BAHAGUWAR RAYUWA.

42 3 0
                                    


ASHIRIN.

  QURRATUL-AYN.

  Yayan nasa na fita a falon ya nemi guri kan kujera ya zauna tare da dafe kansa yana tunani akan wannan al'amari na Azif, bai zata ba sai ji ya yi an dafa kafadarsa ta baya ko bai waiga ba yasan wacece.
   Dora hannunsa ya yi kan hannunta tare juyo da ita gabansa ta nemi guri ta zauna kusa da shi idanuwansu na kallon juna kafin ta furta.

   "Wani abu ya kuma faruwa ne?".

"Aa wannan mafarkin da Azif ke fama da shi, shi ne abinda yafi komai damuna, na rasa mene matsakar na kuma rasa dalilin maimaicin mafarki daya a kullum".

Mamy ta yi ajiyar zuciyar kafin ta furta.

"Addu'a ita ce mafita a kullum, mu cigaba da yi masa ita".

Ya Bukar ya gyad'a kai alamun gamsuwa da matarsa, kafin su mike a tare yana mai riko hannunta suka bar bangaren Azif zuwa nasu bangaren, kowannen su zuciyarsa cike da sake-saken matsalar Azif.

7:45am.

  Bakwai da mintuna arba'in da biyar na safe daidai ya shigo bangaren yayan nasa da sallama ya sanya kai cikin falon suna zaune dukkansu tsakiyar falon gabansu jere da tarkacen abinci domin yin breakfast, (karin safe) kusan a tare suka amsa sallamar suna masu binsa da kallo yana sanya da farin yadi da hula baka haka takalmin dake sanye kafarsa ma baki ne, tsintsiyar hannunsa daure da bakin agogo na fata wanda aka yi wa fuskar agogon ado da duwatsu masu kyalli, takalminsa ya zare safar dake sanyae a kafarsa ta bayyana a fili ya tako zuwa cikin falon yayin da yaran suka yo kansa da gudu suna fadin.

"Uncle Barka da asuba, Good morning".

"Morning twince, amma bana ce gaisuwar barka da asuba tafi dadi ba, akan morning din nan?".

Ya dan bata rai kamar gaske, Yan biyun Suka dube shi da fadin.

"Arfat ce bata jin magana Uncle mun gaya mata..!".

"To shi kenan, zo nan Arfat".

Ya sunkuya tare da daukan yarinyar zuwa kan kafadarsa kafin ya yi murmushi yana fadin.

"Me yasa bakya jin maganar Uncle diyar albarka".

"Allah ina ji, sune dai basu ji".

Ta yi maganar cikin gwarincinta, Azif ya karasa tsakiyar falon kafin ya ajiyeya ya nemi guri ya zauna yana mai cigaba da gaishe da yayansa da matarsa.
    Cikin fara'a suka amsa suma tare da jindadin yanayin da suka ganshi a yanzu, duk da cewar sun san Azif sosai mutum ne dake boye damuwarsa duk runtsi ya kanyi kokarin shimfida murmushi a saman damuwar da ke lullube kan fuskarsa, sai ka yi da gaske kafin ka san gaskiyar abinda ke a jiye a bigiren zuciyarsa.

  Mamy ta miko masa kofi dauke da ruwan Lipton kamar yanda tasan yana so babu madara a hankali ya fara sha yana sauraren hirar yaran sama-sama jefi-jefi zuciyarsa na kokarin bijiro masa da abin da yake kunshe kasan ransa, kamar an mintsine shi ya mike tsaye bayan ya ajiye kofin tea din bai cika cin abu mai nauyi da safe ba, ya dubi yaran da fadin.

   "Ku tashi muje ko? Sauri nake yi yau ban so takwas tamin a gida ba".

Da sauri suka mike tare da daukan school bags dinsu, Arfat dake lafe jikin Mamynta ta dago musu hannu alamun byee, Azif ya yi murmushi ya lakaci hancinta kafin su yi sallama da Yayansa da shima ya mike domin shirin fita.
   Tun kafin ya karasa ya danna key din motar ya bude da gudu yaran suka karasa tare da shigewa yana zuwa mazaunin driver ya shige yana mai sanya wa motar key, tun fitowarsu mai gadi tuni ya bude gate suka fi ce.

Suna tafe a hanya 'yan biyu nata faman yi masa hira amma shi hankalinsa na can wani bangare na daban, har suka isa makarantar Kuntau ya ajiyesu a bakin gate na makaranta tare da juya hancin motarsa ya dauki titin da zai sa da shi ga gurin aikinsa.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now