BAHAGUWAR RAYUWA.

42 2 0
                                    

FITA TA SHA BIYU.

    NA
QURRATUL-AYN.

BAYAN KWANA UKU.

  Yauma kamar kullum yanda suka saba tun safe suke aikin kai kawo na abinci a rumfar Ladi, yayin da suka dan samu hutu na lokaci kalilan suna zaune suna hira inka dauke Shatu da aikin kallonsu kawai take yi, daya daga cikin 'yan matan mai suna Furaira ta dubeta da kulawa kafin ta ce.

    "Ni kam har yanzu a gidan Ladi kike kwana ne?".

"E mana".

"Tab..lallai ke ta musamman ce".

"Ban gane nufinki ba?".

"Tabbas ke ta musamman ce, amma na tambayeki mana?".

"Ina jinki".

"Ladi kuwa ta gabatar da ke".

Shatu ta yi shiru tsayin lokaci tana nazari da tunanin inda maganar ta dosa, kafin ta ce.

"Ni wallahi duk ban gane abin da kike nufi ba".

"Gaskiya ne, dole ki ce baki gane ba kawai dai kina son boyemin ne".

Shatu ta matso kusa da Furaira sosai kafin ta sake magana da fadin.

"Wallahi iyakacin gaskiya ta, ban gane nufinki ba, amma ke ina kike kwana?".

"Can tsallake muke, nan muke kwana bamu kadai bane ba ai, can dinma gidan Ladi ne, amma nan gidanta ne ita kadai sai budurwar data isa takai take saukar da ita anan inda take, shi yasa nace ke ta musamman ce".

  "Amma kwananki nawa a gidanta?".

Shatu ta yi mata nuni da hannu saboda ba tasan yanda zata yi mata lissafin ba.

"Kwana shida..!".

Cewar Furaira yayin data dora da fadin.

"E ba zaki gane abin da nake nufi ba gaskiya, sai gobe insha Allah zaki yi baki manyan mutane, ke kyakkyawa ce, kina da diri darajarki tafi tamu Shatu, cikin kwanaki kadan zaki daina aikin gidan abincin nan nasani".

"Me yasa kika ce haka? Ni bani da inda zanje idan nabar nan".

Shatu ta tambaya, Furaira ta bita da kallo tana mai girgiza kai hade da murmushi sosai ta kara tabbatar da cewar Shatu Bagidajiyarce ta karshe

'Ban da haka, yaci ta fahimci inda zancena ya dosa'.

Ta yi maganar cikin ranta, ta bude baki zata yi magana, Ladi ta iso inda suke cike da fada take fadin.

"Wai uban me kuke tattaunawa haka? Tun dazu nake kwala muku kira, so kuke ku koranmu costumer tun dazu ana jiran kai abinci amma babu wacce ta motsa, ke Shatu maza zonan".

Suka mike a tare suka bar wajen, yayin da Shatu tabi bayan Ladi, Furaira na aikin jifanta da murmushin da ta kasa tantance abin da take nufi.

"Ungo nan waccan motar da kike hangowa can zaki kai kayan ki dawo yanzu".

Ta mikowa Shatu leda viva, ba musu Shatu ta karba tare da juya mata baya ta fice daga rumfar ta nufi inda ta hangi wata bakar mota, glass dinta ma baki ne, baka iya hangen abin da yake ciki, tana isa wajen aka bude murfin motar, Shatu ta mika kayan tana fadin.

"Gashi inji Ladi".

"Shigo mana, kya tsaya daya waje haka?".

Muryar babban mutum ta daki dodon kunnenta, duk da bata ga fuskarsa ba tasan babba ne.

"Ladi ta ce na dawo da wuri ne".

"To babu damuwa, nagode kinji".

Mutumin ya yi murmushinsu na manya, kafin ya miko hannu ya karbi kayan, yana mai miko mata rafar 'yan dari biyar-biyar.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now