WUTA A MASAƘA

By Ayshercool7724

27.8K 1.6K 154

labari akan wata yarinya me rawar kai da rashin jin magana sam, labari akan taɓarɓarewar zumunci, tarbiyya da... More

WUTA A MASAƘA
WUTA A MASAƘA 2
3
WUTA A MASAƘA 4
CHAPTER 5_6
7_8
9_10
11_12
WUTA A MASAƘA 13_14
WITA A MASAƘA 15_16
WUTA A MASAƘA 19_20
WUTA A MASAƘA 21_22
WUTA A MASAƘA 23-24
WUTA A MASAƘA 23_24
WUTA A MASAƘA 27_28
WUTA A MASAƘA 29_30
WUTA A MASAƘA 31_32
33_34
35_36
37_38
37_38
39_40
41_42
43_44
45_46
47_48
47_48
49_50
51-52
53_54

WUTA A MASAƘA 17_18

751 55 4
By Ayshercool7724

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI




17_18


Imran ya kalleta a fusace yace "nan yai miki kama da gidan karuwai ne?" Murguɗa masa baki tayi ta ɗauke kai.

Khalid yace "Amira gidansu Imran ne fa, ki shiga bakomai, baki ga 'yan biki suna shiga suna fita ba"

Ta ƙarewa gidan kallo, sannan ta kalli Imran tace "muje"

Idan Imran ya biyewa Amira, ze iya yi mata dukan tsiya a gurin nan, kawai ya wuce yai gaba, Amira tabi bayansa.

Mata nata tsokanarsa suna ango ka sha ƙanshi.

Cikin gidan suka shiga, ya wuce Falo Amira na biye da shi.

Minal suna zazzaune a falo da ƙawayenta, da babbar Yayarsu Khadija wadda daga Ita se Imran, ita tayi Aure tuntuni.

Khadija ce ta fara ganin Imran da Amira, ta kallesu tai murmushi tace "Imran kai da wa nake ganinka haka kamar Amira?"

Amira dai tayi turus, tana kallon Anty Hadiza.

Jin ance Amira yasa Minal waigowa, duk yadda ake faɗar rashin jin Amira da yadda ta ganta a hoto, ba ta zaci zata ganta a haka a fili ba, tafi kyau da class Sosai a fili.

Imran yace "eh ita ce"

Hadiza tace "masha Allah, Nikam yaushe rabon da inga Amira tun tana ƙarama sosai, yanzu waze ce ita ce, ta zama hamshaƙiyar mace"

Wata a ƙawayen Minal tace "wannan ba ita ce wani mawaƙi yace zata fito a vidon waƙarsa ba?".

Minal ta kwaɓe baki tace "ita ce"

"Wow Gaskiya naji daɗi dana ganta, ashe 'yar uwakku ce, wallahi ni burgeni tayi"

Cikin isa Imran yace "ke minal, ki bar abun da kike kije ki kaita ɗakinki, ki nuna mata toilet tayi salla, Sannan ki bata babban hijjabi"

Amira kuwa kamewa tayi a gefe, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Minal ta zumɓura baki, cikin ƙunƙuni tace "ɗakina, toilet ɗina, kuma kayana, taɓɗijan Allah ya kiyaye inyi sharing da wata"

Cikin muryarsa me razanarwa wasu lokutan yai mata tsawa "dan ubanki me kike cewa? Ni nake miki Magana kike min ƙunƙuni?"

A hargitse Minal tace "A'a Yaya, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba da kai nake ba"

"Kai Sarkin masifa, tun daga ciki ake jiyo hargowarka, lafiya kake wa 'yata shouting haka?" Ammi ce ke maganar lokacin da ta fito daga wani ɗaki.

Ba tsammani ta kalli inda Amira take, sukai ido huɗu da juna, ko za'a naɗe ƙasa a dawo, Amira ba zata manta fuskar Ammi ba, da wasu abubuwa da suka shuɗe shekarun da suka gabata ba.

A wulaƙance ta ƙarewa Amira kallo ta kalli Imran tace "lafiya wannan fa?"

"Abba ne yace inje in taho da ita yau, a fara biki da ita"

"Saboda bikin nata ne, kokuma na ƙanwar uwatta?"

Amira ta ɗago ta kalli Ammi, ta maida kanta ta sunkunyar.

Anty Hadiza tace "Ammi, Amira ce fa ko baki ganeta bane?"

"Ke zam cewa baki ganeta ba, baki da labarin rashin jin da yawon ta zubar ɗin da takeyi, babu inda hotonunata da rashin kunyarta basu shiga ba, kawai se a ɗebo jiki a kawomin ita cikin gida, saboda me to baze yuwu ba, ba a gidan nan ba sedai wani gurin"

Hadiza tace "Haba Ammi, koma menene dalili ne ya kawota, kuma na ɗan lokacine, ana gama biki fa zata tafi"

Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu, aka dinga bawa Ammi rashin gaskiya da nuna mata illar abunda tayi, jin mutane nata surutu ba yadda ta iya, haka ta ƙyale Amira, saboda gudun surutan mutane.

Imran ya kuma kallon Minal yace "bakiji me nace bane?"

Miƙewa Minal tayi, Imran ya kalli Amira yace "ki bita kije ta baki masauki, a baki hijjabi ki rife jikinki"

Duk da sanyi da jikin Amira yayi, hakan be hanata zumɓura baki ba, dan da ta san gidansu Imran ze kawota, da duk tunballen tsiyar da za'ayi sedai ayi ba zata yadda taje gidansu ba.

Minal tai gaba Amira tabi bayanta, suna shiga ɗakin Minal ta juyo ta gallawa Amira harara tace "ga toilet nan ki shiga, kuma ki kula karki sake kimin taɓe taɓen abunda ba shikenan ba, kuma karki min fitsari a ƙasa, kinji na gaya miki"

Amira ba tace uffan ba, dan ta san kome akayi mata Imran ne ya janyo da ya kawota gidan, dan da tana gidansu babu me mata wannan rashin mutunci haka.

A masallaci Imran ya sake haɗuwa da Khalid, suka wuce gidansu Khalid, a hanya Imran ya bashi labarin irin karɓar da Ammi tayiwa Amira.

Khalid yace "ai nasam za'ai haka, ni babbar fargabata ma suzo su san wannan maganar, akwai fa sauran rikici"

Imran yace "bari kawai, aini na zubawa sarautar Allah ido kawai, dan ban san abunyi ba"

"Ka kwantar da hankalinka, Allah ze baka mafita insha Allah"

Seda suka raba dare suna hira, Sannan Imran ya tafi gida, lokacin duk an rurrufe ko ina, kuma be haɗu da Abba ba sam balle ya gayamasa ya ɗakko Amira, dan haka kai tsaye ɗakinsa ya wuce yaje ya kwanta.

Amira kam duk a takure take, ba wanda ya kulata balle ya bata Abinci, ga gajiyar hanya data ɗebo, gashi bata san ko ina ba, Minal da ƙawayenta se wulaƙanci sukewa Amira, Minal tana gaya musu ai Amira karuwace, se wannan guda ɗayar ta farko da tace Amira tana burgeta itace bata biye musu ba.

Da daddare akazo gurin kwanciya, Minal ta kalli Amira tace "kinga, me aiki zata shigo yanzu ta kai ki inda zaki kwana, nan ɗakin zamu kwana ne nida ƙawayena, bama son takura ina fatan kin gane?"

Amira ba tace komai ba, ga kaya tana son canzawa, bata ɗakko komai nata ba, kawai Imran ya kawota ya ajiye yai tafiyarsa, taji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan takaici.

Me aikin ta shigo ɗakin ta kalli minal tace "Anty gani"

"Yawwa, dama zaki wanke min banɗakina ne bana son sharing da jagwalgwalo, kin sanni da ƙyama, kuma an shiga banɗakin But before that, ki kaita inda na gayamiki za ta kwana"

Me aikin ta kalli Amira tace "taho in rakaki"

Ba musu Amira tabi bayan me aikin nan, sedai inda me aikin ta kaita ne ya bata mamaki, abun ya ɗaure mata kai, da faɗi da girman gidan nan, a rasa inda za'a kaita se Kitchen, kitchen ɗinma a cikin store, duk ga kayan Abinci a jibge kamar abun banza, an saka mata tsurara katifa wai ta kwana a gurin.

Amira ta ƙarewa gurin kallo, ta ja tsaki ta fice ta koma falo ta bar me aikin a gurin, ta samu guri a gefen kujaerun falon ta zauna.

Mutane kowa ya samu gurin kwama amma Banda Amira.

Haka ta kwana a falon nan a zaune, ga garin da sanyi ga baƙunta, da Asuba can waje ta fita tai alwala, tana ƙarewa gidan kallo da yadda zata bar gidan nan, ko Imran ya sani kobe sani ba, ta ƙudirce gari na yin haske zata gudu, ta koma Kano.

Yadikko kam ta bugu sosai, dan se an rirriƙeta take iya tashi, amma sam bakinta yaƙi mutuwa, banda zagi da kwashewa Amira albarka ba abunda takeyi, wai itace tai silar faɗuwarta ƙasa.
Umma da su Sadiya suna ta haɗa kaya, zasuje biki ita kuwa tana kwance, duk jiki yayi tsami.

"Wai yanzu niba yadda zakuyi dani, a lallaɓa a tafi dani gurin bikin nan?"

Zailani yace "ina za'a kaiki, ki zame musu kaya? Ya zasuyi dake? Jinyarki za suje suyi kokuma bikin zasu? Kawai ki haƙura ki zauna, a yaran gidan Baffa Salahu ko su Habiba ne suzo su dinga tayaki zama, kafin su dawo Amma wallahi kikace zaki bisu ma wahala zaki sha"

Haka sukayi ta fama da Yadikko, akan lallai se an tafi da ita gurin biki, seda taga ba sarki se Allah ta haƙura da zuwan.

Washegari da Safe suka gama shiri tsaf, suna jiran Fa'iza taje su haɗu a nan gidan su tafi gaba ɗaya.

Amira kuwa gari na fara hasake, wajen ƙarfe takwas na Safe tana tunanin idan ta fita ina zatayi, Anty Hadiza ta fito daga ɗakin Ammi tace "Amira, ya baƙunta?"

Amira ta kalleta tace "lafiya ƙalau, ina kwana?"

"Lafiya ƙalau Amira, naga kina ɗari ɗari ki saki jikinki fa, nan gidanku ne, ki saki jiki da kowa duk 'yan uwanki ne"

"Gidansu a gidan ubanwa? Gidana dai gidan mijina, gidansu yana Kano, kuma 'yan uwan 'yan uwana ne, ta nemi nata 'yan uwan ba nawa ba, mu babu kalarta a 'yan uwana"

Amira tai shiru ta sake sunkunyar da kai, zuciyarta na tafasa, Hadiza tace "Ammi why?"

"Ke dalla rufemin baki ko in zageki yanzun nan"

Suna barin falon Amira ta miƙe daga inda take zaune, dama jakarta na jikinta, ta zira takalmanta tai waje.

Mutane nata shiga suna fita, Amma tana zuwa bakin gate, ɗaya daga masu gadin ya taso ya kalleta yace "ina zaki?"

"Fita zanyi" Amira ta bashi amsa.

"Zuwa ina?" Ya tambayeta.

"Kamar yaya? Su sauran wanda suke fitan tambayarsu kake yi?, Kokuma ni ka raina, dan Allah ka bani guri in fita"

"Gidan ubanwa zaki idan kika fita?" T muryar Imran taji ba tsammani, waiwayowa tayi da sauri ta ganshi a tsaye, sanye da jallabiya fara.

Haɗe rai tayi sosai tace "Ni gida zan tafi, gidanmu zan koma"

"Hmm tunda dama ke kika kawo kanki ko? Kin ɗauka haka nan na kawo ki nan ɗin kina da damar da zaki fitane? Da kin matsa kin fita da se sun harbe ƙafarki da bindiga, sakarya kawai wuce muje ciki ni"

Ai kawai Amira ta sa masa kuka, harda hawaye tace "gaskiya ni ba zan koma ba, haka kawai ni ban san kowa ba ka kawoni ka ajiye ni, se wani kallo na ake ana gayamin magana, ni gaskiya gidanmu zan koma, duk da bamu da komai Amma ni ya fiyemin nan"

Imran ya ƙare mata kallo sannan yace "waye yake gaya miki maganar? Koda yake koma me akayi miki aike kika janyo, ubanwa yace kiyi abinda za'a gaya miki maganar, wuce muje ba gidan uban da zaki, in kinga kin fita daga gidan nan to ni ko Abba ne wani ya fita dake, amma daga nan har ƙarshen layin nan, kika fita zasu dawo dake, wuce mu koma"

"Dan Allah kayi haƙuri, ni wallahi bazan iya zama a gidan nan ba, ka ƙyaleni in koma"

Attention ɗin mutane ya fara dawowa kansu, wata mata tace "Imran yau fa ranar farinciki ce a gareka, banda cin zali dan Allah, nam ba barikin soja bane"

Imran kawai yai murmushi, matar na wucewa ya bugawa Amira wata irin tsawa, me matuƙar razanarwa, a gigice ta nufin cikin gidan da sauri, ya riƙo hannunta, yabi ta bayan gidan da ita zuwa sashin Abba.

Minal kuwa da akan idonta, Amira ke kuka, Imran ya riƙe hannunta se cewa tayi "Ahha baɗala, kar dai Yaya Imran ake gwadawa karuwancin, aikuwa bari inje in gayawa Ammi"

Sashin Abba suka shiga, Amira tana kuka amma tana ƙarewa gurin kallo, dan ita bara taɓa shiga gida me kyan wannan ba a rayuwarta.

Abba yana ganinsu yace "oyoyo 'yar gidan Abba"

Jin muryar Abban ce yasa ta dawo hayyacinta daga kalle kallen da takeyi.

Taje ta samu guri ta zauna, Imran ma ya zauna, Abba yace "ki hau kan kujerar mana" girgiza kai Amira tayi ta sunkunyar da kanta ƙasa.

Abba yace "ai ni be gayamin ɗakko ki ya tafi yi ba, ai da tun daren jiya mun gaisa, se yanzu da safen nan fa ya gayamin" jikin Abba ne ya ɗanyi sanyi, ganin hawaye a idon Amiran.

Abba yace "lafiya kuwa Amira? Imran ko kayi mata wani abun ne?"

Imran yace "Niba abunda na mata"

Amira ta ɗago ta harari Imran, Abba yace "gayamin me yai miki?"

"Ni kawai yake ya ɗakkoni, ban shirya ba ban komai ba, ban taho da komai nawa ba, daga ni se kayan jikina,yazo ya ajiyeni ya tafi, tun a hanya nace ina jin yunwa Amma ya ƙyaleni yazo ya ajiyeni ya tafi, kuma banci Abinci ba, kuma ni dan Allah kace ya maida ni gida, ko tasha a kaini in hau mota in koma, ni bana son zama a nan gidan" tai maganar cikin kuka.

Abba yace "yi haƙuri ya isa haka, besan baki ci Abinci ba, amma ga nawa cna kije ki zuba kici, za'a kawo miki kayan da zaki amfani dasu, kuma ki kwantar da hankalinki anjima 'yan gidanku zasu zo, ki bari suzo idan aka kammala biki sekuyi tafiyarku gida, kuma abunda yasa ya kawoki nan, kinga akwai rigimar da kika janyo, 'yan Sanda suna nemanki Wannan mawaƙin ya kai ƙararraki, kimga Yakamata muyi settling wannan mtsalar be kamata a ce an kama ki ba, kinga da baki je Abujan nan ba da duka haka bata faru ba"

Amira ta share hawayen ta tace "aini dama bance zan fito a waƙarsa ba, kawai nace masa zanyi tunani ne, kuma ni ƙarya yai min, bikin wannan Hassan ɗin, ɗan gidan ƙaramin ministan man fetur muka je, mun samu saɓani dashi, shine suka haɗa baki"

Abba yace "saɓanin me? Kuma meyasa kika je Abuja?"

Amira tace "eh muna harkar bukukuwa, mc da kaɗe kaɗe shine aka gayyacemu can, da mukaje anyi bikin kuma ya biyoni Hotel ɗin da nake muka samu Saɓani".

zuciyar Imran kamar ta fashe, saboda maganar Ihsan data faɗo masa "AN FASA AUREN, SABODA AN KAMASHI A BANƊAKI A HOTEL KARUWA TA RIFE SHI"

Wani irin baƙinciki da takaici suka ziyarci zuciyar Imran, Abba yace "shikenan a bar maganar ta wuce, zanyi waya da mahaifin shi Hassan ɗin, Imran miƙo kayan breakfast ɗin nan ka haɗa mata"

Imran ya kalli Abba zeyi magana, Amma Abba ya girgiza masa kai.

Haka yana ɓacin rai ya haɗawa Amira tea, ga soyayyen dankalin turawa da ƙwai.

Amira tace "ni bana cin wannan shayi kawai zan sha"

Abba yace "saboda me?"

"Ni ƙosai nake so, shi muke ci a gidanmu da Safe"

Abba ya kalli Imran daya ɓata fuska yace "Imran, ko za'a samu me ƙosai a nan kusa?"

A ɗan hasale Imran yace "Abba kai ma dai kasan babu wata me ƙosai a unguwar nan, waye ze sai wani ƙosai? Sekace a ƙauye"

Abba yace "cin ƙosan ne se a ƙauye?, idan aka ɗan zagaya ai za'a iya samu, ka duba ko zaka samo mata mana"

Wani matsiyacin kallo Imran yaiwa Amira, ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba, ya miƙe yana mitar shi a ina ze wani samo ƙosai.

Amira tace "ya barshi ma, zanci wannan ɗin".

Abba yace "to shikenan, dawo ba se kaje ba"

Imran kasa ya jinjina kai ya dawo ya zauna, cike da takaici da ɓacin rai.

Amira ta dinga cin Abincinta, Abba yace "ai Munyi waya da 'yan gidanku, suma sun taho suna hanya, yanzu Imran zeje ya karɓo miki kayanki na fitar biki"

Amira ba tace komai ba, ta cigaba da cin Abincin ta, yayin da Imran ya ɗaure fuska tam.

Ammi ce ta shigo ɗakin Abba, tana zuwa tsakiyar falon tai turus ganin Amira zaune tana cin abincin Abba.

"Ke me kike yi a nan gurin nan, har kike cin abinci a wannan kwanon?"

Abba yace "Amiran ce baki gane ba, kokuma me?"

"In ma na gane ta seme? Me take a nan nake tambaya?"

Gaba ɗaya Amira taji Abincin ya fita daga ranta, saboda masifar Ammi.

Abba yace "nine nace a kawon ita nan"

"Amma inda mutane suke, be isa ta zauna a can ba se an kawota a nan?"

Miƙewa Amira tayi tace "na ƙoshi"

Abba yace "zauna ki ƙarasa cin Abincin ki"

Amira tace "A'a na ƙoshi"

Ta juya zata fita, Imran ya tashi yabi bayan ta, yace "ke karki koma cikin gidan nan, biyoni"

Tabi bayan Imran, part ɗinsa ya nufa ta bishi a baya, suka shiga falonsa, suna shiga ya mai da ƙofa ya kulle yasa key ya kalleta yace

"a nan na yadda ki zauna, karki kuskura kije ko ina daga nan, kinji na gaya miki, kuma wallahi kika min taɓe taɓen abunda ban saki ba, sena ɓata miki rai"

Ba tace komai ba ta zauna akan kujera, tana ƙarewa ɗakin kallo.

Har yai gaba ya juyo yace "kuma wallahi, idan kika sake kika kuma fito da wani iyayi a gaban Abba, wallahi a gaban nasa zan zaneki, sa'anki ne ni da zaki sa a aikeni siyo miki wani ƙosai, sa'anki ne ni?" Ya tambayeta cikin tsawa.

Amira ta girgiza kai, yace "ki sake ki gani, zaki ga yadda zanyi dake, banza kawai".

Shiru tayi bata ce masa komai ba, ya wuce bedroom ɗinsa, ya jima a ciki tana ita kuma tana zaune a falon, tayi shiru kamar mayya, be kula ta ba yazo ya fice daga falon, ya kulleta ta waje.

Tsaki tayi, ta hau kan kujera 3seater, ta kwanta tai shiru tana tunani, gaba ɗaya ranta a ɓace yake, hankalinta duk yayi gida, burinta kawai ta ganta a gida, dan gaba ɗaya gidan nan da mutanen cikin su ba suyi mata ba, Sannan ta ƙwafe Minal akan abun da tayi mata, abun ya ɓata Mata rai sosai.

Ammi kuwa sam Abba ƙim biye mata yayi, taita mitarta harta gaji ta haƙura, daga baya tace "Nayi waya da Babar Ihsan, tace min ance mata an canza gidan da za'ayi jeren kayan amarya, zuwa gidanka na Bamako, shine nace meyasa aka canza? Bayan naga gidan Imran ɗinma babban gidane ya ishe su, ya zasuyi da wannan uban gidan su biyu?"

Abba yace "Eh akwai dalilin yin hakan"

"Meye dalilin?" Ta tambayeshi tana kallonsa.

"Zakiji a nan gaba kaɗan"

"Nifa na kasa gane kanka tunda bikin nan ya ƙarato, meye bazaka gayamin yanzu ba, ni me zance musu suna nan suna jirana in gayamusu dalili, zau tafi jeren kaya?"

"Suma zasu san dililim ba da daɗewa ba, sannan ba wani abun tashin hankali bane" yana gama maganar ya miƙe ya fita ya barta a falon.

Kusan mintuna talatin da fitar Imran, se gashi ya dawo, ya buɗe falon ya ajiye mata leda a gabanta yace "gashi nan, kayan wanka ne a ciki da tooth brush, ga toilet nan a Falo ki shiga kiyi wanka, idan kin ga dama kiyi abunda ban saki ba, in dawo kiga yadda zanyi dake"

Maimakon ta motsa sema lumshe idanunta da tayi, tai masa banza, be sake kulata ba, ya ɗau abunda yake buƙata ya kulle bedroom ɗinsa ya barta a falo, ya kuma kulleta yai tafiyarsa.

Gaba ɗaya suka gama shirinsu, Anty Fa'iza bata ƙara so ba, suka kirata a waya tace musu kayanta da nauyi, dan haka su haɗu a tasha gurin hawa mota.

Yafikko tace "nikam ban so tafiyar nan babu ni ba, amma duk yadda zakuyi Ke Sadiya da kuma ke Amina, kuyi duk yadda zakuyi, ku janyi hankalin yaron nan kanku, ko shi ko kuma mahaifinsa, mu samu ko wata daga cikinku ne ku aura muma, mu huta, kai Amma Amira ta cuceni da ta ka dani ba damar inje gurin nan, shegiya watsatsiyar Yarinya, mara hankali, ko da yake ta yiwa kanta itama, tunda ta tafi gantalinta ba wanda yasan inda take, ita ma ba taje ba, nima banje ba da kunje ku gaywa Alhaji Ali kar ya ga ba 'azo da ita ba, tana can ta tafi iskancinta, sannan dan Allah duk abinda kuka samo ku ɗan ragomin nima"

Haka taita musu zantuka, daga nan suka kama hanya suka tafi tasha, suka haɗu da Fa'iza a can, suka hau Mota.

Dasu Umma sukaje gidan su Imran, suma ba wani takansu Ammi tabi ba, amma duk da haka an basu masauki, an kai musu Abinci, Minal se wani gani gani take musu, kamar taga wani abu na daban.

Amira wuni tayi a cikin falon Imran, ga yunwa ta isheta, ga waya ba caji ta rasa abunda za tayi taji daɗi kawai ta hau kuka, tayi me isarta sannan ta Share hawayenta.

Imran kuwa, suna gurin Bridal shower, shida abokansa dan ya ma manta da wata Amira, shagalinsa kawai yake, sedai lokaci lokaci gabansa ya kan faɗi idan ya tuna mata biyu za'a aura masa, kuma haryanzu daga Ammi har Amaren Babu wanda ya sani.

Se bayan isha'i sannan Imran ya dawo gida, shima a gajiye yake sosai, a harabar gidan 'yan mata matan nan na family ɗin su Ammi suka dinga tsokanarsa, wai dama she yana soyayya gashi harzeyi Aure.

Amina ce ta hango shi, ta tuni da huɗubar Yadikko, ta tsaya 'yan matan nan suka ragu, sannan ta nufi inda Imran yake, tana zuwa ta zube ƙasa ta gaisheshi.

Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa mata yace "she kunzo?"

Tace "eh munzo tun ɗazu, sedai ba'azo da Yadikko ba, tunda Amira ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa bata iya tashi, kuma ita ma Amiran ba'azo da ita ba, babu wanda yasan inda take, tunda ta fice yawonta ba wanda yasan inda take"

Imran yace "Ba yawo ta tafi ba, ni naje na ɗakkota jiya" be kuma cewa komai ba yai gaba abunsa.

Ya bar Amina a tsaye tana mamaki, gurinsu Fa'iza ta koma, tace "wai dama Amira tana gidan nan?"

Fa'iza tace "eh tana nan, tun da muka zo nake zuba ido inga a ina zan ganta, tun jiya Imran yaje ya ɗauketa suka taho"

Sadiya tace "wai shi Imran ɗin da kansa?"

Fa'iza tace "eh mana, har gidana yaje nemanta".

Gaba ɗaya mamaki ne ya cikasu, Amma sukayi shiru, basu kuma cewa komai ba.

Imran yana zuwa ya buɗe falon ya shiga, ya sha Manyan kaya se ƙamshi yake, Amira tana zaune tai tsuru da ita kamar kyanwa, be kulata ba ya wuce ɗakinsa, yaje yai wanka ya canza kaya, ya fito falon yaje ya buɗe fridge ɗinsa, komai yana nan yadda yake, bata taɓa komai ba, ya kalleta babu alamar taci Abinci tun breakfast.

Ya ɗakko wani ƙaton cake, da lemo ya Kawo ya ajiyemata a gabanta, yakuma ɗaukar kayansa yai waje ya kulleta a ciki.

Khalid na ganin Imran yace "Angon biyu lafiya kuwa? Yau a nan zaka kwana ne?"

"Eh waccan yarinyace tai ƙoƙarin guduwa da safe, Allah yasa na nunawa security ita, da tuni ta gudu da safe, shine na kulleta a ɗakina"

Khalid yaita dariya yace "Yaseen kafi son Amira akan Ihsan, irin wannan tattali haka?"

"Nifa daɗina da kai rashin hankali wasu lokutan, ni na gaya maka ina son wannan yarinyar ne? Kawai ba yadda zanyi ne, nasan idan ta gudu nine a wahala, ni za'a sa in tafi yawon nemanta"

Khalid baya son yaja zancen suyi faɗa, dan haka ya ƙyale Imran.

A daren Amira ta cire kayan jikinta, ta wankesu a banɗakin falon Imran, da yake akwai liquid soap a ciki, ta saka sabuwar doguwar rigar jallabiuar daya kawo mata, taƙi yin Bacci saboda kar tana bacci, Imran ya shigo ya shiga toilet ɗin nan yaga kayanta a ciki, dan harda underwears ɗinta ta wanke.
Seda kayan nan suka bushe, ta kwashe su daga banɗakin, Sannan hankalinta ya kwanta, ta kwanta akan doguwar kujera bacci ya ɗauke ta.

Da safe Imran yazo ya kawo mata Abinci, sedai be kulata ba, ya ajiye mata ya tafi, ya maida ita kamar wata ɗaurarriyar Akuyarsa.

Ranar Alhamis yakama za'ayi dinner, kowa nata shiri ana hada hada amma an kulle Amira a ɗaki.
Gashi ance mata 'yan gidansu zasu zo, amma Imran ya kulleta, gashi tana tsoron masa rashin kunya ya casa ta, dan ba kowa a gurin daga shi se ita.

Imran na shiga cikin gida yana son ya karɓi abu a hannun Ammi, Anty Hadiza tace masa "Imran nikam ina Amira ne? 'yan gidansu suna nemanta amma basu ganta ba tunda suka zo"

Imran yace "eh zasu haɗu a gurin dinner, tana ɗakina"

"Me takeyi a ɗakinka?"

"Jiya guduwa taso tayi, shiyasa na rifeta a ɗakin na koma gidansu Khalid, akwai magana fa, naso in samu lokaci in ganki amma ba time"

"Labarta min, meye maganar?"

Imran ya ɗan taɓe baki yace "zaki ji very soon, Yanzu dai nemomin Ammi"

Da ƙyar aka gano Ammi cikin jama'a, ya karɓi abunda ze karɓa ya fita.

Mutane wasu duk sun watse sun tafi gurin make up.

Amira tana kwance tayi shiru, tayi kukan ta gaji, Imran ya buɗe ɗakin ya shiga.

Ya kalleta yace "kinyi wanka?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace nayi

"Kuma shine kika zauna haka busu busu baki shafa mai ba?"

Sekace ya bata man da zata shafa ɗin, banza tai masa kamar bata ji ba.

Ya kuma ajiye mata kaya yace "tashi ki shiga bedroom ɗin nan kisa kayan nan ki ɗauki mai akan mirror ki shafa ki zo ina jiranki yanzun nan"

Ta karɓi kayan ta shiga ɗakin nasa, ta rufe ƙofa se tsaki take tana zumɓura baki, ta ƙarewa dressing mirror ɗin kallo, mayuka kamar na Mace.

Ta buɗe ɗakin ta kalleshi tace "babu me gurguwa a ɗakin"

Ya kalleta yace "wace gurguwar?"

"Shine man da nake shafawa, ni bana shafa irin wannan"

"Kin wuce ko sena zo nayi ball dake? Me kuturwa kike shafawa bame gurguwa ba"

Ta bugo ƙofar da ƙarfi ta koma cikin ɗakin tana tsaki, wani danƙareren less ne, dark blue a cikin ledar, an ɗinka shi riiga da skirt, ko ina aka samu size ɗinta oho? Se takalmi da jakarsa, da mayafi da kayan yari da sarƙa.

Amira ta saka kayan nan tsaf a jikinta, fuskarta babu makeup ba komai, ta ɗaura ɗankwalin tai wani irin kyau, ta kalli gadon Imran, tsaf dashi tai zamanta a kai.

Tana jin yana masifar ba zata fito ba, Amma tai masa banza, a fusace ya buɗe ƙofar bedroom ɗin, ta ɗago idanunta ta kalleshi, kamar ba ita ba, kayan nan sun mata cif a jikinta.

Dama Abba ne yasa yayi wa Usman waya, yace ya bashi lambar Fa'iza yace a taho da size ɗin kayanta da takalmi, shine aka ɗinko mata.

Tana zaune akan gadonsa, "bazaki taso ba kenan? Waye yace ma ki haumin gado?"

Tashi tai daga kan gadon, tana ɗan tura baki, ya kai idonsa kan turarukansa yaga yadda tai masu aiki, ko ina ƙamshi kawai yake.

Kawai ya girgiza kai, dan ya gaji da magana, duk taku ɗaya idan tayi, cike yake da ɗaukar hankali, haka ta taho kamar zata bangaje shi ta fito falon ta tsaya, tana hararsa ta gefen ido.

Suka fito harabar gidan, mayafin kayan na riƙe a hannunta, bata yafa ba, ta riƙe jaka da hannu ɗaya, wani soja ta hanga da uniform a tsaye a jikin wata mota, sukaje bakin motar, Imran yacewa Sojan "gata nan ka kula da abunda nace maka"

Sojan ya jinjina kai, Amira ta kalli sojan ta kalli Imran, Imran Ya haɗe rai yace "idan ta maka rashin Kunya ko taurin kai, ka harbeta ni na saka ka kawon gawarta!!!

Amira tace "Na shiga uku, harbi kuma kamar wata 'yar fashi!!!

Share Please

(🤣🤣 Me Oga Imran ke shirin yine haka? Da cakwalkwalin cakwakiya fa,
Ina jiran jin Comments ɗinku)

Please don't come to my inbox, And start telling me from page 1 please.
Wanda yake nema daga farkon, ya duba watpad @ Ayshercool 7724

Domin gyara, Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680



Continue Reading

You'll Also Like

5.2M 45.3K 53
Welcome to The Wattpad HQ Community Happenings story! We are so glad you're part of our global community. This is the place for readers and writers...
43.6K 797 7
So the BSD characters react to my favorite AU's of Atsushi. I made this as I noticed that there are not a lot of these kinds of stories with BSD. Co...
104K 4.4K 30
Labari ne akan 'yan mata 3 wad'anda suka sha gwagwarmayar duniya suka ga bala'i a rayuwar su kala-kala, labarin ya gino ne akan makirci, yaudara, cin...
18.1K 810 15
Labari akan wata yarinya Hafsat wacce mahaifin su ya rasu mahaimahaifiyar sy ta sake aure in da ta auri mugun miji. shine me mimijin Ummun nnasu yaii...