WUTA A MASAƘA

By Ayshercool7724

27.4K 1.6K 154

labari akan wata yarinya me rawar kai da rashin jin magana sam, labari akan taɓarɓarewar zumunci, tarbiyya da... More

WUTA A MASAƘA
WUTA A MASAƘA 2
3
WUTA A MASAƘA 4
CHAPTER 5_6
7_8
9_10
11_12
WUTA A MASAƘA 13_14
WITA A MASAƘA 15_16
WUTA A MASAƘA 17_18
WUTA A MASAƘA 19_20
WUTA A MASAƘA 21_22
WUTA A MASAƘA 23-24
WUTA A MASAƘA 23_24
WUTA A MASAƘA 27_28
WUTA A MASAƘA 29_30
WUTA A MASAƘA 31_32
33_34
35_36
37_38
37_38
39_40
41_42
45_46
47_48
47_48
49_50
51-52
53_54

43_44

1K 53 10
By Ayshercool7724

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

43_44

Se da Amira ta saki ƙara, sakamakon yadda Imran ya janyo ta da ƙarfi sosai.

Ba sani, ba sabo, ba tausayi, ko sassauci Imran ya aikata abunda zuciyarsa ke raya masa akan Amira, ya aikata abunda yake so kansa tsaye, ba tare da wani tausayi ko rangwame ba, sedai kash duk yadda ya zaci abun ba haka yake ba, saboda abunda ya tarar ya girgiza shi ya bashi mamaki matuƙa, he never thought that Amira was virgin.

Seda ya dawo hankalinsa yaji wata irin nadama ta saukar masa, dan kusan abunda ya aikata ba shi da maraba da Fyaɗe, sedai kawai dan matarsa ce, ya kalli in da Amira ke kwance kukan nata ma ba ya fita, se sheshsheƙa da ajiyar zuciya kawai da take yi.

Hannu bibbiyu ya sa ya dafe kansa, yai shiru yana tunani daban daban a zuciyarsa, kunya da tarin Nadama suka baibaye shi.

A hankali ya kuma kallon Amira, jiki a sanyaye yace "Sannu"

Bata ko motsa ba balle ta amsa, ta cigaba da kuka.

Ya janyo bargo ya lulluɓe ta, ya miƙe jiki a sanyaye ya bar ɗakin.

Gaba ɗaya Amira ta kasa banbance a halin da take ciki, a sume take ko a farke ta kasa ganewa.

Ɗagota Imran yai daga kwanciyar da take, ya ɗaura mata towel, yana ƙoƙarin ɗaukanta amma ta bige hannunsa ta sakko daga kan gadon.

"Ki tsaya in taimaka miki mana, na kai miki ruwa toilet ɗina"

Wani banzan kallo tai masa tace "bana so"

Ta lallaɓa jikinta, ta shiga ban ɗaki, ta nemi guri ta zauna, tana zubar da hawaye.

Imran kuwa sake zama yayai yana tunani, ta yaya Amira zata zama virgin? Dama haka tana faruwa ko kuwa dai dama duk abubuwan da take ba ta aikata Zina?.

Nan damuwa ta tarar masa, ya dinga tunani daban daban, yana cikin tunanin ta buɗe ƙofar banɗakin ta fito.

Imran ya tashi da sauri ya tafi inda take, yana jera mata sannu, sedai a sannun nasa ko ɗaya ba ta amsa ba.

Ta nufi ƙofar fita daga ɗakin.

Da sauri yace "ina kuma zaki? Ki zo ki kwanta a nan, in duba first-aid box ɗina, in baki magani"

"Bana so, ba zan sha ba ka riƙe abunka Imran, ai ni be kamata ka tausayamin ba, saboda Karuwace ni da aka tirsasa ka Aura dan ka taimaka Mata, Alhamdilillah yau burina ya cika, kaine ɗa namiji na farko da na fara sani a rayuwata, kuma kaima ka sheda hakan, dan haka daga rana me kamar irin ta yau, kar ka sake kirana da Karuwa, kuma ka sanar da matarka da 'yan uwan ka ni ba Karuwa bace, abunda yake hanani maida martani idan an gayamin Karuwa, shine bani da hujjar kare kaina, Yanzu kuwa na samu wallahi duk wanda ya kuma cemin Karuwa dai dai nake da shi, zan mayarwa mutum daidai da abunda ya gayamin, ni ba Mazinaciya bace, bana aikata zina ban taɓa ba kuma ba zan fara ba, Imran kome na zama A duniya duk lalacewar da nayi a duniya da sa hannunku a ciki kune sila, kasan irin baƙar wahalar da na sha kuwa? Ka san irin raɗaɗi da zafin maraici kuwa,? Maraici na rashin uwa da uba, kuma na tashi a tsakanin maƙiya, mahaifiyarka taƙi karɓata, na tashi ina gararanba a gari wasu lokutan abunda zanci ya gagarrni, bayan tulin aikin da nake kamar jaka, ba wanda ya damu da ina jin yunwa, ƙishirwa ko bani da lafiya, ba wanda ya damu da wani kalar Abinci zanci a ina zan kwanta, saboda na rasa babban jigo abun jigina wato iyaye, ina da ɗan uwan mahaifiya a raye me tarin dukiya, amma na kasa samun gata, kiyayewar Ubangiji ita ta tsareni har na kawo wannan lokaci, amma idonku ya rufe kun gaza ganin naku laifin, kullum se jifana da muguwar kalma me muni, me ɗacin gaske Karuwa, hmmm don't try to pretend that kana jin tausayina yanzu, a baya na fi buƙatar tausaya wa, da ja a jiki amma ban samu ba, se baƙin wulaƙanci da na fuskanta a gidan ka, bakomai Allahn da ya ɗauki iyayena ya na ƙaunata kuma baze bari in taɓe ba"

Tai maganar hawaye wani na bin wani, tai ficewarta da ga ɗakin, ta tafi ɗakinta ta faɗa akan katifa ta sake fashewa da kuka.

Imran kuwa kasa motsi yai, Lallai an Cutar da Amira da kalma me munin gaske, amma koma da maraici wani abun ita ta janyowa kanta, dan babu yadda Za'ayi mutum yana aikata abunda takeyi ace ba Iskanci take ba, ga raye raye, ga shigar banza da gantali ga tsantsan fitsara da rashin kunya, ba wanda ze yadda ba karuwa ba ce.

Haka Imran yaje yai wanka, duk jikin sa a saluɓe, ya gyara gadon ya nemi guri ya kwanta, tunani duk ya cika masa zuciya tare da matsanancin tausayin Amira.

Da gari ya waye, da kansa yai gyare-gyaren gidan nan gaba ɗaya, ya dafa tea da yake ba wani iya girki yai ba yavfita ya siyo bredi.

Sedai har ƙarfe goma Amira ba ta fito ba, wanda ƙa'idar ta bata wuce ƙarfe takwas duk baccin da za tai, ɗakinta ya nufa ya shiga da sallama, ya hangota kwance akan katifar dake ɗakin a cikin bargo.

Ya ƙarasa ya ɗan janye bargon, ya daddaki filon da ta ke kai yace "Amira ki tashi ki karya, rana ta fara yi, idan yaso in kin karya se muje ko Asibiti ne"

Ƙare masa kallo tayi tace 'meye naka a ciki, da in karya ko kar in karya? Ina ruwanka dani Karuwa ka ƙyaleni mana"

"Naji amma kiyi haƙuri ki tashi, se muje ko Asibitin Barrack ne a duba ki"

"Muje Asibiti kace musu me, You rape your wife because you thought she's not virgin? Haka zaka gaya musu? To ni ba haka nake ba, ko da nake karuwa na san daidai, ba zan taɓa fallasa Asirin Aurena ba"

Imran yace "Amira rape kuma?"

Cikin hawaye tace "akwai maraba da rape da abunda kaimin jiya ne? Babu maraba ai, kuma ka dena wani pretending kana lallaɓani, dan ka samu wani abu daga gareni, seka sakeni daga Garin nan Kano zan koma na gama Aurenka"

Haɗe rai yai yace "dan kinga ina lallaɓaki shine zaki dinga gayamin Magana?"

Tashi zaune tayi tace "An gaya maka ɗin, na faɗa kaji haushi ka rabu dani"

"Naji, amma muje ki karya"

"Ba zanci ba"

Tai maganar tana Share hawaye, Ƙarshe Imran se tashi yai ya bar mata ɗakin, abun duniya ya ishi Imran, tabbas anwa Amira ba daidai ba, mussaman yadda ya dinga dizgaya da kalamai marasa daɗi.

Wunin ranar haka dinga koke koke, kuna taƙi saurarar Imran.

Imran yana ɗakinsa ya kira Khalid a waya.

"Kai lafiya kake kirana a daren nan? Ya kake ya Lagos?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, Amma fa akwai matsala ina cikin damuwa"

"Sarkin matsala, meke faruwa Kuma?"

"Khalid, Amira ce, naiwa Yarinyar nan ba daidai ba, Amira ba Karuwa bace, abun ya bani mamaki, how could this be possible, and worse part of it is that, ta dage wai sena saketa ta koma Kano, ni wannan be dameni ba, ina jin kunya akan abunda nai mata"

Khalid yace "kaga abunda na dinga gaya naka kenan a baya, amma kai kunnen uwar shegu dani Imran, na gaya maka ka sassauta ƙiyayya akan Yarinyar nan, duk da dama can kan son ta, son zuciya ne ya rufe maka ido, kawai seka haƙura ku rabu tunda haka take so, da ka cigaba da gallaza mata"

"Wane irin in saketa kuma? Kaifa ka fiye abun haushi wallahi, wane irin in saketa?"

"To in baka saketa ba me zaka mata? Ace ka Auri yarinya over 4_5 month, amma baka taɓa sauke hakkinta na Aure ba, da lafiyar ka da Komai ka tare a gurin mace ɗaya, gaskiya ba kayi adalci ba, kuma wallahi na goyi bayan ka sawwaƙe mata, tunda ba ka da adalci"

Tsaki Imran yai ya kashe wayarsa, dan kalaman Khalid sun fara fusata shi.

Yai shiruu yana zancen zuci se ga kiran waya, yayi mamakin ganin lambar Ihsan, ya sa hannu ya ɗaga,
"My"

"Na'am Ihsan" ya kira sunanta.

"My ka manta dani baka ta tawa ko?" Tai maganar cikin kuka.

Imran yace "Ihsan me zance, ko ya zan dake? Na taho amma kika kasa kirana a waya, ni ban fushi ba na kiraki a waya, amma nai miki miss calls kusan goma, amma ki ka gaza ɗaukar ko guda ɗaya, ya ki ke son inyi?"

"Wallahi ina kishinka da kewar ka Imran, na kasa samun nutsuwa ko Abinci ba na iya ci, gani nake komai ze iya faruwa, hankalina yaƙi kwanciya sam"

"Ihsan dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki dena ta da hankalinki kar ki saka wani ciwon a kama min ke dan Allah"

"Imran ba zan iya ba, zuciyata kamar zata tsaga ƙirjina, dan Allah ka dawo please"

"Ihsan ta yaya zan dawo? Aiki fa nake yi a nan ɗin"

"Imran zuciyata ta kasa jurewa, dan Allah ka dawo gida"

"Ihsan, kin san ba abune daze yuwu ba, in baro aiki na in dawo ba, kuma kin san nam kusa baza'a bani wani pass ɗin ba"

"Au haka kace? Shikenan nagode Imran, ka dena sona ka dena damuwa dani, koma meye inje baka damu ba ya sameni, shikenan" ta katse wayarta.

Imran yabi wayar da kallo, be taɓa zaton Ihsan na da wannan halayen ba, na tsananin kishi haka da ƙorafi ba, a waje sam ba ta nuna masa wannan halin ba se yanzu, shikam a yanzu duk sedai kowa ma yai haƙuri dan aikin gama ya gama.

Amira kuwa zuwa kwana uku ta samu sauƙi, da ƙwarin jikinta, sedai sam ba ta shiga sabgar Imran, ko girki idan tayi a Kitchen take ajiye masa nasa, ko gaisheshi ta dena yi, harkokinta kawai take, ga fitinanniyar shigar da takeyi ko yana nan ko baya nan, hakan ba ƙaramin hana Imran sukuni yake ba, sam baya jin daɗin yadda take shareshi, take nuna halin ko in kula a gareshi, gefe guda ga wata irin fitana dake damunsa akan Amira, amma yana jin nauyin tunkararta, saboda yasan iya Rashin kyautawa ya aikata mata.

Imran ya dawo daga gurin aiki a matuƙar gajiye, ya zauna a falo da shi da takalminsa da jakarsa, ba wanda ya kai ɗaki ya kashingiɗa ya lumshe ido, Amira ta fito daga ɗakinta sanye da mini skirt da kuma vest, hannunta riƙe da cup taje ta zauna.

Imran ya buɗe ido yana ƙarewa surar jikinta kallo, ya ɗanyi gyaran murya yace "Sannu da gida"

"Yawwa sannu da zuwa"

"Ko zan iya samun Abinci?"

Yana Kitchen ta bashi amsa.

"Dan Allah ki kawomin, na gaji sosai"

Da farko shiru tayi kamar ba taji meya yace ba, se kuma ta tashi ta kawo masa, tana gama ajiyewa ta miƙe zata tafi yace "Ki dawo ki zauna mana"

"A'a zanyi abu a ɗaki ne"

Imran yace "ok shikenan, amma dan Allah ina neman wata alfarma ne"

"Ok ina jinka"

"Dan Allah ina son zaki rakani wani taro ne, in Allah ya kaimu Ranar Saturday"

Kallonsa Amira tayi tace "ba inda zani, wake ado da Karuwa har ya ɗauketa ya shiga da ita taro, wannan ai aikin Ihsan ne matan ƙwarai, ta biyo jirgi ta taho ta raka ka"

"Eh ai yanzu ke nake so ki rakanin tunda ba ta nan, kowa zeje da wani nasa, nikuma kinga daga ni seke a nan"

"Ni da bani da amfani, me zanje in maka? Ko ka manta kace idan kazo dani ba wani amfani da zan maka, idan ka manta ni ina sane"

Tana gama Maganara ta wuce ɗakinta tana cigaba da mita.

Imran yai shiruu, Amira ƙanwarsa ce, gari banza ba ta isa gaya masa Wannan maganganun ba, amma da yake yasan shike da laifi ba abunda ze iya yi mata sedai ido.

Ba yadda be da Amira ba akan ta rakashi, amma tace ko me zeyi ba zata ba.

Haka Imran ya dinga fama da Amira, gefe ga Ihsan da ke kiransa tana sake sauke masa nata shirmen, harya ka ya dena ɗaga wayarta, saboda ɓata masa rai da take yawan yi.

Ranar da Imran zeje taron, bayan ya dawo daga sallr magariba ya shirya ya fito, sedai yana fitowa yaga Amira ta sha Kwalliya cikin doguwar riga dark blue, wadda taji aikin stone Sosai, se walwali suke, ya tsaya yana kallonta, tace "muje ko?"

"Zaki rakani ne?"

Tace "eh"

Imran yai murmushi yace "Masha Allah, muje"

Suka fito tare, Imran ya rufe gida, suka shiga motarsa suka fita.

Tunda Amira ta zo garin nan bata taɓa fita ba ko sau ɗaya se yau, duk da duhu ya fara yi amma hakan be hanata yin kalle kallenta ba, wani Guri suka je Imran yai parking ya fito, amma ita bata fito ba.

Imran yace "munzo ai, ki fito"

"Ina ne nan?"

"In da zan saida ke ne?" Ya bata amsa.

Ta fito tare da faɗin "ai ko ka saida ni ba daraja zan ba, Saboda kasan na gama bin kwararo"

Imran bece komai ba, ya rufe motarsa yai gaba tana binsaa baya.

Wani ƙawataccen ɗakin taro suka shiga, mutane na ta shiga suna fita, wasu da shigar hankali wasu da ta ban haushi, kasancewar gamayyar musulmi ne da wanda ba Musulmi ba.

Imran ya kai Amira wani teburi yace "ki zauna a nan ki jirani, zanje in canza kaya"

Ƙin zama tayi tace "haka kurum, wallahi ba zaka tafi ka barni b, muje tare"

Haka ta bishi har inda ze canza kayan, ta jirashi ya canza ya fito, suka zo suka zauna.

Suna zama ba daɗewa aka fara Rabon Abinci da drinks, Amira tace "wai me za'ayi a nan ɗin ne?"

"Walima aka shiryawa wanda suka samu ƙarin matsayi, da wanda sukai ƙoƙari agurin yaƙi"

Suna maganar aka kawo musu Abinci, da lemuka aka ajiye musu, shinkafa ce fried rice, ta sha kayan lambu ga danƙwaleliyar kaza akan kowanne.

Amira tace "gaskiya nifa ci zanyi"

"Ai dama dan kici aka baki, nima zanci ai"

Amira ta kalli Abincin Imran, ta sa cokali ta ɗauke kazar kan Abincin Imran tace "Wannan kazar dani ta dace, kai ba'a so kayi ƙiba, ni kuma kaga dama can ina da ƙibata"

Imran yace "haka akeyi, a baki taki a bani tawa kice se kin cinye da tawa?"

"Eh ɗin, duka zan cinye na bar maka shinkafar"

"Amira muna da kaji a gida fa, karki ba da mu mana Please"

"Abunka da 'yar ƙauye ai sedai kayi haƙuri kawai, kuma ma aini baka saimin kazar amarci ba, amma ka saiwa Ihsan"

Imran yace "hmm rigumammiya, ai seki cinye"

Yaja shinkafarsa ya fara ci, wasu couples a kusa dasu, duk da basa jin hausa amma su Imran sun burge su, dan ba ƙaramin dariya suia basu b, kai kace wasu masoyane da suka daɗe suna shan soyaya.

Wata soja ce tazo wucewa, ta kalli Imran tace "ya na ga kana cin Abinci ba nama, garin yaya"

Imran ya nuna mata plate ɗin Amira yana murmushi, matar tayi dariya tace "kace anfi ƙarfinka ne, bari akawo maka wata"

Amira tace "ya ƙoshi"

Imran yace "ba se kin kawo wata ba, wannan ɗin ta isa" matar ta wucesu tana musu dariya.

"Kin sa ana kallonmu, muna faɗa akan kaza"

"Eh munyi ɗin ina ruwan wani, wai wannan matar me kama da maza itama soja ce, na ganta da wandon sojoji"

"Allah yasa taji ki, zaki bayani"

Kamar kasan da tana min magana, kawai hangowa nai ta nausheni, dan na ɗauke maka kaza, wai da daga nan se Asibiti emergency, dan wannan hannun nata kamar itace, kamar ba na mace ba, kuma ta na da miji?" tai maganar tana dariya.

Imran kallon Amira yake, she's very Funny and jovial.

Yace "tana da miji hadda yara"

"Taɓ lallai"

Ta sa fork da spoon tana yanko kazar, tana bawa Imran a baki yana karɓe kayarsa.

Aka fara kiran wanda za'a karrama, tace "wai kai baza'a baka ba?"

'ai ban dani, masu ƙwazo ake bawa"

"Kai, ana nufin kai baka da ƙwazon ne? Da na san baza'a baka ba da bzan zo ba wallahi"

Tana cikin mitar aka kira Imran, zumbur ta miƙe tana tafawa Imran, tace "You deserve it dear".

Imran yai murmushi ya kama hannunta, suna tafe ana musu hoto yaje ya karɓo ƙaton frame ɗin da aka bashi, da hotonsa da sunansa, da rank ɗinsa na major, kan a bashi seda aka dinga koɗashi, ana faɗar jajircewarsa.

Amira kamar ita aka bawa, ta karɓe frame ɗin ta riƙe.

Suka dawo in da suke zaune su ka zauna, tace "da ba'a baka ba da tafiyata zanyi"

"Kin san hanya ne in kin tafin"

"Ai da tare zamu tafi, amma tunda an baka tashi Mu tafi gida"

"Ki tsaya a ƙarasa, Yanzu za'a gama"

Basu baro gurin nan ba se bayan goma na dare, tun a hanya Amira ke gyangyaɗi.

Seda Imran ya tsaya a hanya ya sai gasassun kaji, da youghurt me sanyi, sannan suka tafi gida.

Suna zuwa ta bar Imran da kaji, tai ɗakinta da frame ɗin nan, ta na zuwa tai wanka haɗe da alwala ta fito tai salla.

Har ta kwanta Imran ya shigo yace "ga kazarki can na biya a dena min gori, kuma naga kin zo kin kwanta ba ki ci ba"

"Se da na roƙa za'a saimin, na ƙoshi se gobe in Allah ya kaimu zan ci"

Ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita akan katifar, yace "to bani frame ɗina"

"Taɓ, ai ba zan bada wannan frame ɗin ba, idan mun koma gida a falo na zan kafe shi"

"Kin haƙura zamu koma taren ne?"

"A'a, Kano zan tafi, daga nan ba zan tsaya ko ina ba se Kano"

Imran yai ƙasa da murya yace "wai ke meyasa abu baya wucewa a gurinki ne? Ba in da zaki koma se ɗakinki"

"Nifa ka dena wannan kashemin Muryar, dan nayi Imani da Allah da ka sameni saɓanin budurwa haka zaka cigaba da min wulaƙanci, kuma na da baka so, ai matar so ta isheka, ni temakamin a kai"

Shiru Imran yai, be kuma cewa komai ba yana ajiyar zuciya, bi sa kasada ya jarraba Amira ko zata yadda da shi?

Bisa ga mamakinsa, ba taurin kai ba gaddama ta ƙyaleshi yai budurinsa, abun ya bashi mamaki sosai, tabbas yasan da Ihsan a matsayin Amira, ba zata taɓa yadda da shi ba.

Imran ne ya fara tashi ya shiga yai wanka, da kansa ya haɗa mata ruwa itama, bayan ta fito daga banɗakin ta tarar da shi kwance akan katifar.

"Ya naga haka?" Tai maganar tana ɗan haɗe rai.

Imran yace "me kika ganin?"

"Ka tafi ɗakinka mana kwanciya zanyi"

"Ai a nan zan kwana"

"Saboda me?"

"Saboda nan ɗin ɗakin matata ne"

Wani kallon banza Amira taiwa Imran, a ranta tace "lallai wasu mazan halinsu se Allah, ji yadda ya ke wani kwantar da murya wai ɗakin natarsa"

Amira tace "matarka dai Ihsan ba Amira ba"

"Amiran ma matata ce"

"A yanzu ba, amma a baya ai ni ban kai a kalleni a matsayin matar ba"

Amira ta dinga masa tsiwa son ranta, amma Imran ya gaza cewa Komai saboda yasan ba shi da gaskiya.

Taje ta kwanta tana mitar ita gaskiya ya tashi ya bar mata ɗaki, tunda ya gama abunda ya kawo shi.

Imran ya rungumeta sosai sannan yace "Dan Allah Amira abunda ya faru ya wuce Please"

"Baze taɓa wucewa ba"

"Meyasa, dan Allah kiyi haƙuri ya wuce, ban san yadda akai ma kika yadda da ni ba, har kika nuna farinciki ki akan nasarar da na samu, hakan ya nuna baki da riƙo, dan Allah ki yafemin Komai ya wuce, nasan kina da zuciya me kyau Amira"

Amira a ranta tace "Ai nia ba irin sokuwar matarka bace, da zan biyewa abunda yafaru nima in wulaƙantaka ba, in je ka hango wata, da Wannan damar zan mallaki abunda ta gaza riƙewa, in rama cin zarafin da tai min"

A fili kuma tace "Imran ban jina zan taɓa mantawa da mummunar kalmar Karuwa da mutane da yawa suka dinga jifana da Ita, kalma me nauyi da munin gaske, tabbas nasan nayi kuskure da na biyewa son zuciyata na dinga tafka taɓara son raina, ba tare da sauraron maganar kowa ba.
Mutane sun gaza yi min adalci ko yaya, babu wanda yasan dalilin da yasa na zama haka, babu wanda yai tunanin me za'ayi dan tallafar rayuwata, da dawo dani kan hanya se zagi cin mutumci da miyagun maganganu da mummunan fata.
Haƙiƙa maraici abu ne wuya da ɗaci, kuma Allah yana jarabtar bawansa ba dan baya sonsa ba, wanda duk ya tashi cikin maraici idan har ba mariƙi ka samu nagari ba, haka zaka tashi a rayuwa me wahala da ƙunci.

Bayan rasuwar mahaifiyata, na kasance a hannun dangin mahaifina, Yadikko bata ƙaunar kakata, mahaifiyar Abbana, Abbana a hannunta ya ƙarasa tashi, ta asabtar da shi azabtarwa me muni, ta yadda seda ta raba tsakaninsa da mahaifinsa, duk da tsakanin gidan mahaifina da gidan su babanmu ba nisa, amma mahaifiyata ta sha wahala a hannun Yadikko.
Duk da ba itace ta haifi Abbana ba, amma Mamana ta mata biyayya sosai, bayan rasuwar mahaifiyata aka kaiwa Yadikko ni, duk abunda za'amin na cutarwa, yana gani baze iya Magana va, saboda yana mata biyayya kamar mahaifiyarsa.

Ina da shekaru huɗu zuwa biyar mahaifina yai hatsarin mota ya rasu, bayan an share zaman makoki haka na zauna a gidan Yadikko da ya kasance family House, da yawa duk 'ya'yanta ne a gidan da matansu, da ma Abbana shikaɗai Mamansa ta haifa.

Ba wanda ya damu dani a gidan nan, duk da ƙanƙantar shekaruna, hakan baya hana Yadikko da iyalanta azabtar dani, ta hanyar sani aiki me wahala wanda yafi ƙarfina.

Banda duka akan ƙanƙanin laifi, duka wanda shekaruna sunyi ƙanƙanta ai min wannan dukan.

Watarana lokacin ina da shekaru takwas a duniya, Abba yazo daga Kaduna duba ni, ya zo ya tarar bani da lafiya, ga Yadikko ta iya siyasa, dan haka ba'a gane azabtar dani take, tai ta nunawa Abba ai tana sona, suna ƙoƙari a kaina.

Abba ya fito ze tafi, wani maƙocinmu ya samu Abba yace "idan da hali, tunda ɗan uwan mahaifiyata ne, ya tafi dani ya riƙeni, idan ba haka ba izayar da ake min ze iya sawa in rasa raina ko nakasta ni.

Abba yazo Kano, yace lallai tafiya zeyi dani, shi ze riƙeni.

Yadikko tace baze yuwu ba, seda suka kai ruwa rana sosai, sannan Yadikko ta bari ya ɗaukeni ya tafi dani.

Se dai muna zuwa, Ammi ta ganmu tare, ta haɗe rai tace ya ta ganmu mu biyu?.

Yai mata bayani, a take Ammi tace wallahi ba zata riƙeni ba, ɗan riƙo ba ɗan goyo bane, duk abunda zaka masa baza'a gani ba, gar tyn wuri yasan in da ze kaini amma ba gidanta ba, da fari ina ta murna zan baro baƙar wahala da aiken gidanmu, amma karɓar da Ammi tai min yasa na sha jinin jikina, ta dinga faɗa tana ɗaga murya tace a Lallai se na bar gidan.

Abba yace tayi haƙuri washegari ze maida ni, haka akayi kwana na ɗaya a gidanku, ban manta ba akan tiles na kwana, ga sanyi gashi ban saba ba, washegari Abba ya maida ni hannun su Yadikko.

Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka, kullum jiya i yau, maƙocinmu shine ya sani a makaranta, duk yaran gidan nan suna zuwa amma banda ni, maƙocinmu ya sani a makaranta.

Wataran sedai in saci jiki in gudu makaranta, ga rashin Abinci ga rashin kulawa, idan yuwa ta isheni se in daidaici lokacin cin Abinci a maƙota sannan in ci, ta ƙarfi da yaji na koyi kwaɗayi.

Idan aka je Guri naga Abinci jikina har tsuma yake a bani in ci saboda yunwa.

Kaya sedai in an samu kwance a bani in saka, wai salla tayi a saimin kayan salla ba ruwan kowa dani, kuma ga gidan da mahaifina ya mutu ya bari suka saka 'yan haya a ciki, suna karɓe kuɗin, suka ƙi bari a raba gado, ƙarshe baffa salahu ya tashi Auren 'ya aka saida gidan su kai hidimar biki.

Anty Fa'iza itama mamanta ta rasu, 'yar gurin Baffa Salahu ce, itama ta sha wahala sedai ta ta bata kai tawa ba, saboda ita jikar Yadikko ce, itace wataran ta kan kula ta bani kaya ko ta saimin takalmin sawa, saboda tana 'yan sana'oi.

Kasancewar gidan Yadikko akwai manyan samari a gidan, suka fara amfani da damar rashin galihuna, suna nema su lalatani, idan naƙi se asan yadda za'ai a ƙullamin sharrin da za'amin dukan tsiya a gidan, dama Abinci ba ban ake ba se an gadama, ya zaman har daga naƙota se a turo wai inje, a sani wanke wanke share share da aike, wataran in nayi a bani Abinci, wataran nayi a bati, ga rainon 'ya'ya, duk wadda ta haihu a sirikan Yadikko rainon yaron nan a kaina yake.

Sadiya da Amina sun ɗan girmeni, amma kusan kanmu ɗaya saboda ina da jiki, amma duk wani aiki suna zaune sedai a sani, idan kuwa rigima ta haɗani da su, nice bani da gaskiya se zagi da duka da cin mutunci.

Duk motsin da zan, ko inyi laifi ko ƙiriniya irin ta yaro sedai Yadikko tace "Allah ya watsa ni, insha Allah munyi hannun riga ni da abun arziki, yadda kakata ta mutu a tsiyace nima haka zan mutu, kuma se na barwa zuriyar Hafsatu wato kakata mummunan abun kunya"

Tun abun yana damuna har nazo ya dena damuna.

Akwai tazarar gaske daga Makarantar mu zuwa gidanmu, amma haka nake kwasa a ƙafa inje in dawo, har talla Yadikko ta kasamin, bayan ga jikokinta, amma duk da haka ina naniƙe da ita, nice wankinta, kitsonta lallenta, gyaran gurin kwancciyarta, aike idan zata aikeni bangon duniya ne ba zan taɓa musawa ba, zanje da ƙafafuwana.

Ba ni da ƙyuya ko ƙyashi, ga biyayya ga kowa, duk Alkhairi na ga Yadikko da iyalanta hakan be hanasu cigaba da yi min fatan lalacewa ba, an haka ai kayiwa Fa'iza Aure, bayan an kai ruwa rana taƙi aurar wani me kuɗi da suke so ta aura.

Na fara zama budurwa, amma babu kayan gyara, gashi bana son ƙazanta, ina son kayan kwalliya nima in gayara, amma babu me bani, brezia wannan se in Fa'iza ta bani kwancen ta ta, akwai lokacin da wandon da zan saka guda ɗaya ne tak dani, shima duk ya mutu, ba kayan turare ba me saimin audugar da zan amfani da ita lokacin al'ada, gashi na zama budurwa.

Allah yai min ƙirar jiki me ɗaukar hankali, hakan yasa maza suka dinga bina, suna son suyi amfani da rashin gata na su ɓatamin rayuwa.

Duk da haka akan samu na arziki suzo neman Aurena, amma da an zo tambaya se su Baba su ɓatani a gurin iyayen mutum, suce ni mutuniyar banza ce, a faɗar Yadikko ba zan Aure ga su Amina a zaune ba.

Islamiyya da ƙyar na samu nai sakukar Alƙur'ani, saboda kullum cikin korata ake ban biya kudin makaranta ba, ga shi zan kammala sakandire babu kuɗin jarrabawa, nan na shiga tunanin yadda zan na samu kuɗi.

Ina da wata 'yar ƙaramar waya, da na kan kaiwa me caji yaimin turi kyauta, a unguwar su Fa'iza, ya turan funa funai, da raye raye.

Tamu ta zi ɗaya da shi sosai, ya kan cemin ƙanwarsa, ya bani labarin yana da ƙanwa Amira, amma tana ƙarama sosai ta rasu, wasu lokutan har kyautar kuɗi yake bani, abunka da me buƙata ko a'a bana cewa nake karɓewa.

Wataran naje gurin Sultan me caji, akace yana bayan layi gurin wani biki, na bishi can ina zuwa na tarar da shi a can, yana cikin yaran D.J.

Ya koma gefe muna magana, nace masa "Yayana, naje ka turan cigaban series ɗin nan ba ka nan, ashe kana nan"

Sultan yace "eh ina nan, biki aka gayyacemu, ki bari in kin dawo zan turamiki"

Ana haka aka kira Sultan zeyi wata rawa kan zuwan amarya, sedai aka rasa macen da za suyi rawar tare, me DJ ya saka naira dubu goma ga duk yarinyar da tayi wannan rawar.

Take na shiga lissafi da tunani, idan na samu dubu goman nan, zan sai phants, brezia, pad da underwear, bani da takalmi me kyau, gashi ko turare bani da shi, sedai in nai wanka in jiƙa gishiri in shafa.

Ban gama yanke hukunci ba, na tsinci kaina a wannan Filin rawa, saboda burina in samu wannan kuɗin in biya tarin buƙatun da nake da su, wannan shine ma somin faɗawata harkar raye raye...........

Gyra, sharhi, ko shawara

Ayshercool
07063065680

Continue Reading

You'll Also Like

18K 810 15
Labari akan wata yarinya Hafsat wacce mahaifin su ya rasu mahaimahaifiyar sy ta sake aure in da ta auri mugun miji. shine me mimijin Ummun nnasu yaii...
1.4K 123 15
Labarin Innayi da 'ya'yanta.
19.9K 1.2K 31
Labarin wata matashiyar budurwa 'yar hamshaƙin attajiri me murɗaɗɗiyar AƘIDA, Tace So imagination ne da ɓata lokaci katsam.......... 😜 find out in A...
140K 7.5K 82
Being flat broke is hard. To overcome these hardships sometimes take extreme measures, such as choosing to become a manager for the worst team in Blu...