BAHAGUWAR RAYUWA.

46 2 0
                                    

FITA TA SHA HUDU

Na
QURRATUL-AYN

Burki matokin motar ya take da sauri, yayin da matashiyar budurwar dake zaune gefen mai zaman banza ke fadin.
   "Wayyo Mom ! Ba dai mutum kika buge ba?".
   
  Matar da ke yin driving wacce aka kira da Mom ta waigo hankalita a tashe tana mai duban budurwar, ba tare da ta tanka mata ba ta balle murfin motar ta fi ce da sauri, matashiyar budurwar itama ta fito tare da bin bayanta.

Tuni mutane sun taru akan Ishatu har da 'yan sanda mutum biyu, suna daf da isa Mom ta koma da sauri cikin mota ta dauko ID card nata tare da dawowa wajen, ta yi wa police din nuni da shi ita din ma'aikaciyar lafiya ce a private hospital din dake kusa da wajen, kai tsaye aka dauki Ishatu wacce har wannan lokacin bata San inda kanta yake ba, aka sanyata cikin mota kafin daga bisani Auntyn ita da budurwar suka shiga motar Police din suka biyo su a baya, kai tsaye asibitin aka wuce da Shatu, kasancewar suna tare da police take aka shige da ita emergency Mom ce likitan data tsaya akanta, cikin ikon Allah ba ta yi wani rauni ba illa buguwa da ta yi a hannu da kafa, tsoro ne ya yi sanadiyyar sumewarta a wajen, bayan kammala mata dukkan abinda ya da ce, aka fito da ita zuwa dakin da zata huta, matashiyar budurwar ta shige dakin ita ma tare da neman daya daga cikin kujerun ta zauna tana mai duban Auntyn da fadin.

  "Ki je ki kammala komai, zan kula da ita".

Auntyn ta gyada kai tare da fi ce wa daga dakin ta koma wajen police din.

Bayan mintuna goma sha biyar da fitar Auntyn, Ishatu ta fara motsi alamun farkawa, budurwar ta taso daga inda take zaune tare da dawowa daidai kan Shatu ta tsaya tana sauraron farfadowarta, a hankali Ishatu ta bude idonta tare da karewa dakin kallo kafin ta sauke kallonta akan fuskar budurwar dake tsaye kanta tana murmushi, kokarin tashi zaune Ishatu ta fara yi, ganin hakan ya sanya budurwar taimaka mata ta zauna, tana fadin.

"Sannu ko?".

"Yauwa sannu".

Ishatu ta mayar mata tana mai cigaba da fadin.

"Inane nan, me nake yi anan kuma?".

Ta yi tambayar tana mai duban hannunta da aka sanyawa Karin ruwa, ta kara da cewar.

"Mene wannan din?".

Takai dayan hannun tana kokarin zarewa, budurwar ta rike hannunta tana fadin.

"Asibiti ne nan, kar ki cire zaki jawa kanki matsala".

Shatu ta bita da kallon mamaki da tambaya cikin ranta amma ta gagara furtawa, budurwar ta yi murmushi tare da dorawa da fadin.

"Sunana Salima, mune tsautsayi ya giftawa muka bigeki da mota".

Ishatu ta dubeta ba tare da ta ce komai ba, ta kai hannunta tare da dafe kanta cike da tariyar abinda ya faru gareta, daidai sanda aka turo kofar dakin Aunty ta shigo cike da fara'a tana fadin.

"Alhamdulillahi ta farka? Dama bana tunanin zata kai wani lokaci da dukkan alamu zamu iya tafiya gida".

"Ita kuma nan zamu barta?".

"Aa muje gida Abbanki ya dawo yanzu ya yi min waya, zuwa da safe sai mu rakata gida insha Allah kafin sannan jikin ya kara warwarewa".

Takai maganar tare da cire wa Shatu karin ruwan dake hannunta, ta mikar da ita tsaye da fadin.

"Salima riketa mu tafi".

A tare suka fito da ga cikin clinic din, sauran ma'aikatan na yi mata Allah kara kiyaye wa, har zuwa inda suka yi parking motarsu, gidan baya Salima ta zaunar da Shatu tare da rufe kofar motar ita kuma ta bude gidan gaba ta zauna, Mom ta shige mazaunin driver tare da sanyawa motar key ta fi ce daga harabar clinic din.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now