EMAAN

By Zaynabyusuuf

13.3K 391 1

delve into the interesting story of emaan and alameen hate-love story which will get you in suspense from sta... More

PAGE 01
PAGE 02
PAGE 04
PAGE 05
PAGE 06
PAGE 07
PAGE 08
PAGE 09
PAGE 10
PAGE 11
PAGE 12
PAGE 13
PAGE 14
PAGE 15
PAGE 16
PAGE 17
PAGE 18
PAGE 19
PAGE 20
PAGE 21
PAGE 22
PART 23
PAGE 24
PAGE 25
PAGE 26
PAGE 27
PAGE 28
PAGE 29
PAGE 30
PAGE 31
PAGE 32
PAGE 33
PAGE 34
PAGE 35
PAGE 36
PAGE 37
PAGE 38
PAGE 39
PAGE 40
PAGE 41
PAGE 42
PAGE 43
PAGE 44
PAGE 45
PAGE 46
PAGE 47
PAGE 48
PAGE 49
PAGE 50
PAGE 51
PAGE 52
PAGE 53
PAGE 54
PAGE 55
PAGE 56
PAGE 57
PAGE 58
PAGE 59
PAGE 60
PAGE 61
PAGE 62
PAGE 63
PAGE 64
PAGE 65
PAGE 66
PAGE 67
PAGE 68
PAGE 69
PAGE 70
PAGE 71
PAGE 72
PAGE 73
PAGE 74
PAGE 75
PAGE 76
PAGE 77
PAGE 78
PAGE 79
PAGE 80

PAGE 03

215 6 0
By Zaynabyusuuf

Eman...🥀

https://arewabooks.com/book?id=64a568cb8194f8956681682b

Episode 3

    I couldn't say a word,saina bita da rakiyar idanu har ta fice daga dakin,jiki asake nakoma Na zauna shirim ina sak'a da warwara,alokaci daya Na tsinci kaina cikin sabon tashin hankali,saboda babban burina shine zamtowa matar Aliyu,it's my dream tun ranar damuka had'u,I can't afford to lose him,my life will be incomplete without him,na tabbatar rashin Aliyu a kusa dani will make my life miserable,he's my happiness,my peace and comfort zone,sosai zuciyata ke azalzalata akan na karba wayata wurin umma,i really want to know his stand akan abinda ya faru,even though I'm quite sure yana cikin mawuyacin hali but Aliyu will never abandon me even in his wildest dreams,na tabbatar baze tab'a matsawa daga gefena ba matukar yana raye.

But why am i feeling scared and restless?zuciyata ta kasa samun nutsuwa akan maganar aurenmu,ina ji ajikina tamkar wani mugun abu ne zai kara faruwa dani,domin aduk lokacin da mutum ya sab'awa iyayen shi sakamakon baze mishi  kyau ba,take me as an example,ban duba rayuwar k'unci da bakin cikin da umma tayi ba agidan babana,gashi abinda yafaru dani na kokarin dakushe mata farin cikin data samu agidan Abba,da ace na bi maganar umma da haka bata faru ba,k'addarace ta fitar dani alokacin da umma ta zana mini layin shamaki,fitar data jawo mini bala'i da masifa take kokarin tarwatsa mini rayuwata,just one mistake but my life is crumbling.I couldn't control my tears,saboda shi kadai ne idan nayi nake samun relief,i really want to discuss about my problems with umma,amma banda wannan right din kamar yadda ta fad'a,na lalata yar siririyar alaqar data rage tsakaninmu,dama can babu wata shakuwa mai karfi,umma uwa ce agareni amma Sam babu fahimtar juna atsakanin mu,bazan ce komai akan babana ba wanda nazame mishi tamkar kwallon mangoro wanda yake alla alla ya wurgar don ya huta da k'udaje,rubuce take a kundun kaddarata bana sahun masu sa'a arayuwa,duk wani abu dazai zama silar farin cikina I end of losing it,that is my destiny!.

Shigowar Salima da inteesar ne yasa na d'ago jajayen idanuna ina kallon su,wata azababbiyar kunyah ce ta lullubeni,sainayi saurin saukar da kaina k'asa domin bazan iya cigaba da had'a ido dasu ba,Salima ce ta zauna agefen dama inteesar ana hagu,one look din dana musu naga tsantsar tausayina a kwayar idanunsu,salima ce ta riqo hannuna tace

"Eman whatever happens you're my sister,kin zamto yar uwarmu ta jini,abu mafi muhimmanci shine ka aikata kuskure kuma kayi realising cewar yes I made a mistake shima rahama ce,bana bin boka ba'a buga min k'asa amma na tabbatar bazaki aikata abinda akace kinyi ba,idan kuwa ya kasance dagaske ne bazan daina mamaki ba har karshen rayuwata,domin Tabbas jarabta ce daga Allah,Eman kinada tarbiyya daidai misali,burin kowacce uwa,held your head high kidena sunkuyar da kanki k'asa cikin kunyah matukar you're innocent saboda the truth shall always prevail,ita gaskiya d'aya ce".!

Ajiyar zuciyah ta sauke sannan tacigaba da fadin"karkiyi overthinking akan komai,kibar lamarin ki awurin Allah batareda damuwa ba ko fargaba,sannan ki karbi duk wani yanayi da kika tsinci kanki da hannu bibbiyu kisa aranki they're part of your destiny,Eman duk rintsi duk wuya kicigaba da addua da niyyar Allah shine me komai,asannu zai kawo haske cikin lamarin ki".

Hannu biyu nasa na rungume Salima iya k'arfina,ta zame min big sister dinda na rasa long time ago,Allah yajikan sabeeha yasa ta huta,Salima always reminds me of my sister sabeeha wacce rasuwar ta is still fresh in my mind,tasha baqar wahala kafin takoma ga Allah.inteesar ce ta katse mini gajeran tunanina ta hanyar cewa

"Eman you're my sister no matter what happens,no matter what life throws at you,we'll always be there for you ".kukan danake riqewa ne ya kufce mini,na rungumesu iya karfina ina fadin

"Nagode,nagode,nagode".

Salima tace"inteesar zubo mana abinci,tun breakfast ban kara cin komai ba,Na tabbatar Eman ma najin yunwar".da toh ta amsa sannan ta fice,a main kitchen ta tarar da mummy a zaune tana ordering workers suna zuzzuba abinci,ta kalli inteesar tace

"Intee abincin ku na falo".
Inteesar tace"Anty Salima ce tace azuba mana da ita da Eman,a d'aki zamuci". Riqe baki mummy tayi cikeda takaici tace"banda Salima ina ruwanta da shiga sabgar yar iskar Yarinyar can?mara tarbiyya me jawo ma iyayenta abin kunya da abin fad'e...".
Zuwan hjy kwaise ne yasa mummy saurin yin shiru,saide already taji abinda ta fada.

Cikeda izza hjy tace"ki bada aiken Salima kin barmin 'ya atsaye". hjy kwaise mace ce mai matukar son 'ya'yanta,aduniya ta tabbatar batada kamar su shiyasa take iya bakin kokarin ganin ta kyautata musu,tabangaren su yadda suke tsananin sonta rubutu ne me tsaho,kome suka samo awurinta suke dire shi daga mazan har matan.

A babban tray aka shirya musu nasu abinci,inteesar ta tafi kai musu,hakan yasa mummy cewa"wai ni hjy ya ake ciki da auren Eman ne?ko baku tattauna da Alhaji ba".

Cikin nuna isa tace"bamu tattauna ba tukunna ".
Mama da zuwan ta kitchen din kenan tace"ai in shaa Allah sai maganar auren ta watse,taya eman zatayi aure ga 'ya'yan mu zube agida?".
Mummy tace"itace babbar damuwata,kuma Aliyu d'an mukhtar Marshal,in shaa Allah sai maganar auren tabi ta shanun sarki".shiru hjy kwaise tayi domin ta tabbatar alokacin da zuciyar mutum ta kamu da ciwon hassada alokacin mutum ya kulla amintaka da bakin ciki.

Ya Salima da inteesar ne suka tursasa naci abinci,shima banason suji wani Iri kamar ban gode musu ba,sun tsaya mini alokacin da kowa ke guduna,Sosai Ya Salima ta mini nasiha me ratsa jiki,daga karshe tace"karki sa kanki cikin damuwa akan maganar auren ki,kome yafaru dama haka Allah ya kaddara".

—-
Misalin k'arfe tara da minti sha biyu ne na dare,falon Alhaji mukhtar Marshal cike da uncles din Aliyu biyu,Mommy,Anty hind da ya Abubakar,Aliyu na daga can gefe cikin tsananin damuwa,yana kaunar Eman kuma yanajin zai iya zama da ita acikin kowani hali,duk da hes so disappointed sannan yanajin taci amanar shi but kaunarta na zaune daram abirnin zuciyar shi.

Alhaji mukhtar marshal ne ya bud'e taron da addua,yacigaba da cewa"magana ce gameda auren Aliyu,zanyi bayanin stands dina gameda abinda yafaru,But Aliyu kasani cewar komai wuya komai runtsi bazan hanaka abinda kake so ba".
Yacigaba da fadin"Eman yar gidan Alhaji kabeer wanda Alhaji Abdulhameed Abubakar safana ke riqe da ita mutuniyar kirki ce tun daga farkon rayuwarta,munyi bincke tun daga haihuwarta zuwa yanzu bamu samu wani abu daya nuna cewar yar iska bace,sai shekaranjiya da alamarin yafaru,dan Haka bazan tab'a shaidar eman da abin banza ba,saboda yadda rayuwar ta ke kewaye da magauta wanda basason cigaban ta,kallo d'aya nayiwa eman na tabbatar she's the best for my son,Amma ance idan mutum zaiyi aure dabi'a da tarbiyya should be no one,na tabbatar kana waswasin auren Eman,sannan bazaka daina ba,Aure da zargi bazai yiwu ba Aliyu,dan haka agaban kowa na baka damar yin tunani daga yanzu zuwa gobe inda zaka fad'i matsayar ka agaban magabatan Eman,idan kuma ka cimma matsayar ayanzu saika shaida min,shawara d'aya zan baka,kabi zab'in zuciyarka,nikuma nayi alqawarin zan tsaya maka abisa zab'in ka".

Uncle Aminu yace"Abinda mahaifinka ya fada shine gaskiyar maganar,mu iyayenka ne masu San farin cikinka,kayi tunani saboda kaine zaka zauna da Eman,kafi kowa sanin hukuncin dayakamata ka d'auka".

Cikeda tashin hankali mommy tace"abinda baze tab'a yiwuwa ba kenan,tun ranar da abin ya faru maganar aure ta mutu,bazan yadda d'ana ya auri yar iska ba,bazai yiwu  na zuba idanu acuci d'ana ba,saboda haka banga amfanin wannan meeting dinba,Aliyu bazai auri eman ba,shine kawai".

Murya na rawa Aliyu yace"amma mommy Ina son Eman..."
Tayi saurin katse shi tahanyar cewa"rufe mini baki,shashasha kawai sakarai wanda baisan ciwon kanshi ba,Aliyu har yanzu kai yaro ne bazaka fahimci illar auren Eman ba sai nan gaba idan ka kara hankali,saboda haka bazan bari ka aureta ba,wannan alqawari ne na daukarwa kaina,idan kuma ka nace saika ka aureta ina me tabbatar maka saide kayi sabuwar uwa kamar yadda zakayi sabon Aure".

Afusace Alhaji Marshal yace"baki isa ki hana Aliyu auren Eman ba matukar ina raye kuma nine uban shi". ya tabbatar mata.,runtse idanu Aliyu yayi sanda mommy tace"nima I'll never accept this marriage never".wannan shine karo na farko da Aliyu yaji suna sa'insa agaban shi kuma ta dalilin shi,he couldn't bare to see his parents fighting,sai ya miqe jiki ba kwari ya koma bedroom dinshi yana juya maganar da baban shi yayi.

_dan haka agaban kowa na baka damar yin tunani daga yanzu zuwa gobe inda zaka fad'i matsayar ka agaban magabatan Eman,idan kuma ka cimma matsayar ayanzu saika shaida min,shawara d'aya zan baka,kabi zab'in zuciyarka,nikuma nayi alqawarin zan tsaya maka abisa zab'in ka_

Ya dad'e yana jujjuya maganar Baban shi,wacce yake ganin tafi  zuwa daidai da zab'in zuciyar shi,amma kafin ya yanke hukunci dole sai yayi magana da Eman,jiki ba kwari ya dauki wayarshi iphone 14 pro max yayi dialling number dinta,lokacin wayar na gefen umma tanata juyata,aranta tana aiyya Eman bazata kara ganin wayar ba sai ranar da aka daura mata aure,ganin mai kiran ne yasa umma ta runtse idanu,domin yazama dole takaiwa Eman wayar saboda halin dasuke ciki magana mai muhimmanci zasuyi,jiki ba kwari tashiga dakin Eman,lokacin goma da rabi na dare ya wuce,nakasa samun peace,hakan yasa na dauko Alqur'ani ina karantawa,ganin umma yasa nayi shiru,ta miqo mini wayar batareda tace komai ba,kiran farko ya katse sai ana biyun tabani ,da sauri na karba ina kallonta tareda danna answer button,ta juya tareda saurin ficewa daga dakin.

"Hello"naji muryar Aliyuna,masoyina,the absolute love of my life,kuka mai sauti na fashe dashi maimakon na yi magana,the moment I've been waiting for tun lokacin da abinda yafaru,I know my Aliyu will always be there for me.

"Eman,pls stop crying ".yafada muryar shi very low,azahirin gaskiya samun masoyi kamar Aliyu abune mai wahala,ya damu da damuwarta duk da shima yana cikin damuwar.

"Kinsan illar kukanki agareni Eman,dan Allah ki daina,magana nakiraki muyi,maganar fahimta akan future dinmu".yacigaba da cewa"abinda yafaru ya rigada ya faru,inasonki Eman,inasonki Eman,Inasonki Eman,and I'm ready to make a sacrifice for you,amma..."sai kuma yayi shiru,kuka nake fitarwa ahankali,domin koni ina mamakin irin son da Aliyuna ke min.

"Eman I'll go against the world for you,you know that,Eman zan aureki kamar yadda nayi niyya akaron farko,da sharadin baze kara kamaki da irin wannan laifin ba,da sharadin idan haka ta sake faruwa it'll be the end of whatever we have,koda kuwa bayan auren mu ne zan hakura dake!!!!.".

"Thank you Aliyu,nagode ".shine kawai abinda na iya furtawa,nakasa had'a kalaman dazasu wanke ni daga d'aurin zato,banida zab'i fa ce karbar laifin da kaddarata ta damk'a mini.

"I love you ".itace kalmar da Aliyuna ya fada ta karshe batareda yajira amsa taba ya kashe wayar shi,samun kaina nayi da rungume wayar ina furta"I love you more".wasu hawaye na zubo min,kwanciya nayi akan rug tareda lulawa duniyar tunani,ina meyi ma Allah godiya daya bar mini Aliyu acikin rayuwata.

Shigowar umma ce tasa Na miqe zaune,bata ce mini komai ba ta miqo hannu,jiki asanyaye na miqa mata wayar,tanaso ta tambayeni yadda mukayi da Aliyu amma takasa,sai tayi saurin fita daga dakin.

Washegari sai tara na safe Na farka daga bacci,nayi mamaki Sosai dana kalli agogo,hakan baya rasa nasaba da wayar da mukayi da Aliyu na,wacce tabani assurance har yau har gobe Aliyu is mine.wanka nayi agaggauce nasaka plain black abaya ko mai ban shafa ba,dayake karfe goma sha daya na safe su Aliyu zasu zo,yaran gida duk sun tafi makaranta sauran ni kadai.

Saliha daya daga cikin masu aiki ce takawo mini breakfast wanda kallo daya na mishi na watsar,gabadaya banda apetite,burina kawai naga zuwansu Aliyu,ina cikin wannan tunanin umma tashigo.

"Ina kwana umma"na fada ina kallon yadda ta rame within few days.

"Da ban kwana ba zaki ganni?"saitayi Jim sannan tacigaba da cewa
"Sai ki tashi muje su Aliyu sunzo,yaro mai hankali da nustuwa da tarbiyya,Eman kin cuci kanki inde ba'a cimma matsaya ba,kin jawo ma kanki Matsala, da hannunki kika lalata rayuwarki,I won't ever blame them idan sukace sun fasa".
Kuka mara sauti na fara,dukda Aliyu assured me,amma iyayenshi fa?

"Yau da safe naji mummy da mama na maganar,suna yin tofin Allah tsine,burinsu shine afasa auren,sun ci alwashin sai sun zuba ruwa akasa sunsha saboda farin ciki,sun faffada min maganganu masu zafi ta dalilin abinda kika aikata,banida tacewa daga hmmm sai hmmm uwar gulma tayi cikin shege".tana gama fadin haka tafice daga dakin nabi bayanta kamar tsohuwar munafuka hawaye na zubo min.

Kallona Aliyu keyi ko blinking eyes bayayi haka nima kallonshi nakeyi,acan gefe Na zauna sannan na gaishe da kowa cikeda girmamawa,har lokacin idanun Aliyu suna kaina masu fitar da ruwan hawaye.....

https://chat.whatsapp.com/JBW41FiQjju590lKMlEoay

For those that want to join my WhatsApp group.

Written by Zaynab Yusuf✍🏼

Continue Reading

You'll Also Like

9.3K 103 1
Khairiyya was lost and couldn't think of a perfect solution to what happened. At last she decided to keep it a secret forever without telling anyone...
3.3M 189K 77
Nobody ever loved him; she was the first who loved him. He did not have a family and then one day she entered into his life and became a world for h...
250K 20.3K 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin w...
17.8K 2.2K 24
A girl in her early twenties find her self in a battle between getting married off to any one or choosing the right spouse. will she be determined to...