BAHAGUWAR RAYUWA.

54 3 0
                                    


Na
QURRATUL-AYN.

Wattpad@JannatQurratulayn.

FITA TA BAKWAI.

Wasa-wasa kwanaki da wuni sai shudewa suke, yayin da ciwo na Inna keta kara ta'azzara a gefe guda kuma yanda Zainaba ta dauki abin ke baiwa iyayenta tsoro a kullum, tun ana fita neman Shatu tare da yakinin ganinta wata rana har an hakura, sun zubawa sarautar Allah ido cike da burin komai jimawa zata dawo.

     A bangaren Shatu kuwa ciwukan jikinta suna yin sauki cikin kudura ta Ubangiji ta fara jin dan karfi cikin jikinta, yauma kamar kullum Kamar yanda suka saba tsayin kwanaki goma sha biyu kenan tana zaune cikin kogon dutsen ba tare da ta yi zabi guda daya da Manya ya bata ba, haka kuma a kullum ta duniya zai kawo mata abincin da zata ci amma yanda ya kawo shi haka zai zo ya dauki abinsa, domin ta riga da ta salwantar da rayuwarta ta fidda rai daga son cigaba da rayuwa a duniya kaf, a ganinta matakin kin cin abinci kadai ya isa ya halakata kowa ya huta, anata tunanin idan ta mutu dole Manya zai fidda gawarta idan anga gawarta dole zasu ajiye dukkan makaman yakinsu su fuskanci abin da ya damesu saboda tana da tabbacin babu wanda yasan Manya ne ya saceta, domin ta yarda da gaskiyarsa saboda Manya mutum ne wanda duk rashin imaninsa abu guda ya tsana karya kamar yanda baya so a yi masa karya haka baya kaunar ya yi ta akan kansa, kome zai yi akan gaskiyar sa yake yinsa.

   "Na fahimci kin shirya bayar da rayuwarki akan ki cigaba da zama dani?".

Ganin bata bashi amsa ba ya cigaba da fadin.

"Ki yarda da aurena ki yi rayuwar farin ciki na har abada, idan ta kama zamu iya barin kauyen nan muje muyi rayuwar 'yanci".

"Allah ya kiyashe ni aikin dana sani Manya, ko maza sun kare tir da rayuwa tare da kai, abin kyama ne ma a ce kaine ka zamto miji a gare ni, a yanzuma ji nake kamar na gama kazanta da har jikina ya gogu da naka, kaicona da wannan muguwar kaddarar..!".

Tass...ya dauketa da wani gigitaccen mari wanda ya yi sanadiyyar gilmawar wani haske ta gefan idonta, ya shafe mintuna kafin ganinta ya daidaita, amma duk da wannan gigitaccen marin daya sharara mata ko gezau a idonta bare kasan marin ya shigeta illa gefan fuskarta daya tashi nan da nan, Manya ya dafe kansa kadan tare da sosa keyarsa a lokaci guda kafin ya ce.

"Kin ga abin da kaifin bakinki ya ja miki ko? Ki dinga tsarkake kalamanki akaina domin ni ba mugu bane a gareki nasan na keta haddinki amma bai kai abin da zaki kirani da wadan nan manyan kalaman ba saboda ko kina so ko baki so tun da kika ce haka tabbas dolenki zaki yi rayuwa tare da ni da yiyuwar samun albarka na daga 'ya'ya wannan alkawarina ne, Manya baya caba alkawari kamar yanda bana daukar alkwari sai ina da tabbacin iya cikawa to na yi wannan alkawarin Shatu ke tawa ce har a bada".

Ya dauki abin da yake kawo mata abincin ya fice da shi, Ishatu ta yi baya da kanta cikin daci da kunar zuci ta buga shi jikin bangon dutsen sosai zafin ya shiga jikinta, amma ji ta yi wannan ba komai ba ne akan radadin ciwon da Manya ya ji mata a zuciyarta ji take tamkar idan ta sake wani yunkuri zuciyarta zata ita tarwatse wa nan take, fuskarta ta cuca cikin cinyoyinta da nufin zub da hawaye ko ta samu saukin abinda yake tokari daga makogwaronta har kasan zuciyarta, amma ko gezau, sanyin dake busota kadan-kadan shi ne ma yake neman daga mata hankali fiye da ciwon cikin da yake neman ta kura mata a lokaci guda.

Cikin abin da bai wuce dakika ba ta fara kakkarwa da dukkan alamu na sanyin zazzabi ne, kamar daga sama ta ji an lullubeta da abu ta dago kai da sauri wanda ta yi tsammani shidin ta gani, bata damu ba kasancewar bata da kwarin gwiwar yin wani yunkura a yanzu, yanda ya ji hucin zafin jikinta na huro shi abin ya daga masa hankali matuka, ya ga bashi da wani zabi wanda ya wuce ya tsaya yin jinya indai yana son ci gaba da ganinta a raye dole ne ya kula da ita da a halin da take ciki a yanzu, ficewa ya yi da sauri domin neman mafita ta karshe.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now