Komai yayi farko yana da karshe

40 0 0
                                    

⚔️SADAUKIN BURHAAN ⚔️
_Daukar fansa cigaban izzah ko mulki_

Na
*Jameey Yar'mutan kankia ce ❣*

*Alhmdulh komai yayi farko to zaiyi karshe haka maganar take inji masu karin magana, kimamin wata takwas kenan ina typing din wannan buk din, wata shidda kuma ina posting dinsa, tun muka fara IZZAH KO MULKI munyi wata biyu muna yinshi sannan kuma mu ka shiga DAUKAR FANSA WATO SADAUKIN BURHAAN, shine mukayi wata hudu muna yinshi, tom yau ga rana Allah ya kawo yau 4 ga nov 2020 Allah ya so ya yarda yau mungama litafin baki dayanshi, wannan abun murnane a garemu mu dukanmu nida ku baki daya😁*

*ina miƙa godiya ta ga duk wani masoyina dake a social media, har da maƙiyana duk ina masu fatan nasara gami da alkhari, sannan ina gdy sosai ga masoyana wanda suke sayan paid book dina, dan ko kun rike ma'ana kamar yanda nace karki fitarman da litafi waje kuma kuka rike amana baku fitar ba hakan yayi man dadi sosai da sosai, ba abunda zance daku sai Allah ya bar kauna da zuminci Amin*

Page 126&130 ➡️🔚





Bayan kwana arba'in gimbiya Zubaina ta fita ruwan zafi, ita da ya'yanta suna cikin koshin Lfy, yau yakama ranar girkin gimbiya Asma'u ita da hadimai sai hidima sukeyi kamar ba gobe, fadila baiwar gimbiya Zubaina taje madafa wajen gimbiya Asma'u tafada mata sakon uwar dakin nata, duk da banji abinda ta fada ba saidai gimbiya Asma'u tayi murmushi cikin jin dadi, a wajen gimbiya Safiyyah kuwa ta riga da tayi nauyi sosai, dan ko aiki ta aje batayi kulawa ta musamman, take samu daga wajen mijin ta har da abokan zaman ta, a sashen gimbiya Mardiyyah kuwa tayi tunda Allah yasa aka haifa mata jikoki bata wasa da lamarin ta, kullin saita sa an dauko mata su Ariff wajen ta suke yini dan aiki yai ma gimbiya Asma'u yawa, wani lokacin ma harda su Alim take ansowa duk da ya kasance yau suka fita ruwan zafi saida ta sa Jummai tadaka gumba akayi sadaka, a wajen Sarki Abduljalal zaune yake shida yan uwan shi suna ta raha dan zuwa yanzun ba karamin hadin kai ya shiga tsakanin shi da Abdullahi ba sai waziri Basheer da yazama kamar wani ɗan uwan shi, na jini......

FA'DAH

Yau Sarki Muhammad ne da manyan yan fa'dar shi suna meeting a babban hall din fa'da kowa yayi shiru na yan mintoci Sarki Muhammad ne yafara magana cikin izzah wadda baisan yana aiwatar da ita koda yake ai abin a jinin jikin shi yake magana yafara cikin  ƙaushin murya saida ya maido hankalin su wajen shi sannan yace "Dalilin dayasa na taraku anan badan komai ba saidai ince maku kusani Burhaan da kuka sani a da ba itaba ce a yanzun ya zama ga duk wani mai mikami a cikin Masarautar nan ta Burhaan ya kasance kowa ya rike girman da matsayi na wannan Masarautar, kamar Maji dadin Burhaan kowa yasan aikin shi shine kula da alamura na Masatauta duk wani walwala da sauran kayan jin dadi hakkin shi duba da dan uwana Shattemarh nai nan hakan yaja ra'ayina zan ba Huzaifa Kabir gilba rikon wannan kujera kafin wani lokaci, sannan Sarkin taska da Sarkin rumbu inasan a fiddo dda abinci a rabama talakawa da bayi na sannan a hadama kowa da kudin cefane, na bada wannan dokar duk bayan wata ukku za'a dinga mutunta su da daraja su ta hanyar basu kayan masarufi, duk da suna bayi amman inasan a dinga basu yanci ana basu uzuri na haramta kyara da wulakanta bawa, saidai abinda ba'arasa na yau da gobe dafatan za'a yi anfani da abinda na gaya maku bansan ku ketare doka ta yin hakan babban kuskure ne a gareku dafatan kowa ya fahimta, dan haka yanzun inaso Sarkin taska da Sarkin rumbu a kalkashin ikon maajin Burhaan da kutashi aje afara badawa, amman a fara ta taskar bayi, Allah yataimaka yabamu ikon sauke wannan nauyin lfy........

Yana komawa gida dakin shi ya shiga yayi wanka ya fito ya fara shirya wa kenan saiga gimbiya Asma'u rungume shi tayi kanshin turaren ta ya sanar dashi zuwan farin cikin tashi juyawa yayi yai facing fuskarta yana fura fuska  a hankali itako ta rufe idan ta sai farin ciki takeyi hannu yasaka yana shafa gefen fuskar ta, sannan yafara kiss dinta itama shafa bayan shi takeyi tana kiss haka sukaita yan wasan ni, rike mata hannu yayi yafara magana "Umman Ariff mekika shafa haka? Murmushi yayi sannan tace "Rabin raina ba komai, bane da ya wuce kaunar ka, lumshe ido yayi sannan ya dagata ya zaunar da ita a gefen gado yace mata"kice uwar gida kuma ran gida inbake ba gida Umman Ameer me zai hana ki kara taimaka wannan jajirtaccen angon kanwan nan taki Nainah wajen adalci da kula da ragamar gida! Sunkuyar da kanta tayi a saman kirjin shi a hankali, tace"shikenan angon gimbiya Zubaina mijin gimbiya Safiyyah uban ya'yan gimbiya Asma'u insha Allahu zaka sameni a cikin kulawa ta musamman da daukar gabata a kowane fanni da kasani ina tareda kai mijina, ina kaunar ka Abban Alim da Ayyan Allah ya raya maka zuriar ka mijina wani irin dadi yaji ya rungume matar shi yana kara jin sonta a cikin zuciyar shi, sannan ya saketa a hankali kama hannun shi tayi sai kallan ta yakeyi zaunar dashi tayi bakin gado tana shafa mashi mai harta gama ta fiddo mashi kaya ta tayashi shirywa ta feshe kayan ra da turare suka fito a tare ta sashen gimbiya Safiyyah sukaje harta gama kintsawa murmushi sukai mata shiga sukayi ciki ya yi mata kiss a goshi sannan ya rada mata a kunne ya baby na suke kina kulaman dasu ko? gyada mashi kai tayi, riko hannun ta yayi suka fita baki dayan su zuwa sashen gimbiya Zubaina can zasuci abincin, can gimbiya Asma'u tasaka aka kaishi, suna zuwa suka nufi wajen dining jamasu  kujera yayi suka zauna ya shiga dakin gimbiya Zubaina tana shafa humra ya shiga rike hannun ta yayi da sauri ta juya sakar mata murmushi, yayi mai dauke da tsantsar kaunar ta a cikin zuciyar shi, Nainah ta ya ruwan zafi yau kingama sannu da kokari farin ciki na abin alfaharina ina kaunar ki Nainah......

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 04, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SADAUKIN BURHAAN CIGABAN IZZAH KO MULKIWhere stories live. Discover now