DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 48- Kauyawa

138 23 2
By PrincessAmrah

Page 48

Shiga na yi cikin asibitin na kira wata nurse na shaida mata abin da ke tafe da ni. Da hanzarinta ta dauko gadon dora marassa lafiya, ta tura shi muka koma wurin motar. Da taimako na da na Babanta muka dora ta a kan gadon, ba mu ankara ba har muka fama ta ta fashe da wani irin narkakken kuka.

Sannu kawai muke yi mata har muka karasa dakin da ake ajiye su domin jiran likita.
Waigawa na yi da nufin tambayar nurse din wani abu amma sai na ga ba ta nan, sai Anti Khadija ce kawai ta rafka uban tagumi.
Yunkurin ficewa na yi amma sai ta kamo hannuna. Cikin rauni ta bude baki ta ce,
"Na san ni mai laifi ce a wurinki Khairi, don Allah..."

Na gyada mata kai kawai tare da hana ta maganar, na fice daga dakin. Yanzu duk ba lokacin wannan bayanan ba ne, ba su ba ne a gabana.

Babu jimawa sai ga likitan ya zo. Tare da shi muka shiga dakin da wasu nurses.
"Za ki iya jiran mu a nan barrister. Bari mu matsa wurin can in duba raunukan."
Na zauna kan daya daga cikin kujerun da ke jere cikin dakin. Shi da wata nurse suka tura gadon zuwa inda wani labule yake domin duba ciwukan da ke jikinta.

Sun dan jima suna dubawar, fiye fa minti talatin, sai ga su sun turo gadon nata sun dawo da shi inda yake da. Ya dubi Anti Khadija da duk ta zama wata iri, ya ce,
"Baiwar Allah ke ce mahaifiyarta?"
Ta daga kai cikin kuka ta ce,
"E, ni ce."

Gajeren tsaki ya saki,
"Ba ku kyauta ba gaskiya. Kun kuwa san irin raunukan da ke jikin yarinyar nan har sun fara rubewa saboda rashin kula? Wannan wace irin asibiti ce kuka kai ta wadda sam ba su san makamar aikinsu ba?"
Na yi caraf na ce,
"Doctor ai sun dauke ta daga asibitin ne wai saboda gudun abun kunya. Suna tsoron kar zaman asibitin ya janyo tonuwar asirin fyaden da aka yi mata."

Fuskarsa murtuke ya sake duban ta ya ce,
"Ashe a birni ma ana samun irin haka. Ni na dauka tuni an waye an daina ire-iren wadannan abubuwan? Ai ga shi nan a kokarinku na ganin an rufa mata asiri, za ku nakasa mata rayuwa. Wallahi raunukan da ke jikinta ba kanana ba ne, ga dinkin da aka yi mata shi ma babu kula, har ya fara kumbura, nan da lokaci kadan za ta fara wari in da ba a kawo ta nan ba."
Ya dubi nurses din da ke biye da shi ya ce,
"Ku buyo ni zan fada muku abin da za ku fara kafin komai."
"Doctor idan ka rubuta results ina jiran report din ciwukan."
"In shaa Allahu."
Ya fadi hade da ficewa suka mara masa baya.

***

A cikin kwana uku Hannatu ta dan fara samun saukin raunukanta. Har tafiyarta ta fara dan daidaita duk da dai har yanzu da sauran ta. Sai dai rashin walwalar nan har yanzu yana nan, shiru-shiru da ita kamar ba Hannatun nan mai son hayaniya da wasa ba. Bakidaya ta sauya, ko magana ta yi da wuya a gane abin da ta ce saboda a hankali take yi.

Dakin na shiga da file dinta a hannuna, na amsa gaisuwar da Mamanta ta yi min kafin na zauna a bakin gadonta ina murmushi.
"Alhamdulillahi jiki ya fara sauki ko Hannatu? Na gan ki zaune ba kamar kullum ba."
Ba tare da na jira me za ta ce ba na dubi Anti Khadija na ce,
"Za ki iya ba mu wuri mu yi magana? Don ba lallai ta iya fadan komai ba a gabanki."
Ba tare da ta ce komai ba ta tashi jiki sanyaye ta fita.
Na dawo da kallo na ga Hannatun, na janyo sunayen nan da Babanta ya ba ni, sannan na ce,
"Duk abin da na tambaye ki, ki bude baki ki ba ni amsa in dai kin sani Hannatu. Hakan ne kawai zai sanya mu yin nasara a kotu. Amma idan kika yi shiru, kin ga ni ban san komai ba a game da abin da ya faru. Duka-duka kwana uku ne ya rage mana mu shiga kotun. Tuni an tura wa suspects din namu sammaci."
Na dafa kafadarta, cikin karfafa mata guiwa na ce,
"Ina so ki sani Hannatu, wannan abin da ya faru ba shi ne karshen farincikinki ba. Na san ba za ki rasa jin labarin irin hakan ta taba faruwa da ni ba. Amma ina nake yanzu? Hakan ya komar da ni baya? Ba ga ni nan ba a gabanki a matsayin Lawyer, wadda ke kokarin kwatar miki fansa ba? To ki daure kin ji? Ki sanya wa zuciyarki salama, duk abin da kika ga ya faru a rayuwarki da ma can haka Allah Ya rubuta miki. Kuma in shaa Allahu rayuwarki za ta yi kyau kamar yadda tawa ta yi kyau a yanzu, watakila ma fiye da hakan."
Ta jinjina kai, tana kokarin yin murmushin da ya gagara ba ta hadin kai.

"Yawwa kanwata. Da farko dai, ina so ki fada min dalilin da ya sanya kike zargin su ne suka haike miki."
Ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya ta ce,
"Duk na ga fuskokinsu. A lokacin da dayan ya fara..."
Kuka ya kufce mata. Ban hana ta ba, har sai da ta yi mai isar ta, sannan ta ci gaba,
"Da ya fara, su sauran suna jiran sa ya gama, shi kuma bai gama ba sai ga wani abu kamar ya cije shi, da farko ya dauka maciji ne sai kuma ya ga wani kwaro ne, a lokacin duk da ina kuka ina ihu amma sai da na gode wa Allah, don na zaci kubuta zan yi daga hannunsa. Amma sai ga wannan na biyun ya ci gaba. Ina kuka ina komai amma bai kyale ni ba har sai da ya gama don kansa, na ukun ma ya yi nashi, daidai na hudun zai fara kenan sai ga muryar wasu kauyawa mata da miji, sun ratso ne daga kauyukan nan da ke bayan Poly. Suna jin muryoyinsu sai suka fara yunkurin guduwa. Guda dayan nan da sunansa ke k'asa, shi ne kadai bai riga ya fara ba. Shi ya sa ma da farko ban bayar da sunansa ba da na farkon nan, wanda wani abu ya ciza ba, Daddyna ne ya ce in hada har da su."

Cike da tausayi nake sauraren ta, kafin na ce,
"To da ma kin san su ne?"
Ta jinjina kai,
"Na san su. Biyun nan suna aikin gini ne a sababbin gine-ginen da ake yi a cikin estate dinmu. Da yake Daddy ke kwangilar yin su, sai yake dan turo su gida a wasu lokutan karban masa sako. Su kuma wadannan biyun, ba aikin ginin suke yi ba, Kamar caretakers ne dai, ina ganin su amma ban san takamaiman me suke yi ba."

Mamaki sosai ya kama ni. To su kuwa me zai sanya su haike wa Hannatu bayan sun san ta san su, ba su gudun tonuwar asirinsu?
"Da ma tun da na fito daga cikin makaranta na lura kamar akwai masu bi na, a bakin gate din makaranar na tsaya ina jiran napep, sai in ji motsi a bayana amma da na waiga sai in ga babu kowa. A tsorace dai na samu napep din na hau. Amma tun ban yi nisa ba sai ga Ibro ya tsayar da shi ya shiga gaba, Saminu kuma ya zauna a baya kusa da ni. Da na ga su ne, kuma na san su, sai na dan samu nutsuwa. Can sai Saminu ya ce,
"Shiga wannan kwanar."
Babu musu mai napep ya shiga kwanar, na yi mamakin me zai kai su hanyar dajin nan, sai kuma na tuna ai akwai kauyuka a ciki, watakila can za su je.
Sai dai muna kutsawa ciki, muka hango ragowar biyun, sai suka ce ya dakata daga nan. Da karfi Ahmadu ya janyo ni na fado kasa. Mai napep ya ce
"Haba Mallam! Ya da haka kuma? Me za ku yi mata?"
"Fyade za mu yi mata sannan mu kashe ta. Ko akwai magana?"
Kugunsa ya gwada masa, ina kai ido na ga wuka ce, mai napep ya yi saurin dafe bakinsa hade da kunna napep din ya tafi yana fadin
"Allah Ya kyauta."
Ni kuwa kuka na fashe da shi ina tambayar su me na yi musu? Me ya sa suka kawo ni wurin nan? Sai dai kafin in gama tambayar su suka ba ni amsar tambayar abin da suka kawo ni su yi min, kamar yadda suka fada wa mai napep.
"Kashe ki za mu yi, sai muka zabi hanyar da mu ma za mu karu da ke kafin ki wuce lahira."
Na dubi Ila da ke maganar, su din nan dai ne da Babana yake kyautata mawa sosai. Har abinci ake ba su gidanmu a wasu lokutan.
Daga nan ne fa suka fara..."
Ta kara fashewa da kuka.
"A lokacin da kauyawan nan suka zo, cikin tsoro suka bar wurin, amma har suka tafi suna waiwayena don tabbatar da ina raye ko kuwa na mutu. Gani na a baje kamar marar numfashi ya sa suka samu nutsuwar tafiya.
Can kuma sai ga su sun dawo, macen ta kara fuskarta a saitin zuciyata, jin ina numfashi ya sanya ta fada wa mijinta, ai ina raye.
Wadannan kauyawan su suka kai ni asibiti, amma aka ce ba za a karbe ni ba dole sai da 'yan sanda. Kasantuwar asibitin da Momina ke aiki ne ya sanya wata nurse ta gane ni, shi ne ta je ta kira Momin a lokacin ba ita ke duty ba. Shi ne ta zo."

Na sauke ajiyar zuciya. Kenan idan har haka ne babu wata doguwar shari'a a cikin wannan al'amarin. Idan har magina ne suka haike mata, waye zai tsaya musu a kotu? Ina suke da kudin daukar lauya? Ina ji a jikina komai zai zo mana da sauki.

Na sake duban ta na ce,
"Su wadannan kauyawan, akwai yadda za a yi mu same su?"
Ta gyada kai,
"Ko ganin su na yi ba lallai ba ne in tuna fuskokinsu ba. Mai napep din da ya kawo ni kadai zan iya ganewa idan na gan shi, sai dai ganin nashi ne zai yi wuya, don a ranar ne na fara ganin shi din. Idan kuwa zan ga napep din tashi kai tsaye zan gane ta. Don har lambarta sai da na karanta kafin in shiga, saboda tashin hankalin bibiya ta din nan da jikina ya ba ni ana yi. Na koyi hakan ne daga wurin wata kawata, ta ce ita ma Babanta ya fada mata, duk sadda makamancin haka ya faru da ita, ta tabbatar da ta duba lambar mota ko kuma napep kafin ta shiga. Idan still hankalin nata bai kwanta ba bayan tana ciki, sai ta tura wa mahaifin nata text da lambar wannan motar ko napep din."
Ta dire zancen tana kuka sosai.

Na dan shafi fuskata,
"Kar ki damu, in shaa Allahu mu ne nan masu nasara. Ni dai fatana Allah Ya ba ki lafiya, Ya kuma sassauta miki zuciyarki."
A bisa lebenta ta amsa da amin.
Daga nan na tashi na tafi, ina fita Anti Khadija ta taso ta shige dakin tana yi tana waige na.

Da na koma Office na shaida wa Barrister Fa'iz duk yadda muka yi da Hannatu, sai cewa ya yi,
"Kuma kina tunanin ba sanya su aka yi su yi ba?"
Na yi shiru ina nazari...kuma fa hakan ma zai iya yiwuwa. Ballantana kuma sai da suka ce kashe ta za su yi, me ta yi musu da za su kashe ta babu gaira babu dalili?
"Kuma fa haka ne Barrister. Idan kuwa har sanya su aka yi, na tabbata dole za a saman musu Lawyer. Tirkashi!"

Wayata ce ta dauki kara. Barrister Nuruddeen ne, sai da gabana ya fadi kafin in dauka, na gaishe shi ya ce,
"Idan ba ku komai ke da Barrister Fa'iz, ko za ku iya samu na a office yanzu?"
"Yes Sir, ga mu nan zuwa yanzun nan in shaa Allah."
Na yanke wayar hade da shaida masa. Ya ce,
"To Allah Ya sa alkhairi ne."

A tare muka doshi office din, na rasa dalilin da ya sa gabana ke faduwa har muka karasa, bayan mun yi knocking ya ba mu izinin shiga, muka shiga Barrister Fa'iz a gaba ina biye da shi.




Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

11.1K 72 15
está es una historia donde nos demuestran que el amor no tiene límites te vas a enamorar de un mafioso? no importa en esta historia te lo demostrarem...
13.8K 1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
132K 8.6K 55
Kallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi
19.4K 1.7K 100
labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa.