DARE DUBU

Af PrincessAmrah

11.6K 1.6K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... Mere

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 19- Kura Da Fatar Akuya

164 31 0
Af PrincessAmrah

Page 19

Da dare ya yi yau kuma sai bacci ya sace ni ba tare da na yi aune ba, ballantana kuma Aysha da ta kwaso gajiya kuma da ma ita bacci gare ta sosai.
Wannan dalilin ne ya sa ba mu sani ba ko an sake fita ko kuma ba a fita ba. Sai gabanin sallar asuba na farka, a lokacin biyar saura. Na tashi na bude wasu documents da aka tura min daga Office, dukkansu wasu assignments ne da aka taba yi wadanda suke da kamanceceniya da nawa. A hankali nake dubawa na ga irin gwagwarmayar da aka sha kafin daga baya a yi nasara. Na bude wani, shi ma dai kusan hakan ne amma shi an yi failing don har ma'aikacinmu aka kashe, amma daga baya an sha gumurzu don wannan kisan shi ya balle komai aka kama duk masu laifin.
Gabana ne ya dan fadi, sai kuma na yi gaggawar gayyato wa kaina karfin hali ina tuna yadda komai ke zuwar min da sauki, duk da har yanzu babu wani takamaimai suspect tunda ban gane ko wace ce a gidan ba. Sai dai na sani tunda har akwai din, sannu a hankali zan gane ta.

***
Kwanaki suka ci gaba da tafiya har muka cinye wata daya ba tare da komai ya faru ba, duk da koyaushe cikin dari-dari muke, don Oga ya fada mana a kowanne lokaci muna iya jin an sace mu, duk da ba fatan haka muke a yanzu ba har sai mun tabbatar da suspects din namu sannan.

A makaranta muna kebe ni da Mallam Shamsu, don a tsayin lokacin nan wata irin shakuwa ce ta kullu tsakaninmu tamkar mun shekara da sanin juna. Ya fada min yana so na sai dai ban amince masa ba har yanzu jiran amsata yake yi, ni kuwa irin abun nan ne sai na gama wana shi, ta yadda ba zai ketare duk wani zabi ko umurnina ba.

Ya dube ni ya ga wayata nake latsawa, sai ya yi yunkurin fizgewa amma na yi gaggawar tamke ta tam a jikina. A take na daure fuska, don duk shirina da mutum ban yarda ya ce zai karbi wayata ba, ballantana kuma wannan da yake cikin wadanda nake zargi.
Ganin na daure fuska ya sanya shi fadin
"Ki yi hakuri idan na yi laifi."
"Kar ka sake yi min irin haka in dai kana so mu shirya. Ba na so."

Ya yi gajeren murmushi,
"To shi kenan 'yan matana, ba zan sake ba in shaa Allah. Ki yafe min."

Na jinjina kai alamun na hakura. Ya ce
"To ki yi murmushi mana."

Murmushin kuwa na yi hade da kallon shi.

"Wai ni kam har sai zuwa yaushe ne zan samu amsata? Na yi hakurin, na jira amma har yau dai ban ji komai ba. Ba ki san yadda nake ji ba ne Safina, komai zai iya faruwa idan aka wuce yau ban samu amsata ba."

Na dan sunkuyar da kaina irin alamun kunya.
"Kafin in ba ka amsa ni ma akwai alfarmar da nake nema a wurinka."
Na fada ina karantar yanayinsa.
"Aikin nan da na taba jin kana fada wa su Mallam Abu kana samun kudi da shi, nake so ni ma a dora ni a kai."

Idanuwa ya bude alamun mamaki. Na gane ya tsorata ainun da maganata, kuma da ma abin da nake so kenan. Sai na sake maimaitawa idona na kansa.
"Idan kuma ba zan samu ba shi kenan."
Da wata irin murya na fadi haka, muryar da ni kaina ban taba tsammanin ina da irinta ba.

Cikin rawar murya ya ce
"Wannan aikin namu mai wahala ne...ba za ki iya shi ba Safina, ba irin aikin da ya kamace ki ba ne."

Na yi kokarin boye mamakina na ce
"Kamar yaya ba zan iya ba? Kallon ragguwa kake yi min ko me?"

Ya gyada kai,
"Ba haka ba ne. Kawai dai..."
"Kawai dai me Shamsu? Me kake nufi?"

Sai da ya dan waiga haggu da damansa, ya tabbatar da babu kowa da zai iya jin sa sannan ya ce
"Aiki ne mai matukar hatsari, ni ma kaina a tsorace nake da shi, sam-sam babu kwanciyar hankali a cikinsa."

Sai a yanzu ne na tabbatar da zargin da nake yi a kansa, da alama shi ma informer ne, ta wannan hanyar ce yake samun kudi bayan albashinsa.

"Kai kuwa wane irin aiki ne da kai kanka ba ka da kwanciyar hankali da shi amma kuma kake yi?"

Ya sake waigawa, sannan ya juyo ya ce min
"Ki bar maganar nan kawai Feena, ina gudun kar in fada miki wani abu ya same ki, don ko a yanzu ma harinki ake yi, ni ne nake ta kokarin kaucewa saboda son da nake miki. Shi ya sa kika ga jiya ina tambayarki yaushe za ki tafi, ba na so wani abu ya same ki saboda son da nake yi miki."

Na ci gaba da bin sa da kallon mamaki, ganin yadda zufa ta wanke shi a take, duk da iskar daminar da take kadawa.

"A yau din nan ko gobe ake harin sace ko ke ko 'yar'uwar can taki Zainab. Ke aka so a dauke na ce a bari sai kin tafi kin dawo don akwai wani zargi da nake yi game da ke. Amma ita matar gidan da kike, ta ba su tabbacin ba yanzu za ki tafi ba wai ta ji kin ce sai bayan sati biyu."

Na dafe kaina ina ci gaba da kallonshi,
"Ya aka yi ka san duk wannan abubuwan? Kar dai..."
Na dinga nuna shi da yatsa, ina son ya gane mamakin da maganganunsa suka saka ni, saboda kar ma ya darsa wani zargi a kaina, duk da na fahimci soko ne, ga kuma tsananin kauna ta da yake yi, wadda da alama ita ce ta yi tasirin da har ya kasa boye min sirrinsa.

"Yau zan fada miki wani sirri, saboda tsananin kaunarki da nake yi, na kuma yarda da ke, na tabbata ba za ki taba fitar min da sirri ba. Amana ce na ba ki ki taimaka ki rike min ita."

Na jinjina masa kai, ya ci gaba da cewa
"Akwai wadanda nake yi wa aiki a boye. Amma har ga Allah, asali ba da son raina ba ne, ba ni da zabin da ya wuce hakan ne. Kafin kuma daga baya na gamsu eh hanya ce da zan bi in dace."
Ya dan yi shiru yana son ci gaba, amma da alama zuciyarsa cike take fal da tsoro, ya juya ya ga babu kowa da ke kusa da mu, kafin ya ce
"Kidnappers din da ke addabar kauyukan Katsina da Zamfara, ina daya daga cikin masu kai musu boyayyun bayanai."

Na zabura, zabura kuma har cikin zuciyata. Wace irin yarda ce ya yi da ni da har yake fada min wannan zancen mai matukar nauyi?

"Na san dole za ki yi mamaki jin da ni ake hada baki ana zalunci, sai dai kar ki manta, da dan gari ne aka ci gari.
Kamar yadda na fada miki da farko ba da son raina na yi aiki da su ba face kokarin ceto rayuwata daga kangin mutuwa.
A wata rana ne muna aikin gona aka zo har inda muke aikin aka sace mahaifina da wasu tsirarun mutane, mu biyu aka bar mu saboda mu isar da bayani ga mutanen garinmu. Hankulanmu sun tashi sosai saboda kudin da aka nema ba mu da su. A karshe ma sai suka sayar da su ga wadanda ke can wuraren jihar Niger, su kuma suka ninka adadin kudin da za a bayar.
Kwatsam wadannan na yankinmu sai suka bukaci ganawa da mu, cike da tsoro da fargaba muka same su har cikin dajin wuraren Meshe, muka tattauna da su sosai, a cikin tattaunawar ne suka ce idan har muka ba su hadin kai to za su biya kudin fansar iyayenmu a sake su.
A lokacin wani bargon farinciki na ji ya lullube ni, ni dai babban burina shi ne a sakar min mahaifi, wanda bai da ko wadatacciyar lafiya ma.
Suka ce muna da zabi guda biyu.
Ko dai mu dinga sanar da su abubuwan da ake ciki a kauyenmu, ko kuma mu bari a kashe mana iyaye.

Ban hangi munin da abun zai iya yi a gaba ba sai kawai na amince, shi ma wancan gudan ya amince, sai kuwa aka sakar mana iyaye bayan kwana biyu kacal. Daga nan muka fara wannan mummunan aikin tare da su.
Sun gargade mu kan cewa duk ranar da muka yi kuskuren fitar da zancen nan za su kashe mu, sannan su kashe iyayen namu, su kashe duk ahalinmu ma.
Gani nake yi ai wannan ba komai ba ne, na amince muka ci gaba da aiki har zuwa lokacin da suka fara biyanmu makudan kudade, musamman idan muka fada musu wani abu mai muhimmanci.
Tun ina kin abun har na fara so, ganin na tsira da raina, sannan mahaifina ma ya tsira. Ga kuma kudin da nake samu masu tarin yawa.

Wannan shi ne mafari, kuma ire-irena muna da yawa a garin nan, don wallahi duk wanda aka sace a garin nan to da hadin bakin wani informer ne.
Ba zan boye miki komai ba, ni kaina nan mutanen da aka sace ta dalilina suna da yawa, wasu ma ba 'yan garin nan ba ne. Dalibai kuwa sun kai goma ko ma fin haka. Akwai wasu fa bayan ni, za mu iya kai goma ko ma fin hakan."

Lallai fa da gaske da dan gari ake cin gari. Yanzu duk wannan abin da ake yi, da abubuwan da suke faruwa a garuruwan jihar Katsina da Zamfara, kenan duk da hadin bakin mutanenmu ne?
Na yi mamaki kwarai, ban kuma gama dawowa daga duniyar mamakin ba na ji ya ci gaba da cewa
"Akwai irinmu da yawa fa, wasu ba za ki ji su a bakina ba. Kawai dai ki bi a hankali, sannan so samu gobe ko jibi ki bar garin nan. Zan zo har gidanku in nemi aurenki. Don idan kika dawo nan da sunan matar aure, babu wanda zai taba ki, musamman kuma matata."
Ya karasa maganar yana dariya.

Da a ce ya san wani irin munin fuskarsa da nake gani a yanzu da tabbas ba zai yi min wannan murmushin ba.
Shin ta yaya ma kasarmu za ta zauna lafiya?
Ta ina za a iya samun saukin wadannan mugayen mutanen bayan lullube suke da mutanen cikinmu?
Wannan shi ake kira kura da fatar akuya.

"Kar ki bari ki kara kwana biyu a garin nan. Da ma ina ta Neman hanyar da zan fada miki amma ban san ta inda ma zan fara ba. Ba na so wani abu ya same ki,  ba zan so a kai ki wannan mugun wurin ba."

Ya maimaita min cikin yanayin damuwa.
To ni me ma zan ce masa kuma?
In ce masa ba zan tafi ba har sai na kammala aikin da na zo yi?
Ko kuma fada masa zan yi ba za su iya yi min komai ba?

Na hadiyi yawu mai daci, cikin daburcewa na ce
"Zan tafi, zan koma in yi tunani a kai."
Kawai na mike hade da barin wurin, zuciyata sai bugawa take da sauri, ba wai tsoro nake ji ba, zallar mamakin abin da kunnuwana suka jiye mini ne.
Lallai mutum mugun icce!



Amrah A Mashi❤️

Fortsæt med at læse

You'll Also Like

239K 9.9K 25
"မောင် မဆိုးစမ်းနဲ့ကွယ်" "ကျုပ်ကိုမချုပ်ခြယ်နဲ့"
191K 15.4K 42
story is starting with a business tycoon Vansh raisinghania and a middle class girl Riddhima. Vansh hates women because of his past and he wants a su...
45.1K 2.2K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...
19.5K 1.7K 100
labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa.