5&10

40 3 0
                                    

⚔️SADAUKIN BURHAAN ⚔️ _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_

A Kingdom Story👑

    *NA*
*Jameelah Jameey*
 
*Ya'r mutan kankia ce❣️*

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOC*

'''kungiya d'aya tamkar da dubu.🤙'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

*Marubuciyar👇*
*NANA JAWAHEER*
*GIMBIYA HAKIMA*
*IZZAH KO MULKI*
*SANADIN LINK*
*A GIDAN HAYA*
        
              And know

*SADAUKIN BURHAAN*_(daukar fansa cigaban Izzah ko mulki)_
             

*BISSIMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

  naira #300kacal zan_ _baku shi yan VIP kuma naira #600,duk mai bukata yaima wa'annan numbobin magana_ _07034464517 ko 08160508316_

_Free Pages_

_Page 6 to 10_

A bangaren Shattemarh kuwa yakasa zaune yakasa tsaye addua kawai yakeyi duk duniya taimashi kunci zuwa yanzun har Asma'u tafara suma kamar mai iska haihuwa ta gagareta koda Mai gidan yace ya shigo ya duba halin da matar shi take ciki kin shiga dakin yayi saboda baisan yaga tsaraicin Asma'u yana bala'in kishin dan uwanshi Sadauki duk da mutanan basu san ba matar shi bace, matar gidan ce ta fita da gudu ta kira wata tsohuwar mata aikinta kenan karbar haihuwa duk wahalar ta Allah ya hore mata dubaru na haihuwa gari gari ake zuwa adauketa ta karbi haihuwa da sauri suka shigo da wani akwatin ta akabasu waje ita da Asma'u tajika magani ta bude bakinta ta zuba mata ta hade a wahale sannan ta shafa mata a fuska baki daya cikin Asma'u ya juya da karfi kamar zata mutu haka taji nan matar ta shafa mata wani amara aikuwa ko minti goma baaiba cikin ikon Allah haihuwa ta taho gadan gadan cikin ikon Allah da dausayin sa Asma'u ta sintilo kwakkyawan dan'ta mai kama da uban sa kwabo da kwabo, tana haihuwar sa ta suma bata san inda kanta yake ba, daman tun tana nakudar matar gidan ta dafa ruwan zafi amma baki dayan su hankalin su ya koma kan dan da ta haifa saboda tunda aka haifeshi baiyi kuka ba shiyasa hankalin tsohuwar nan ya tashi ta daga shi ta sadda kanshi kasa tana buga mashi kugu amma yayi shiru hakan yasa ta dibo wani magani ta jika ta siyaya mashi a baki kamar aikin sihiri sai a lokacin ya duka uban kuka take Shattemarh yayi sijjada ya godema Allah yasan Asma'u ta sauka lfy, ajishi gefe tayi sannn takoma kan Asma'u....itakuma matar gidan wadda wannan tsohuwar ta kira da zaliha ta debo ruwa ta wanke jaririn tas sannan takara tsarkake shi,sannan ta dauko kaya ta saka mashi takai ma Shattemarh shi tunda ya kalli yaron Shattemarh ke kukan farin ciki....itako Asma'u takai awa daya sannan ta dawo cikin hayyacin ta,  wannan tsohuwar da suke kira da inna ita taima Asma'u wanka da kanta ta gasata.........

Ba karamin farin ciki ya kama Shattemarh ba bayan la'asar inna tagama gyara Asma'u taba zaliha magunguna tace abata a kunu ko fira na sati biyu nan ta kira Shattemarh tagaya mashi dan da aka haifa jefa ya same shi tun yana cikin ciki dan gaskia da kyal zai rayu koda ya rayu zai sha wahala kafin in lafiyayye ne yasamu lfy, amma a dinga yi mashi wanka da wani garin magani ta basu godiya yaimata sannan ya bata kudi masu tsoka yaimata godiya mai tarin yawa duk abin nan ashe zaliha taji ba karamin tausayawa Asma'u taiba gata da karancin shekaru amma ta hadu ta iftila'in rayuwa danma Allah yasa rayayya ce da anrasata ba ta bata lokaci ba ta hadama Asma'u kunun kanwa, ta zuba mata maganin da inna ta bata ta matsamata saida ta shanye shi, cikin ikon Allah sadda za'ai mangariba ruwan nono yazo nan Zaliha ta gwada mata yanda zatayi feeding din jaririn ta, aiko ba laifi yana sha, lokacin Asma'u ta dauki dan'ta ba karamin son shine ke shigarta ba a lokaci daya sai kalln shi take koda batasan yaya Muhd dinta ba dayana yaro amma tasan suna kama da jaririn ta,ana gama isha'i Shattemarh ya shigo da Malan Audu sunan mai gidan kenan ya dauki dan yai mai addua sannan yai masu barka yaba Shattemarh jaririn, sai kallan dan yakeyi yana kara shiga cikin zuciyar shi, kallan ta yayi yace wane suna kika zabawa danki? Kallan shi tayi cike da mamaki"da'na fa kace karkaman ta yanzun baida uban da ya wuceka a duniya karka manta yaya Muhd yace baisan cikina balle dan nan, dan haka na mallakama ka wannan dan damn yace ya barmaka kyauta baiso!!! "Hmmm Asma'u kenan kinsan Sadauki bai cikin hayyacin shi komai zai iya aikatawa amma wlh duk duniya baida buri da ya wuce na wannan dan kuma yana son shi yana kaunar shi kune iyalin shi kuma farin cikin shi inasan dan uwa na kuma ina kaunar sa kamar ciki daya muka kwanta wlh Asma'u duk abinda zamuyi ma Sadauki dagani har Tafeedah bazamu biya shiba, duk cikin mu bamai mutun ci da kishin dan uwanshi kamar Sadauki shiyasa kikaga naba rayuwar shi mahimmanci kiyafe mashi lallai an cutar dake amma kisani bayin kanshi bane bake kadai ba duk wani makusancin shi anzalin ceshu dan haka wannan dan na Muhammad Abduljalaal Muhammad ne, dan haka me kike so a sama dan nan? "Shikenan yaya Shattemarh na fahimci ka, kuma nayafema yaya Muhd,kuma inasan a sama shi suna AHMAD....arazane Shattemarh ya kalleta,"meyasa bazaki sama shi sunan Mai Martaba ba? "Yaya Shattemarh ko shi kanshi abinda mahaifin shi zaiyi kenan ka canci haka kabada gudun muwa mai yawa daga rayuwata da wannan yaron haka da rayuwar Abba da Ammi harda Juwairiyyah dashi kanshi Sadauki dik kabada gaggarumar gudun muwa bamu da abinda zamu saka maka da shi ya wuce ince Allah yasaka maka da mafificin alkhairy yabar zumunci mai daurewa har abada "bakomai Asma'u ba abinda ban iyayi akan iyalan Sadauki Allah yarayama na shi cikin aminci....."Ameen ya Allah, nan yaima shi huduba yasa mashi sunan Ahmad kamar yanda ta bukata.....gashi Allah yaraya Ahmad bisa sunnar maaiki SAW,ke kuma Allah yakara maki lfy mai anfani, "Ameen yayana nagode sosai

SADAUKIN BURHAAN CIGABAN IZZAH KO MULKINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ