DARE DUBU

Por PrincessAmrah

11.4K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... Más

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 25- Kiran Sirri

149 30 0
Por PrincessAmrah

Page 25

A ranar ko kadan ban runtsa ba, kamar yadda na yi wancan kwanan, to wannan ma haka na yi shi. Farincikina daya shi ne kubutar da Ummu za ta samu, tunda kudinta sun hadu, ina da yakinin watakila ma har ta koma gida. Sai kuma na hau tunani; ko Baba ne da kansa zai zo daukarta?
Yaya zai ji a lokacin da ya ganta?
Ummana, ya za ta ji idan ta ga Ummu ba tare da ni ba?
Wane irin hali za ta shiga?
Na dinga rera wani irin kuka, irin busasshen nan wanda babu hawaye cikinsa, tsaf hawayen sun gama soyewa a cikin zuciyata.
Haka na kwana babu mai rarrashi, har zuwa lokacin da gari ya waye aka aiko kira na.

Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, ina sakin hamdala domin dai na san ni ma watakila kudin nawa ne suka hadu, ko kadan ban kawo wa raina ba kubuta zan yi ba, sai dai, ko da muka isa mumbarin shaidan kamar yadda na yi masa lakabi, a fusace na ga fuskar Ogansu. Ya dube ni sau daya ya dauke kai, sannan ya ce
"Wannan matsiyaciyar yarinyar na gaji da ganin ta. Ku tafi da ita ku kakkarya min kafafuwanta, ko ku yi ta marin fuskarta har sai ta kurumce, ku dai nakasa ta kafin ku dora ta a hanyar gida, so nake ko da za ta koma ta dinga tunawa da mu, ba za ta ci mu a banza ba Wallahi."

Na dinga wata irin rawar jiki, bakina na ambaton sunan Allah, ban farga ba kawai na ji Zaki ya dauke ni daf, kamar karamar yarinya. Wasu mutum uku suka biyo bayanmu. Sai da muka isa inda baburansu suke, sannan ya hau wani, ya kira sunan Gadda cewa ya zo ya tallabe ni a babur dinsa, su kuma wadancan cikon biyun suka hau babur guda.

Mun yi tafiya mai nisa duk idanuwana a nade, kafin muka dakata, ya kashe babur din sannan suka sauke ni tare da warware bakin abin da suka kulle min idanuwa.
Hankalina tashe ina son tambayar su dalilin tsayawar a take kuma sai na samar wa kaina amsa, watakila a nan ne za su nakastanin da Ogansu ya ce su yi.
Ban gama dawowa daga tunanin ba na ji ya ja ni da karfin tsiya ya kutsa wurin wasu itace da ni, ihu nake da karfi saboda a daidai lokacin na fahimci inda ya dosa, so yake ya raba ni da mutuncina. Na dinga kuka da karfin gaske ko akwai mutanen kwarai da za su gittawa su zo su taimake ni, amma ina! Wannan shi ne ihunka banza, kuruwarka wofi! Wurin tsit yake sai kukan tsuntsaye.
Ina ju ina gani a daidai wannan lokacin suka shigi mutuncina, suka shige ni ta karfi da yaji, suka keta haddina.
Na yi kuka tun ina jin sautin kukan a cikin kunnuwana har na daina. Na ji zafi irin wanda ban taba jin ko kwatankwacinsa ba. Radadin da zuciyata ke yi kuwa har ya so ya zarce na azabar shiga ta da suka yi. Zaki na gamawa Rabson ya amsa, tun ina gane abin da suke yi, har na daina fahimtar komai, har zuwa sadda numfashina kawai ke shiga da fita amma babu abin da ke motsawa daga jikina. Kunnuwana suna ji, suna kuma daukar komai zuwa cikin zuciyata, sai dai ba zan iya wani katabus ba, sassan jikina duka sun tsaya da aiki.
Na ji sadda da karfi ya kwala kiran Zaki yana fadin
"Ka yi aiki da yawa, tun ban yi nisa ba fa yarinyar nan ba ta numfashi, da kyar idan ba ta mutu ba."
Da alama bai fahimci ina numfashin ba shi ya sa ya fadi haka.

Ban sani ba ko shi ma Zakin ya fahimci na mutu, na dai ji motsinsu sun tako zuwa inda nake, sannan na ji sadda wani ya dauke ni, amma tun daga nan ban kara sanin abin da ya faru ba, ban san ina suka kai ni ba har aka tsince ni, ban kuma san a wanne irin hali aka tsince ni ba.

***
Shin yaya aka yi aka kashe Ummu bayan kuma an biya kudin garkuwarta, kuma Ogansu da kansa ya ba da izinin kai ta madakata?
Me ya sa suka kashe ta?
Yaya aka yi ni da ba a biya kudin fansata ba Ogansu ya ce kar a kashe ni amma ita da aka biya nata sai aka kashe ta?
A wane wuri aka tsinci gawarta?

Zumbur na tashi zaune, me ya sa duk ban yi wannan tunanin ba sai yanzu?
Me ya sa tun a baya ban taba tunanin tambayar Baba ko Mama ba?
Ya kamata a yanzu in sani, ya zama lallai in sake bincike a kan wannan al'amarin; kar fa a je abin da nake tsammani ba shi ba ne, kar komai ya sauya daga nawa zargin.
Tabbas ina da bukatar sanin wasu abubuwa a yanzu, ina son ganin Baba, ina son ya amsa min wasu tambayoyi.
Sai dai kuna duk gaggawar asara ai ta jira samu. Dole ne sai na jira in gama da wannan assignment din sannan, don wallahi ba zan bar wannan maganar ba!
Matukar ba su Zaki suka kashe Ummu ba, to ya zama dole a gare ni in ci gaba da wani binciken har zuwa sadda zan gano komai.
Sannan ina da bukatar yi wa Shamsu wasu tambayoyi domin tabbatar da wadanda nake zargi su ne wadanda suka sace mu.

Washegari a makaranta na zauna jiran Shamsu, don a yau din nan nake son gane ko su waye, idan har ta tabbata su din ne, kenan aiki guda daya tal ya rage min, shi ne in tabbatar da wadanda suka kashe Ummu. Idan ta tabbata su din ne, shi kenan na gama aikina, sai kuma next assignment.
Amma idan lamarin ya sha bamban, ya zamana ba su ba ne suka sace mu, kuma ba su suka kashe Ummu ba, aiki ya dawo sabo dal.

Ina zaune sai ga Shamsu ya iso, da annuri a fuskarsa ya yi min sallama, tsananin kuncin da nake ciki ya sanya na kasa sakar masa fuska. Ganin kamar zai iya fahimtar wani abun ya sanya ni kirkiro murmushi na gaishe shi.

Mun dan yi hira sama-sama, kafin muka fada kan batun satar Aysha. Na shaida masa an sace kawata, me ya sa bai yi kokarin kubutar da ita ba?
Gyada kansa ya yi, ya ce
"Ba zai yiwu ba ne Feena, dole ne sai sun dauke ta tunda sun sanya wa ransu. Na fada miki ke suke hari, ina ta bakin kokarina ne wurin ganin ba su yi miki komai ba."

Na hau tunanin ta inda zan fara tambayarsa sunayen wasu daga cikin wadanda yake yi wa aiki amma sai na kasa. Ban san ta inda zan bullo masa ba. Can dai na nisa na ce
"Mene ne sunan Ogan kidnappers din? Don in tabbatar ko shi ne ya kira mahaifinta."
Ya dan yi murmushi,
"Su ai ba sa amfani da suna daya. Idan yau kin ji wani to gobe za su sauya ne. Amma dai asalin sunan wannan Ogan, shi ne Oga Rabe..."
Kwalkwal na kwalo idanuwa, tabbas su ne, tunda har sunan Ogan ya kasance ya zo daya, kenan sauran yaran ma duk su ne.
Ta tabbata dai wadanda nake zargin ne, hasashena ya tabbata!
Sai kuma fatan ya zamana su suka kashe Ummu. Zan samu tabbacin ne ta hanyoyi guda biyu. Hanya ta farko shi ne idan na samu bayanin da nake so daga wurin Baba ko Mama. Hanya ta biyu kuma idan na tabbatar da hakan daga bakin su Zaki; ina fatan Allah Ya ba mu nasarar kama su in ji daga gare su.

"Ya dai?"
Ya tambaye ni ganin yadda na yi shiru ina tunani.
Sai kuma na ji ya ja salati hade da dora hannu bisa kai.
"Na shiga uku!"
Ya furta bayan salatin.
"Lafiya?"
Na tambaya, a tunanina ko yana regretting fada min sunan ne, amma sai ji na yi ya ce
"Saurara ki ji...ba ki ji wata kara ba?"
Na kuwa kasa kunne amma ban ji komai ba. Can kuma sai ga karar, a hankali; wadda idan dai ba fada maka aka yi ba ba za ka taba jin ta ba. A hankali na ce
"Na ji, ga ta nan ma yanzu."
Bai sauke hannunsa daga bisa kai ba ya ce
"Neman gaggawa ake yi min, tunda har ake ta yin karar babu sassautawa. Ki tashi ki je aji kawai, bari in je in ji ko lafiya.
Ya tafin kuwa, ni kuma na bar makarantar ma duka saboda ba na cikin mood din da zan iya koyarwa, kuma ga headmaster da ba na jin zan iya daukar surutunsa a yanzu.

Washegari muka tashi da mummunan labarin kashe Mallam Shamsu, an tsinci gawarsa a can bayan azuzuwan makarantar, da alama ya kwana babu rai ma.

Sosai mutuwar ta dake ni, na ji zafi, na kuma fahimci kamar sun gane yana fitar musu da sirrika ne, ko kuma kila sun ji sadda muke hirar nan ta karshe da shi, shi ne dalilin yi masa wannan kiran na gaggawa, ashe ganin karshe ne na yi masa, ashe dukkan sirrikansu da ya fitar, ya sanar da ni, su za su zama silar mutuwarsa.
A take na ji wani irin hawaye ya zubo min. Wannan wace irin rayuwa ce?
Wace irin rayuwa muke ciki wadda rayuwar mutum take ba a bakin komai ba?
Allah Ya tsara komai, sai da na gama jin duk wasu bayanai daga gare shi sannan aka kashe shi.
Na yi kuka, irin wanda na jima ban yi irinsa ba.
Jin mutuwar Shamsu na yi har cikin zuciyata, sosai ta tsinka dukkan jijiyoyin jikina, ta tuno mini da mutuwar 'yar'uwata Ummu, na ji komai ya dawo min sabo dal, tamkar a lokacin ne aka yi komai.

A daki na wuni ranar, na kasa ci na kasa sha, alwalla kawai ke fitar da ni. A daki kuwa daga addu'a sai zurfaffen tunani, ina ji a jikina lokaci ya yi, lokacin da za mu tarwatsa kowa da komai, lokacin da za mu gama da duk azzaluman da ke lullube cikin dazukan yankinmu.

Bayan maghriba da kyar na iya fita, saboda ina son magana da Oga Ahmad, ina son na sanar da shi halin da ake ciki na kisan Shamsu.

Ko da na kira shi ya dauka, jin muryata kadai ya san ba lafiya ba. Cikin kidimewa yake tambaya ta ko lafiya amma sai na kara barkewa da wani irin kuka, kukan da na rasa wanda zan yi wa shi domin ya rarrashe ni.



Amrah A Mashi❤️

Seguir leyendo

También te gustarán

13.8K 1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
222K 9.3K 25
"မောင် မဆိုးစမ်းနဲ့ကွယ်" "ကျုပ်ကိုမချုပ်ခြယ်နဲ့"
806K 69.4K 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zaz...
191K 15.4K 42
story is starting with a business tycoon Vansh raisinghania and a middle class girl Riddhima. Vansh hates women because of his past and he wants a su...