KARRAMAWAR ANSARAWA ★

21 5 0
                                    

Annabi (S.A.W) ya zauna tsawon lokaci a gidan Abu Ayyubal Ansari.

Abu Ayyubal Ansari yayi farin ciki kasancewar Annabi a gidansa ya sauka, domin lokacin da Annabi ya shiga Madinah babu wani gida da yake wucewa face sun yi riƙo da linzamin taguwarsa suna masa magiyar ya zauna a tare da su amma sai ma'aiki ya basu umarnin su ƙyale wannan taguwa hakika ita abar umarta ce... A ƙarshe dai gidan Abu Ayyuba shi ne ya zama inda Annabi zai zauna kafin kuma inda taguwar ta zauna ya zamana an gine shi ya zama mazauni da kuma masallacin Ma'aiki (S.A.W).

Abu Ayyuba ya zaɓarwa Annabi sama a gidansa wato bene yace Annabi ya zauna a nan, amma Annabi sai ya ƙi, saboda ɗan gida shi ne ya dace sa sama. Amma saboda karamchi na Abu Ayyuba sai ya ƙi yarda ya zauna a saman.

Kasan lokacin da akace mai karamchi zai karrama mafi karamchi, to tabbas mafi karamchin zai yi duk mai yiyuwa yaga cewa bai tauye haƙƙin mai karramawar ba. Don haka Annabi bai yarda ya karɓi saman ba, da dai yaga Abu Ayyuba ya dage sai Annabi yace masa yayi hakuri, abin da yasa yafi son kasan shi ne saboda masu tururuwar zuwa wajensa don ganawa da shi.

Wannan kuwa ba sai na gaya mana yadda mutane suke tururuwar zuwa ganin Annabi ba.

Shi kuwa Abu Ayyuba, ji yake kamar yayiwa Allah laifi, don me zai hau bene alhalin Annabi yana kasa? Don me zai taka inda karkashinsa a nan Annabi yake?

Abu Ayyuba baya cin abinci, idan suka girka Annabi ne farkon wanda zai ci, sannan su kuma su ci abin da ya rage, harma rige-rigen cin gurbin da Annabi ya taɓa suke.

Akwai lokacin da aka samu akasi ruwa ya zubi akan saman inda Abu Ayyuba yake, nan take hankalinsa ya tashi domin baya son ruwan ya ratsa ya zuba jikin Annabi. Haka suka dauko soson katifarsu ta kwanciya suka rinka tsane ruwan da shi...

Allahu Akbar.

Tabbas babu wani sarki, babu wani mahaluƙi abin halitta da ya samu daidai da kwatankwacin irin gatan da Annabi ya samu daga sahabbansa.

Ana haka a Madinah kawai sai zazzabi ya rufarwa masulmai da sukai hijira, yau wannan babu lafiya gobe wancan. Amma Allah ya kiyaye Annabi bai yi ba. Abin ya damu Annabi mutuka. Domin yana mutukar son sahabbansa, ya rasa meke masa daɗi, don haka sai ya roƙi Allah sauƙi ga mutanensa, itama kuma Madinah ya nema mata albarka, ai kuwa sai Allah ya amsa roƙonsa.

A cikin shekara ta farko da yin hijira aka kammala gina masallachin Annabi.

Annabi ya haɗa yan'uwantaka ta musulunchi tsakanin Muhajirai masu hijira da Ansarawa mutanen Madinah. Wanda idan mukace zamu zayyano irin soyayya da taimako da take tsakaninsu to da tabbas sai mun tsawaita bayani kuma da sai zuƙata sun jijjika idanuwa sun zubda hawaye musamman idan muka duba da yadda musulmai suke a wannan zamani... Inama ace rayuwa na da tsayi da na bugi ƙirji wajen wannan hidimar don neman kusanci da kuma kusantowa da al'umma nesa kusa... Amma da yardar Allah indai akwai tsawon rai muna nan tafe da bayanai akan rayuwar sahabbai ɗaiɗaikunsu da kuma a jimlace.

A cikin wannan shekara dai Annabi ya rubuta ko mu ce ya ƙulla alaƙa da makwabtansa na gefe-gefe da cikin Madinah musamman Yahudawa.

A cikin wannan shekara dai Annabi ya tare da masoyiyarsa kuma uwarmu Nana Aisha. Wadda a karkashin sama (dandaryar kasa) ba a riski wata mata mai ilminta ba a duniyar musulunchi. Mai daraja, tarbiyya da falala. Allah ka tashe mu da ita ranar Alƙiyama. Itace fa wannan wadda daga saman bakwai Allah ya wanketa, kuma itace dai wadda daga saman bakwai mala'ika Jibril ya sakko duniya don kawai ya isar mata da gaisuwar Allah. Ba don gudun tsawaitawa ba, aida mun yada zango a nan munji tarihin wannan baiwar Allah. Kamar yadda Ibn Taimiyya (R) da wasu malamai suka bayyana cewa Idan za a duba al'ummar Annabi da kuma abin da suka amfana da shi to kaf matan Annabi babu kamar Nana A'ishah (R.A), idan kuma za a duba wadda shi Annabi (S.A.W) ya fi amfana da ita to kaf cikin matansa babu kamar Nana Khadija (R.A).

A cikin wannan shekara ne dai aka shar'anta kiran sallah. Akwai wasu ruwayoyin da suke cewa an shar'antashi a makka ko a isra'i amma dukkaninsu basu inganta ba. (Siratun Nabawiyya 63).

Yahudawa kuwa waƴanda sune suka rinƙa yiwa mutanen Madinah bushara da zuwan Annabi sai baƙin ciki da Hassada ta hana su yin imani. Don me shugaban Annabawa bai fito daga cikinsu ba?

Sai kaɗan daga cikinsu ne suka musulunta kamar Abdullahi Ibn Salaam. Shima a wannan shekara ta farko ya musulunta.

Mutanen Madinah suna jin daɗi, amma kuma ruwa yana musu wahala, domin kuwa rijiyar da ake diban ruwan ta kafirai ce. Kuma musulmai sai sun biya kuɗi suke ɗiban ruwa. Da wahala tai wahala sai Annabi yayi shela cewa wanene zai siya wannan rijiya a saka masa da Aljanna. Sai wannan namijin kyakkyawan Sahabin nan wanda ya auri ƴaƴan Annabi guda biyu lokaci dabam dabam wato Sahabi Usman ya siyeta. Kuma ya mallakawa musulmai ita. Annabi yayi masa bushara da Aljanna.

Nayi rantsuwa da Allah, numfashi guda da Sahabi Usman (R.A) yayi tare da manzon tsira, yafi rayuwar masu tuhumarsa da zaginsa kakaf albarka. Tun daga na farkonsu da na karshensu.

A dai wannan shekara aka sauya sallar azahar da la'asar daga raka'a bibbiyu zuwa raka'a hudu.

A cikin shekara ta farko ne kuma aka halatta jihadi. Saɓanin kafin hijira da ba a umarci musulmi da komai ba sai haƙuri.

Zamu yada zango anan

Sai kuma a rubutu na gaba da yardar Allah!

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)Where stories live. Discover now