DARE DUBU

By PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 05- Masauki

257 27 0
By PrincessAmrah

Page 05

Ban san me ya sake faruwa ba daga nan, kawai dai abu daya da na sani shi ne na ji kamar wani hayaki ko hoda a ido da hancina.

Tsakanin kwanaki da awanni, ban san adadin da na salwantar ba, illa dai na bude ido na gan ni yashe cikin kashi da fitsari, Ummu daga gefena ita ba ta ma farka ba. Na yi firgigit ina kokarin tuna abin da ya faru, sai dai na gagara tuna komai sai hirar nan tamu ta karshe da murmushin da Ummu ta yi min.
Cikin azama na hau jijjiga ta, sai dai tamkar mai baccin mutuwa haka ta kasance. Na sake bugunta da karfi, ta yi firgigit ta tashi zaune tana bi na da kallo, sannan ta ci gaba da kallon mataccen dakin da muke yashe, zarnin fitsari mai garwaye da wani irin hamami na ratsawa a na'urar shiga da ficen iskanmu.

Dif! Dif! Dif, haka muka dinga jin karar taku tana kusanto mu, can sai ga wani sangamemen mutum, fuskarsa duk dinke-dinke tamkar dinkakkiyar kwarya, sannan idanuwansa jajur masu ban tsoro.
Kallo na ya yi sannan ya kalli Ummu, ta yanayin kallon kawai na san cewa alkiyarmu ta tsaya!

"Ku taso ku zo, Oga yana son ganin ku."
Ya fada da kakkaurar muryarsa mai kama da duman girke.
Alamar motsi babu wacce ta yi a cikinmu, har sai da ya daka mana tsawa sannan muka mike cikin azama muka mara masa baya.

Mun yi tafiya mai dan nisa, kafin muka isa cikin wasu bukkoki, irin asalin na fulanin nan masu tafiya kiwo. Bayan mun isa cikin wata babbar bukka, mutumin nan wanda a take zuciyata ta yi masa huduba da Sangami, ya ba mu umurnin shiga. Babu musu kuwa muka afka, zuciyata sai biya salati take amma bakina ya gagara furtawa.

Kasa ya zube, cikin girmamawa ya ce
"Oga, ga sabuwar ganima nan. Sai dai a inda muka samo su, babu alamun za a samu abun kwarai."

Dariya da karfi wanda ya kira da Ogan ya yi, kafin ya murtuke fuskarsa tamkar ba shi ba ne ya gama dariya, cikin muryarsa ta Fulanin daji ya ce
"Wa yake raina kadan? Ai ko gidansu ne a sayar a biya kudin fansarsu."

Na kalli Ummu, ta kalle ni. Sai a sannan ne muka fahimci komai, kenan dai wadannan su ne ake kira da 'yan garkuwa da mutane. Kamar Ogan ya fahimci maganar zucin da nake yi, sai cewa ya yi,
"Ku 'yan gata ne idan har aka yi mana yadda muke so, babu wanda zai yi muku ko kwarzane, za ku koma gida lami lafiya."
Sannan ya sake kyakyacewa da dariya.

Dukkan gabban jikina kyarma suke yi, na kalli Ummu da jikinta ya jike sharkaf da zufa, sannan na dawo da duba na ga Ogan da ke magana da Sangami.

"Daga mafari suke yanzu?"
"Eh, Oga. Daga can na dauko su."

Da alama wurin nan da muka farka can ne suke kira da mafari. Ban gama dawowa daga tunanin da nake yi ba, na ji ya ci gaba da cewa,
"Ka umurci Zaki da ya ba su wajen kwana, sannan Lanti ta ba su duk abin da ya dace. Kar a cunkusa su cikin wadanda suka kwana biyu, don wadannan ina tsammanin an kusa aika su lahira, saboda ba zan lamunci rikonsu a nan su zame mana wani nauyi ba alhali an ki kawo kudin fansarsu."

Dariya Sangami ya yi, sannan ya juye ya kalle mu ya ce
"Ku wuce mu tafi."

Babu musu muka bi bayansa, ya kai mu can wata bukkar inda muka samu ire-irensu da yawa, wasu na zukar sigari, wasu na daga kwalba da alama ta giya ce, sannan wasu karta suke yi, kuma abun mamakin har da mata.

"Zaki."
Ya kwala kiran sa. Wanda ya kira da Zakin ya ce
"Ya dai? Mutum na tsaka da harkarsa za a nemi takura masa."

Sangami ya tsuke fuska tamau ya ce
"Oga ya ce a ba su masauki. Ke kuma Lanti, an ce ki ba su duk abin da ya dace. Sababbin kamun nan ne na shekaranjiya."

A cikin zuciyata na maimaita shekaranjiya. Kenan kwananmu biyu da zuwa wannan mummunan wuri, irin wurin da ban taba mafarkin ko makusancina zai zo ba ballanta ni da aminiyata.

Da karfi Lanti ta sa hannu ta tangale min keya ganin ba na tafiya da hanzari. Riga da wandon jeans ne a jikinta sun dame ta sosai, kanta sanye da hular hana-salla. Cikin muryar fulani ta ce
"Dalla can ki saki jiki ki yi tafiya tun kafin na sauya miki kama."
A tsorace na kara takawa, da ma can komai nawa a hankali nake yin sa, ballantana kuma da wannan abun ya faru, wanda zuciyata ta gaza daina harbawa da sauri-sauri saboda zallar tashin hankalin da ke dabaibaye da mu, tamkar a mafarki haka na dinga ganin komai.

Can wurin wani gini aka kai mu, ginin kamar tsarin azuzuwan makaranta haka yake, Zaki ya duba wani daki wanda ke da saukin mutane, duka-duka mata uku ne, daga wata dattijuwa sai budurwa da karamar yarinya a ciki. Ya dube mu ya ce
"Nan shi ne masaukinku. Ku sani cewa rayuwarku a hannunmu take, za ku iya wasa da ita ne ta hanyar yunkurin guduwa ko akasinsa. Sannan idan har kun yi dace da iyaye nagari masu son ku, ba za ku jima ba za a sallame ku. Amma matukar ba a turo mana abin da muke so ba kan kari, ba mu jin wahalar aika mutum kiyama."
Ya kece da wata irin dariya, hatta sassan jikinsa sai da suka motsa. Ya fice daga dakin ba tare da ya saurari abin da Lanti ke ce masa ba.

Bin bayansa ta yi, babu jimawa sai ga ta dauke da tukwane guda biyu da karamin risho, irin 4 corner asalin na da, ta dire su a gabanmu.
"Ga kayan aiki nan, wannan risho din kowanne cike yake da kalanzir, sannan ga tukwane da ludayi. Rahi za ta kawo muku sauran abubuwan. Kar in ji ko ganin kun aikata abin da bai dace ba, don ba wuya za ku shiga yanayin da sai kun yi da na sani."
Daga haka ta fice daga dakin.

Sai a lokacin na ji wani irin kuka mai zafi ya taso mini. Wannan wace irin rayuwa ce? Rayuwar da ake fatali da 'yancin mutum...rayuwar da kana ji kana gani ka koma bawan wasu ba tare da ya biya kudin sayenka ba.
Da karfi na fada jikin Ummu ina kara fasa wani kukan, sai dai ina jin sautin nata, sai na yi gaggawar dagowa, na ga yadda kafadarta ke hawa da sauka alamun zallar abin da ke zuciyarta ne take fitarwa. Sai kawai na ji wani irin kwarin guiwa ya zo min, da yatsu biyu na sharce nawa hawayen, na hau rarrashinta ina dan bubbuga bayanta amma kamar ma tunzura ta nake yi.
A cikin wannan halin Rahi ta shigo, da karfi ta jefe mu da ledoji guda biyu.
"Ga shi nan kowa ta dauki guda daya. Idan kun so ku kashe kanku saboda kuka."
Ta fita ta bar mu.

Babbar matar da muka tarar cikin dakin ita ta tattara mana ledojin da har kayan ciki sun fara zubewa, cikin sanyin murya ta ce,
"Duk wannan koke-koken da kuke yi babu abin da za su amfana muku, mu ma nan mun yi mun gaji mun daina. Gara ma ku dauki kayan amfaninku ku san kun mora, don idan suka kare lokacin da suka dibar muku bai yi ba, sai dai ku karata, ba za su sake ba ku wasu ba."

Na karbi ledar na duba, shinkafa ce da wake, daban-daban daure a leda, sannan taliya leda biyu macaroni guda daya. Ga kullin gishiri da manja. Sai wata karamar leda kuma brush ne da toothpaste, da sabulun wanka. Sai kuma ashana kwara guda.
Dayar ledar ma abin da yake ciki kenan.
A cikin zuciyata na ce 'abun na yi ne wai ungozoma da adda.'
Na mika wa Ummu tata amma ko kallon ledar ba ta yi ba ballanta ta karba. Sai na hada da tawa na ajiye inda tukwane da rishonmu suke.

"Ku yi hakuri ku jingina lamarinku ga Allah, ku daina kuka don idan kuka fara ciwo a nan babu magani balle allura, wahalar banza za ku sha sannan a karshe ku gaji ku mike. Abu daya zai zama makaminku shi ne ibada. Kar ku yi wasa da sallah da addu'a, sannan azumi, yanzu haka shi ke dauke a bakina."
Matar ta sake fadi cikin rarrashi.

Sai a sannan na tuna da sallolin da suke bisa kanmu. Na kama hannun Ummu na mikar da ita, sannan na tambayi matar,
"Mama ina za mu samu ruwan alwalla?"

"Akwai jarka a nan waje, sannan akwai ruwa ma a bandakin can da ke jere da sauran dakuna. Ku samu har ruwa ku dan watsa ko za ku ji dadin jikinku."

Ni fa mamaki sosai ma lamarin ya dinga ba ni. Wai garkuwa da mu aka yi amma komai da gata? Kenan har ma wanka mutum zai iya yi? Sai kuma na daina mamaki tunowa da na yi har da sabulun wanka aka ba mu.

"Ki daina mamaki kin ji, a nan fa ba laifi mata galihu gare su, maza ne dai 'yan wahala, ko kadan ba a sassauta musu. Laifi kadan za ku ji karar alburushi an dauke kan wani. Ko jiya dai a nan an kashe wani dattijo, mahaifin wannan yarinyar..."
Ta nuna budurwar da ke zaune, tunda aka kawo mu dakin ba ta yi magana ba, sai a lokacin ma na lura da yadda idanuwanta suka kumbure suntum alamun ta sha kuka ba kadan ba.

"Kawai don tana kai masa abinci idan ta dafa. Sun ce mata ta daina kai masa, to kin san lamari na iyaye, ita kuma ta yi taurin kai ta ki dainawa, wallahi a karshe dai kansa suka huce, sun kashe bawan Allahn nan har lahira."

Kuka budurwar ta kara rushewa da shi a lokacin da matar ta kai aya. Mamaki hade da tausayi suka yi dirar mikiya a cikin zuciyata. Rashin imanin wadannan mutanen ya shallake tunanina.



Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

65K 5.7K 36
U+Z ဒီနေ့မင်းလွင် + ဒီယောရာဇာဓိရာဇ်
156K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...
16.8K 882 32
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace m...
5.2K 465 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zat...