BAHAGUWAR RAYUWA.

50 1 0
                                    

SHA TAKWAS.

MAINA.

    "Fad'i dukkan sharad'inka a shirye nake domin cika maka su ko da kuwa fansar raina ne, indai zaka amince da bukata ta".

Tsaraki ya yi gajeriyar dariya kafin ya sake daidaita tsayuwarsa yakai dubansa fuskar Dan Zabuwa a karo na kusan hudu, kafin ya fara magana da fadin.

"Tabbas zan amince da Manya ya auri Mairamu idan har zaka dawo da kambun tsarafi gare ni, zan yarda na sadaukar da fansar gaba idan har ka amince ka damka kambun sarautar ahalin mu guda biyu a hannuna, wanda kakanmu ya kwace daga hannun Mahaifina, zan yarda da auren ne kawai idan ya kasance ka durkusar da karfi da iko na Manya, idan har ka aminta da wadan nan sharadin to shirye nake ko yanzu basai anjiba ba ko gobe a daura wannan aure".

Dan zabuwa ya zubawa Tsaraki idanuwa tsayin wasu dakikai yana nazartar gaskiyar al'amarin daya zo masa da su wanda bai yi tunanin hakan daga Tsaraki ba, domin abin da ya bukata abubuwa ne masu matukar wahala, amma da ya tuna da gudan jininsa tilo daya tal a duniya mafi soyuwa a gareshi sai ya ji a shirye yake ya sadaukar da komai daya mallaka domin samun lafiyarsa, dago kai ya yi yakai dubansa ga Tsaraki wanda shima kallon nasa yake yi fuskarsa fal murmushi domin yasan ko babu komai ya yi abin da zai wulakantar da Dan Zabuwa a kauyen Maina, shi kuwa Dan Zabuwa ba tare da sake nazartar yanayin Tsaraki ba ya cigaba da fadin.

"Zan baka dukkan abin da ka ambata, amma akan sharadi guda daya".

"Ina jinka".

"Sai idan ka yi alkawari da kambun tsafi ba zaka cutar dani da yarona ba*.

"Na yi alkwari, kuma kasan nasan girman alkawari zan rike kalmar da yakininta, bazan canja abin da na fada ba".

"Shi kenan zuwa daren yau ka zo gidana zan baka dukkan abin da ka bukata"

"An gama"

Da ga haka suka yi sallama kowa ya yi hanyarsa, Tsaraki cike da dumbin farin ciki da murnar cin galaba akan Dan Zabuwa, Dan Zabuwa kuwa abin duniya ya yi masa yawa, yana ganin zai aikata babban kuskure ne zunubi mai girma, amma idan ya tuna lafiyar yaronsa sai ya ji a ransa hakan ba komai ba ne.

KANO.

WASHE GARI.

  Bayan ta idar sallar asuba tana zaune kan abin sallar tana addu'o'inta, saboda sabo da tashi a gidan su Salima, har ta soma zame mata jiki, bacci ne ya sace ta anan inda take zaune, kamar daga sama taji yo tashin bugun kofar dakin nata, firgigit ta farka tare da murje ido ta nufi bakin kofar da fad'in.

  "Waye ne?".

"Hafsy ce".

Ta bata amsa a daidai sanda ta bude kofar, da murmushi suka dubi juna Ishatu na fad'in.

"Bismillah shigo mana".

Hafsy ta sanya kai cikin dakin tana mai cigaba da fad'in.

"Kin jini shiru sai yanzu Allah ya yi dawowar mu, kai amma dakin naki ya yi kyau wallahi".

Ta kare maganar tana mai ajiye manyan ledojin data shigo da su kafin ta nemi gefan katifa ta zauna, ta sake duban Ishatu dake tsaye tana binta da kallon mamakin jin cewar tun daren jiya sai yanzu ta dawo.

  "Ishatu lafiya kuwa?".

Ishatu ta dawo daga duniyar tunanin da murmushi shimfide saman fuskarta kafin ta ce.

  "Kenan ba gida kika kwana ba?".

Hafsy ta yi dariya ba tare da ta bata amsa ba ta cigaba da magana.

"Kin ga duba cikin waccan karamar locker akwai plate da sauran kayayyaki kitchen dauko nan mu yi breakfast dan wallahi da yunwa na dawo, wannan shegiyar dinner a bushe basu tanadi abincin kirki ba sai kayan shaye-shaye na banza".

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now