DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 10- Fushin Masoyi...

195 27 0
By PrincessAmrah

Page 10

Umma ta hada kudade masu dan kauri ta ba ni ta ce in je kasuwar tsaitsaye inda ake sayar da wayoyi in sayi mai kyau daidai da kudina. Na yi farinciki sosai na kuma jinjina wa kokarinta don fiye da rabin jarin nata ne ta kwashe don kawai ta faranta min rai. Ni kuwa me zan yi na biya wannan baiwar Allah bisa ga jajircewarta duk da babu bango abun jingina a rayuwarta?
Ni da Safra muka je, wata Tecno karama mai kyau muka samu kuma kirar android da ban taba mafarkin samu a yanzu ba. Na sayi layi a take aka yi min rijista muka dawo gida. Ai ranar na yi nishadi irin wanda ake jimawa ba a ga na yi ba tun bayan da aka yi garkuwa da mu.

Wata kawata Salma ta kawo min ziyara take shaida min aurenta ya kusa za ta zo ta kawo min katin gayyata. Na harare ta
"Ba ki kyauta ba Salma, sai da aka kusa bikin ma sannan za ki fada min?"
"Ba haka ba ne Khairi, tun sadda aka sa ranar ba ki da lafiya ne, kuma kin ga babu dadi kina fama da jinya in zo da batun aurena. Amma ki yi hakuri in shaa Allahu ana buga kati ke ce ta farkon kawowa."

Na yi murmushi kawai ina tunanin rayuwa. Ni ko sai yaushe ne ma zan baiwa wani damar yin soyayya da ni ballanta har in yi auren? Na tuna ko wancan satin sai da wani matashi ya zo har gida ya nemi ganawa da ni amma na kore shi. Haka cikin muna jarabawa ma wani har gida ya biyo ni na masa korar kare. Ba na jin zan iya ba wani dama, dukka auren ma ba ya kaina, ba na tunanin zan yi rayuwa irin ta kowacce diya mace. Tunin duniya aka yi fatali da martabata, ni kuwa me ya yi saura a rayuwata da zan yi tinkaho da shi?
Sai kawai na ji gumi a fuskata ashe kwalla ce nake yi ban sani ba. Salma da ba ta san dawan garin ba ta tsorata da kukan nawa amma a karshe sai kawai na yi mata murmushi ina mai ba ta tabbacin wani dalilin ne can daban ya sanya ni kuka ba saboda ita ba ne.

Bayan na fita rakiyar ta ne take ce min yaushe admission dinmu zai fito?
"Ba burina in ci gaba da karatu ba Salma, ko da zan ci gaba to gaskiya ba yanzu ba. So nake in samu aikin tsaro ko ma wanne iri ne."

Ido ta zaro mamaki na bayyanuwa a fuskarta.
"Aikin tsaro kuma Khairi? Ta yaya ke da kike mace za ki yi shi? Wahala fa ake sha."
"Wahala ba ta kisa Salma, idan dai zan samu na yi alkawari zan jure. Sa kai aka ce ya fi bauta ciwo."

Ta sauke ajiyar zuciya hade da fadin
"Haka ne. Amma dai na tausaya miki wallahi."
"Babu komai fa in shaa Allahu zan iya. Ni dai burina kawai in samu."
"To yanzu jamb din taki hakura za ki yi da ita shi kenan ki yi asarar duk wannan uban makin da kika samu? Oh! Abin da mutane ke nema yau ga wata ta samu amma tana neman barin ta ta bi iska."

Na kirkiro murmushin da bai da alaka da nishadi na ce
"Ba ita nake buri ba, shi ya sa tun farko na nunar da ba na son cikewar aka tilasta ni."

Mamaki bai kau daga fuskar Salma ba ta ce
"Ai shi kenan, Allah Ya taimaka. Ki dinga dubawa ta online duk sadda za a yi daukar ma'aikata ki cika ko Allah zai sa a dace. Na ji ma an ce an bude portal na Nigerian army. Ki gwada ko Allah zai sa ki haye tunda dai abun dace ne."

Na ji dadi kwarai muka yi sallama ta fita. Ban yi shawara da kowa ba na shiga shafin Nigerian army din, na kuwa ci karo da wurin da mutum zai cike tunda a bude yake. Na cika komai a raina ina addu'ar Allah Ya sa in dace.

Ina zaune daki sai ga Safra ta shigo tana ce min wai in je Mama na kira na. Na yi mamaki kwarai don wannan din wani sabon abu ne amma dai na amsa da to na fita. Umma ba ta nan tun safe ta je sare-saren kayanta da suka ja.
Ko da na je gidan na tarar kwalema suke yi ashe, kusan komai an fitar da shi waje. Bayan na gaishe ta ta amsa min da sakin fuska, ta miko min wata leda mai makimancin girma ta ce
"Wasu daga cikin abubuwan Ummu ne wadanda ba ki da irinsu. Wannan kyauta ce daga gare ni a matsayina na uwa. Idan kuma ba za ki iya amfani da su ba ki ba Safra da Sadiya. Ko kuma ki ajiye a matsayin tarihi."

Har yanzu na kasa sabawa da rashin Ummu. Matukar aka yi min zancenta sai in ji komai yana sabunta kansa. Da kuka na karba ina godiya, ita ma Mama nata idanuwan cika suka yi da kwalla amma ina kallon ta tana kokarin mayar da su.

"Na gode Mama..."
Kadai na iya furtawa ina jin zuciyata tamkar za ta tarwatsa allon kirjina ta fito waje.

Da na isa gida na bude, akwai tarin littattafai ire-iren wadanda Ummu ke yawan karantawa wanda suka shafi Nigerian politics, sannan akwai na constitution da sauransu. Ko da ma can ita akwai karance-karance, ni kuwa a bar ni dai da karatun English da Hausa novels kawai kwata-kwata wadancan ba su dame ni ba.
Sai na tuno watarana da na je gidan su na tarar tana karatun wani katon littafi na dinga sallama amma ba ta san ina yi ba.

Ina shiga na fizge littafin hade da yin tsaki.
"Yo wannan ma ai iskanci ne a yi ta sallama mutum bai san ana yi ba."

Ta tashi zaune tana murmushi.
"Allah Ya ba ki hakuri ni ban ma ji ki ba."
"Yo da ma ya za a yi ki ji ni kin tasa wannan tulelen littafi a gaba kina karantawa. Ni na kasa gane dadin da kike ji a karatun wannan littattafai."

Ta dan tabe baki.
"Ke dai ba za ki gane ba tunda ba ki san dadinsu ba. Kin ga wannan, yana bayani ne a kan matsalolin insecurities da suke addabar kasar nan. Wani marubuci mai suna Bamai A Dabuwa dan jihar Jigawa ya rubuta shi. Ni ba ki ji ma yadda nake jinjina wa rashin tsoron sa ba. Ba ya ko gudun gwamnati ta kama shi a kan wannan rubutun."

Na kalle ta don ni ban ma gane inda ta dosa ba, ta ci gaba da cewa
"Da a ce kuma gwamnati za ta yi wa wannan rubutun nashi kyakkyawar fahimta wallahi da an samu gyare-gyare sosai ta fuskar tsaro. To matsalar kawai ba lallai ba ne ya isa gare su. Kin ga wannan shafin..."
Ta bude wani wuri tana gwada min,
"A kan hanyoyin da jami'an tsaro za su iya bi ne su magance matsalolin fyade da fashi da makami. Sannan chapter din gaba kuma tana magana a kan kidnapping da hanyoyin da za a iya magance sa idan har gwamnati ta so."

Na rufe littafin ina ajiyewa a gefenta.
"Yanzu duk mene ne mahadina da wannan dogon sentences din? Da wannan da ma textbooks din medicine kika samo mana, kika yi musu irin wannan hardar ni kuma ki dinga karantar da ni. Kin zo kina abin da ba zai taba amfananmu da komai ba."

Murmushinta mai kyau ta yi hade da kai min duka a kafada.
"Ba za ki gane ba Khairi, amma ina mai tabbatar miki matukar kika rungume su, akwai lokacin da za su iya yi miki amfani..."

***
Lokacin da za su iya yi min amfani, ina tunanin wannan shi ne lokacin da Ummu ke magana, lokacin da zan karanta su ina mai yakinin iliminsu zai kai ni matakin da nake son zuwa.
Na kara dauko wani littafin ina duba bangonsa, exactly shi ne wanda na tarar tana karantawa din nan, fuskar littafin inuwar mutane ne sama da biyar, wasunsu rike da bindiga, wasu kuma makamai irin su adda da sauransu. Yana da shafuka sama da dubu biyu. Babba ne sosai irin mai kama da dictionary. Na fara tunanin ta yadda zan fara karanta wannan uba-uban littafi amma sai na jure, saboda na san ba a hawa gini dole sai da matattaka.

Ina budewa wata farar takarda ta fado daga cikinsa, kafin in bude na duba rubutun jiki, rubutuna ne, na rubuta
Dear UmmulKhairi.

Na saki murmushi mai hade da ruwan hawaye. Na tuna sadda na yi mata wannan rubutun, wani lokaci da dan'uwansu ya nuna yana son ta amma ta ki shi, shi ne ya biyo ta hanya ta in tsaya masa don ba karamin son ta yake yi ba.
Da zarar na dauko mata zancen sai ta tashi ta ba ni wuri, ta kama jin haushi na kawai saboda ina damun ta da zancensa.
Ranar da ta je gidanmu muna tsaka da hira na dauko mata zancen Nasir, a take ta tsuke fuska kamar ba ita ba ce ta gama dariya. Na ce
"Daure fuska ba ya miki kyau Ummu. Wai ke wace irin mutum ce kamar dai wadda aljani ya aura? Shin mene ne matsalar Nasir? Mutumin nan yana son ki so na hakika, ya jure ruk wani wulakanci naki ya ki ya yi zuciya amma ke sai kunna sa kike yi. Ni ki fada min matsalar sa idan har na gamsu zan kyale ki da zancensa."

Ta bata rai hade da mikewa.
"Ni ba ni da lokacinki, kuma tunda ba za ki taya ni kin abin da nake ki ba kin ga tafiya ta, babu ruwana da ke, ba zan sake zuwa gidanku ba."

Mikewar na yi ni ma ina kokarin boye dariyar da nake yi,
"Habawa aminiyata...kawata...'yar'uwata ya da mikewa kuma..."
Dariya ta nemi cin karfina.

Dariyar da nake ta kalar hasalar da ita, ta nufi hanyar fita ina kiran sunanta amma ko waiwaye babu ta fice, ni kuma dariyar da nake yi ta hana ni aikata katabus, abun ne nata kamar shafar jinnu.

"Duwawu nake mai dadin zama, in dai ni ce ina nan zaune za ki zo ki same ni."

Kamar wasa sai ba ta zo din ba, aka kwana aka wuni har aka sake wani kwanan ba ta zo ba, ni kuma a lokacin Umma ba ta nan ta yi tafiya, ta bar mu da su Safra sai kanwarta Anti Marwa bazawara ce ta kawo ta zauna da mu kafin ta dawo, ita kuma ta je asibiti wajen wata kawarta babu yadda za a yi in fita har sai ta dawo.
Har dare ba ta dawo ba sai daf da karfe goma, lokacin kuma ba halin in fita dole sai da safe. Gari na wayewa ta sake cewa za ta fita wani irin takaici ya kume ni. Wai an kawo ta don ta zauna da mu amma ba ta zama kullum sai yawo.
Na fada mata ina son zuwa gidan su Ummu ta ce ba yadda za a yi in fita in bar gida babu kowa tunda Safra da Sadiya sun tafi makaranta. A dole sai dai in bari har wata safiyar sannan in je.

Raina a bace na zauna ina fama da kewar aminiyata, sai kawai wata hikima ta zo min, na nemi takarda da biro na hau rubuta mata wannan takardar, su Safra na dawowa na ba su suka kai mata. Ai kuwa ba a kara minti talatin ba sai ga ta ta shigo gidan tana min harar wasa.

***

Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

11.1K 72 15
está es una historia donde nos demuestran que el amor no tiene límites te vas a enamorar de un mafioso? no importa en esta historia te lo demostrarem...
5.2K 465 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zat...
45.1K 2.2K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...
2.3M 70.4K 98
Previously called Older Brothers Part 1 Completed (Alternate version) part 2 Ongoing "T-trust me?" "Always." It was the promise that they were never...