DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 12- Samu da Rashi

161 22 0
By PrincessAmrah

Page 12

Washegari haka na tashin sukuku babu kuzari. Ita Umma ta yi tsammanin ko ba ni da lafiya ne har da ballo min paracetamol ta yi wai in sha. A ganin ta kamata ya yi in tashi da kuzarin wannan kyakkyawan labari na jiya. Eh tabbas na tashi da nishadi, amma ba nishadi irin wanda take tunani ba, wani nishadi ne da gare ni ne kadai yake nishadi ba gare ta ba. Rashin sanin madafa ne ya sanya ni rashin kuzarin.

Da yamma bayan Anti Maryam ta tashi daga wurin aiki sai ga ta ta zo. Na dai yi kokarin gayyato karfin hali na shimfida annuri a saman fuskata ko don kada ta ga tamkar na yi biris da nata kokarin ne. Sun sha hira ita da Umma kafin ta karbi takarduna cikin envelope muka yi bankwana ta tafi.

Bayan tafiyarta na fuskanci Umma, har ga Allah ban san ta ina ma zan fara ba, sai dai kuma barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa. Dole ne in har ina son cikar burina in yi mata maganar tun ma kafin lokaci ya kure min.
Gani ta yi ina ta murza 'yan yatsuna irin yadda nake yi a duk sadda nake da bukatar wani abu tun ba yanzu ba, tun muna da kananan shekaru.
Ta ajiye barar magin da take yi ta fuskance ni tare da mayar da dukkan hankalinta gare ni ta ce
"UmmulKhairi yaya aka yi? Akwai damuwa ne?"
Na jinjina kaina ina jin rashin kwarin guiwa na dabaibaye ni.
"Ki fadi ko ma mene ne, ni mahaifiyarki ce, idan har ba ki fada min damuwarki ba waye za ki fada wa? Sannan ni mai ba ki maganin dukkan damuwarki ce matukar bai fi karfina ba."

Kalamanta sun dan sanyaya zuciyata, sai dai har ga Allah ta ba ni tausayi don da alama ba ta san kalar maganar da zan yi mata ba shi ya sa har ta iya lallaba ni.
"Umma da ma...da ma..."
Na kasa fadin komai kirjina na bugawa da wani irin karfi.

Ta kama hannuwana ta soka a cikin nata, ta hau kokarin hada idanuwa da ni amma na ki yarda don ma kar in kasa maganata.
A hankali na ji bugun zuciyata yana daidaita, wani irin courage yana zuwar min, sannan cikin sanyin murya na ce
"Umma, na samu aiki."

Cikin rashin fahimta ta dinga bi na da kallo, ganin ba ta fahimci komai din ba ya sanya ni ci gaba da cewa
"Na samu aikin jami'ar tsaro kamar yadda nake so. Jiya suka tura min ta email wai nan da wata daya za mu fara training. Aikin DSS ne."

Shiru ta yi kawai tana watsa min wani irin kallo, irin kallon ba ki da hankali.

"Umma zan iya hakura da admission din can na Cairo, tunda na samu abin da nake ta son in samu, kamar ba sai na je..."

"Ke da Allah can rufe min baki shashashar yarinya! Ni na zaci kin fara hankali Khairi ashe tunanin banza na yi? Idan ma mafarki kike yi tun wuri ki farka, don ni dai ba zan taba barinki ki tafi ki yi aikin jami'ar tsaro ba. To ina ruwan biri da gada? Mene ne hadin danga da garafuni? Ke da kike mace ai aikin jami'ar tsaro ba naki ba ne, aikin maza ne, mazan ma masu iya katabus ba kowanne kashi tusa ba. Ban amince ba, ba kuma zam taba amince miki ba. In dai har da yawuna za ki tafi to ba za ki je ba. Kar kuma in sake jin wannan maganar daga yanzu!"

Na san za a rina tabbas, don shawo kan Umma ba abu ba ne mai sauki. Har gara ma da a ce ban samu wani admission ba watakila za ta amince. Amma a yanzu dai da kusan komai ya kammala, na sani sai an kai ruwa rana kafin ta amince min.

A wannan dare ko baccin kirki ban samu na yi ba. Da safe na tashi na fara aiki kamar yadda na saba, bayan na kammala komai na sake tinkarar Umma da maganar sai dai ina farawa dole na yi shiru saboda ban ma ga fuskar da zan ci gaba ba. Daga nan kuma sai na hau tunanin ta inda zan bullo mata ta amince, don gaskiya ina ji a jikina alkhairina yana tare da zama jami'ar tsaro.

Hijabi na saka na fito na tarar da ita tsakar gida zaune da list na 'yan bashi a hannunta tana dubawa. Na duka har kasa sannan na shaida mata ina son zuwa gidan Mama.
"A dawo lafiya."
Ta fada ni kuma na mike na fice ina tunanin wannan ita ce hanya mai sauki da zan iya bi domin a shawo kanta ta bar ni da zabina.

Ban wani tsaya bata wa kaina lokaci ba da na je, na hau kora wa Mama bayanin komai sannan na karasa cike da rauni,
"Mama watakila idan kin sa baki Umma za ta bar ni in je, wallahi ko da na tafi inda suke so din ba lallai ba ne in mayar da hankalina a kai tunda tun farko ba can ne nake so ba."

Ajiyar zuciya Mama ta sauke, ta ce
"Kin zo da zance mai rauni Khairi. Ni wallahi ban ma san ta inda zan fara tinkarar Fatima da wannan batu ba."

Na sassauta muryata ina sanya hannuna a cikin nata,
"Ki daure dai Mama, na san Umma tana jin maganarki sosai, za ta iya amincewa."

Sai dai, na manta da cewa zuciyar Umman tawa karfi gare ta, irin karfin karfe mai wahalar lankwasuwa. Mama ta zo gidanmu, ta kuma yi bakin kokarinta amma Umma ta kafe a kan kafiyarta kan cewa ba zan tafi aikin DSS ba, sam bai dace da ni ba. Ko da a ce ban samu wani gurbin karatun ba ita ba za ta taba zura min idanuwa in tafi aikin da ya kasance na maza ne ba.
Bayan tafiyar Mama sai abun ya juyo kaina, ta hau ni da fada, inda take hawa ba ta nan take sauka ba, wai na kai karar ta a tunanina za a iya juya ta, to zuwan Mama bai amfana komai ba don ita kanta ta fahimce ta a karshe ta kuma goyi bayan kar a bar ni in je inda nake so.

Rayuwa ta yi mini zafi, rana zafi inuwa kuna. Hatta sakar min fuska Umma ta daina, idan na dauki aiki zan yi sai ta kwace, ko dai ta yi da kanta ko kuma ta sanya Safra ko Sadiya su yi. Na yi ban hakurin na kankar da kai amma ta ki yafe min. A karshe ma cewa ta yi in dai har ina son ta yafe min to sai dai in bar wani batun DSS, in rungumi gurbin karatun da na samu wanda ba kowa ne yake samunsa ba.
Na yi kukan, na fada wa Allah damuwata, na yi addu'a, na neman zabin alkhairi a wurin Allah, a karshe na bar wa Allah lamurrana tare da shaida wa Umma na dangana, zan tafi inda take son in je din.
Tun daga nan sai muka koma kamar yadda muke a baya, kamar babu abin da ya faru.

Ana saura kwana uku a shiga training din DSS sai ga Anti Maryam ta zo, tun daga yanayin fuskarta na san akwai damuwa. Muka gaisa tare da tambayarta yara ta ce lafiyansu kalau.

"Umma, wani mummunan labari ne na zo da shi."
Ba Umma ba, ni kaina da ba ni ta kira ba sai da gabana ya fadi, duk muka mayar da hankalinmu gare ta. Ta ci gaba da fadin
"Ana kyautata zaton Kaita ba zai fito a primaries ba. Kuma dai matukar bai fito primaries din ba babu shi babu takara, don haka ba zai taba samun mukamin da yake so ba."
Ta sauke ajiyar zuciya cike da alhini ta ci gaba da magana,
"Shi ne mai gidana ya ce in fada muku gaskiya, ko da Kaita ya dauki nauyin karatun yaran nan a yanzu, to ba lallai ba ne ya ci gaba idan tafiya ta yi tafiya, matukar ba shi ya ci zabe ba. Kuma matsalar, da suka sake tuntubarsa sai cewa ya yi wai kudin shekara ne zai biya wa yaran, kafin cikar shekarar zai yi renewing dinsa. To kun ga kuwa idan har bai ci zabe ba ta yaya zai ci gaba da biya wa yaran talakawa kudin karatu? Da yawan yaranmu muna kallo, za su nisa da karatu a kasar waje, amma sai masu kudin su kasa karasa biya musu karatunsu, a karshe da kyar suke hada kudin jirgin da za su dawo gida ma, sun yi asarar shekarun da suka faro a karatun.
Gudun faruwar irin haka ne Abban su Rukayya ke yi, ya ce gara a dan jinkirta har mu ga abin da Allah zai yi, idan har an gyara ya fito primary election din, sai su tafi. Amma matukar bai samu ba gara a nemi wata hanyar kawai, Allah ba zai hana mu yadda za a yi ba."

Ta yanayin muryarya kadai za a tabbatar da cike take da rauni. Na karanci hakan kwarai a cikin idanuwanta.
Umma ma sam lamarin bai yi mata dadi ba don idanuwanta cika suka yi taf da kwalla, yayin da yanayina ya dinga reto a kan lilon da ke sakale tsakanin bakinciki da farinciki.
Tuni na sare cewa ba zan tafi DSS dina ba, har na sanya wa zuciyata cewa na amince da tafiya Cairo in karanci law din, sai dai a yanzu da na ji labarin ya sha bamban, sai na samu wani irin courage, ina jin cewa kamar ban makara ba, watakila DSS din nan da na samu alkhairi ne gare ni, da duk al'ummata ma.

"Babu komai Maryama, kila babu alkhairi ne a cikin tafiyar. Sau da dama akan so abu amma sai ya zama ba alkhairi ba ne gare mu, sannan akwai sadda muke kin abu sai kuma ya kasance shi ne alkhairi a rayuwarmu."
"Haka ne Umma. In shaa Allahu nasara ce ke bibiye da rayuwar Khairi. Sannan za mu ci gaba da cuku-cuku har zuwa sadda za mu samu abin da muke so. Shi wannan Kaitan, akwai yiwuwar ya samu wani mukamin a gaba in dai jam'iyyarsu ta haye. Kun ga tunda yana da kudurin alkhairi sai mu kyautata masa zato."

Na sauke ajiyar zuciya, tabbas muna kyautata masa zato, ina ji a jikina zan iya karantar Law din amma a can gaba idan rai da rayuwa sun bayar da dama, a lokacin da burina ya cika.

"Kin yi bakin kokarinki Sista Maryam, Allah ne kadai zai iya biyan ki. Mun gode kin ji, Allah Ya albarkaci zuri'arki Ya ba ku zaman lafiya da maigidanki."
"Amin Umma. Babu komai yi wa kai ne. Yanzu ga shi abokan karatunta da suka samu admission a university tuni sun yi nisa a semester, kila ma sun kusan fara jarabawa. Don an dade da rufe registration, sai dai mu jira wata shekarar idan muna da rabon gani."
"Haka ne. Kafin wata shekarar kuma sai ta fara aikin da ta samu mu gani, watakila shi ne ma alkhairin nata."

Wani irin bargon farinciki na ji ya lullube ni, kalaman nan na Umma sun ba ni tabbacin kenan za ta bar ni in tafi wurin training dina tunda har ta fara yi wa Anti Maryam maganar.

"Ta samu wani aikin ne Umma?"
Anti Maryam ta tambaya tana yawata idanuwanta a kaina.

"Eh ta samu Maryama. Ni na hana ta saboda wannan karatun da za ta tafi. Ina jin bai fi kwana biyu ko uku ba su fara training. Jami'ar tsaron dai da ba na so shi ne ta samu."


Amrah A Mashi❤️😊

Continue Reading

You'll Also Like

19.4K 1.7K 100
labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa.
5.1K 465 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zat...
12.3K 606 53
MAKAUNIYAR RAYUWA- KASHI NA UKU- BABI ASHIRIN### Fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke,alherin Allah ya kai gareku, ubangijin Allah ya biyaw...