BAHAGUWAR RAYUWA.

36 1 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

15.

Yanayin da Mom ta taddasu abin sosai ya yi mata dadi, musamman su Hussain sun saki jiki da Shatu kamar dama can sun santa, takawa ta yi zuwa garesu tana fadin.

   "Auntyn Yara".

Dukkansu suka waigo cike da murna, su Auta suka sauka daga kan gadon da gudu suna masu rungumeta da fadin.

"Oyoyo Mom, mun dawo bakya nan".

"Gani yanzu gareku Autar Dad".

"Mom, Dad ya ce ke kika samo mana wannan Auntyn?".

Cewar Auta dake rike da hannun Mom, da murmushi Mom ta dubeta kafin ta bata amsa.

"E mana, kuna sonta ne?".

"Sosai Mom, fatan dai ita ba zata tafi ba, kamar yanda Aunty Hidaya ta yi mana".

"Aa tana nan tare zaku zauna, karku da mu".

Ihu suka yi a tare suna masu kara rungume Mom din cike da farin ciki, Ishatu kuwa dariya ta sanya kasa-kasa yayin da tarin farin ciki ke lullube gare ta.

Mom ta dubi Salima kafin ta ce.

"Yaushe zata fara zuwa islamiyyar?".

Baki washe Salima ta dubi Mom din, kafin ta mayarwa da Mom amsa.

"Lah ! Dad ya fada miki ashe?".

Mom ta dauke fuska cikin dariyar Salima kasa-kasa ganin yanayin da ta yi, kafin ta ce

"E ya fada min".

"Amma na ji dadi wallahi, ai gobe a sabar sai mu tafi tare".

"Allah ya kaimu lafiya, bari na je gun Balaraba na ji abin da za'a girka mana".

Tana fadin hakan ta juya tare da fice wa daga dakin ranta fari tas, ganin yanayin da ta samu iyalin nata.

WASHE GARI.

Tsaye suke falo cikin shigar islamiyya hijab milki har kasa, Auta da Twins na sanye da uniform maroon wanda shi ne kalar nasu, Dad na zaune falon akasan carpet hannunsa rike da jarida yana karantawa, durkusawa suka yi har kasa suka gaishe da shi, cike da farin ciki ya dubi iyalan nasa yana amsawa kafin ya kamo hannun Auta ya rike yana fadin.
  "Uwata ta kaina".

"Ina kwana?".

Muryar Shatu ta daki kunnuwansa, a hankali ya dago kai ya yi mata duba daya kafin ya sauke kallon kan fuskar Mom ya amsa cike da fara'a, wannan shi ne ganinta da shi na farko a fili, saboda duk gidan ga hotunansa nan, sai ta ga a fili cikar zati da dattakonsa a fili sun fi bayyana, haka yanayi na kyawu da zubi, suna kama da Salima sosai sai dai ta fishi farin fata da manyan idanuwa, hannun Ishatu Auta ta kama tana duban Mom da Dad kafin ta ce.

"A yi mana Addu'a".

"Allah kiyaye min ku Auta".

Suka hada baki wajen fadi, kafin su dubi juna murmushi, su Ishatu suka fice daga falon saboda lokaci na daf da kurewa.
        Driver tuni ya gama ready suna shiga mota ya ja suka fice, Mai gadi ya mayar da kofar gate din ya rufe.

Bayan isarsu sai da suka raka su Twins class kafin su kai Auta daga nan suka shiga office na shugan makarantar, tuni an riga da an gama yi wa Shatu komai kai tsaye ajinta aka rakata tare da Salima, sai bayan da ta tabbatar ta zauna sannan ta wuce nasu ajin.

Wasa-wasa kwanaki da wuni suna shudewa har Shatu ta shafe sati guda cur a gidan, sabo sosai ya shiga tsakaninsu tana jin dadin zama a gidan domin babu abin da ake nuna mata na banbanci musamman Mom tana ji da ita kamar yanda take kulawa da iyalanta,  a bangaren Dad ma haka abin yake dukkan abin da zai siya to ciki har da na Shatu baya taba mantawa da cewar tana zaune a gidansa, rayuwarsu gwanin ban sha'awa da tsayawa a rai, duk sanda Dad yake gari sai a raba dare ana hira cikin raha da kaunar juna, tun hakan na takura Shatu har ya zamana itama ta saba ta saki jiki sosai, wani lokacin ita ke basu labarin yanayin kauyensu da ire-iren al'adunsu.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now