa Aure da mutuwa da haihuwa duk lokaci garesu,lokacin mu ne bai zoba ".
"Rufe mini baki shashasha kawai sakarya,ay bakin naki ne da aure da haihuwa nada lokaci,Allah dakanshi yace tashi na taimake ka,amma ku kun baje agida kuna mini wa'azin kasuwa,Allah wadaran naka ya lalace".
Cikin yanayin rashin jin dadi Sadeeya tace"kiyi hakuri mummy,komai yanada lokaci...".
Tsawa ta daka mata sannan tace"lokacin ubanki,daga anyi magana ku fara cewa lokaci,ku riqa ma lokaci sharri,gara ku tashi ku mik'e mu had'a karfi da k'arfe mu yaki wannan bakin jinin naku".
Afiya tace"aikuwa dai abinda mummy tafada gaskiya ne,dole sai mun tashi tsaye akan wannan lamarin".
Rafee'ah tace"mu tashi muyi mene?Addua kawai zamu cigaba dayi Allah ya kawo mana".wata uwar harara mummy ta watsawa Rafee'ah tana jin kamar ta tashi ta rufeta da duka,Sadeeya wacce sam bata San hayaniya ta miqe ta shige daki,mummy tabi bayanta da cewa"kya tashi ki tafi mana tunda an fada maki gaskiya,yara sai rashin son gaskiya,nide wllhi da azamanin da na haifeki keda Rafee'ah cewa zanyi an mini canjen'ya'ya gabadaya baku da zuciya".haka tacigaba da banbami kamar masifar tace zata kawo musu mijin.
Tunda suka fita nake karatun Al-Qur'ani saboda banason yin tunanin komai ayanzu,my heart is broken and heavy,kamar yadda Ya Fauza tafada idan Na sanya damuwa acikin zuciyata tabbas zan kamu da ciwo,wata zuciyar tace ba gara ki kamu da ciwon ba ki mutu ki huta,Astagfirullah na furta ina runtse idona masu fitar da ruwan hawaye,sallah ce kawai ke tashina daga inda nake,ko takan abinci banbi sai bayan la'asar ganin yunwa na kokarin yi mini illa yasa na shiga kitchen,sai na rasa me zan girka gabadaya brain dina tadaina functioning Sosai,farar Basmati Rice na dafa da beef sauce,a medium size warmers Na juye abincin sannan na zuba nawa acikin Bowl din Asad,dakyar nake tura abincin saboda gabadaya bakina babu taste,kawai ina cine saboda maganin yunwa,sallamar Ya Sadeeq ce tasa Na d'ago tareda mayarda kaina kasa alokaci daya,murya can kasa nace"welcome back".saida ya karaso har dining din sannan yace"thank you "yana jin dadin cin abincin dana keyi,daga haka bai bai ce komai ba ya haye sama,agaggauce na kammala cin abincin na shige daki araina ina tunanin Ya Sadeeq na rigasu dawowa kenan,tunda su Anum sai 6 haka Ya Fauza,ina cikin wannan tunanin naji ana knocking dakin,na waro manyan idona tareda mikewa asanyaye na mirda handle kofar ta bud'e,Ya Sadeeq nagani ya canza kaya izuwa farar jallabiya mai tsananin kyau da tsada,yace...

EMAANWhere stories live. Discover now