DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa

Page 60- Komai Ya Yi Farko...

290 32 2
By PrincessAmrah

Page 60

Sai da muka tsagaita da dariyarmu sannan na ce mata,
"Kin san Allah, tun da na tashi na yi wayo burina kenan in zama likita. Ni da Ummu. Don ba zan manta ba har akwai lokacin da muka dinga musu da wata kawarmu a kan wai ba za mu iya zama likitoci ba, saboda yaran masu kudi su kawai ke iya zama likita. A lokacin har hawaye sai da na yi, don ba karamin sace min guiwa ta yi ba. Ummu ce mai karfin halin ce mata ba wani mai kudi, mu tare muke da Allah kuma Shi zai zama jagoranmu.
Kuma wai kin san abun haushin ma?"
Ta gyada kai murmushi bai bace daga fuskarta ba. Na dora da
"Ina dawowa gida nake ba Ummata labarin yarinyar, sai cewa ta yi wai ai gaskiya yarinyar ta fada mana. Waye zai tsaya mana mu zama likitoci? Ai kuwa sai na kara barkewa da kuka. Da na ba Ummu labari duk da hakan ba ta karaya ba. Ta ci gaba da karfafar guiwata har na ji cewa za mu iya din; da kudi ko babu. Tun daga nan sai muka fara kiran kanmu da Dakta. Sai da Mama ta yi tsaye sannan muka daina. Ta ce wai muna ce wa junanmu Dakta sai ka ce da gaske."
Na dire maganar da dariya sosai.
"A lokacin har sai da Baba ya ce ta bar mu da sunayenmu mana, tunda mu muka zabi hakan yana mana fatan wata rana mu tabbata likitocin. Ta ce idan mun zama daktocin gasken ma kira kanmu da haka, amma dai ba yanzu ba. Muna ji muna gani muka hakura da Dakta Ummu da Dakta Khairi."
Muka ci gaba da dariya sosai.

Can kuma sai na koma serious, na ce,
"Kin san Allah ni dai kina macenki ban san me za ki yi da Psychology ba. Da a ce ma second degree ne da sauki."
Da murmushinta ta ce,
"Idan kika ce in sauya wani sai in sauya Anti. Ai ke din Yayata ce."
Na gyada kai,
"A'a Hannatu. Ba zan hana ki karantar ra'ayinki ba. Ki je ki yi, ina yi miki fatan alkhairi."

Hakan ba karamin yi mata dadi ya yi ba. Ta ce,
"In shaa Allahu Anti, kamar yadda ke da marigayiya kuka kasa samun cikar burinku na zama likitoci, Ummu ga ta nan, takwararku, ita za ta cike muku wannan burin. Za ta zama likita, babbar likita. Da izinin Allah."

Ummu da ke tsaye tana jin mu ta saki murmushi, ta ce,
"Ai da ma Daddyna ya ce so yake idan na girma in zama Doctor saboda in dinga duba marassa lafiya ina samun lada."
Murmushi kawai na yi ina kallon su.
Hannatu ta kalle ni ta ce,
"Da izinin Allah za ta cika muku wannan mafarkin."

Mun jima muna hira sai daf da maghriba Hannatu ta tafi. Sai na hau tunanin lokacin da take kuka tana sanar da ni nunatan da ake yi a Poly. Wai duk inda ta gitta sai ta ga ana zund'enta, wasu ma a bayyane suke gulmarta wai ita ce wadda aka yi wa fyade. Don dole tana ji tana gani ta hakura da zuwa makarantar, saboda zuciyarta ba za ta iya dauka ba, sai ma tayar mata da tsohon tabo da suke yi.
A lokacin na yi ta ba ta baki amma ta ce ita fa ba za ta iya ci gaba da zuwa makarantar nan ba. Dole na bar ta. Ta rubuta jamb kuma still ba ta samu ba. Shi ne Allah Ya taimake ta ta samu Havard din, kuma babanta ya tsaya mata, saboda tsananin tausayin rayuwarta ta yake yi.

***

Kwanaki sun ci gaba da shudewa har cikina ya isa haihuwa. Tun kafin cikar lokacin haihuwar aka shaida min ba zan iya haihuwa da kaina ba saboda an hango 'yar matsala. Dole sai dai idan EDD dina ya cika, in je a yi min CS.
Yana cika din kuwa muka tattara komai na bukata, tare da Nusaiba da Sadiya muka isa asibitin, a lokacin Haidar ya yi tafiya zuwa jihar Rivers a kan wani aiki.

Babu bata lokaci aka yi min aiki, aka ciro min sunkucecen yarona, mai kama da mahaifinsa.
Kwananmu hudu aka ba ni sallama saboda jikin nawa ya yi kyau sosai. Kuma a ranar Haidar ya dawo don da ma bakidaya hankalinsa na gare ni.

Da ya zo ya ga jaririn, tamkar zai yi kuka saboda farincikin yau ya samu magaji mai kama sak da shi. Har sai da na dinga yi musu dariya shi da Ummu yau an samu wanda ya shiga tsakaninsu. Ya dubi Ummu da ke shirin yin kuka ya ce,
"Rabu da ita my darling, ba ki da mahadi har abada. Kowa ya sani da tsohuwar zuma ake magani. Don haka ke daya ce a nan,"
Ya nuna saitin zuciyarsa. Sai kuwa ta hau dariya har da tsallen dadi, ta fita tana kwala kiran Afreen wai ta zo ta ji Daddy ya ce ya fi son ta a kan baby brother dinsu.

Bayan ta fita ya dawo da hankalinsa gare ni. Sai da ya yi min kyakkyawar sumba, kafin ya kwantar da jaririn a kan katifarsa. Ya ce,
"Ga haihuwar Ummu, ban nemi zabinki ba. Haka Afreen ma duka ni na yi musu suna. A yanzu da muka samu wannan, na yarje miki, ki zabi duk sunan da kike so da shi zan yi masa huduba."

Kwarai na ji dadin zabin da ya ba ni. Na saki sassanyan murmushi ina duban sa. Na ce,
"Na zabar masa Abubakar Saddiq, sunan mahaifina. Ina masa fatan ya kasance da halayen takwaransa na ainahi, Sayyiduna Abubakar."
Ya kalli cikin idona, da murmushi ya ce,
"Madalla da wannan suna mai tarin girma da ma'ana. Allah Ya yi masa albarka, Ya albarkaci rayuwarsa shi da 'yan'uwansa."
Na amsa da amin.

Tun daga nan sai kowa ya shaida sunansa Abubakar amma za mu dinga kisan sa da Sadiq. Da na fada wa Umma sunan da aka samu, har sai da na ji sautin kuka a cikin muryarta. Ta ji dadi da na yi wa mijinta takwara. Amma duk da haka sai ta ce,
"Me ya sa ba ki yi karar sanya Ahmad, sunan mahaifinsa ba?"
Na yi murmushi.
"Ah kun ga Hajiya Umma, ana so ana kaiwa market. Ai shi ya ba ni zabi, ni kuma na ga tunda ga Afreen sunan Mami, wannan karan sai a juya."
Ta ce,
"Shi kenan, kun kyauta sosai. Allah Ya yi muku albarka, Ya raya muku zuri'a."
Ban ce amin ba sai dai na fada a cikin zuciya, saboda kawaici irin na yarinyar Hausawa.

Wannan karan ba a yi taron suna ba, na makale da hujjar CS da aka yi min. Muka ci gaba da kula da Sadiq dinmu, a gefe guda kuma ina zuwa aikina hankali kwance.

Abubakar na da shekara daya da rabi approval dina na zuwa karin karatu ya fito. Ko da na fada wa Haidar ba karamin farinciki ya yi ba. Ya ce sai in yaye Sadiq din tunda da ma ya isa yayen. Bayan kwana biyu, ranar Juma'a na yaye shi.

Ina ta shirye-shiryen tafiya Columbia, can South America, sai ga Haidar ya shigo daki. Ya rungume ni hade da kissing goshina ya ce,
"Albishirinki."
Na dago kaina da annuri na ce,
"Goro, fari kal."
Ya ce,
"Na dauki hutun karshen shekara, tare za mu yi tafiyar nan. Daga can in karasa hutuna na good three months tare da matata. Idan na gama duka sannan zan dawo."

Na kuwa rungume shi ina jin wani irin farinciki yana lullube ni. Da ma tunanin yadda zan tafi in bar mijina har shekara biyu nake yi. Amma idan muka tafi tare, at least zan rage wani haushin.
Ya rungume ni hade da cewa,
"Idan ma na dawo din, zan samu lokaci mu kawo miki ziyara ni da yarana. Sannan ke ma ko nan da shekara ne kya dawo gida ai."

Na daga masa kai.
"Thank you so much my Darling husband. Madalla da samun miji nagari irin Aliyu Haidar. Daya tamkar dubu. Mijin Ummu Baban Ummu."
A bayyane na ci gaba da nuna masa farincikin da kalamansa suka sanya ni.

Daga nan sai muka ci gaba da shirin tafiya tare. A bangare guda kuma zuciyata cike take da zulumin kewar yarana da zan yi, musamman Sadiq da yake karami kuma sabon dan yaye.

Mun yi bankwana da iyaye da dangi, daga nan jirginmu ya lula sai Columbia. Tare muka dinga zuwa makarantar  da Haidar har sai da na gama duk wasu cike-cike, ya rage saura sati biyu mu fara shiga aji. A cikin sati biyun nan ko rana babu wanda ya gani a cikinmu. Kullum muna cikin daki muna kashe junanmu da soyayya. Soyayyar da ko farkon aurenmu ba ta kai ta ba. Duk wani motsi nawa a jikin Haidar ne. Tamkar cingam haka na kasance masa. A tsayin zaman nan mun mori junanmu da kyau. Hatta wayoyinmu a kashe suke, sai bayan kwana biyu ko uku mu kunna mu dan yi waya da gida da kuma yaranmu sannan mu mayar da su a kashe.

Ko da na fara zuwa lecture ma kullum na dawo tare muke. Ga weekend kuma haka za mu karaci yawonmu makale da juna, kuma babu wanda ya damu da hakan ko kadan.
Muna video call da su Ummu a Tab dinsu akai-akai.
A haka har hutun Haidar ya kare. Na sha kuka sosai a lokacin da zai tafi. Saboda wata irin rayuwa ce muka yi a Columbia mai cike da tsaftatacciyar kauna. Sai da ya yi ta yi min kalamai masu dadi sannan na dan hakura. Amma a daren ba mu runtsa ba har gari ya waye. Tare muka je Airport, ban kuma tafi ba har sai da jirginsu ya tashi.

Shekara na zagayowa na koma Nigeria kamar yadda Haidar ya yi min alkawari. A lokacin ne kuma aka yi bikin Nusaiba da wani Malaminsu likita shi ma. Mun sha hidima sosai, ni da kaina na kai Nusaiba dakin mijinta, a lokacin za ta shiga shekara ta biyar a makaranta.
Yarana sun ji dadin gani na, kamar yadda ni ma din na ji dadin ganin su. Haka sauran 'yan'uwa kowa sai farinciki yake yi.
Wata biyu cif na yi, na tafi Columbia.

***
Bayan Shekara Biyu.

Shirye-shiryen graduation dinmu ake ta yi. Na roki Haidar a kan ya zo domin ni ma in waiga in ga nawa a wurin, musamman kuma kokarin da na san na yi zan samu award. Ina zaune kan teburin karatuna na ji door bell, daga inda nake na latsa remote kofar ta bude, kamar daga sama sai ganin Haidar na yi. Na rufe bakina cike da farinciki ina ma rasa abin da zan fada, sai ga Ummu da Afreen biye da ita. Sai kuma ga Sadiya kanwata dauke da Sadiq. Ai da karfi na buga tsallen murna. Na ma rasa wa zan runguma a cikinsu tsabar farinciki.

Sadiq na karba daga hannun Sadiya, yaron ya yi kiba sosai kamar ba shi ba. Shekara hudu yake nema a yanzu amma sai ka ce ya haura biyar ma. Ummu da Afreen ma sun zama 'yanmata. Don Ummu wani irin tsayi gare ta, har ma ta kusan kamo ni tsawo.

Na ji dadin ganin su, don rasa ma abin da zan ce na yi fiye da minti biyar sai dariya. A karshe dai na yi musu order din abinci da abun sha. Sai kuma Afreen ta hau ba ni labarin sun sha zaman jirgi har sai da jikinta ya yi ciwo.

Washegari muka rankaya zuwa wurin graduation dinmu. Award daya na yi tsammani amma sai ga har guda uku na samu. Mun yi murna, yarana ma sun taya ni murna. Haka mijina da kanwata ma.

Bayan mun dawo gida Nigeria, Haidar ya shaida min ya biya mana kujerar Makka, ni a matsayin tukuicin kammala karatuna. Sai shi, Mami da kuma Umma. Na ji dadin da har ma na rasa ta yadda zan nuna shi. Haka Umma ma.
Ranar da na je gida na fada mata har da rawar murna ta yi. Ta ce,
"Rabona da rawa tun ta aurena Khairi. Amma yau dole in taka saboda wannan zance."
Ina dariya na ce
"To ai Umma sadaka ya kamata ki yi, ko kuma sajdatul shukri."
Ta dafe baki tana dariya, sannan ta yi sujjadar.

Bayan ta dago ta ce,
"Ai sadaka dole ce da ma Khairi. Wannan abun alkhairi ai dole a gode wa Allah."

Cikin farinciki ni ma nake shaida mata da nawa albishirin.
"Tun kafin in tafi Columbia na sanya ana ginin babban masallaci a unguwarmu Umma, saboda karancin masallatan wurin, kuma babu babba ma. Shi kuma wannan har sallar Juma'a ma za a dinga yi a cikinsa. Kuma na gina shi ne musamman domin Ummu, da kuma mahaifina. A matsayin sadakatul-jariya. Ina fatan ladar ta dinga kai musu har cikin kabarinsu."

Har da kukan dadi Mama ta yi a lokacin da Umma ke shaida mata. Ta kara jinjina wa wannan kokarin nawa, wanda hakan ya faru ne da bisa ga kokarin jajirtaccen mijina Aliyu Haidar Ahmad Turaki.

KARKAREWA

Tun daga kan Sadiq, sai Allah bai sake ba ni wata haihuwar ba, duk da babu planning, Allah ne bai kawo ba. Mun kuma rungumi yaranmu guda uku, cike da kauna da soyayya; ba irin soyayyar iyayen zamani ba, wadda babu alfanu a cikinta saboda rashin tarbiyyar kwarai.

UmmulKhairi Aliyu Ahmad Turaki, ta zama cikakkiyar likita, inda ta koma fannin Gynaecology, saboda karancin likitoci mata, sannan bisa shawarar mahaifiyarta ni, UmmulKhairi Abubakar. Afreen-Radiya, ta koma bangaren mahaifiyarta, inda ta zama kwararriyar lauya mai aiki da hukumar Federal Ministry of Justice, yayin da Abubakar Sadiq yake shekararsa ta karshe a jami'a, inda yake da burin gajin mahaifinsa Aliyu Turaki, ko dai ya zama DSS, ko wani nau'i na jami'in tsaro. Kuma UmmulKhairi da Aliyu suka goyi bayansa dari bisa dari.

Kasarmu ta Nigeria sosai ta samu saukin kidnappers, ko in ce da yawan 'yan ta'adda sun saraya, sun ba da kai bori ya hau, inda suka tafi can inda da ma can muka saba jiyo labaransu, wato a wasu kasashen na waje, ba da tamu ta Nigeria ba.
Fyade da UmmulKhairi Abubakar Sadiq ke da burin dakusar da shi a kasar, tuni burinta ya cika. Duk da ba za a ce rankatakaf an daina ba, sai dai yawaitar lauyoyi ire-iren ni UmmulKhairi, ya janyo da yawan fyaden ya tafi.
Ina fatan wata rana za a wayi gari sai dai mu ji sunansa, ko kuma mu ji labarinsa a wasu kasashen.

***

Kamar yadda ni Amrah, nake buri da fatan kidnapping da raping ya tafi har abada daga wannan kasar tamu. (Duk da ba abu ne mai sauki ba, amma fata na gari lamiri inji mallam Bahaushe).

***
Alhamdulillah!
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki. A yau na kawo karshen wannan labarin nawa mai suna DARE DUBU...Labarin da wasu gabobin na cikinsa sun faru da gaske. Wasu kuma kirkirar su kawai na yi.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki, inda na yi kuskure Ya yafe min. Inda na yi daidai kuma Ya ba ni ladar, da ni da ku bakidaya.

Labarin DARE DUBU...labari ne da na rubuta shi a cikin kwanakin da ba su zarta ashirin ba (20 days). Kuma ban taba dora alkalamina zan rubuta shi na ajiye wai saboda bacewar idea ba; hakan ya faru ne bisa ga jimawar da labarin ya yi a cikin kwanyata (fiye da shekara biyu) ina son yin sa amma Allah bai ba ni iko ba (Shi ya sa ya wadatu da kyakkyawan bincike). Dukkanin abin da labarin ya kunsa, abubuwa ne da suka jima suna ci min tuwo a kwarya. Tun daga kan kidnapping, raping, har zuwa cin hanci da rashawa. Uwa-uba kuma kiyayyar da ake nunawa ga raped victims, har ta kai ta kawo suna rasa mazajen aure. Shi ya sa na yi amfani da wata baiwa da Allah Ya ba ni (Rubutun Zube) na isar da wannan gajeren sako zuwa ga mutane, tare da hope din zai yi amfani ga wasu daga cikin wadanda suka karanta shi.
Sai kuma batun kawance, ko kuma in ce aminci da soyayya ta tsakani da Allah. Ba wai dole sai 'yan'uwa na jini kadai ake so da zuciya daya ba. Akwai mutanen da Allah zai jeho a cikin rayuwarka, za su zarce ma wani jinin naka. Haka kuma za su fi wani jinin damuwa da damuwarka.
Kawance takwarorin juna; UmmulKhairi da UmmulKhairi, ba wai iya ku masu karatu abun ya burge ba, har ni din da na kirkire su, na ba su suna iridaya, sannan na kirkira kaddarorinsu. Duk da cewa dayar matacciya ce a cikin labarin, sai dai haskawa (flashback), amma hakan bai hana kaunarta shiga zukatan masu karatu ba. Hakan kuwa ya faru ne bisa ga kyawawan halayenta (kyawun hali yana janyo soyayya da farin jini ga mutane).
Na sani da yawanku sun burge ku, to ba wai iya burgewar kawai nake so ba, so nake ku ma ku riki aminnanku da daraja irin yadda Ummu ta riki Khairi, ko kuma Khairi ta riki Ummu da zuciyarta daya. Ku so junanku, tamkar UmmulKhairi da UmmulKhairi. Ku cika muradan junanku, ku kyautata bayan junanku a lokacin da dayanku ya kauce (ya bar duniya) kamar yadda Khairi ta riki bayan Ummu har bayan ba ta a duniyar.

Sannan wani sako game da aikin DSS, na sani ba duk iyaye ba ne za su yarje wa diyansu mata su rungumi wannan aikin saboda daukar da ake yi na maza zalla ne. To ku sani, aikin DSS ya sha bamban da sauran jami'an tsaro. Aiki ne mai cike da tsaro da tsari, aikin da kana iya zama da mace fiye da shekara ba ma tare da ka san cewa shi take yi ba.
Idan har iyaye za su dinga barin diyansu ga ire-iren ayyukan nan, ba shakka za a samu dakushewar 'yan ta'adda, ko in ce za su dinga bincike ta karkashin kasa domin kawo dakilewar da yawan munanan dabi'un mutane.

Na gode ga masoyana da suka bibiyi labarin nan har ya kawo karshe. Fatan dukkanin darussan ciki za ku dauke su ku yi amfani da su, tare da yin watsi da shirmen da na tafka a kan rashin sani (ajizancin dan'Adam).

Sai mun hadu a wasu littattafan nawa, masu suna HAKKIN RAI, da kuma MAKARKASHIYA, a cikin shekarar 2024 idan Allah Ya nuna mana da rai da kuma lafiya. Ina kyautata zaton labaran nan biyu za su sha bamban da AMRAH NAKE SO, BAKUWAR FUSKA, MATAR AMIR, GIMBIYA SA'ADIYYA, UMMU HAIDAR, ZAFIN SO, DAFIN SO, RADIYA, TSANTSAR ZALUNCI, DAUKAKA DAGA ALLAH, RAMUWAR GAYYA, DOCTOR RAFIQ, JINNUL-ASHIQ, YAUDARA, YARIMA SAIFULLAH, FADILA DA NABILA, KHAULAT, HAKKIN UWA, WATA SHARI'A, WATA DUNIYA, INA ZAN GA KDEEY?, MAHAKURCI...,SO DA SHAKUWA, SHI NE SILA, da kuma DARE DUBU...
Taku har kullum, diyar Auwal Maman Auwal (Aman) sannan Matar Aliyu Sadauki.

Gaisuwa ta musamman ga ahalin marubuta, masu karatu, da kuma masoyana. 'Yan'uwana RAZ, 'yan'uwana ALZAZ, kungiyata NAGARTA, na gode da kauna.

Princess Amrah ke muku fatan alkhairi.
Wattpad: PrincessAmrah
Email: amratuauwal20@gmail.com
Instagram: amrah_princess
TikTok- amrahs_kitchen
YouTube: amrah's kitchen
Facebook: amrah auwal

Na gode, na gode, na gode masoyana.

Continue Reading

You'll Also Like

19.5K 1.7K 100
labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa.
191K 15.4K 42
story is starting with a business tycoon Vansh raisinghania and a middle class girl Riddhima. Vansh hates women because of his past and he wants a su...
2.3K 231 15
Saboda yadda mahaifin mu ya din ga saka Mana suna Fatima, har se da nayi tunanin ko Muna da alaka da shi'a ne, saboda Naga yawancin sune mutanen da k...
807K 69.4K 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zaz...