Komai yayi farko yana da karshe

Start from the beginning
                                    

hannu ta saka taja kumatun shi a hankali tana sakar mashi murmushi mai sanyaya zuciya, daukar Alim yayi ya sumbace shi sannan ya kwanatar dashi, ya dauki Ayyan sai kallo yakeyi shima kwantar dashi yayi kusa da dan uwan shi,sakarma juna murmushi sukayi jin shigowar Fadila yasa ta barmata yaran dan ta kulama ta dasu hannun su sarke suka tafi har dining sai shagwaba take zabgawa san ranta, nan akai saving dinsu suka fara cin abinci cikin nishadi saiba mijin su kulawa sukeyi lallai Sadauki ya kara yarda b abinda yakai aure dadi bare in iyalan ka na zaune lfy sai jin dadi yake yana kara jin son matan nashi..... A wajen su Barde kuwa yau asabar aka daura masu aure shida kanin shi Jarmai inda suka auri yan uwan mahaifiyar su, Barde ya auri yar yayan Umman su, Rukayya Adam da Abbas Hamza Muhammad, sai Jarmai ya auri yar kanwar Umman su Zainab Hassan da Yasir Hamza Muhammad dukkan su akan sadaki Foam Hamsin aka shafa fatiha aka raba shaidin aure ranar haka aka wuni ana shagali har dare daman kakan su ya basu gidaje anan aka kai masu amaren su, cikin ikon Allah anguna sun tare da matan su cikin farin ciki da lumana haka sukaita zaman su kowa naba dan uwan shi kulawa ta musamman........

Allah yataimaki Sarkin Burhaan Allah yakara maka nasara sakone daga kasar NIGER cikin birnin Agadas wasika ce akace inkawo maka hannuna hannun ka Allah yakara ma Sarki lfy da nisan kwana, ya dukar da kanshi kasa hakan yasa Sarki Muhammad murmusawa ya miƙa hannu ya karba ya bude ta yafara karantawa, murmushi ya saki cikeda farin mikama Magatakarda wasikar yayi ya bashi izinin karantawa agaban kowa kamar haka......

*Asslamu alaikum*

_Fatan alkhairy dan uwana aminina masoyina da fatan sakona ya sameku cikin aminci da farin ciki, inaima albishir Allah ya sauki matata lfy munsamu karuwar ya'ya biyu mace da namiji dukkan su, suna cikin aminci da cikakakkar lfy, daga dan uwanka Mukhtar Abubakar Tafeedah,bissalam_

Duk wanda me fadar nan saida yaji dadin wannan albishir din, sakawa yayi aka bashi masauki da kayan Abinci tashi yayi cikeda zumudi ba inda ya sauka sai sashen Ammi isketa yayi zaune saman sallaya, gaisheta yayi dan shiru yayi ganin yanda yaketa murmushi hakan yasa ya gane yana cikin farin ciki, jin ta tambaye shi yasa shi kallan ta, "daga ninka kana cikin farin ciki me yafaru fadaman? "Ammi yau din nan na sake zama Abba, "tofah kardai Safiyyah ta sauka aina dauka da dan sauran  lokaci"Aaa Ammi, kanwata ta sauka dazun sakon Tafeedah ya sameni ta samu tagwaye mace da namiji.....wani irin dadi ya ziyarci Ammi sai murna takeyi magana tayi"kace auta ta haihu kenan Allah sarki autata, ranar yaushe, sosa keya yayi yace"yau kwana ukku kenan jibi zamu tafi insha Allah, "Allah yakaimu sai kutafi da gimbiya Maryama, sai gimbiya Sa'adatu saiku barni da Safiyyah Jummai zata bata kulawa, saidai kana ganin tafiya da Zubaina zai yuyu kuwa? "Ammi ai za'ayi masu tanti akan doki ba abinda zai same su, komai lfy lou kinga daga can saitaga gida tunda duk jaha daya suke, garine banbanci daman kinga tunda tayi aure bata je gida ba, "kuma ka kawo hanzari, kabari gobe zanje wajen Abban ka abinda mukayi dashi zakajini, yakamta a hada komai na uwa da kayan bukata ajema auta dasu, "Ai Ammi kibar komai hannu na ba abunda bazan ma auta ba, baki da damuwa "Allah yaimaka albarka, "Ameen Ammi, magana ta kuma yi mashi "ko Asiya tasani kuwa? Da tayi zaman bakwai "gaskia bana tunanin basu jiba nasan Tafeedah zai turama su da sako, bari inje insan abinda yakamata ayi kafin zuwa jibi sai mukoma da dan aiken kamar hakan zaifi "shikenan nima din ai shiri zanyi duk inba su Maryama dan aikama ta kaima duk abinda akasan zata so, kai shawara da matan ka sai aimata ina sauraran ka, "toh Addanah ki huta lfy.....

Yana isa sashen shi ya iske su sai fira sukeyi sun saka kaya iri daya bakaramin tafiya da imanin shi, sukayi ba wani irin dadi yaji tsakiyar su ya zauna a saman kafat hakan yasa Safiyyah ta kwanta a saman cinyar shi Asma'u kedan yimata tausa kafafun ta sun kumbura, itako Zubaina kallan kyakkyawar fuskar mijin nata takeyi taga sai murmushi yakeyi tasan akwai albishir, ruwa ta zuna a kofi ta bashi, a baki yasha cikin kauna Asma'u da Zubaina har hada baki suke wajen tambayar shi ganin yana ta farin ciki, murmushi yayi wanda harda sauti ya fita ganin matan nasa nasan jin gulma, aiko saida yagama jansu da tsokana sannan ya fada masu "ku shirya jibi zamuje Agadas kanwar ku ta haihu, ai da sauri Asma'u ta rungume shi si murna suke itama Zubaina dadi kawai takeji danko Safiyyah takasa magana saidai tace su autar Ammi angirma Allah ya raya baki dayan su suka amsa da Ameen, riko hannun su yayi sannan ya fara tambayar su me yakamata a hada mata idan za'a je haka kowa taita fadar albarka cin bakin ta karshe dai suka yanke shawarar hada mata kayan uwa da na babies haka kowa cikin matan tafara shirin hadama Juwairiyyah gift batare da mijin su ya sani ba hatta Safiyyah daba zuwa zatai ba saida ta hada nata gudumwar zata bada akai mata, A sashen Mai Martaba kuwa Ammi ce zaune a gafen shi tagama dama mashi fura tabashi yasha sannan ta fada mashi ranar da aka fidda za'ayi tafiyar tabbas yaji dadi ganin yanda Mukhtar ya rike mashi yarsa da mutunci yasan yayi sa'ar suriki na kwarai kudade masu yawa yaba Ammi yace duk abinda ake bukata asiyoma autar shi, godiya tai mashi, sannan tai mashi sallama dan zuwa wajen su Sa'adatu susan abinda ya dace su sayawa yar tasu a matsayin su na iyaye, shima Turaki yafadawa Halimatu ta shirya da ita zai tafi sai matar Hussain gimbiya Hafsat zasubar gimbiya Khadija da Safiyyah a gida wajen su Ammi, dan ta debema Safiyyah kewa a wajen Shattemarh, kuwa Nafeesa ke kwance asaman cinyar shi itama labor takeyi a sama sama sai tausan rabin rain nashi yakeyi yau kimamin kwana biyu kenan da isowar sakon aminin nashi Tafeedah ya karanta kuma yaji dadi matuka dan har walimar murna saida ya hada akayi, dan yasan bazai samu damar zuwa Agadas ba ganin matar shi haihuwa ko yau ko gobe saidai yaba dan aike wasika zuwa ga Tafeedah da sakon kaya da kudi yace aba mai jego yana masu barka da fatan alkhairy, koda aka kai sako yakaran ta shi

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 04, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SADAUKIN BURHAAN CIGABAN IZZAH KO MULKIWhere stories live. Discover now