WUTA A MASAƘA

By Ayshercool7724

27.6K 1.6K 154

labari akan wata yarinya me rawar kai da rashin jin magana sam, labari akan taɓarɓarewar zumunci, tarbiyya da... More

WUTA A MASAƘA
WUTA A MASAƘA 2
3
WUTA A MASAƘA 4
CHAPTER 5_6
7_8
9_10
11_12
WUTA A MASAƘA 13_14
WITA A MASAƘA 15_16
WUTA A MASAƘA 17_18
WUTA A MASAƘA 19_20
WUTA A MASAƘA 21_22
WUTA A MASAƘA 23-24
WUTA A MASAƘA 23_24
WUTA A MASAƘA 27_28
WUTA A MASAƘA 29_30
WUTA A MASAƘA 31_32
33_34
35_36
37_38
37_38
39_40
41_42
43_44
45_46
47_48
47_48
51-52
53_54

49_50

970 66 13
By Ayshercool7724


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.





49_50

Imran ya kalli Amira a gigice yace "Amira meye haka? Lafiya kuwa, meyafaru?"

Cikin kuka tace "wani abu naji a jikinka kamar ƙadangare"

"Ƙadangare kuma Amira? Bakomai a jikina fa"

"Wallahi ƙadangare ne a jikin ka"

Ya tashi ya kunna fitla, ya cire vest ɗin jikinsa, ya juyo mata bayan yace "kin gani bakomai a jikina"

Ƙirjin Amira se dukan uku uku yake ta na sake ƙare masa kallo, tabbas bakomai a jikinsa, amma ita kam taji tamkar ƙadangare ne a jikinsa.

Da ƙyar ya lallaɓata ta yadda ba komai a jikinsa, ta dawo ta kwanta, a cikin matsananciyar fargaba ta yadda da Imran, dan gani take kamar da ya taɓa ta zata ga ƙadangaren.

Imran ya manta da batun ƙadangare, ya sha soyayyar sa, sedai har sukai wanka bacci ya ɗauke shi Amira ba tai bacci ba.

Ta dinga juyi tana karanto duk Addu'ar da ta zo bakinta.

Can bacci ya ɗauketa, sedai tai mafarki ƙadangaru sun babibaye jikinta, haka ta kuma tashi a razane tana gumi, ƙarshe haka ta kasa bacci, har Asuba tayi.

Gaba ɗaya fargabar komawa baccin ma take, dan haka ta zauna akan dadduma ta cigaba da lazimi, gari na yin haske ta fita Kitchen ta ɗora breakfast.

Har ta kammala Imran yana baccin sa, seda tai wanka ta shirya tsaf tai kwalliya cikin ƙananan kaya, sannan ta tafi bedroom ɗin da Imran ke kwance, ta kunna turaren wuta.

Ta hau gadon da yake kwance, ta ɗan yaye bargon jikinsa, ta hau kansa tace "My cwt Amran, wake up na, babyn ka na jin yunwa fa"

Murmushi yai ya sake gyara kwanciyarsa, itama murmushin tayi, ta zira hannunta cikin bargon da niyyar ta rungumoshi, sedai taji ta danƙi ƙadangare.

Take ta zunduma ihu, ta dire daga kan gadon da gudu tana kurma uban ihu.

A zabure ya miƙe yace "Amira lafiya wai? Meye hakane?"

"Wallahi ƙadangare ne a jikin ka"

"Wai wane irin ƙadangare ne haka? Bakomai a jikina, ki kwantar da hankalinki"

Yai maganar yana ƙoƙarin tunkaro ta, amma ta sake fasa ihu a gigice tace "ba ga ƙadangaren nam yana bin ka ba, kar ka zo in da nake, gashi nan ina kallo yana binka"

Wan ƙaton ƙadangare Amira ke gani a jikin Imran, girmansa ya shallake girman ƙadangaren da take gani a zahiri, gashi a duniya Amira ray tsani ƙadangare.

Ganin Imran ze tinkaro ta yasa ta jiya ta zura da gudu Falo tana ihu, ihun Amira da Ihsan ta jiyo ysa ta fito da sauri.

Garin gudu Amira tai gware bango, ta faɗi a gurin, amma ta miƙe ta kuma sheƙawa a guje.

Imran ya biyo ta yana "dan Allah Amira ki tsaya, kar ki jiwa kanki ciwo ko abunda ke cikinki"

Ina idonta ya rufe tai waje da gudun gaske, kan ta je gate Imran ya cin mata, ya riƙota gam.

Wata gigitacciyar ƙara ta saki, tamkar wadda ake yayyanka wa da wuƙa, ganin Imran yana nema ya ɗorata a kan ƙadangaren da ke jikinsa.

Silalewa tayi sumammiya a jikinsa, cikin damuwa ya ɗauke ta zuwa falo, ya shimfiɗe ta.

Ya ɗaga kai ya kalli Ihsan da ke binsu da ido yace "Ihsan dan Allah bani ruwa in shafa mata ko zata tashi"

Wata uwar harara ta banka masa ace "Allah ya kiyaye, Allah yasa daga haka ma ta mutu, alhakina ne ya kamata koma menene"

Ta ja tsaki tai tafiyarta, seda Imran ya buɗe baki dan mamaki, ya tashi ya shimfiɗe Amira, ya tafi fridge ya ɗakko ruwa me sanyi, yazo ya fara shafa mata.

Ajiyar zuciya ta ding saukewa, a hankali yace "Amira kina gani na"?

Da sauri ta buɗe ido, tana ganin Imran ta miƙe zumbur daga jikinsa, ta fara ja da baya tace "dan girman Allah ka dena zuwa in da nake, kaje ka cire ƙadangaren da ke jikin ka, dan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ka tashi ka bar falon nan, kaje ka cire abun da ke jikin ka"

A ɗimauce Imran yace "Amira, jikina ba komai ni bana ganin komai fa"

Kuka ta sake fashewa da shi tana ja da baya, tana ƙoƙarin miƙewa ta sake artawa a na kare.

Ya nufo ta da sauri ze sake riƙeta amma ta faɗi a gurin.

Yasa hannu ya ɗauke ta, ya maida ita falonta, yaje ya kwantar da Ita.

Ya ɗakko wayarsa ya kira Abba, bugu biyu Abba ya ɗaga yace "Soja marmari daga nesa"

"Abba akwai matsala"

Abba yace "subhanallah, matsalar me?"

"Abba Amira, na easay meke damunta, tun jiya take koke koke tana ihu, sam na kasa gane kanta"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Amiran meya sameta?"

"Ban sani ba Abba, da naje kusa da ita take fara ihu, na rasa meke damunta"

Abba yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya kawo mana ɗauki, gashi ina Kebbi yanzu haka, amma kira antynta a waya ka mata bayani, duk yadda ake ciki ka gayamin"

"To Abba Nagode"
ya katse wayar ya kira wayar Anty, Anty ta ɗaga da sallama, ko gaisjeta be tsaya yi ba yace "Anty Amira ba lafiya fa"

"Subhanallah jikin ne?"

"Anty tun jiya take ihu, na kasa gane kanta yanzu haka tana sume ne, sam ba ta son ko in da take inje fa"

"Yasalam, gani nam zuwa, kwantar da hankalinka gani nan"

Imran ya ajiye wayar yana cigaba da kallon Amira, dake numfashi kaɗan kaɗan.

Befi mintuna arba'in ba, sega Anty ta iso a kiɗime, kai tsaye ta nufi ɓangaren Amira, taje ta tarar da ita a kwance kamar gawa, Imran ya zuba mata ido yayi tagumi.

Anty tace "Imran, meya sami 'yata?"

"Anty nima ban sani ba, gaba ɗaya taƙi tsaywa ma in fuskanci meke damunta, se ihu kawai take'

Anty taje ta kama hannun Amira, ta ɗaure ta nemo jijiya tai mata wata allura, Sannan ta sa Imran ya dinga shafa mata ruwa me sanyin gaske.

Wata irin ajiyar zuciya tayi, kamar za ta shiɗe Sannan ta koma numfashi normal.

A hankali Amira ta buɗe ido,ta kalli Anty tace "Anty yaushe ki ka zo?"

"Yanzun nan Amira, mijinki yai min waya ba ki da lafiya, kinga bani da kwanciyar hankali kenan"

Amira za tai Magana idinta ya sauka a na Imran, aikuwa ta zabura ta ƙanƙame Anty tana salati.

Anty tace "Amira lafiya kuwaa?"

"Anty dan Allah ke ki gaya masa ko zeji, ki ce masa yaje ya cire ƙadangarem da ke jikin sa wai shi baya ganinsa"

Anty tace "wani irin ƙadamgare kuma? Ai bakomai a jikinsa"

"Wallahi akwai, wai Anty kema ba kya ganinsa ne, dan Allah karku ce nika ɗai nake ganinsa, gashi nan a kwance a ƙirjinsa fa"

Anty tace "shikenan yi shiru, Kai Imran nima naga ƙadangarwn nan, kaje ka cire shi daga jikinka"

Anty tai maganar tana ƙiftawa Imran ido.

Imran jiki a sanyaye ya bar falon yana waiwayen Amira.

Anty tace "ya tafi cirewa, ki kwantar da hankalinki ki yi ta Addu'a kinji?"

"To Anty ina yi, nace masa yaje cire ƙadangare a jikinsa, amma yaaƙi kuma binsa yake"

Anty tace "ai yanzu yaje cirewa, tashi ki karya, naji yace baki ci komai ba"

Amty ta zubawa Amira Abinci, ta sata a gaba taci.

Imran kam barin Gidan yai gaba ɗaya, har bayan azahar Anty na tare da Amira.

Seda ta tabattar Amira ta ɗan sami nutsuwa sannan ta kunna mata karatun Alqur'ani.

A hankali bacci yai awon gaba da Amira.

Wajen la'asar Imran ya dawo, ya tarar Anty ba ta tafi ba cikin damuwa yace *Anty ya ake ciki? Ya jikin nata?"

Anty tace "jiki Alhamdilillah, amma ina tunanin ko ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta ne ta na bata wrong perception, ko dai wani abun daban.

Amma ga karatun Alqur'ani nan na saka mata, ka cigaba da kula da ita zuwa Gobe in Allah ya kaimu muga yadda hali zeyi"

Imran yace "to Anty, amma ina fatan cikin jikinta be samu matsala ba, saboda faɗuwar da ta dinga yi"

"Cikinta yana lafiya ƙalau, da wani abu na fita za ta gayamin, sedai ka kula sosai"

Imran yai ajiyar zuciya yace *to Alhamdilillah, insha Allah zan kula nagode sosai Anty'

Su kai sallama ta tafi.

Ga mamakin Imran har wajen magariba Amira ba ta Tashi ba.

Gashi yanzu fargabar zuwa in sa take yake, kar yaje ta sake birkicewa.

Haka nan ya daure ya koma gurin Amira, ya ga halin da take ciki.

Ya tarar da ita ta na ta bacci, ko motsin kirki ba tayi, ga sautin karatun Alqur'ani na tashi.

Seda ya tabbatar lafiyar ta ƙalau, sannan ya koma babban falo.

Aka fara kiraye kirayen sallar magariba, yai alwala amma yana gudun ya fita salla, Amira bw san a ya zata farka ba, gashi ita Ihsan ko a jikinta kamar mara imani.

Da yai alawara falon ya dawo ya tada sallar magariba.

Amira kam kamar wadda aka tasa ta farka, tai miƙa tana faɗin Alhamdilillah.

Sedai taji kamar wani abu na bin ƙafarta, ta tashi zaune da sauri ta ga meye, taga ƙanana 'ya'yan ƙadangare.

Aikuwa ta diro daga kan gadon nan tana tsalle tana faɗin "Innalillahi wa innalillahi raji'un"

A guje Imran ya sallame sallar da ta tayar,yayi part ɗinta da gudu.

Yana zuwa su kai karo tana ƙoƙarin fitowa da gudu, ta cire skirt ɗin jikinta ta yar, ta cire rigar jikinta, ta na ƙoƙarin yage vest ɗin ciki.

Imran yana ƙoƙarin riƙeta ta kuma tozali da ƙadangaren da take gani a jikinsa, sun ƙari sun zama uku.

Nan ma wani uban ihun ta zunduma, ta juya da gudu zata koma, gwanin ban tausayi ga ciki a jikinta, amma sam hakan baya hanata zurawa da gudu dan nemawa kanta mafita.

Sosai take ihu kamar ta zare, abunda ba taso ɗin dai Imran ya riƙeta gam yana karanta mata duk Addu'ar da tazo bakinsa.

Da farko da yaji jikinta ya saki ya zata baccin ta koma, seda ya lura da kyau ya ga ashe suma tayi.

Imran yai shiru yana rungume da ita yace "What happens to you my dear, meya sameki Amira na? Ubangiji Allah ka kawo mana mafita kai mana ɗauki a lamarin marainiyar nan, Allah ka yaye mata abunda yake damunta.

Ya ɗauketa zuwa cikin bedroom kan gadonta, ya kwantar da ita, ya sake kunna mata karatun Alqur'ani, sannan ya kulle ɗakin ya tada salla.

Bayan ya idar ma Addu'a yaita mata, na fatan samun lafiya daga kowane irin ciwo ne ma ke damunta.

Har wajen sha biyun dare Imran be rintsa ba, yana gadin Amira.

Bacci ne ya ɗan sace shi, ba tare da ya sani ba baccin nasa ya fara nisa sosy.

Cikin baccin ya kuma jin hargowarta, ya buɗe idonsa a razane, ya ga ta sake cire kayan jikinta tana ƙoƙarin buɗe ƙofar, se jijjiga ƙofar take tana waige waige tana ihu.

Imran ya janyo ta, ya rirriƙeta ya dinga karanta mata duk abinda yazo bakinsa, sedai ga mamakinsa da ta fara abun seta fara yunƙurin faɗuwa, dan yau kam ta faɗi be san iyaka ba.

Ihsan kuwa tsaki tai, dan sun uzzura mata, Amira ta hanata sakewa da ihun da takeyi.

Ta taso ta kulle ƙofar part ɗin ta tace "Ai kaɗan ma kika gani, da haka hauka har abada haka zaki tayin shi, ba ke ba hankali har abada, zaki san kin auri mijina, kina ƙoƙarin mallake shi, kaima da ƙafafuwanka zaka dawo, idan kaga ta haukace ta dena amfana maka Komai"

Taja tsaki ta rufe ƙofarta.

Imran kuwa yadda yaga rana haka yaga dare, sam ne rintsa ba saboda yadda larurara Amira ke neman shallake tunanin sa.

A nan ɗakin nata yai sallar Asuba, ga abun damuwar ita bata hayyacinta gaba ɗaya balle a samu tai sallar.

Bayan ya idar da sallar Asuba, tana sume, haka yai mata wanka ya kintsa ta, ya sa ta a mota ya fita.

Ƙarfe Bakwai saura se gashi a gidan Anty.

Fadila ce ta buɗewa Imran ƙofar falo, ta ganshi da Amira a hannunsa, ta bashi guri ya shiga yaje ya kwantar da ita.

Fadila tace "Imran, lafiya kuwa? Meya sameta haka? Jikin ne dai?"
Imran yai ajiyar zuciya yace "kuyi haƙuri na zi muku da sassafe, jiya sam ba muyi bacci ba, na kasa gane kan Amira gaba ɗaya"

Yai maganar cikin karaya, Fadila tace "Subhanallah, insha Allah zata warware, bari inwa Anty magana"

Fadila ta shiga ciki, Imran kuma ya zubawa Amira ido dake shimfiɗe kamar ba rai a jikinta.

Anty na fitowa tai salati tace "Imran ba dai jikin ne ba?"

Imran kamar ze kuka yace "Anty na tsorata da abun da Amira ta yi, daga tafiyar ki jiya zuwa wayewar gari, kayan jikinta take cirewa tana ihu, wai ƙadangaru ne suke binta, faɗuwa kuwa ta faɗi ba'a dadi se suma, da ta farka se ihu, Allah yasa ba wani abu ne ya sameta a ƙwaƙwalwa ba, Allah ya sa Amira ba taɓun hankali ta samu ba"

Abun mamaki sega ƙwalla a idon Imran, Anty tace "haba Imran, ka kwantar da hankalinka ka karɓi ƙaddara a yadda tazo maka, ni nafi tunanin wannan ciwon nata shafar aljanu ne, ina ga gurin masu ruƙiyya zamu"

Fadila tace "ko kuma Asiri a kai mata ba"

Anty tace "ƙaniyar ki, wane irin Asiri kuma ana zaune ƙalau? Waye ze mata wani Asiri? Duk abunda ya samu bawa yace Allah karya kuskura yace wani ne yai masa, Allah da ya ɗora maka ze yaye maka, idan ma wani ne Allah yana kallo, kul na kuma jin zamcen Asirin nan"

Fadila tai ajiyar zuciya kawai, wannan abu in ba Asirin ba, shekaranjiya suna tare da Amira lafiya ƙalau, suna shirin dawowar Imran, katsam kuma se a wayi gari daga dawowarsa ta zama haka?

Imran yace "Anty meye abunyi to?"

"Abunyi shine kaje gida mu gani, idan ba ta ganinka ko zata da wo hayyacinta sosai, idan kuma ba haka ba dole ma dai se an dangaan da malaman ruƙiya'"

"Ai ni Anty bana son ayi abun kauce hanya ne, ko ai shirka"

"Haba Imran, kamar banje Islamiyya ba, ai da ayar Allah za'a mata magani, kaje gida bakomai Allah ya yaye mata"

Imran yace "Ameen" ya muƙe ze tafi, ya zubawa Amira Ido, daga jiya zuwa yau tayi wata uwar rama, duk tayi wani iri.

Ya girgiza kai ya fita jikin sa a sanyaye, saboda ya tsorata da lamarin Amiran.

Gidan Anty Hadiza ya nufa, duk da da 'yar tafiya daga gidan Anty zuwa gidan Hadiza, amma haka Imran ya tafi.

Yai sa'a mijinta ya fita kai yara makaranta daga nan ze tafi Office.

"Imran lafiya na ganka da safiyar nan? Yaushe rabonka da gidana tun da na ganka taka ce ta kawo ka"

Imran ya jinjina kai ya zauna cike da damuwa yace "Khadija ina cikin damuwa, bani da mataimaki se Allah, Ammi yakamata in kaiwa damuwata, sedai ba dama kullum sedai cikin zarya nake gidan Alhaji Hashim, Anty ke min komai, na fara jin nauyin baiwar Allah nan ina ganin kamar ina ɗora mata nauyi da yawa, ke kuma ba wani shiga cikin mu kike ba kina gefe, tunda ba a gidanmu kika tashi ba, bana son ma Ammi tasan wani abu, shima faɗa za tayi"

"Ni se wata magana kake sama a ƙasa, meyafaru wai?"

"Khadija, Kin san dai Ammi ba ta son Amira tana ce mata karuwa"

"Eh na sani"

"Khadija wallahi Amira ba karuwa bace, ni kaina nayi mamaki gami da nadamar abunda nai mata a baya, Amira ba karuwa bace"

Khadija tace "ai ni Anty ce ta fara gayamin, tace a zaman da tai da Amira, da yadda tabi hikimomi daban daban, bata ga wani abu da ya nuna Amiran karuwa bace"

Imran yace "duk da tarin wulaƙanci da na dinga mata, ban taɓa bata hakkinta na Aure ba, se tafiyar nan da mukayi Lagos tare, a nan na gane ba karuwa bace, katsam Allah ya bata rabo"

Khadija tace "Ahh masha Allah, abun ba labari, kace Mun kusa ɗaukar ɗan Imran"

"Khadija ki dena wasa mana, Ammi taje har gida taci mutuncin Amira, tace bata yadda ba ma wai cikin ba nawa bane, ga Ihsan ta haɗa min zafi ta tayar min da hankali, saboda kishi da rashin mutunci, nayi nayi ta bini muje Lagos tare taƙi, nika ɗai na tafi, seda nai wata biyu na dawo, sedai tunda na dawo Amira ma ta birkice, da ta ganni se ta fara ihu tana zabure zabure wai ƙadangare take gani a jikina"

"Ƙadangare kuma?"

"Eh, wallahi jiya ko bacci ba muyi ba, tai ta cire kayanta tana ihu, Allah yasa ba haukacewa za tai ba"

Khadija tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu Ina Amiran take?"

"Tana gidan Anty na barta"

"Meyasa baka kawota nan ba? Ni matsalata da kai zurfin cikinka yai yawa Imran, ni laifi ne idan ka kawomin ita nan? 'yar uwata ce fa ƙanwata ce, ai ba zamu haɗu mu biyewa Ammi ba"

"To aini gaba ɗaya na rasa abunyi ne deeja"

"Shikenan, kar ka damu insha Allah zata warke, ka koma gida zanje in duba ta amma ka kwantar da hankalin ka"

Taita rarrashin sa, ta sa shi yaci Abinci sannan ya tafi gida.

Abun takaicin da yaje gidanma, Ihsan ta wanke ƙafarta ta fice nata guri, dan sam abunda ya samu Amira be dameta ba.

Amira kam har Azahar sannan ta farka, ta ganta a gidan Anty, ta kalli Fadila tace "yaushe na zo nan?"

"Imran ne ya kawo ki"

Ɗan zaro ido Amira Tayi tace "dan girman Allah kar ku bari yazo in da nake, wallahi ƙadangaren jikin sa ze kasheni"

Fadila tace "Ai ba ya nan, ya koma Lagos ma gaba ɗaya"

Seda Amira ta ji haka sannan hankalinta ya kwanta, Anty ta shigo tasa Amira tai alwala, ta rama sallolin da ake binta, ta ɗau Alqur'ani tana karantawa.

Anty tana gefe tana kallonta, Imran ya kira Anty a waya dan jin ya jikinta, Amira na jin muryar Imran a waya, ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta.

Abun ya ɗaurewa Anty kai sosai, tabbas maganar Fadila akwai ƙamshin gaskiya a ciki, ze iya yuwuwa sihiri ne a kaiwa Amira, ko muma dai sheɗanu ke damunta.

Anty ta kawar da duk wani abu da zesa Ayi ko da zacen Imran gaba ɗaya.

Da daddare Anty Hadiza taje duba Amira, sedai tayi mamakin ganin yadda Amiran tai wata uwar rama, duk ta canza kamanni.

Anty Hadiza ta jimanta yadda taga jikin Amira, abun ya shallake yadda take tunani sosai.

Amira ko zancen Imran ba ta son ji, kowani abu da yake da alaƙa da shi, idan har ba za'ai mata zancen sa ba to zata zauna lafiya ƙalau, amma da anyi zancensa za ta fara zabure zabure kamar za ta hau bori.

Anty ta dage da saka karatun Alqur'ani ba dare ba rana, dan Amira yanzu ko san ibadar ba tayi, seta takura mata take salla, ta yi azkar ga ciki na ƙara girma yana fitowa dan ya shiga wata na shida, amma wani lokacin idan abun ya motsa, haka zata ga ƙadangarun nan na binta, ta miƙe tana ihu tana cire kayan jikinta, haka za ta faɗi ƙasa ga ciki a jikinta.

Imran ma yai muguwar rama, ko Abincin kirki baya iya ci, kullum cikin yi wa Amira Addu'a yake, akan Allah ya bata lafiya, ko tambayar Anty ze ya jikin Amira sedai ta chat ko message, in ba haka ba da taji da shi ake waya zata rikice.

Ihsan kam ko da wasa ba ta taɓa tambayarsa ya me jiki ba, ba abunda yai mata zafi yawonta ma ta sa a gaba, ko ta tambaye shi ko bata tambaya ba ba ya hana ta ficewarta, ko gurin aiki ko gurin ƙawayenta.

Imran ya tattarata ya watasar shima, ya koma ɓangaren Amira ya tare gaba ɗaya, idan ya tuna irin Karamci da soyayya da haƙuri da Amira take da shi, da kawaici ya tuna halin da take ciki yanzu gaba ɗaya se jikinsa yai sanyu, ya shiga damuwa.

Da safe yana shirin fita, dan yana sa ran washegari ze koma aiki, Ammi ta kirashi a waya tace yaje gida tana son ganinsa.

Haka ya shirya ya tafi, sedai kamar kullum yana zuwa ƙorafine da faɗa akan Ihsan.

Imran yace "Ammi baki san halin da Amira take ci ba? Ammi Amira na fama da larura gaba ɗaya hankalina ba'a kwance yake ba, na rasa ya zanyi"

"To Ihsan ce ta ɗora mata da zaka tattara ta kai watsi da ita? Ko kuwa ba ta da haƙƙi akanka ne? Ba ruwanka da ita ba ruwanka da Abincinta ba ruwanka da komai na ta, haka akeyi, ko ita ta ɗora mata?"

Wani irin takaici ya kama Imran, ita Ihsan kwananta nawa da ƙaurace masa, amma ta samu bakin kawo ƙararsa dan wulaƙanci da rashin sanin ciwon kai.

"Ammi, yanzu rashin lafiyar Amira ba abun dubawa bace? Haba Ammi Amira fa mutum ce ba dabba ba, yau ko dabbace idan tana cikin halin larura zaka tausaya mata, Ammi yau ko kafiri da yafi kowa saɓon Ubangiji Allah yana son kayansa tun da ya halicce shi, ballanta na Amira da abunda take aikatawa daban abunda ake zargin ta da shi daban, kuma ko hakane abunda ake faɗar tana aikatawa, ta cancanci a tausayawa halin da take ciki Ammi, marainiya ce ki hasaso ace ba ranki ne makamancin halin da Amira ta shiga ya faru da wani daga cikin mu, haba Ammi ke fa uwace"

Ya ƙarasa maganar cikin matsananciyar damuwa, ya tashi ya bar mata gidan gaba ɗaya.

Gidan sa ya wuce ya tafi cike da damuwa, yana zuwa ya tarar da Ihsan ta naɗe a falo tana kallo tana cin chips.

Ya je ya kashe tv ya kalleta a fusace yace "Ihsan ban taɓa tunanin rashin imaninki ya kai haka ba, kina kallon halin da abokiyar zamanki ke ciki amma ko a jikinki"

A fusace ta kalleshi tace "to me kake so in muku? Ni na ɗora mata ina ruwana da abinda ya sameta kai ta shafa kai da ita, kuma hakkina ne ya kama ta, dama ƙarshen karuwa kenan, Allah ne ya tashi kamata"

Imran ji yai zuciyarsa tana wani irin tafasa, yaji kamar ya shaƙo Ihsan ya kakkaryata kowa ma ya huta.

Ya dage ya daidaita nutsuwarsa, kawai ya bar falon.

Ta raka shi da harara tace "ai baƙi ciki yanzu ka fara, sema kaga ana ɗaɗɗaure ta, ana kai ta gidan mahaukata tukuna za kayi bayani"

Ta tashi taje ta sake kunna television ta cigaba da kallonta.

Washegari da asubar fari, ko sallama Imran be wa Ihsan ba ya tafi, ya koma Lagos.

Abba ya dawo Kaduna, ko gida beje ba ya tafi gidan Alhaji Hashim, dan duba Amira, Sedai shima yayi mamakin ganin yadda Amiran ta koma.

Yaga da gaske sam ba ta son zancen Imran, ga duhu da rama tayi.

Suka tatauna da Anty, suka tsaya akan ai ta mata saukar Alqur'ani ba abunda ya gagari Allah.

Imran yana gurin aiki amma hankalinsa na Kaduna kan halin da Amira ke ciki, kullum cikin addu'a yake Allah ya yaye mata abun da ke damunta.

Kusan watannin Amira biyu a haka, aka samu ta dena guje guje da ƙoƙarin cire kayan jikinta, sedai ba ta Magana, dan seta wuni ba tace uffan ba.

Abba ya samu Ammi da faɗa, ya nuna mata matuƙar ɓacin ransa akan rashin nuna damuwa da halin da Amira ke ciki, dan ko duba ta ba ta je ba.

Ba shiri Ammi tai shirin zuwa duba Amira, saboda tijarar da ta sha a gurin Abba.

Ta fuskanci yadda ran Abba ya ɓaci komai ma ze iya aikatawa, dan haka ta lallaɓa shi, ya kaita gidan Anty da daddare ta duba Amiran.

Tun da su Ammi suka shiga falon, ta zubawa Ammi ido, Abinci ne a gabanta tana cakala, Anty na ta takura mata ta ci.

Ammi tayi mamakin yadda cikin Amira yai girma sosai.

Tunda suka shigo, Amira ta ƙurawa Ammi ido.

Abba yace "Amira, ya akayi ne?"

Amira ta fashe da kuka tace "Abba ka ganta ko, ta hana Imran ɗina zuwa gurina, ya dena zuwa in da nake, ya dena kulani ya tafi ya barni" tai maganar kamar ƙaramar Yarinya tana kuka.

Anty tace "Amira dagaske kina son ganin Imran?"

Amira ta jinjina kai tana kuka tace "bayan ya dena zuwa gurina, kuma ina son in ganshi"

Abba yace "to ai ke kika ce ba kya son yazo in da kike"

"Ni bance ba, ina son in Ganshi"

Abba yace "Alhamdilillah, sauƙi ya fara samuwa, Allah ya krɓa mana"

Ammi tace "haka dama ta koma?"

Anty tace "mhmm, me zamu ce Jamila? Ai naga baki damu da halin da take ciki ba"

Ammi za tai Magana aka kira Abba a waya, yana ɗagawa aka sanar da shi, Imran ya faɗi a gurin aiki, an kai shi Asibiti jininsa ya hau, baya gane wanda yake kansa ma!!!

Amin afuwa ban editing ba, kuma ina cikin sabgar biki ne, ayi haƙuri.

Ayshercool
07063065680

Continue Reading

You'll Also Like

7.1K 310 36
labari mai matukar ban tausayi, son zuciya, soyaaya mai zafi da shiga rai, hadi da nadama.....
180K 4.1K 53
❝ i loved you so hard for a time, i've tried to ration it out all my life. ❞ kate martin x fem! oc
38.4K 3.3K 22
'YA CE kamar kowa wadda ta taso cikin ɗabi'a da al'ada irin ta BAHAUSHE! "Me ta ke so? Me nene burinta?" Babu wanda ya taɓa tambayarta. Kalma ɗay...
216K 1.1K 33
This is a mix of different animes that have smut in them