DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.4K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 32- Nusaiba

152 22 1
By PrincessAmrah

Page 32

Sosai Umma ta yi min nasihar da sai da ta shige ni sosai, lokaci guda na ji na gamsu da dole sai hakan ta faru da rayuwata, zan kuma rungumi komai a yadda ya zo min.

Washegari na koma Office. Ko da na je ban ko tinkari office din Oga Ahmad ba. Kai tsaye office dinmu na je, sai dai ina zama ba da jimawa ba aka aiko kira na in ji Oga Ahmad din. Ji na yi kamar kar in je sai dai babu damar hakan. Na dan shafi fuskata sannan na fada wa Aysha zan je in dawo ta kula min da kayana kar iska ya dauke takardun da nake cikin dubawa.

Ina zuwa Office din nashi na yi knocking sannan na shiga. Shi kadai ne zaune a gaban computer yana tabawa, fuskar nan tashi tamkar bai taba dariya ba, idanuwansa dauke da bakin gilashin da ya mamaye dukkan zagayen idonsa.

K'amewa na yi a gabansa, ban ko motsa ba sai da ya ba ni izini sannan na sara masa, hade da gaishe shi na zauna kan daya daga cikin kujerun da suke gaban teburinsa.

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya dauke dubansa daga computer din ya kalle ni, muna hada ido ya sakar min sassanyan murmushin nan nashi mai tafiya da dukkan kuzarina.

"I have no right da zan hana ki sara min tunda dokar aikinmu ce hakan. Yaya kike? Ya Umma da kannena?"
Na sunkuyar da kaina ina amsa masa da lafiya lau.
"Ma shaa Allah. Ina fatan dai ba ki yi kuka ba. Jiya na kira ki kafin in kwanta amma wayarki a kashe. Kin hana ni jin muryarkin nan da ke sanyaya zuciyar dan marayan Allah."

Dariya na yi a hankali jin yana kiran kansa da maraya, garjejen kato da shi.
"Ba da gangan na kashe wayar ba Sir, ba mu da wuta ne sai tsakiyar dare aka kawo mana."
Ya dan langabe kai hade da fadin
"To ya zan yi, na dai yi managing yin bacci amma mara dadi tunda ban ji muryarki ba."

Shiru na yi ina son fada masa zan tafi kar a fara zarginmu ma, sai ji na yi ya ce
"Dalilin da ya sanya ni kiran ki, shi ne; an sanya date din da za a ba ki award ne a kan aikin nan da kika yi na Kanya Village. Award din ma daga can sama aka turo shi bayan na rubuta application din ina son a ba ki saboda namijin kokarin da kika yi, duk da assignment dinki ne na farko. So, you should start the preparation, in the next three days za a yi taron karrama ki a nan, in shaa Allah."

Wani irin dadi ne ya kume ni, ni har ma na manta da zancen bayar da award din da ya yi min tun kafin in tafi hutu.

"You can go. And please kar ki sake yin wani kukan, idanuwanki sun nuna kin sha kuka sosai. Everything is going to be alright. Nusaiba za ta zo gidanku an jima idan an tashi daga aiki."

Dagowa na yi da niyyar tambayar sa shi kuma fa? Ba ya ce zai je su yi magana da Umma ba?
Karaf idanuwansa suka shiga cikin nawa, sai kawai na ji ba ni ma ba kuzarin yi masa wata tambaya. Da kyar na taka na fice daga office din, ina tunanin dalilin da zai sanya Nusaiba zuwa gidanmu duk da Maminsu na kokarin yi mana iyaka da Haidar din.

Ko da na koma ban wani aikata abun kirki ba, zuciyata sai sake-sake kawai take yi min har zuwa lokacin tashi sai ga kiran Haidar. Ko da na dauka cewa kawai ya yi in fito mu tafi. Ba musu na hada komai nawa na yi wa Aysha sallama na same shi can waje motarsa kunne yana jira na.
Da na shiga motar ko kala ba ta hada mu ba har muka hau kan babban titi. Cikin sanyin muryarsa ya ce
"Bai kamata in boye miki komai ba Buttercup, Mami ta dauka da zafi, ta ce ba da yawunta ba zan aure ki..."
Da wani irin karfi na dago fuskata na kalle shi, shi ma din ni yake kallo duk da tukin da yake yi.
"Amma muna kan kokarinmu ne, Salima za ta zo garin gobe, sannan babbar Yayarmu Anti Jamila ma ta ce za ta zo goben. In shaa Allahu za a yi ta ta kare, don dukkansu sun goyi bayan aurena da ke. Ita Nusaiba don ki tabbatar babu komai a ranta ne ma ya sanya ta cewa za ta zo wurinki yau."

Wani irin sanyi na ji a cikin zuciyata, ko ba komai sarkin yawa ya fi sarkin karfi. Wani irin hope na ji ya shige ni, don da tuni na sare, amma a yanzu da yake fada min 'yan'uwansa sun goyi bayansa, sai na samu kwarin guiwa.
Na saki sassanyan murmushi.

"To shi ne kuma duk ka yi wani sanyi bayan kuma kana da hope?"
Na fada a kokarina na ganin na sanyaya zuciyarsa.
Ya saki gajeren murmushi.
"Ba za ki gane ba ne Khairi, wallahi jiya ko bacci ban yi ba sai tunanin halin da zan iya shiga idan na rasa ki kawai nake. Ba za ki fahimce ni ba duk yadda na so fada miki sirrin ruhina,  wallahi dukkanin bugun zuciyata tare da ke yake tafiya. Na taba yin aure a baya, amma Allah Ya sani duk ban tsinci kaina a wannan yanayin ba, ban sani ba ko don auren hadi ne ni da Maryam ba, kyautatawarta gare ni ya sanya ta saye zuciyata bayan auren namu."

Na yi shiru ina saurarensa.
"Mami ce ta hada mu saboda diyar aminiyarta ce. Ban yi mata musu ba duk da ko kadan ban ji soyayyar Maryam din ba, amma ganin ita din uwa ce wadda ta isa gare ni ya sanya kai tsaye na amince na aure ta ba tare da ko taba ganin juna mun yi ba sai lokacin hidimar auren."
Ya dan yi shiru, sannan ya ce
"Ya kamata ko don wannan Mami ta bar ni da zabina."

Ni dai shiru na masa har ya kai aya. Jin na ki cewa komai ya sanya shi yin murmushi,
"Kin bar ni da kidana da rawata ko? At least say something da zai faranta zuciyata, don wallahi a dagule take, karfin hali ne kawai nake yi. Aikin ma yau na dai zo ne amma ban iya yin komai ba duk da tarin abubuwan da suke gabana."

"Ni ma ban iya yin komai ba fa Allah..."
"Ke kuma me ya hana?"
"Tunanin abin da ya faru fa. Jiya ban yi baccin ba kamar yadda kai ma ba ka yi shi ba."

A daidai sadda ya kalle ni ni ma shi nake kallo, ya saki kyakkyawan murmushi ya ce
"You love me that much?"
Na ji kunya na sunkuyar da kaina ina murmushi.

"Kin san wani abu? In shaa Allahu ba za a kara wata biyar ba mu yi aure ba. Na gaji haka nan. I need you."

Ban dago kaina ba ina jin shi ya ci gaba da zantukan da suke neman fin karfina.
A kofar gida ya sauke ni sannan ya tafi bayan ya fada min kalmar I love you ya fi cikin carbi.
Don haka wani irin sakayau na ji zuciyata, duk kuncin nan da na kwana na tashi da shi na neme shi na rasa.

***
Tun da na isa na fada wa su Safra zancen zuwan Nusaiba suka hau shirin tarbarta. Ina zaune ina kallon su sai nan da nan suke yi, dambun shinkafa mai zogala da gyada suka yi, sai lemon chapman da ya ji lime and cucumber slices. Ni har mamakin yaushe Safra ta iya hada kayan 'yan gayu haka nake.

Sai da suka kammala duka suka shirya komai sai kawai na fashe da dariya. Duk suka dago suka kalle ni da mamakin dariyar tawa tunda ba a yi wani abun ban dariya ba. Ganin duk suna kallo na har Umma, ya sanya ni fadin
"Sai kuwa ta ce ta fasa zuwa, ko kuma idan ta zo ta ce ta koshi."

Umma ma dariyar ta yi tana sauraren sokana ta.
"Allah Ya ba ki lafiya Khairi."
Ta fada tana gyada kai. Safra da Sadiya kam speechless suka zama. Fuskar dai Safra ta nuna alamun takaici amma ba ta furta komai ba sai shigewar ta da ta yi daki.

Ba a wani jima ba sai ga kiran Haidar ya shigo wayata. Na faki idon Umma na ga ba ma ta ni take yi ba, sai na dauka.
"Nusaiba na waje, ta ce ki je ki shigo da ita ciki."
Kawai ya fada ba tare da ko sallamata ya amsa ba.
"Da kanki take son ki fito wai."
Ya sake fadi hade da yanke wayar.

Jilbaab na sanya har kasa tare da fada wa Umma zan je in shigo da Nusaiba ta iso.
"Da ba ki kira Sadiya ta je ta shigo da ita ba?"
"A'a Umma tunda sun riga sun shiga daki bari kawai in je. Tana kofar gida."

Na fice ban saurari me take fadi ba kuma.
Tun daga kofar gida na hangi motarsa daga can gefe, Nusaiba zaune gaban motar.
Muna hada ido ta sakar min murmushi, ta yi yunkurin bude motar amma sai na ga ta koma ta zauna. Hakan ya sanya ni takawa a nutse na isa inda motar take, ina kokarin janye idanuwana daga duban sa.

Bude motar na yi ina mata sannu da zuwa, fuskata dauke da murmushi.
"Je ki ciki Nusi. Ke kuma shigo."
Ya fada cikin bayar da umurni.
Babu musu na shiga bayan Nusaiba ta fito.

"Ina wuni?"
Na gaishe shi a hankali ba tare da na kalle shi ba. Jin shiru babu amsa ya sanya ni maimaitawa.
"Au, wai da ni kike? Ai ba ki kama suna ba, idan ma ba za ki kama sunan ba ai sai ki kalle ni don in tabbatar da ni kike."
Da murmushi na dago na kalle shin, shi ma murmushin yake yi sannan ya amsa.

"Ashe tare kuke, shi ne ka yi min wayo ko."
Yanayin yadda na yi maganar cike da shagwaba ban ma san na yi ba sai bayan ta fito na yi saurin dafe bakina ina dariya.

"Ban dauka tare za mu zo ba fa. An yi sa'a na je gidan ne ta roke ni in kawo ta. Daga nan kuma sai na zabi  in bagarar da ke. Shi ya sa na ce ki fito da kanki, ina son ganin ki kafin in wuce don babu tabbacin zan iya dawowa in dauke ta. Na so mu yi magana da Umma amma na bari har gobe idan su Salima sun iso."

Na daga kai ba tare da na furta komai ba.
"Ki ci gaba da yi mana addu'a kin ji? Allah na tare da mu. Ko yau din nan na tarar da Anti Khadija gidan, jikina na ba ni wata zugar ta koma yi, amma Allah Ya fi ta. In shaa Allahu komai zai daidaita."
"In shaa Allah."
Na maimaita cikin sanyin murya.

Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

13.8K 1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
224K 9.4K 25
"မောင် မဆိုးစမ်းနဲ့ကွယ်" "ကျုပ်ကိုမချုပ်ခြယ်နဲ့"
98.9K 6.5K 16
حسيت كل جسمي مات من الخوف ورجفه لزمتني شنو الي جاي يصير ياربي ماجاي يستوعب عقلي شنو الي أسوي راح اروح بالرجلين ! اباوع الة متمد گبالي وأگع شلون أگعد...
155K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...