FIRST NIGHT

927 62 3
                                    

💞 '''HEARBEAT''' 💞
          *JIDDAH*

NIMCYLUV

'''CHAPTER 40-41
  FRIST  NIGHT'''

'''Wattpad@Nimcyluv'''

              Chapter

          ...12:30 angwaye suka ƙarasa gidansu dake NASARAWA gidaje ne guda biyu iri ɗaya sak na Aryan ne a farko saina Irfan,horn Irfan yay a gaban tafkeken get ɗin gidan nasa cikin ƙaramin lokaci mai gadi ya wangale masa get ɗin tare da matsawa baya domin ya bashi damar shiga da motar cikin harabar gidan,cikin nutsuwa Irfan ya sako hancin motar cikin harabar gidan,parking yay a parking space tare da kashe motar idonsa ya lumshe haɗi da cije lips ɗinsa sam ya manta da wani Najeeb ganin tunaninsa zai wargatsa masa plan ɗinsa,yasa ya tattara komai ya barwa gobe,a hankali ya ware idonsa tare da mannasu kan Jiddah wacce ta rufe idonta da alamu ta gaji sosai,murmushi tare da buɗe murfin motar ya fita zuwa side ɗin da take zaune,yana zuwa ya buɗe ƙofar tare dasa hannu ya ɗauke ta cak zuwa jikinsa,firgigit ta farka daga ɗan baccin daya fara ɗaukanta,zillo ya farayi da ƙafarta a ƙoƙarinta nason kwace jikinta daga nata,cije jajayen kyawawan laɓɓasa yay tare da waresu yace"kijimin yarinya bata son na samu ladan ɗauka"hannu  tasa ta ɗan daki ƙirjinsa ba tare data ce komai "do what ever you want to do indai zanji ƙamshin jikinki mai albarka"Irfan ya faɗi hakan dai² lokacin da suka ƙarasu wata ƙofar glass mai ɗan duhu hannu yasa ya danna wani ɗan madanni ƙofar ta buɗe,wow babban parlo ne wanda ya wadatu da kayan zamani komai daka sani na parlo a kwaishi,wata ƴar hanya yabi kaɗan ya tarar da wata ƙofa nan ma saida ya danna wani madanni sannan ƙofar ta buɗe,nan kuma ɗan ƙaramin parlo ne mai kyau da kuma tsarin gaske komai na parlon pink ne ga wasu fitulo masu different colour sai   wal-wal suke a parlon,gefe guda kuma inda yake da ɗan steps na bene daining area ne mai kyau daga nan akwai  ƙofa wacce zata fitar dake garden daga nan kana ganin flat ɗin swming pool,direta yay tsakiyar parlo yana dry baice komai ba ya haura saman steps ɗin bene da alama shine flat ɗinsa,taune lips ɗinta tayi a ranta tana mai farin ciki da kuma jin daɗin samun namiji jajir tacce mai kyau da haiba da kuma tsarin halitta haɗi da gwarjini da kuma cikar zati kamar na mijinta Irfan,haƙiƙa tana ganin dukkan wani buri da kuma muradin rai da zuciyarta sun gama cika tana ganin tafi ko wacce sa'a a nan gidan duniya,ƙara kallon tafkeken gidan tayi da kuma abinda yake cikinta,gdy ta shiga yiwa iyayenta domin sunyi namijin ƙoƙarin wajan ƙawata gidan,wasu siraran hawaye ne suka shiga sauka daga cikin idonta,hankali ta buɗe cute pink lips ɗinta tace"madallah da samun miji na gari kamar sanyin idaniyata my nusfiƙhayat Irfan,madallah da samun jigo da kuma farin cikin raina iyaye nagari masu son farin cikin ƴar ƴansu tabbas bana da kamarku a nan gidan duniya,ubangiji ya haskaka zuciyarka dan hasken Annabi Muhammad S.A.W"tana faɗin hakan tasa hannu akan handle ɗin ƙofar ɗakin dake gefen steps ɗin benen ta shiga.





*IRFAN*
   yana ƙarasawa flat ɗin nasa isa wata ƙofar glass mai kyan gske hannu yasa a handle ɗin ƙofar ya danna kansa ciki nan ƙafarsa ta shige cikin wani italian capert milk,royal bed ne a ɗakin wanda yaji bedsheet gefe guda kuma wadrope ce duguwa,daga gefe akwai dressing mirrow wanda yaji kayan shafa,gefen mirrow'n akwai ɗan ƙaramin frezer mai kyau kalar ash,sai duguwar kujera daga side ɗin bed da kuma ƙaramin table,daret bathroom ya shige yana zuwa ya shiga cire kayan jikinsa tare da sakasu cikin dursbin na saka kaya marasa kyau,shower ya kunna tare da tsaya inda ruwan yake yaɗan dafe hannayensa cikin bango ruwan ya shiga dukan back naked  body ɗinsa,saida ruwan ya daki bayansa sosai sannan ya ɗago kansa ruwan ya fara dukan tulin sumarsa,ya ɗaukin lokaci a haka kafin ya fara wanka yana gamawa yay brush da alwala tare da ɗaura ɗan madaidaicin towel a waist ɗinsa,cikin saurin ya shiga gyara gashin kansa tare ɗigar ruwa,versline ya shafa mai sauƙin shafa sannan ya fesa body spray tare da shafa Arabian Ohud a jikinsa,har lokacin ruwa na ɗiga a kwantaccen gashin ƙirjinsa baƙi siɗik,wanda boxer ya ɗauka ya saka tare da zura jallabiya a jikinsa yana gama komai ya kashe hasken ɗaki tare da fita ya sauka ƙasa,kansa tsaye ya shige flat ɗinta wani ƙamshin mai sanyi ne ya daki hancinsa ɗan ruga idonsa yay saman bed tana kwance tsakiyar bed ta cure waje guda da alama tayi wanka dan sanye take da ƴar ƙaramar rigar bacci light blue mara hannu rigar da ƙyar tazu mata laps ɗinta,ta tattare gashin kanta waje guda tayi masa tufka tsakiyar kanta,lumshe lulu eyes ɗinsa yay lokacin da idonsa ya sauka saman laɓɓanta ta take ta mamul² dasu,ƙarasawa yay wajanta tare da zama gefe bed ɗin tattausan hannunsa  ya ɗura akan tafin ƙafarta ji kake kiiiiii ya jawota har zuwa inda yake,cikin sauri ta buɗe idonta sbd tsoron daga kamata ganin shine zaune gabanta yasa ta kwaɓe fuska kamar zatai kuka,ido ya zuba mata ya naji tamkar ya lasheta gaba ɗaya ya maidata ciki ya huta sbd wani fifinannan sonta dake barazanar tarwatsa masa zuciya a hankali yace"oyya!!! tashi kiyi al'wala muyi sallah"turo baki tayi gaba harza tace tayi sallah sai kuma ta fasa dan bata son yi masa musu,cikin sanyi jiki ta miƙe zuwa bathroom ɗin ɗakinta,da ido ya bita taune laɓɓa yay ganin yadda hips ɗinta ke juyawa ta cikin ƴar rigar baccin da take jikinta,"Ya rabba ƙaramar yarinyar tana son sauyamin lissafi no Irfan control your self haba"




JIDDAWhere stories live. Discover now