DARE DUBU

Oleh PrincessAmrah

11.4K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... Lebih Banyak

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 21- Suspect

174 32 0
Oleh PrincessAmrah

Page 21

Da fita zan yi in tabbatar wa idona amma sai na zauna dai gudun kar a zargi wani abun daga gare ni. Ina jin yadda yaran ke tsorace da alama an saba yi musu allurar riga-kafin ne kuma suna jin tsoro sosai.
Na ji matar da suke kira da Inna Azumi ta ce
"Yara gara ma ku sanya wa zuciyarku salama don duk guje-gujen nan ba shi zai hana a yi muku allura ba. Kun fi kowa sanin halin mahaifinku, shi yake yi wa masu allurar ma masauki, sannan ya taya su shelanta wa mutane a kan su turo yaransu a yi musu allurar riga-kafi, to kuwa ta yaya za ku yi tsammanin za ku ketare ta?
Ko wancan karan dai ba yadda ban yi da shi ba a kan a rabu da ku ko dan Khalifa da ke ta kuka amma ya tilasta sai an yi din."

Haka dai suka dinga ce-ce-ku-ce da sauran matan, yaran kuwa ba su fita ba don na ji sun ce a nan masu allurar za su kwana sai washegari ne za a yi.

Mikewa na yi bayan na yafa mayafina, ina da bukatar yin magana da Oga, don haka na gaggauta fita ba tare da ko tanka wa matan da ke tsakar gidan ba na fice zuwa wurin dutsen yin waya.
Tun kafin ma in isa wurin dutsen idanuwana suka shiga cikin na Sagir, shi din dai ne sanye da fararen kaya irin na malaman asibiti masu yin allura, sannan ga wasu su uku ma daban duk da irin kayan, hannuwansu rike da wasu manyan robobi da ke dauke da kayan aiki.
Bai ko nuna alamar ya gan ni ba ballantana ya nuna ya san ni, ni ma din kuma haka, na fauze kawai hade da fiddo wayata na latsa kiran Oga.

Bayan ya dauka, ba mu ko gaisa ba ya ce
"Sagir ya iso, ya zo a yanayin da ba ki fahimta ba ko? Na san haduwa da shi za ta yi miki wahala amma mun riga mun gama tsara komai. A makarantar da kike aiki za su yi nasu aikin su ma. Ki fita da wuri, idan kin je shi zai yi abin da ya dace. Dukka aikin da zai yi ba zai wuce na kwana biyu ba zai koma Meshe, in ya so a duk sadda kike da bukatarsa sai ya dawo. Na yi tunanin duk wasu hanyoyin da suka dace ne amma babu mai bullewa saboda Aysha da ke hannunsu, a yanzu kusan komai muka yi za su iya dago mu, amma ina da yakinin wannan hanyar, ba za su iya gane komai ba.
Ki je kawai, ki kuma kwantar da hankalinki."
"Okay Sir. Na gode."

Daga nan na koma cikin gidan ina gayyato wa kaina karfin halin da ba na tattare da shi ko alama.

Washegari kuwa da wurin na shirya, ko tsayawa karyawa ban yi ba na goya jakata kawai na fice zuwa makaranta.
Da ma kuma makarantar ba wani tsari gare su ba, tun daga kan malamai har daliban ba su zuwa da wuri, wannan ne ya ba mu damar ganawa da Sagir da wani daga cikin ma'aikatanmu da ban ma san shi ba, da alama a wani garin yake aiki ba cikin Katsina ba. Sai kuma mutum biyu ma'aikatan lafiya daban.

"Hankalina ya tashi sosai Oga Sagir, tun da na ji zancen satar Aysha na gaza aikata komai face tunani."

Ya saki murmushi ya ce
"Everything is going to be alright. Ke da kike jami'ar tsaro kina karaya to ina ga sauran civilian kuma? Sai kin dake fa, wannan din ba komai ba ne. Duk abin da ake son a samu nasara dole ne sai an sha gwagwarmaya kafin a dace. Yanzu dai duk ba wannan ba, ba mu da isasshen lokaci.
Oga ya ce in fada miki kar ki yi wasa da yawo da cellular phone dinki ta aiki, sannan ki dinga ajewa a inda kika san za su yi wahalar gani. Kamar har da sakaci ne ya sanya suka yi saurin gane akwai makamai a jikin Aysha. Wannan 'yar bindigar da ba ta wuce ta sanya ta cikin pant ba ta yaya za ta bari har a gane akwai ta jikinta? Abun akwai daure kai.
To ke sai kin kula sosai dan a yanzu ke ce kadai hope dinmu, muna kuma kyautata zaton za a dace din.
Ki kara shiga jikin Shamsu, so muke mu gane kaf informers din garin nan, kuma ta hanyarsa ce kawai a yanzu nake da yakinin za mu gane din tunda ya riga ya fara ma.
And lastly, ya ce ki daina zuwa neman network idan za ki yi waya da shi, just use your cellular phone za ki samu service a duk inda kike, ki kira shi idan akwai wata matsala, ba dole sai kin tura masa komai ta whatsapp ba tunda shi dai dole sai da service mai kyau."

Daga nan ya bude jakarsa ta goyo, sai ga wata katuwar leda ya ba ni, ya ce
"Wannan kuma sako ne inji shi Oga Turaki, ya ce a ba ki."
Murmushin da ya shimfida a saman fuskarsa ba karamin mamaki ya ba ni ba. Na so tambayarsa dalili sai kuma na kyale shi kawai tunda a yanzu duk ba ta wannan muke ba.
Har na juya zan tafi ya kira sunana.
"Idan akwai wata matsala ni ne mutum na farko da za ki kira, gobe za mu gama aiki a nan zan koma Meshe, zan jira ki a can tare da wasu daga cikin ma'aikatanmu. Don ke na zo, kar ki yi kasa a guiwa wajen sanar da ni dukkan damuwarki."

Na jinjina kai hade da barin wurin, a lokacin wasu daga cikin dalibai sun fara zuwa, amma babu malami ko daya, headmaster ma da ya kasance shugaba bai zo ba.

Ledar da aka kawo min na bude jaka da nufin in tura amma saboda girmanta ya sanya ba ta shiga ba, ga shi kuma ba na son budewa a gaban mutane saboda tsaro. Dogon hijabina da ya cika jakar na ciro na sanya a jikina, cikin sa'a ina tura ledar tsaf ta shige.

Na ci gaba da kallon yadda iyayen yara suke taso yaransu gaba domin a yi musu allura, na kara jinjina wa Maigari, domin kuwa jajirtaccen mutum ne mai son ganin al'ummarsa ta tsaftace, sai dai bai sani ba yana gini ne ana lalata masa foundation, kuma daga cikin gidansa ma.

Cike da gwanancewa su Sagir ke yi wa yaran allura, kodayake mutum biyu daga cikinsu ma'aikatan asibitin ne na gaske, Sagir da wani daya ne ma'aikatanmu.
Har kusan azahar ana yi kafin suka dakatar da zunmar sai gobe kuma a ci gaba.
A lokacin ne ni ma na koma gida.

Babbar ledar na bude bayan na jawo ta daga cikin jaka, kayan makulashe ne kala-kala, irin su dangin cake, biscuits, da kuma chocolates kala-kala, wasu ma ban taba ganin irinsu ba.
Sai kuma ga wata takarda da babban baki an rubuta;

GOOD LUCK. WISHING YOU NOTHING BUT THE BEST.

Na saki murmushi ina kara dudduba sauran kayan masu tarin yawa, ashe shi ya sa ledar take da girma tulin kaya ne aka shaka mata.

Tabbas Oga ya san idon gajiyayye; jiya-jiyan nan nake zancen ba ni da sauran abin da zan ci dole yau in fara fita ina saye, sai ga shi Allah Ya ji kaina na samu har ma da dorin abin da da ba ni da shi.
Na fasa chocolate din max na fara sha ina jin matukar dadinta. Sannan na fitar da guda biyu na ajiye wa yaran Amarya su ma su sha, ina ganin kirkinta da yaranta sosai.
Kuma ina kyautata zaton in dai aka kara kwana uku ban tabbatar da wace ce informer din kidnappers ba, to zan bugi cikin Amarya, watakila cikin hikima zan iya samun wani bayani daga gare ta, musamman kuma a kan Inna Azumi da ta kasance number one suspect dita.

Ina cikin sha kuwa sai ga ta ta shigo, ta yi min sannu da zuwa na amsa, sannan na mika mata chocolates din guda biyu na ce ta bai wa su Farida. Kai tsaye ta ce in bar shi wallahi tunda ta lura ban saba da irin abincinsu ba, ba ci nake ba, kayan makulashen ne kadai abincina.
Ni kuma na dage a kan lallai sai ta karba ba ita na ba ba yara na ba. Ta yi murmushi gami da godiya sannan ta karba.

Sai da aka yi kwana biyu ina kasa kunnuwana ba na jin motsin fita, Sagir ma har sun gama aikinsu sun tafi, da dare ina rike da wayata sai kawai na jiyo takun nan dai da nake da bukatar ji. Na tashi a hankali tare da fara takawa, har sai da na tabbatar da ta fita sannan ni ma din na fita, yau ba na jin akwai wata magana ko wani abu da zai firgita ni wanda zai hana ni tsayawa ganin ko wace ce, so nake ita ma din ta gan ni, tunda already sun san ko ni wace ce.

Sai dai abun mamaki, ko da na kasa kunnena sai ji na yi wani na fadin,
"Wallahi yarinyar nan ta tsorata mu fa. Duk a zatonmu jami'ar tsaro ce, amma mun ba ta duk wani tsoro, mun zare idon, duka dai magana guda ce, wai mahaifinta ya ba ta bindigar nan da karamar wuka saboda tsaro, don ya san yadda yanayin yankin nan yake. Da fari ban yarda ba amma ganin duk dukan da Fati da Kausar ke yi mata ta kafe a kan maganarta guda ya sanya na gamsu hakan ne. Saboda a duk jikinta bayan wadannan makaman guda biyu, babu wata shaida da za ta tabbatar mana akwai wani dalilin zuwan ta garin nan baya ga bautar kasa. So yanzu mun samu sassauci, gobe ma za mu karbi lambar wayar mahaifin nata mu kira shi, idan yana son 'yarsa ya fiddo kudi, don da alama za a samu matsiyatan kudi a wurin iyayenta."

Suka kwashe da dariya. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sosai na ji dadi har da guntun murmushi na yi. Tabbas babu abin da ya fi karfin addu'a, na sani har da addu'a da muka dage da ita ya sanya lamarin bai cabe mana ba kamar yadda muka yi tsammani.

"Ina kayan abincin da za ki saya? Kin san lamarin yana neman gagararmu, fita ta yi wuya saboda barazanar da gwamnati ke yi mana, duk da ba lallai ba ne ta iya din."
Ban ji abin da ta fada ba sai godiyarsu kawai da na ji.

Na taka a hankali na koma wajen bandakin da ke da 'yar tazara zuwa kofar. Ina tsaye daga jikin katangar na hange ta ta taho, kamar kullum, yau ma fuskarta rufe da kallabinta, ta ci gaba da sanda, ba ta lura da ni ba har sai da na dan yi gyaran murya, ai kuwa ta tsorata matuka, da alama jikinta rawa yake saboda akwai hasken farin wata, kuma ya haska min dukkan jikinta, face fuskarta kawai da take kudundune da kallabi.

Babu tsoro ko diso na karasa inda take, ban ce komai ba sai kallabin nata da na janye, da karfi na sanya hannuna na daga fuskarta, idanuwanta cikin nawa da nake bin ta da wani irin kallo, irin wanda ban taba yi wa wani mahaluki irinsa ba.




Amrah A Mashi❤️

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

191K 15.4K 42
story is starting with a business tycoon Vansh raisinghania and a middle class girl Riddhima. Vansh hates women because of his past and he wants a su...
43K 3.6K 37
"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki..... "ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin...
11.1K 72 15
está es una historia donde nos demuestran que el amor no tiene límites te vas a enamorar de un mafioso? no importa en esta historia te lo demostrarem...
224K 9.4K 25
"မောင် မဆိုးစမ်းနဲ့ကွယ်" "ကျုပ်ကိုမချုပ်ခြယ်နဲ့"