DARE DUBU

By PrincessAmrah

12.7K 1.6K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 17- Headmaster

192 28 0
By PrincessAmrah

Page 17

Na maimaita kalaman da na jiyo daga bakinta, don tun daga wannan ban kuma sake mayar da hankali in ji abin da suke fadi ba. Na dai samu bayanin da nake so, wato ko ma wace ce wannan matar, a nan gidan take, sannan tana da alaka da 'yan garkuwa da mutanen da ke kauyen, uwa-uba ma ita ke ba su bayani, irin wadanda ake kira da informers.

Da ma jikina ya ba ni tabbas akwai mai yi wa maigari zagon kasa, don daga yanayin kalamansa na jiya na fahimci akwai wata a kasa, akwai munafukin da ke jikinsa sosai wanda kuma shi ne yake isar da sakon gare su.

Jin alamun za ta tafi ya sanya ni gaggauta tafiya, ina rufe kofar dakin tana shigowa gidan, kiris ya hana ma da ta gan ni. Na gode wa Allah da ba ta gan ni din ba.
Na koma makwancina ina ta aikin sauke ajiyar zuciya. Ya zama dole gobe da sassafe in yi magana da daya daga cikin ma'aikatanmu, so samu ma Oga Ahmad. Na san idan na samu network duk sakunan da na tura masa ta whatsapp za su je masa. Don haka da safe abin da zan fara yi kenan, in je wurin dutsen nan tunda an ce kofar gidan maigarin ne ba ma da nisa ba.

Wannan dare dai haka na cinye shi babu bacci, kodayake da ma ba baccin na zo yi ba, aiki na zo yi wa kasata, don haka dole ne in jure, in cire komai in yi abin da ya dace.

Da sassafe sai ga koko da kosai wai inji maigari. Na karba da godiya don ba zan iya cewa a bar shi ba, kuma ba zan ci ba tunda haka dokar aikinmu ta tanadar mana. Ba a jima ba kuma sai ga Amarya ita ma da nata kwanon na dumamen tuwo. Sai ga sauran matan maigari biyun kowacce da nata langar kuma abinci ne a ciki. Na ji dadi kwarai saboda yadda suka karrama ni, da ma an ce mutumin kauye akwai karamci.

Jakata ta goyo na bude na ciro cake din leda da lemu, ban bari kowa ya gani ba saboda yaran ma duk ba su nan, Amarya kuma ta fita can wurin kishiyoyinta. Na ci cake dina da lemo na koshi sannan na tattara wadancan kwanukan sai da daya daga cikin yaran Amarya ta shigo na ba ta na ce ta fitar na koshi.

Towel dina na wanka na daura tare da zuba doguwar hijabi na dauki kayan wankana. Ina fitowa Amarya da azamarta ta je ta zuba min ruwan wanka don da ma ta riga ta dora. Har bandakin ta je ta dan wawwanke shi sama-sama sannan ta ce in shiga. Sosai na ji matar ta shiga raina, tana da matukar kirki da karamci, ya ita ya mijinta.
Sai dai har ita din ban yarda da ita ba, aikinmu babu yarda a cikinsa ko kadan.
Na yi mata godiya sannan na je na yi wankan.

Bayan na shirya na sanya kayana na NYSC, na dan yafa farin mayafi sannan na fito na yi musu sallama cewa zan tafi makarantar da aka tura ni.

"Kin san makarantar ne ko in sa Farida ta raka ki?"
Amarya ta tambaye ni tana goge hannunta bayan ta ciro shi daga bokitin da take wanki.
"A'a gaskiya ban sani ba sai an raka ni. Amma kafin nan zan tsaya a gaban dutsen can in yi waya da 'yan gidanmu sannan in wuce."
"To shi kenan. Kafin ki gama za ta jira ki kofar gida."
Na yi mata godiya sannan na fice.

Cikin sa'a kuwa ina isa na kunna DATA sai ga sakuna sun fara shigowa, na yi hamdala don ba karamin dadi na ji ba.
Na latsa kiran Oga Ahmad, bayan ya dauka na gaishe shi cikin girmamawa ya ce
"Ina cikin ganin sakunanki da ke shigowa kenan kika kira ni."
Na amsa da
"To bari in jira har ka duba Yallabai. Don kauyen ne babu service sai an je wurin wani dutse. Kuma yanzu haka na fito ne zan tafi makaranta."
"Haka ne, na sani ai. Ko kin manta duk sai da muka binciko komai kafin ki je?"
Murmushi kawai na yi, kit ya kashe kiran.
Daga nan na kira Umma muka gaisa, ta sake yi min fatan alkhairi sannan na kira Mama, ita ma addu'a ta yi min sosai muka yi sallama.
Sai na kara samun wani irin kwarin guiwa. To wanda ke tare da addu'ar iyaye me zai bata masa rai har ya tsorata?
Na saki murmushin jin dadi. Sai kuma na tuno da Anti Maryam, na latsa kiran ta ita ma.

"Habawa Khairi, amana ba ta ce haka ba."
Ta fada bayan ta daga wayar.
Da murmushi na ce
"Na karbi laifina Anti Maryam, a yi hakuri a yafe ni."
Ita ma murmushin ta yi,
"Shi kenan to tunda ma har kin san laifinki."
"Laifuka dai za ki ce Anti Maryam,"
Na fadi ina dariya.
"To yanzu dai kin san babban laifinki? Wai har ki yi tafiya ban sani ba. Kuma na tambayi Umma ta ce ita ma kanta ba ta san takamaiman inda kika je ba. Ai da sai a mana sallama ko kanwata?"

Ya za a yi kuwa in fada mata zan yi ta tafiya? Ko Ummata ta dai san zan yi tafiyar amma ba ta san inda zan je ba. Komai namu na sirri ne da rashin yarda, ba kuma wai ana koyar da mu rashin yarda da iyaye ba ne, ana gudun kar ka sanar da su su ma kuma su sanar da wasu, daga nan sai a lalata mana aiki. Kodayake, wasu iyayen ma kansu ba abun yarda ba ne ballanta a aiki irin namu wanda yake aikin sirrin da ko a tsakanin junan namu ma ba kowa ba ne yake sani.

Hakuri na sake ba ta sannan muka yi sallama na yanke wayar. Muna gamawa sai ga kiran Oga Ahmad ya shigo, kafin in ce komai na ji ya ce
"Babu bakon abu a wurina UmmulKhairi, kusan duk abin da aka fada miki na ji shi jiya bayan tafiyarki, don bincike na sake yi sosai kuma ina jira ki nutsu ne da ma mu sake magana.
Yanzu dai ki cire duk wani tsoro da zai iya darsar miki, ki kwantar da hankalinki. Aysha za ta zo gobe ko jibi, tare za ku yi bautar kasar. Sannan Sagir ma zai zo, amma shi ba yanzu ba, sai mun ga gudun ruwan abun.
Abu daya da nake so da ke shi ne, da kanki kadai za ki yarda, har ita wadda kike dakin nata kar ki aminta da ita..."

"Yawwa Sir..."
Na katse shi,
"Ina da suspect a cikin gidan maigarin ma."
Gajeren murmushi ya yi,
"Na san za a rina ai, shi ya sa na dinga maimaita miki don't trust anyone. Da kanki kadai za ki yarda Khairi. And about the suspect, kar ki yi magana kawai ki share, tsakar dare ki rubuto min komai, sannan you have to be very careful, ki yi taka-tsan-tsan, idan Aysha ta zo ki san da kalar yaren da za ku dinga yin magana. Ban ce ku yi Turanci ba. Da Hausa za ku yi, amma ku kiyaye harshenku."
"Okay Sir, in shaa Allah."
"Ki je ki yi aikinki, inda duk ya shige miki duhu ki tuntube ni, sannan idan wata matsalar ta taso, use your office cellular phone ki kira emergency call, ma'aikatanmu da ke Meshe za su kawo miki agaji, because they are at your service."
"Thank you Sir. In shaa Allahu alkhairi zai faru. Za mu yi komai mu gama good and sound."
"Allah Ya sa."
Ya fadi hade da yanke wayar.

Magana da shi ta kara min kwarin guiwa kamar wanda na samu bayan gama waya da Ummana da Mamana.
A hankali na tako zuwa kofar gidan inda yarinya ke jira na.
A hanya sai tufka da warwara nake yi, tunani kawai nake yi ta yadda matar gida za ta ha'inci 'yan gida, har ma da 'yan garinsu, a hada baki da ita don a cuce su.

Na dubi yarinyar da ta rako ni, da annuri a fuskata na ce
"Babu nisa ne makarantar?"
"Eh an kusa."
Ta fada tana nuna hanyar da hannu,
"Daga an sha kwanar can shi kenan an zo."

Tambayar da nake ta son yi mata ce na yi karfin halin yi,
"Wai kuwa in tambaye ki Farida, Yayanku da aka taba sacewa aka kashe shi, mahaifiyarsa tana gidanku ko ba ta nan?"

Ta dan tabe baki ta ce
"Mamansa ta rasu an ce tun yana dan yaro kamar ni. A hannun Inna Azumi yake."
'Inna Azumi.'
Na maimaita a cikin zuciyata, a zahiri kuma na ce
"Wace ce Inna Azumi?"
"Ita ce babba duka a gidan."
Ta ba ni amsa cikin halin ko'inkula.
"Yaranta nawa ita? Duk suna gidan su ma?"
"Ba ta taba haihuwa ba fa. Yayan nan namu ne dai take riko, wasu ma duk sun dauka danta ne. Ba ki ga yadda ta sha kuka ba sadda aka sace shi. Da aka tsinci gawarsa kuwa har da suma ta yi."

Sosai maganar tata ta ja hankalina, zuciya mai sake-sake, sai ta hau saka min wani al'amari. Kuma tun daga nan sai ban sake cewa komai ba, har muka karasa makarantar.

Azuzuwan makarantar duka ba za su wuce guda goma ba, sai offices guda biyu daga gefe sai bandaki ma guda biyu.
Kai tsaye office din da aka ce min na headmaster na nufa, na same shi wani kazami da shi kayansa kace-kace babu wanki, kansa a cukurkude ga uwar datti kamar ya shekara bai wanke ba.
Na gaishe shi ya amsa ba tare da ya kalle ni ba, sai dai jin murya ta ya sanya fuskarsa cika da mamaki, da alama ya yi mamakin gani na tunda an ce an dan jima ba a samu masu bautar kasa zun zo ba.

"Hajiya daga ina?"
Ya fada cikin sigar rainin wayo irin na zo makarantar da yake shugabanci.

"Daga cikin garin Katsina nake, an turo ni ne bautar kasa a makarantarka. Ga takardar..."
Na mika masa takardar da aka ba ni daga can NYSC camp din Katsina.
Ya karba ya duba, ya yi min 'yan cike-ciken da ya kamata sannan ya mayar min.
"Za ki koyar da 'yan aji biyu, aji uku, aji hudu, aji biyar, aji..."
Na zaro ido ina kallon sa, da alama so yake ya jibga min aikin da ba a yi a makarantar. Ban ko jira jin sauran bayanin nashi ba na ce,
"Duk yaya zan yi da wannan aikin Mallam? Ai ya yi yawa."

Ya tabe baki yana rubutunsa a wata tsohuwar takarda da duk ta yage, biron ma kanta ta tsufa har ta gaji ruwan cikinta saura kadan ya kare.

"Idan ba za ki iya ba kina iya komawa daga inda kika fito. Ai ba a ce miki muna da rashin ma'aikata ba."

Kamar in ce to idan ba rashin ma'aikatan ba me zai sa a kila min wannan uban aikin? Sai kuma na yi shiru ina kallon sa. Da alama mutumin zai yi wuyar sha'ani.
Ya dauki hularsa ya karkata a saman kai, sannan ya dago kai ya dube ni. Na dan runtse idona ina mamakin wane irin mutum ne wannan, sai kawai gani na yi ya sakar min murmushi, ya hau kallo na tun daga sama har kasa, kafin ya dan sude lebensa ya ce
"Ke za ki zabi ma ajin da za ki koyar. Kina iya zamanki ki huta ma ba sai kin koyar da komai ba tunda daliban namu ba wani yawa ne da su ba."

Gyada kai kawai na yi ina al'ajabin mutanen zamanin nan. Yanzun nan yake batun jibga min aiki, a yanzu kuma har ya canja shawarar in zauna in huta idan ba ni da bukatar aikin.



Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

22.8K 203 17
Shay protects a girl who has piercing red eyes from people who try to use her for her power to heal the sick and injured and to keep her from falling...
157K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...
15.7K 1.1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
857 65 13
Labarin soyayyar Aaliyah Badamasi Bulama da Sa'eed Aliyu Modibbo a shekarun 80's...