DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 40- Reconciliation

160 23 0
By PrincessAmrah

Page 40

Da wani irin rashin kuzari Haidar ya tako ya karaso kusa da ni. Cikin idanuwansa na kalla, na ga yadda duk suka zurma, zagayensu ya fara yin bak'i-bak'i saboda rashin bacci.
Cikin sassanyar murya ya ce
"Ko za ki zo in mayar da ke gida tunda ga su Salima nan sun zo?"
Na gyada kai,
"Bai kamata in tafi ba don sun zo. Yadda take mahaifiyarsu ni ma haka take uwata. Don haka zan zauna, har sai Mami ta tashi na ga yanayin jikin nata."

Da alama ba ya son yawan magana hakan ya sanya shi kawai daga kai ya koma kan wata kujera tare da hada kansa da guiwa. Bakidaya jikina ya karasa yin sanyi; ganin mutum mai karfin hali irin Haidar a cikin wannan hali, dole hankalina ya tashi. Ji nake tamkar in je in yi ta ba shi baki har sai zuciyarsa ta sanyaya.

Can kuma sai ga Sista Khadija ta zo sanye da fararen kayan nurses da alama wurin aiki za ta wuce. Biye da ita 'yar budurwa ce wadda ko Sadiyarmu za ta iya girmanta; tsakanin shekara goma sha biyu zuwa sha uku dai.
Duk da haushin ta da nake ji hakan bai hana ni gaishe ta ba, sai dai ko kallon inda nake ba ta yi ba ta zarce inda Nusaiba, Aunty Jamila, da Anti Salima suke. Budurwar da ke tare da itan ce ta gaishe ni da murmushi ni ma na mayar mata na karfin hali. Na gane diyarta ce saboda kamar da suke yi, kuma ina jin sunan Hannatu a bakin Nusaiba tana cewa babbar diyar Anti Khadija.

Ganin su ya sanya Haidar zuwa inda nake, ya ce,
"Ba na so ranki ya baci alhali muna cikin alhinin ciwon Mami. Ki zo mu je in kai ki gida, in ya so idan kin kimtsa kin karya sai ki dawo."
Na bude baki na ce,
"Da alama wurin aiki za ta..."
"I insist."
Ya fada hade da yanke min magana.

Dole na je wurin su Nusaiba na shaida musu zan je gida in yi wanka sai in dawo. Kasa-kasa na ji Anti Khadija tana fadin
"Da ma tunda ba uwar mutum ce a kwance ba ai dole a tafi gida. Kodayake ba ma bukatar kingin..."

"Anti Khadija!"
Nusaiba ta fada cikin wani irin bacin rai da bai boye kansa ba a cikin muryarta.
"Wai sai yaushe ne za ki kyale baiwar Allah'n nan ta sarara ne? Sai yaushe ne za ki gane bawa ba ya taba tsallake wa kaddararsa?"

"Watakila sai ranar da na fito mata a mutum, na nunar mata da ina kaunar matata, sannan ne za ta fita sabgata da ta iyalina."
Haidar ne ya yi wannan maganar cikin bacin rai.

"Ya isa! Ya isa haka dukkanku. Haba! Mene ne haka wai? Ga mahaifiyarmu can kwance kan gadon asibiti har yanzu ba mu san a wanne hali take ba amma ku ga ku nan kuna kokarin tayar da hatsaniya a cikin asibiti. Da me za mu ji? Ciwon Mami ko rikicinku?"

Haidar ya dubi Anti Jamila da ta yi wannan maganar. Bai ce komai ba, sai dai ta cikin idanuwansa za a fahimci zafin da zuciyarsa take ciki. Ya ja hannuna ba tare da ko sallama mun yi da su ba muka tafi.

Tun da muka tafi babu wanda ya ce uffan har muka isa gida. Bayan na fito daga mota kai tsaye dakina na nufa. Na shiga na yi brush sannan na sakar wa kaina ruwan zafi saboda gajiyar da ke tattare da ni; ga ta hidimar taro jiya, ga kuma ta kwanan zaune.

Bayan na fito na shafa mai, na bi da body milk din Dukhan by Ayn, sai na ji wata irin nutsuwa tana sauko min, hakika kamshi rahma ne, musamman kuma kamshi irin na Dukhan by Ayn. Duk yadda aka yi wa mutum bayaninsu ba lallai ya fahimta ba har sai idan ya gwada ne zai tabbatar da hakan (+234 808 892 9221).

Doguwar rigar atamfa na saka, ko tsayawa gyara gashina ban yi ba kawai na daura dankwali sannan na hau kakkabe-kakkabe duk da babu wani datti a gidan.
Daga nan na nufi kitchen na ga komai akwai na abinci. Plantain da kwai na soya sannan na dafa shayi mai kayan kamshi na kwashe a cikin flask na kai komai dining na jera.
Daga nan na dora farar shinkafa da dankalin turawa, a gefe guda kuma na dora tafashen naman kaza na zuba kayan kamshi.

Dakin da nake hasashen na Haidar ne na nufa. Na tarar da shi ya yi wanka amma bai sanya kaya ba sai kai da guiwa da ya hada. Har na shiga bai san na shiga ba, na fahimci hakan ne ta dalilin rashin amsa sallamar da na yi.

Sai da na zauna a gefensa, har jikinsa yana dan gogar nawa sannan ya farga na shigo. Ya sanya hannunsa ya dan janyo ni na shigo cikin jikinsa, bai ce komai ba sai dan shafa ni da yake yi a hankali, ni kuwa bai san hakan neman rikita ni yake ba musamman da ya kasance akwai 'yar lemar ruwan wanka a jikinsa.
Kokarin zamewa nake amma bai ba ni damar hakan ba.
Cikin rashin walwala na ce,
"Ka kimtsa ka fito ga breakfast can na hada."
Ya sauke ajiyar zuciya,
"Da sauri haka?"
Na daga masa kai.
Ya kirkiro murmushi ya ce,
"Sannu da kokari."
Na jinjina kai ina kokarin mikewa amma sai gyada min kai da ya yi ya ce,
"Duba a cikin closet din can ki samo min kaya, marassa nauyi please."
Na mike tare da nufan closet din. Kaya ne jibge tamkar kayan mata, an yi arranging dinsu da kyau, ga wani irin kamshi da suke fitarwa. Wani navy blue lallausan yadi ne na fiddo na kawo masa.
"Ki duba dayan side din akwai inner wears, ki dauko wanda za su yi matching da kayan."
Mamakinsa kawai nake. Wai ashe maza ma sun san matching? Kamar ya san tunanin da nake yi, sai ya yi murmushi hade da fadin,
"Kin ga yadin ai transparent ne, babu yadda za a yi a sanya red ko green inners."
Murmushin na yi ni ma cike da kunya na karasa na ciro masa vest da boxer bakake.
Ina ba shi ya kama hannuna ya rike don kar in fita. Na tsaya ina kallon shi, sai ya kama ni ya zaunar a bakin gado, shi kuma ya fara kokarin sanya kayansa.
Wani irin bargon kunya na ji ya lullube ni, na gaggauta sunkuyar da kaina ina kara tabbatar da lallai Haidar bai san kunya ba.
Sai da ya fesa body spary bayan ya sanya inners din sannan ya saka sauran kayan duk ina satar kallon sa.
Da ya gama duka ya kama hannuna ya mikar, muka nufi hanyar fita.

Duk yadda na so ya ci abun kirki bai cin ba, kuma na masa uzuri saboda ciwon mahaifiya ba dadi. Ni ma din kaina karfin hali ne don sosai ciwon nata ya dake ni. Bayan mun gama ya koma parlor ya zauna ni kuma na nufi kitchen na ci gaba da girkina.
Kasantuwar miyar kaza ce ya sanya na dan dauki lokaci ban gama ba. Sai bayan azahar na hada komai a warmers sannan na nufi sallah, a lokacin shi ma ya tafi masallaci.

Ina fitowa na tarar ya dawo. Kallo na ya yi ya ce
"Kin gama mu tafi?"
Na daga masa kai hade da komawa daki. Hijabi mai matsakaicin tsayi na sa bayan na kashe kamshin girkina da ya kama ni da khumrar Dukhan by Ayn, na fito. Na iske har ya dauki babban basket din ya kai mota.
Bayan na rufe gidan na je ni ma na shiga motar.
Ina shiga ya dago kansa ya kalle ni, ya dan lumshe idanuwansa ya bude a kaina, kafin a hankali ya ce
"Je ki canja kaya."

Cikin mamaki na kalle shi, kafin in tambaye shi dalili sai cewa ya yi,
"Me ya sa kika sanya turare alhali kin san akwai maza asibitin?"
Gajerar ajiyar zuciya na sauke hade da guntun murmushi.
"Kamshin ai ba ya tashi fa, kai ma don muna daf da juna ne ya sanya ka ji. Khumra ce ta Dukhan by Ayn, kamshinsa ba mai tashi ba ne."

Cikin gamsuwa ya jinjina kai, sannan ya tayar da motar muka tafi.

Da muka isa ya kira Nusaiba ta shaida masa an mayar da Mamin amenity suna room 18. Kai tsaye can din muka nufa yana dauke da katon basket din abincin.

Alhamdulillahi Mami ta farfado, sai dai kamar yadda na yi tunani, bakinta ya dan karkace sannan gefenta guda na dama ya dan shagide.
Da sallama a bakina na karasa cikin dakin, kamar daga sama na ji muryarta ta ce,
"UmmulKhairi, zo nan kin ji..."
Mamaki ya kama ni, baiwar Allah muryar ma da kyar take fitowa, ga kuka da take yi.
Da sanyin jiki na nufi bakin gadon, tsoro-tsoro nake ji amma sai ta min alama da in mika mata hannuna, na kuwa mika matan ta saka a cikin nata na haggu. Mun dan jima a haka, kafin ta ce,
"Ki yi hakuri UmmulKhairi, ki yafe min duk abin da ya faru."
Wani irin kukan dadi na fashe da shi, ina maimaita kalmar alhamdulillahi a cikin zuciyata.
"Tun da na farka na neme ki aka ce a tsaye kika kwana cike da alhinin ciwon nan nawa, kin tafi gida ne saboda zuwan Khadija. Ban san da wanne baki ma zan fada miki ki yafe min ba..."
"Ki bar zancen Mami, komai ya wuce. Ban taba rike komai ba wallahi. Ke uwa ce, kuma ba a fushi da uwa."

Ta gyada kanta cikin hawaye, dalla-dalla maganarta ke fita ta ce,
"Duk da haka dai, na k'i ki ba gaira ba dalili, an cusa min tsanarki ba tare da wani kwakkwarar hujja ba. Wallahi na yi nadama. Allah Ya sani tun farko ina son ki, zugar Khadija ce ta yi tasiri gare ni. Amma komai ya wuce, Allah mai yanzu-yanzu Ya gwada min iyakata. In shaa Allahu in dai Allah Ya sa na mike, zan kaunace ki tamkar Nusaibata."

Dukkan wadanda ke dakin babu wanda bai murmusa ba, ciki har da Hannatu da ke zaune kusa da Nusaiba. Haidar ma annurin da ya kwana ya wuni babu shi ne na tsinta a saman fuskarsa. Haka su Anti Salima. A take dakin ya dauki wani irin nishadi wanda aka rasa tun jiya da daddare.
Hannatu na kalla na ga yadda take dariya, hakan ya tabbatar min da maganar Nusaiba da ke cewa yarinyar tana da hankali, sam ba ta biyo halin mahaifiyarta ba. A take na ji kaunarta ta shiga raina, don karara ta fara nuna min soyayya, na kuma gamsu da soyayyar gaskiya ce. Da ma tuni Nusaiba ke fada min Hannatu na so na sosai, har akwai ma zuwan da ta yi gidanmu wanda ta so ta biyo ta amma kunyar abubuwan da Mamanta ke yi ya hana ta zuwa.



Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

807K 69.4K 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zaz...
11.1K 72 15
está es una historia donde nos demuestran que el amor no tiene límites te vas a enamorar de un mafioso? no importa en esta historia te lo demostrarem...
2.3M 70.5K 98
Previously called Older Brothers Part 1 Completed (Alternate version) part 2 Ongoing "T-trust me?" "Always." It was the promise that they were never...
538K 35.2K 76
A story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......