DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 59- Bakar Manufa

146 21 0
By PrincessAmrah

Page 59

Na yarda da shawarar Haidar, na latsa kiran ta. Wayar na fara bugawa ta dauka. Na ce,
"Hajiya, kamar yadda na shaida miki zan yi shawara da mijina, to mun yi din. Sai ki fada min sadda kike da dama, ki same ni a Office mu yi magana."

Ta yi murmushi,
"Ba na son mu hadu a Office ne Barrista. Kin san lamari da manya, muna da bukatar privacy gaskiya."

Haidar ya daga min kai alaman in amince. Na ce
"Okay babu damuwa. Ki fada min inda za mu hadu, gobe daga Office sai in same ki."

Muryarta ta bayyana farincikin jin na amince, ta ce,
"Akwai guess house din Honorable Sani Giginya, da ke kan sabon titin Kwado. Mind if we meet there?"
Nan ma daga min kan Haidar ya yi.
"Yes ba damuwa. Zan zo wurin biyu na rana, in shaa Allah."
Daga haka muka yi sallama, ta yanke kiran.

Washegari daga wurin aiki na wuce inda ta kwatanta min, a can muka hadu da Haidar kamar yadda muka tsara ba zan je ni kadai ba. Ya yi zaune a cikin motarsa ni kuma na shiga ciki. Maigadi ya san da zuwa na, shi ya yi min iso zuwa babban parlor mai cike da kayan more rayuwa.

Can zaune na hangi Hajiya Lami, sanye da wasu irin kaya na alfarma, hannu da wuyanta duk gwalagwalai. Sannan a kusa da ita akwai wata budurwar da a shekaru ba za ta wuce Nusaiba ba. Sai kuma Honorable Sani Giginya zaune, suna hira na karasa ciki.

Gani na ya sanya su yin shiru tare da mayar da hankulansu gare mu. Na gaishe su cikin girmamawa, sannan ta ce,
"Ki zauna da kyau Barrista."
Na zauna kujerar da ke kusa da tata.

Kwala kiran wani ta yi ta ce a kawo min abun motsa baki. Babu jimawa sai ga wani matashi dauke da babban tray ya ajiye a gabana. Na dauke duba na daga tray din, na kalli Hajiya Lami. Na ce
"Hajiya, sauri nake na bar yara a gida ban koma ba daga wurin aiki."

Ta kalli yarinyar da ke zaunen, ta ce mata ta tashi ta shiga ciki ko kuma ta fita waje. Sannan ta dawo da hankalinta gare ni.

"Kamar yadda na fada miki jiya, ko nawa kike so zan biya ki a kan ki yi min wannan aikin Barrista. Wannan yarinyar da kike gani, ita ce aka yi wa fyaden, 'yar kanwata ce ta zo daga birnin London. To an rasa gane ko su wane ne suka aikata, don ba ta san su ba, kuma babu kowa a wurin da aka yi din. A takaice dai, babu wani suspect.
A lokacin an kai ta asibiti, kuma muna da duk wasu medical reports a ajiye.
A takaice dai Barrista, so nake mu dora alhakin fyden sunkutukum ga dan gidan abokin hamayyarmu, Alhaji Kabiru Darazo, saboda muna son bata masa suna, mu bata tafiyar tashi, musamman ganin yadda mutane ke son shi, suke son zuri'arsa saboda kamilanci.
Na san ba zai zauna ba shi ma, idan aka kai masa sammaci dole za su nemi nasu lauyan, watakila ma wanda ya fi ki. To ban damu ba ko mu ci ko mu fadi. Babban burina dai ki kawo hujjojin da za su gamsar da mutane cewa yaron ya aikata, ko da ba su gamsar da alkali ba."

Kallon ta nake har ta yi ta gama tare da mamakin abin da take son in aikata din. Wannan wace irin rayuwa ce wadda mutum ke zabar duniya a kan lahirarsa? Me ya sa mutane suke manta cewa Allah na ganin kowa da komai? Me ya sa suke manta cewa akwai mutuwa akwai hisabi, sannan akwai ranar tashin alkiyama? Wannan wane irin mummunan kazafi ne suke son dora wa wanda bai ji ba bai gani ba kawai saboda neman duniya?
Jin na yi shiru ina kallon ta ya sanya ta zaro bandir guda na Dalar Amurka, kuma duk kwaya daya da ke cikin bandir din, Dala dari ce. Na kalli kudin sau daya hade da janyo kallo na don ma kar su shagaltar da ni.
Wani bandir din ta sake daukowa ta dora a kan na farkon. Kafin in dauke kallo na ta sake dire wani; bandir uku kenan.
Na dago na kalle ta, sai gani na yi ta sakar min murmushi.

"Duk wadannan kudaden za su iya zama naki Barrista, za ki samu mafiyansu ma idan har kika tsaya mana a wannan aikin. Ba abu ne mai sauki ba, saboda samun hujjojin za su iya yin wahala. Sai dai ba ke kadai za mu bari da aikin ba; za mu samu wadanda za su taya ki samun hujjar, da duk shaidun da suka dace."

Na shafi gumin da ke tsattsafowa a saman goshina. Kudi dai ga su nan masu tarin yawa, sai dai na banza, domin kuwa ko za su ba ni irinsu sau goma ba zan iya yi musu wannan aikin ba. Ba zan iya aikata wannan babbar ta'asar ba. Ba don irin haka na karanci lauya ba, ban zama lauya domin in taya a zalunci bayin Allah ba. Na karanci lauya ne saboda ire-iren matayen da ake rabawa da martabarsu ta karfi da yaji, ko kuma yara kanana; maza ko mata da ake haike mawa. Ba na fatan ranar da za ta zo da zan yi aikin zalunci kawai saboda abun duniya; abun duniyan da zai kare watarana ya bar ni da Ubangijin da na saba mawa dominsu.
Wannan wata jarabawa ce Allah ke yi min ta hanyar Hajiya Lami, domin ganin zan tsallake ta, ko kuwa kudi za su rude ni in afka ga halaka?

Muryar Honorable Giginya na ji ya ce,
"Wannan daga aljihun Hajiya Lami ne kawai. Idan har kika yi mana aikin nan, akwai nawa na musamman, wanda za su iya zarce adadin wannan ma. Kawai mu burinmu duniya ta gamsu dan gidan Kabiru Darazo, dan iskan yaro ne mai keta haddin mata."

Ganin kamar shirun da na yi ya sanya suke daukar zan amince, ya sanya ni tattara kudin na mayar da su kusa da Hajiya Lami. Mikewa na yi tsaye, na dube ta cikin ido na ce,
"Ki yi hakuri Hajiya, ba zan iya yin wannan aikin ba. Ku ci gaba da cigiya na tabbata za ku samu lauya mai irin halinku da zai yi muku wannan aikin saboda kudinku, amma ni dai gaskiya ba zan iya ba, ban fara wannan aikin domin kudi su halakar da ni ba.
Ku yi hakuri idan maganata ta bata muku rai, wallahi ba zan iya ba ne."
Har na tafi, sai kuma na juyo na ce,
"Na yi alkawari zan adana muku sirrinku."

Daga haka na fice, ban ko jira jin abin da suke fadi ba.
Hankalina tashe na bar kofar gidan. Sai da na kira Haidar a waya na shaida masa na gama, sannan na shiga motata na tayar, shi ma din ya tada tashi muka tafi bumper-to-bumper.

Da muka isa gida, tun a parking area na fara ba shi labarin yadda muka yi da su. Isar mu parlor da oyoyo din da yaranmu ke yi mana ya sanya na dakata da ba shi labarin, muka rungumi yaran cike da tsantsar soyayya.

Sai daga baya ne na ci gaba da ba shi labarin. Ya yi mamaki kwarai, ta yadda mutane za su zauna su kirkira zance kawai don samun nasararsu ta duniya, kamar ba za a je lahira ba.
"Kin burge ni sosai Buttercup da ba ki yarda kudinsu sun yi tasiri a gare ki ba. Wallahi na tsani zalunci da azzalumai. Haba! Ina amfanin ma wata rayuwar? Wasu kudin ai ba su da rana in dai ba na neman lada ba ne ba."
"Ai da ma Daddy na fada maka jikina bai ba ni abun kirki ba ne."
Na fada ina kallon shi. Ya ce,
"Tabbas kin fada. Kin ga wannan wani battle ne tsakanin kudi, da farar zuciyarki. Idan har kika bari kudi suka ci galaba, to shi kenan fa sun bude miki kofar ci gaba da neman zunubi, tare da kai kanki ga wuta, amma matukar farar zuciyarki ta yi galaba a kan makudan kudade, tabbas Allah zai kasance tare da ke a kodayaushe, zai kuma ci gaba da shige miki gaba a dukkanin lamurranki."

Ban ba shi amsa ba sanadiyyar karar shigowar text message a wayata. Na dauka na duba. Lambar nan ce ta Hajiya Lami, don da ma ban yi saving dinta ba, amma kuma ina ganin ta zan gane. Na bude message na shiga.

'Ki yi tunani da kyau Barrista, idan har kin canja shawara, muna maraba da ke, daga nan zuwa kwana uku. Zan kara miki bandir ukku a kan wanda na ajiye a gabanki, kin ga bandir shidda kenan. Ban da wanda Honorable ma zai ba ki.'

A bayyane na karanta. Haidar ya ce,
"Ai ko da a ce za su ba ki kudin da ba za ki kara yin talauci ba idan kin karba, ba za ki taba amincewa da aikin nan ba. Babu amfanin dukiyar da aka same ta ta hanyar haramun. Wannan dalilin ne ya sa da yawa daga cikin lauyoyi da alkalai suke afkawa ga halaka. To kudi ne kana ji kana gani, ba wani aiki mai yawa za ka yi ba sun zama mallakinka. Ba kowa ba ne zai iya bari su wuce shi, sai mai tsananin karfin zuciya, mai tsaftatacciyar zuciya irin matata."
Ya karasa da shafar fuskata yana murmushi.
Ni ma murmushin na sakar masa. Ya shafi lebena, kafin a hankali ya hada bakinsa da nawa, cike da bege, zallar soyayya, da kuma kewata da ya yi na kwanakin nan da nake yawan fama da ciwuka.

***
Ina zaune sai ga kiran Hannatu a wayata. Ta gaishe ni sannan ta tambaye ni idan ina gida ga ta nan zuwa. Na fada mata babu inda zan je, sai ta zo.
Babu jimawa sosai sai ga ta ta iso.
Su Afreen suka shiga jikinta saboda tsananin sabon da suka yi da ita, tana yawan zuwa gidan, sannan su ma ina kai su can su yi weekend wani lokacin, saboda sun saba sosai, kuma Anti Khadija ma tana cewa a kai su.

Bayan sun gama duk oyoyonsu ne ta dawo kusa da ni ta zauna. Cikin farinciki take shaida min ta samu admission a Havard University, kuma Daddynta ya ce zai kai ta.
"Alhamdulillahi."
Na furta a bayyane ina bayyana nawa farincikin.
"Kin gani ko Hanna, dukkan hani ga Allah baiwa ne. Kwanaki kin yi ta damuwa na zaman banzan da kike yi tun da kika bar Poly. Ga shi nan yanzu ba ma a kasar za ki yi karatu ba. Gaskiya am very happy for you wallahi. Wane course za ki karanta?"

Da annurinta ta ce
"Psychology suka ba ni Anti Khairi. Kuma da ma shi na nema."
Na yi dariya na ce,
"Ilimin sanin dan'Adam kike son koya kenan?"
Ita ma ta yi dariyar.
"It was my dream tun ina yarinya karama."
"Me ya sa?"
Na tambaya ina kallon ta.
"Haka kawai masu wannan ilimin suke burge ni Anti."
Na gyada kai na ce
"Ina ma laifin a ce Psychology Doctor ce? Ina son wannan fannin fa. Kawai dai kin san kana naka ne Allah na naShi, kuma naShin shi ne na gaskiya. Na so zama likita Allah ne bai nufa ba."
Hannatu ta yi dariya, sannan ta ce,
"Ai Anti da wuya ki ga yaron da ya tashi ba da burin zama likita ba. Kuma a cikin mutum dari masu wannan burin, da wuya ki samu goma da suke samun nasarar zama likitocin. Na rasa yadda aka yi haka. Sai ki ga mai burin zama likita ya kare a karantar Economics."
Muka sa dariya a tare.


Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

5.1K 463 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zat...
191K 15.4K 42
story is starting with a business tycoon Vansh raisinghania and a middle class girl Riddhima. Vansh hates women because of his past and he wants a su...
155K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...
2.3M 70.3K 98
Previously called Older Brothers Part 1 Completed (Alternate version) part 2 Ongoing "T-trust me?" "Always." It was the promise that they were never...