FITA ZUWA BADR

11 3 0
                                    

Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)

Yanayin yanda sahabbai suka ga Annabi ya basu umarni, da kuma yadda suka ga bai damu da cewa da yawansu su fita ba sai sukayi tsammanin ba yaki za'a gwabza ba. Don haka adadin musulman yayi karanchi sosai. Domin kuwa wayanda suke da dabbobi amma a nesa Annabi bai basu umarni suje su dauko ba, hasalima da sukai niyyar su dauko dakatar dasu yayi bai kuma tsaya jiransu ba yayi gaba tare da sauran sahabbai. 

A karshe Annabi ya fita da sahabbai adadin Dari uku da goma sha uku (313). Cikinsu mutum dari biyu da arba'in da yan kai duka mutanen madina ne, wato Ansarawa, ragowar kuwa mutanen Makkah ne ma'abota hijira wato muhajirai.  

(Nurul Yakeen 89)

Kasancewar Abu sufyan masanin hanya, bayan ya turawa kafiran Makkah abinda ke gab da faruwa na tare ayarinsu da za'ai, saiya sauya hanya, kuma cikin sa'a sai ya kewaye wa su Annabi. Ganin ya tsira saiya tura da sako zuwa ga kafiran Makkah yana umartarsu dasu koma tunda babu abinda ya same ayarin dama kariya ce yake neman to kuma gashi ya kaucewa shirin su Annabi Muhammad (S.A.W). Amma sai Kuraishawa suka ki yarda su koma, sukace yadda suka fito da karfi babu abinda zai maidasu gida. Karfinsu zai kara fitowa fili idan ka kwatantashi da karfin rundunar sahabbai.  Suka rinka murna domin su tunaninsu lokacin fatattaka sahabbai ne yayi...

Lokacin da labarin irin shirin da kafirai sukai ya zowa Annabi (S.A.W) sai hankalinsa ya tashi bawai yana tunanin rayuwarsa bane, abinda yake tunani shine masoyansa Sahabbai da kuma makomar da'awar musulunchi. Saidai kuma tare da hakan yasan Allah (S.W.A) yana sane kuma zai kawo mafita. 

Tare da cewa Annabi Muhammad (S.A.W) yafi sahabbai kakaf kaifin basiri, ilmi da kuma fahimtar addini amma a tare ds hakan sai ya juyo da al'amarin garesu yana mai neman shawara. Mutum na farko Abubakar (R.A) shine ya fara jawabi, bayan ya gama Sahabi Umar (R.A) shima yayi nasan jawabin duka su biyun sukai magana mai kyau. Allah ya kara yarda a garesu. Mikdad ibn Amru shima ya tashi yayi magana yana mai nuna goyon bayansa. Shima Annabi yayi masa addu'a.

Amma a hakan Annabi bai yanke hukunchi ba, ko kasan saboda me? Saboda mutanen madina basuyi magana ba, su kuma sunyi shiru ne saboda girmama Muhajirai domin suna ganin cewa tawagar da take da Abubakar da Umar da sauran manyan sahabbai ita yafi kamata tayi magana. Shi kuma Annabi yaji maganar mutanen mutanen Makkah masu hijira don haka yanzu Ansarawa yake da burin ji.  

Annabi saiya nemi a bashi shawara bayan neman farko da yayi, anan sai Sa'ad Bn Mu'azu ya gane abinda ke nufi don haka saiyayi magana mai sosa zuciya mai nuna tsananin goyon bayansu ga ma'aikin Allah (S.A.W). Annabi yaji dadin maganar kuma ta burgeshi game da nishadantar dashi. Kuma daga nan ne fa aka san cewa yaki aka fito. Amma maimakon juma'a su noke sai abu ya faskara domin ba zasu iya barin masoyinsu ba. 

Karkashin wannan zamu gane wani darasi; Akwai wasu abubuwa da Allah da kansa cikin littafinSa mai tsarki ya nemi Annabin rahama ya rinka yi dangane da hakkin sahabbai.

. فاعف عنهم واستغفر لهم، و شاورهم في الأمر

1. Yi musu afuwa idan sukai masa laifi. An umarceshi da haka domin su sahabbai ba ma'asumai bane kamar shi.

2. Ya nema musu gafara idan sunyi laifi, da kuma cikin ibadunsa. Idan shi sukaiwa laifin ma yayi afuwa to ya hada da nema musu gafara a wajen Allah.

3. Ya rinka shawara dasu idan al'amari ya taso masa na yau da kullum.

Ayar nanan cikin Ali imran 159 da bayani a jimlace.

Yan'uwa ya kake tunanin nagartar mutanen da Allah da kansa ne ya umarchi mafi girman halitta da ya rinka neman shawararsu? Anya akwai hankali ga mutumin da yake sukar mutunen da Allah yayiwa irin wannan karramawar.

Hakanan umarnin ya sauka akan Annabi ne, amma hukuncin ya game dukkanin al'umma.

1. Yiwa sahabbai afuwa shine kawar da kai daga laifukan da suka aiwatar tare da kamewa bisa rigingimu da sabani daya shiga tsakaninsu.

2. Nema musu gafara shine nema musu gafara a wajen Allah (S.W.A) kamar yadda wata ayar ta zo da haka 6aro-6aro.

3. Yin shawara da su shine komawa zuwa ga fahimtarsu akan ayoyin Qur'ani da Hadisan ma'aiki (S.A.W). 

Wannan hasashe nane kawai, kuma ina ganin daidaine domin babu kuskure a ciki. Idan akwai tsawon rai da nisan kwana da yardar Allah zamuyi karin haske akan wannan batu.

Munji adadin rundunar musulmai dari uku da sha uku ne, rakuman hawa guda saba'in sai kuma dawakai biyu ko uku. Mutum uku ake hadawa akan dabba guda. Idan wannan ya gaji sai wannan ya hau.

Annabi Muhammad da kansa su uku ne akan rakumi guda. Da shi (S.A.W) da gwarzon namiji Aliyu (R.A) da kuma Marsad ibn Abi Marsad.

Aliyu da Marsad suka bukaci Annabi ya hau abin hawan su zasuyi tattaki, su sun yarda zasu jurewa zafin rana da wahalar tafiyar. amma sai Annabi yaki yarda harma ya nuna musu cewa su biyun basu fishi karfin jiki donyin tattaki ba, kuma kamar yadda suke kwadayin lada shima haka yake kwadayin lada don haka yadda zasu samu ladan tafiya a kasa shima yana son samun wannan ladan. Hadisin na nan cikin Musnad da Ibn Hibban. 

Ashe da Annabi ake rige-rigen yin ayyukan lada.

Ina mai cewa shi Annabi kawai yake so, soyayyar Annabi kawai ya rike ba ruwansa da aiki don baya son lada? To wannan raddi ne gareka.

Babban abinda zakayi ka burge Annabi idan har da gaske kana sonsa to shine kayi aiki tukuru don neman lada da yardar Allah. Annabi zaiyi alfahari da masoya masu aiki ne ba masoya masu labewa ba.

Karfin Rundunar Musulmai da ta kafirai bazai hadu ba, domin su kafirai kusan su dubu suka fito, tare da rakuma dari bakawai da dawakai dari.

Kowace runduna na tafe kusancinta da abokiyar gwabzawarta yana karuwa.

Zamu dakata anan.

Sai kuma a rubutu na gaba.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)Where stories live. Discover now